Ka Yi Farin Ciki Tare Da Allah Mai Farin Ciki
“A ƙarewa, ’yan’uwa, ku zauna lafiya. . . . Allah kuwa na ƙauna da na salama za ya zauna tare da ku.”—2 KORINTHIYAWA 13:11.
1, 2. (a) Me ya sa mutane da yawa ba sa farin ciki a rayuwa? (b) Menene farin ciki, kuma ta yaya za mu iya samunsa?
A CIKIN kwanakin nan masu ban tsoro, mutane da yawa ba su ga dalilin farin ciki ba. Yayin da bala’i ya faɗo musu ko kuma wani da suke ƙauna, za su iya ji yadda Ayuba na dā ya ji, da ya ce: “Mutum, haihuwar mace kwanakinsa kaɗanna ne, cike da wahala kuma.” (Ayuba 14:1) Ba a kāre Kiristoci ba daga wahala da wuya na waɗannan “miyagun zamanu” ba, shi ya sa ba abin mamaki ba ne a ga bayin Jehovah masu aminci sukan yi sanyin gwiwa.—2 Timothawus 3:1.
2 Duk da haka, Kiristoci za su iya yin farin ciki ko a ƙarƙashin gwaji ma. (Ayukan Manzanni 5:40, 41) Don ka fahimci yadda wannan zai yiwu, da farko ka yi la’akari da abin da farin ciki yake nufi. An ba da ma’anar farin ciki cewa “jiye-jiyen da wani zato ko tsammani ta iza domin wani abu mai kyau.”a Saboda haka, idan muka ɗauki lokaci muka binciki albarkarmu na yanzu sa’an nan kuma muna tunanin farin ciki da ke zuwa a nan gaba dominmu a sabuwar duniya ta Allah, za mu yi farin ciki.
3. A wane azanci ne za a iya cewa aƙalla kowa yana da dalilan yin farin ciki?
3 Kowa yana da wata albarka da zai yi godiya dominta. Shugaban iyali yana iya hasarar aikinsa. Daidai ne, ya damu. Yana son ya yi tanadi wa waɗanda yake ƙauna. Duk da haka, idan yana da ƙarfi da kuma ƙoshin lafiya, ya yi godiya domin wannan. Idan ya sami aikin yi zai yi aiki tuƙuru. A wata sassa kuma, mace Kirista wataƙila ta kamu farat ɗaya da mugun ciwo da ke raunanata. Duk da haka, tana iya godiya domin toƙarawa da abokai da waɗanda suke cikin iyali suke yi cikin ƙauna domin ta fuskanci ciwon cikin daraja da ƙarfin zuciya. Dukan Kiristoci kuma, ko da wane irin yanayi suke ciki, za su iya yin farin ciki domin gatar sanin Jehovah, ‘Allah mai farin ciki,’ da kuma Yesu Kristi, ‘Mai Iko makaɗaici mai farin ciki.’ (1 Timothawus 1:11; 6:15) Hakika, Jehovah Allah da Yesu Kristi suna farin ciki sosai. Sun riƙe farin cikinsu duk da cewa yanayin duniya ya bambanta ƙwarai daga yadda Jehovah ya nufe sa a farko. Misalinsu zai iya taimakonmu sosai game da yadda za mu riƙe farin cikinmu.
Ba Su Taɓa Hasarar Farin Cikinsu Ba
4, 5. (a) Yaya Jehovah ya ji yayin da mutane na farko suka yi tawaye? (b) A wace hanya ce Jehovah yake kasancewa da hali mai kyau wajen mutane?
4 A gonar Adnin, Adamu da Hawa’u sun more cikakkiyar lafiyar jiki da kuma kamilcaccen azantai. Suna da aiki mai kyau da za su yi a cikin yanayi mai kyau don yin aikin. Mafi kyau duka, suna da gatar yin magana da Jehovah kullum. Nufin Allah ne cewa su more rayuwa mai farin ciki a nan gaba. Amma, iyayenmu na farko ba su gamsu ba sam da dukan waɗannan kyauta; suka saci ’ya’yan itace daga “itace na sanin nagarta da mugunta.” Wannan halin rashin biyayya ne ya kafa tushen dukan baƙin ciki da muke gani a yau, mu ’ya’yansu.—Farawa 2:15-17; 3:6; Romawa 5:12.
5 Amma, Jehovah bai ƙyale butulcin Adamu da Hawa’u ya hana shi farin ciki ba. Yana da gaba gaɗi cewa aƙalla wasu cikin ’ya’yansu za su so su bauta masa. Yana da gaba gaɗi sosai har da, kafin ma Adamu da Hawa’u su haifi ɗansu na fari ya sanar da nufinsa na son ya fanshi masu biyayya daga zuriyarsu! (Farawa 1:31; 3:15) A cikin ƙarnuka da suka biyo baya, yawancin mutane sun bi sawun Adamu da Hawa’u, amma Jehovah bai juya bayansa ba ga iyalin bil adam saboda bazuwar rashin biyayya. Maimakon haka, ya kafa ido a kan maza da mata da suke ‘faranta masa rai,’ waɗanda suke ƙoƙari na musamman don su faranta masa rai domin suna ƙaunarsa.—Misalai 27:11; Ibraniyawa 6:10.
6, 7. Waɗanne abubuwa suka taimake Yesu ya kasance da farin ciki?
6 Yesu kuma fa—yaya ya riƙe farin cikinsa? Shi babbar halitta ce na ruhu a sama, Yesu yana da zarafin ya bincika ayyukan maza da mata a duniya. A bayyane rashin cikarsu yake, duk da haka Yesu ya ƙaunace su. (Misalai 8:31) Daga baya, lokacin da ya zo duniya kuma ‘ya zauna a wