Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w00 8/1 pp. 24-29
  • ‘Wurin Masu Filako Hikima Take’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Wurin Masu Filako Hikima Take’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Bulus—‘Ma’aikaci’ Kuma ‘Wakili’
  • Filako a Ɗaukar Gatarmu
  • Gidiyon—“Auta” ne a Gidan Ubansa
  • Nuna Filako da Hikima
  • Yesu—Misali Mafi Girma na Filako
  • Ka Yi Koyi da Misalin Filako na Yesu
  • Shin Kasancewa da Tawali’u Tsohon Yayi Ne?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Za Ka Iya Zama Mai Tawali’u Sa’ad da Kake Fuskantar Jaraba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Dattawa, Ku Yi Koyi da Gideyon
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Ka Bauta wa Allah Cikin Saukin Kai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
w00 8/1 pp. 24-29

‘Wurin Masu Filako Hikima Take’

“Me ne Ubangiji ya ke biɗa gareka kuma, . . . ka yi tafiya da [filako] tare da Allahnka?”—MIKAH 6:8.

1, 2. Menene filako, kuma ta yaya ya bambanta daga girman kai?

SANNANEN manzo ya ƙi ya jawo hankali ga kansa. Wani alƙali Ba’isra’ile ya kira kansa mafi ƙanƙanta a gidan ubansa. Mutum mafi girma da ya taɓa rayuwa ya yarda cewa ikonsa yana da iyaka. Kowanne cikin mutanen nan ya nuna filako.

2 Filako kishiyar girman kai ne. Mutum mai filako ba ya ganin ya iya wani abu sosai kuma ba ya ɗaukan kansa cewa ra’ayinsa ne ya fi kyau. Maimakon fahariya, kumburi, ko kuma dogon buri, mai filako ko da yaushe ya san iyakarsa. Shi ya sa yake daraja ra’ayoyin wasu kuma yake yin la’akari da su da kuma yadda suke ji.

3. A wace hanya ce “wurin masu filako hikima take”?

3 Da dalili mai kyau kuwa Littafi Mai-Tsarki ya ce: “Wurin masu filako hikima take.” (Misalai 11:2, NW ) Mai filako yana da hikima domin yana bin tafarkin da Allah ya gamsu da shi, yana guje wa ruhun girman kai da ke kaiwa ga kunya. (Misalai 8:13; 1 Bitrus 5:5) Bayin Allah da yawa sun tabbatar da hikimar zama da filako ta wurin yanayin rayuwansu. Bari mu bincika misalai uku da aka ambata a izifi na farko.

Bulus—‘Ma’aikaci’ Kuma ‘Wakili’

4. Wace gata ta musamman ce Bulus ya more?

4 Bulus sananne ne tsakanin Kiristoci na farko, kuma an fahimci hakan. A cikin hidimarsa, ya yi tafiye-tafiye na dubban kilomitoci a cikin teku da kuma a ƙasa, kuma ya kafa ikklisiyoyi da yawa. Ƙari ga haka, Jehovah ya albarkaci Bulus da ru’uyoyi da kyautar iya furta wasu harsuna. (1 Korinthiyawa 14:18; 2 Korinthiyawa 12:1-5) Ya kuma hure Bulus ya rubuta wasiƙu 14 da yanzu sashen Nassosin Kirista na Helenanci ne. Hakika, za a iya cewa ayyukan Bulus sun wuce na sauran manzannin.—1 Korinthiyawa 15:10.

5. Ta yaya Bulus ya nuna cewa shi mai filako ne?

5 Tun da yake Bulus yana kan gaba cikin ayyukan Kirista, wasu za su yi tsammanin yana nuna kansa ga kowa, har ma ya busa kakaki wa kansa game da ikonsa. Amma ba haka ba ne, Bulus mai filako ne. Ya kira kansa “autan manzanni,” ya daɗa cewa: “Ban isa a ce da ni manzo ba, da shi ke na tsananta ikklisiya ta Allah.” (1 Korinthiyawa 15:9) Da yake matsanancin Kiristoci ne dā, Bulus bai manta cewa ta wurin alheri ne kawai ya samu dangantaka da Allah ba, har kuma ya more gatar hidima ta musamman. (Yohanna 6:44; Afisawa 2:8) Shi ya sa Bulus bai ji cewa abubuwa da yawa da ya cim ma cikin hidima za su sa ya fi wasu ba.—1 Korinthiyawa 9:16.

6. Yaya Bulus ya nuna filako a sha’aninsa da Korantiyawa?

6 Filakon Bulus ya bayyana musamman a yadda ya bi da Korantiyawa. Hakika, wasu cikinsu suna ƙaunar waɗanda suke ganin sanannun masu kula ne, waɗannan sun haɗa da Appolos, Kefas, da Bulus kansa. (1 Korinthiyawa 1:11-15) Amma Bulus bai nemi yabo daga Korantiyawa ko kuma ya yi abu domin ya burge su ba. Yayin da ya ziyarce su, ba “da gwanintar zance [ya] zo ba ko da hikima.” Maimako, Bulus ya ce game da kansa da abokansa: “Mu fa, sai a yi lissafinmu hakanan, ma’aikatan Kristi ne, wakilai na asiran Allah kuma.”a—1 Korinthiyawa 2:1-5; 4:1.

7. Yaya Bulus ya nuna filako har a lokacin da yake ba da gargaɗi?

7 Bulus ya kuma nuna filako a lokacin da yake ba da gargaɗi mai ƙarfi da kuma ja-gora. Ya roƙi ’yan’uwansa Kiristoci “bisa ga jiyejiyenƙai na Allah” kuma “sabili da ƙauna” maimakon ƙarfin ikonsa na manzonci. (Romawa 12:1, 2; Filimon 8, 9) Me ya sa Bulus ya yi wannan? Domin da gaske ya ɗauki kansa ‘abokin aiki’ na ’yan’uwansa, ba ‘mai sarautar bangaskiyarsu ba.’ (2 Korinthiyawa 1:24) Babu shakka domin filakon Bulus ne ya sa ya zama ƙaunatacce musamman ga ikklisiyoyin Kirista na ƙarni na farko.—Ayukan Manzanni 20:36-38.

Filako a Ɗaukar Gatarmu

8, 9. (a) Me ya sa za mu kasance da filako a yadda muke ɗaukan kanmu? (b) Ta yaya waɗanda suke da wasu nawaya za su nuna filako?

8 Bulus ya kafa misali mai kyau wa Kiristoci a yau. Ko yaya yawan nawayoyin da aka ba mu, kada mu ɗauki kanmu mun fi wasu. Bulus ya rubuta: “Gama idan mutum ya zaci kansa wani abu ne, shi kuwa ba kome ba ne, ruɗin kansa ya ke yi.” (Galatiyawa 6:3) Me ya sa? Domin “dukan mutane sun yi zunubi, sun kasa kuma ga darajar Allah.” (Romawa 3:23; 5:12) I, kada mu manta cewa dukanmu mun gaji zunubi da mutuwa daga Adamu. Gata ta musamman ba ta ’yantar da mu daga yanayinmu na zunubi ba. (Mai-Wa’azi 9:2) Yadda yake da gaske a zancen Bulus, ta wurin alheri ne kawai mutane za su iya samun dangantaka da Allah, har ma su bauta masa ta samun wasu gata.—Romawa 3:12, 24.

9 Fahimtar wannan, mutum mai filako ba zai yi muguwar sha’awar gatarsa ba ko ya yi fahariya don abubuwa da ya cim ma. (1 Korinthiyawa 4:7) Yayin da yake ba da gargaɗi ko yin ja-gora, zai yi haka kamar abokin aiki—ba kamar ubangida ba. Ba daidai ba ne wani da ya shahara a wani abu sosai ya nemi yabo daga ’yan’uwa ko kuma ya jawo hankalin masu bi ga kansa. (Misalai 25:27; Matta 6:2-4) Yabo da ya cancanta daga wajen wasu yake fitowa—kuma zai zo ba tare da an nema ba. Idan muka samu haka, bai kamata mu ƙyale ya sa mu ɗaukaka kanmu fiye da yadda ya kamata ba.—Misalai 27:2; Romawa 12:3.

10. Ka bayyana yadda wasu da ake ganinsu kamar tsiyayyu ne suna iya zama “madawata cikin bangaskiya.”

10 Idan aka ba mu wata nawaya, filako zai taimake mu guje jawo hankali ga kanmu, muna nuna cewa ikklisiya tana ci gaba domin ƙoƙarce-ƙoƙarce da kuma iyawarmu ne kawai. Alal misali, wataƙila mun iya koyarwa sosai. (Afisawa 4:11, 12) Amma, idan muna da filako za mu fahimci cewa yawancin darussa da ake koya a taro ba daga dakalin magana ake koya ba. Ba ka farin ciki idan ka ga, alal misali gwauruwa da take zuwa Majami’ar Mulki babu fasawa da yaranta a ƙarƙashin ja-gorarta? Ko kuma wani da yake baƙin ciki da ke zuwa taro babu fasawa duk da yadda yake ji kullum cewa bai cancanta ba? Ko kuma matashi da yake ci gaba a ruhaniya duk da munanan tasiri na makaranta da kuma na wasu wurare? (Zabura 84:10) Wataƙila waɗannan mutane ba sanannu ne sosai ba. Yawancin gwajin aminci da suke fuskanta, mutane kalilan ne suke sani. Duk da haka, ƙila ‘mawadata ne cikin bangaskiya’ daidai da waɗanda sanannu ne. (Yaƙub 2:5) Ballantana ma, samun tagomashin Jehovah a ƙarshe ta wurin aminci ne.—Matta 10:22; 1 Korinthiyawa 4:2.

Gidiyon—“Auta” ne a Gidan Ubansa

11. A wace hanya ce Gidiyon ya nuna filako wajen magana da mala’ikan Allah?

11 Gidiyon, ƙaƙƙarfan matashi na ƙabilar Manassa, ya rayu ne a lokacin bala’i cikin tarihin Isra’ila. Mutanen Allah sun wahala na shekara bakwai domin zaluncin Madanayawa. Amma, yanzu lokaci ya kai da Jehovah zai ceci mutanensa. Shi ya sa, mala’ika ya bayyana wa Gidiyon, ya ce: “Ubangiji yana tare da kai, ya jarumi.” Gidiyon mai filako ne, saboda haka bai nuna muguwar sha’awa ga yabon nan ba. Maimako, cikin ladabi ya ce wa mala’ikan: “Ya ubangijina, idan Ubangiji yana tare da mu, don menene dukan wannan masifa ta same mu?” Mala’ikan ya fayyace wa Gidiyon al’amura kuma ya gaya masa: “Ka ceci Isra’ila daga hannun Madayanawa.” Yaya Gidiyon ya amsa? Maimakon kasance da muguwar sha’awa a kan aiki da aka ba shi don ya zama sanannen jarumin ƙasar, Gidiyon ya amsa: “Ubangiji, da me zan ceci Isra’ila? Ga shi, dangina mafi-ƙanƙanci ne cikin Manassa, ni ma auta ne cikin gidan ubana.” Lallai wannan filako ne!—Alƙalawa 6:11-15.

12. Yaya Gidiyon ya nuna hikima a cika aikinsa?

12 Kafin ya aika Gidiyon zuwa yaƙi, Jehovah ya gwada shi. Ta yaya? An ce Gidiyon ya farfasa bagadin Ba’al kuma ya tsare gumakan da ke kusa da shi. Wannan aikin yana bukatar ƙarfin zuciya, amma Gidiyon ya nuna filako da kuma hikima a hanyar da ya cika wannan aikin. Maimakon yin haka a fili don kowa ya gan shi, Gidiyon ya je da dare lokacin da kusan babu wanda zai gan shi. Bugu da ƙari, Gidiyon ya yi aikinsa da hikima. Ya je da bayi goma—ƙila domin wasu su yi gadi yayin da sauran kuma za su taimaka masa halaka bagadin har da gumakan.b Yadda yake dai, tare da albarkar Jehovah, Gidiyon ya cika aikinsa, daga baya kuma Allah ya yi amfani da shi ya ’yantar da Isra’ilawa daga hannun Madayanawa.—Alƙalawa 6:25-27.

Nuna Filako da Hikima

13, 14. (a) Ta yaya za mu nuna filako yayin da aka ba mu wata gatar hidima? (b) Ta yaya Ɗan’uwa A. H. Macmillan ya kafa misali mai kyau a nuna filako?

13 Muna da abin da za mu koya da yawa daga filakon Gidiyon. Alal misali, yaya muke ji yayin da mun sami wata gatar hidima? Da farko muna tunanin girman ko darajar da take tafe da ita? Ko kuwa cikin filako muna addu’a cewa ko za mu iya cika abin da aikin yake bukata? Ɗan’uwa A. H. Macmillan, wanda ya gama hidimarsa ta duniya a shekara ta 1966, ya kafa misali a zancen nan. C. T. Russell, shugaban Watch Tower Society na farko, ya taɓa tambayar Ɗan’uwa Macmillan wanene yake tunanin zai iya kula da aikin idan ba ya nan. A cikin zancensu, Ɗan’uwa Macmillan bai ɗaukaka kansa ba, ko da zai iya zama da sauƙi ya yi haka. A ƙarshe, Ɗan’uwa Russell ya ce Ɗan’uwa Macmillan ya karɓi aikin. “Na tsaya a wajen ban iya cewa uffan ba,” Macmillan ya rubuta da shekaru suka shige. “Na yi tunaninsa sosai, sau da yawa, na yi addu’a game da shi kafin daga baya na gaya masa cewa zan yi iyakar ƙoƙari na in taimaka masa.”

14 Bai daɗe ba, sai Ɗan’uwa Russell ya rasu, babu wanda zai shugabanci Watch Tower Society kuma tukuna. Tun da yake Ɗan’uwa Macmillan ne yake kula da aikin lokacin da Ɗan’uwa Russell ya yi tafiyarsa ta wa’azi na ƙarshe, wani ɗan’uwa ya ce: “Mac, ai kai ka ke da zarafin ɗaukan matsayin nan. Kai ne wakilin Ɗan’uwa Russell na musamman kafin ya tafi, ya kuma gaya wa dukanmu mu yi abin da ka ce. To, ga shi ya tafi kuwa bai sake dawowa ba. Kamar dai kai ne za ka ci gaba da shugabanci.” Ɗan’uwa Macmillan ya ce: “Ɗan’uwa, ba haka ya kamata a duba zancen ba ai. Wannan aikin Ubangiji ne kuma duk matsayin da mutum ya samu cikin ƙungiyar Ubangiji shi ne abin da Ubangiji ya ga ya dace ya ba shi; kuma na tabbata ba ni ba ne na dace da aikin nan ba.” Sai Ɗan’uwa Macmillan ya gabatar da wani ga wannan matsayin. Kamar Gidiyon, ya ɗauki kansa da filako—hali da ya kamata mu kasance da shi ke nan.

15. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya nuna fahimi yayin da muke wa’azi ga wasu?

15 Ya kamata mu ma mu kasance da filako a yadda muke cika aikin da aka ba mu. Gidiyon yana da hikima, da ya yi ƙoƙarin kada ya iza fushin masu hamayya babu gaira. Hakanan ma, cikin aikinmu na wa’azi, ya kamata mu kasance da filako da kuma hikima a yadda muke yi wa wasu magana. Gaskiya, muna cikin yaƙi na ruhaniya da za mu “rushe wurare masu-ƙarfi” da “zace-zace.” (2 Korinthiyawa 10:4, 5) Amma kada mu raina wasu ko kuma mu ba su dalilin da za su ga laifin saƙonmu. Maimako, ya kamata mu daraja ra’ayoyinsu, mu ambata abin da mu da su muka gaskata, sai kuma mu ci gaba da sashen saƙonmu mai kyau.—Ayukan Manzanni 22:1-3; 1 Korinthiyawa 9:22; Ru’ya ta Yohanna 21:4.

Yesu—Misali Mafi Girma na Filako

16. Yaya Yesu ya nuna cewa yana da filako?

16 Misalin filako mafi kyau na Yesu Kristi ne.c Duk da yadda yake kurkusa da Ubansa, Yesu ya gane cewa wasu al’amura sun wuce ikon da yake da shi. (Yohanna 1:14) Alal misali, lokacin da mamar Yaƙub da Yohanna ta biɗa cewa ’ya’yanta biyu su zauna a gefen Yesu cikin mulkinsa, Yesu ya ce: “Zama ga hannun damana, da hannun haguna, ba nawa ba ne da zan bayar.” (Matta 20:20-23) A wani lokaci kuma Yesu ya ce a fili: “Ni bisa ga kaina ban iya kome ba . . . ba na bin nufin kaina ba, amma nufin wanda ya aiko ni.”—Yohanna 5:30; 14:28; Filibbiyawa 2:5, 6.

17. Yaya Yesu ya nuna filako a yin sha’ani da wasu?

17 Yesu ya fi mutane ajizai a kowace hanya, kuma yana da ikon da babu wanda ya fi sa da ya samu daga wurin Ubansa, Jehovah. Duk da haka, Yesu ya kasance da filako a yin sha’ani da mabiyansa. Bai dulmayar su da nuna iliminsa mai yawa ba. Ya lura kuma kula da bukatunsu na mutane sosai. (Matta 15:32; 26:40, 41; Markus 6:31) Saboda haka, ko da Yesu kamili ne, bai biɗi kamilta ba. Bai taɓa biɗan almajiransa su yi abin da ba za su iya yi ba, kuma bai taɓa ɗaura musu abin da ba za su iya ɗauka ba. (Yohanna 16:12) Abin da ya sa ke nan mutane da yawa sun iske shi mai ba da wartsakewa!—Matta 11:29.

Ka Yi Koyi da Misalin Filako na Yesu

18, 19. Ta yaya za mu iya yin koyi da Yesu a (a) yadda muke ganin kanmu, da kuma (b) yadda muke bi da wasu?

18 Idan mutum mafi girma da ya taɓa rayuwa ya nuna filako, ai muna bukatar mu nuna haka sosai. Mutane ajizai sau da yawa ba sa son su yarda cewa ba su da iko na duka duka ba. Amma, a yin koyi da Yesu, Kiristoci suna fama su kasance masu filako. Ba sa fahariyar da zai hana su su ba wasu da sun cancanta nawaya ba; ba kuwa suna girman kai ko ƙin yarda su bi ja-goranci daga waɗanda suke da iko ba. Nuna ruhun haɗin kai, suna sa abubuwa su tafi “da hankali bisa ga ƙa’ida kuma.”—1 Korinthiyawa 14:40.

19 Filako kuma zai taimake mu mu biɗi abin da ke daidai daga wasu kuma lura da bukatunsu. (Filibbiyawa 4:5) Wataƙila muna da fasaha da abubuwan da wasu ba su da shi. Duk da haka, idan muna da filako, ba za mu zaci cewa wasu kullum su yi yadda muke so ba. Da sanin cewa kowanne mutum yana da iyakarsa, za mu ƙyale filako ya sa mu yafe wa wasu laifinsu. Bitrus ya rubuta: “Gaba da kome kuma ku zama da ƙauna mai-huruwa zuwa ga junanku; gama ƙauna tana suturtadda tulin zunubai.”—1 Bitrus 4:8.

20. Me za mu yi don mu sha kan wata alamar rashin filako?

20 Kamar yadda mun riga mun koya, lallai hikima wajen masu filako take. Amma idan ka ga kana da alamar rashin filako ko girman kai fa? Kada ka yi sanyin gwiwa. Maimako, ka bi misalin Dauda da ya yi addu’a haka: “Daga wurin masu-girman kai; Kada ka bari su yi iko da ni.” (Zabura 19:13) Ta wurin yin koyi da mutane kamar su Bulus, Gidiyon, da—mafi girma—Yesu Kristi, mu da kanmu za mu ga gaskiyar kalmomin nan: ‘Hikima wajen masu filako take.’—Misalai 11:2.

[Hasiya]

a Kalmar Helenancin nan da aka juya “ma’aikata” yana iya nufin bawa wanda yake riƙe labule a babban jirgin ruwa. Ana iya ba wa “wakilai” ƙarin nawaya, wataƙila na kula da wani babban gida. Duk da haka, wakili da bawan duk ɗaya ne a gaban iyayengijinsu.

b Kada a aza cewa hikima da hankali da Gidiyon ya nuna alama ce ta tsoro. Akasarin haka, Ibraniyawa 11:32-38 ya tabbatar da gaba gaɗinsa, da ya nuna Gidiyon cikin waɗanda aka “ƙarfafa su” da waɗanda “suka zama ƙarfafa cikin yaƙi.”

c Tun da filako yana nufin mutum ya san iyakacin abin zai iya yi ne, ba za a iya cewa Jehovah yana da filako ba. Amma, mai tawali’u ne.—Zabura 18:35.

Ka Tuna?

• Menene filako?

• Ta yaya za mu iya yin koyi da filako na Bulus?

• Menene za mu iya koya game da filako daga misalin Gidiyon?

• Ta yaya Yesu ya kafa misali mafi kyau na filako?

[Hoto a shafi na 25]

Filakon Bulus ya jawo shi kusa da ’yan’uwansa Kirista

[Hoto a shafi na 27]

Gidiyon ya nuna fahimi a cika nufin Allah

[Hoto a shafi na 28]

Yesu, Ɗan Allah, ya nuna filako a dukan abin da ya yi

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba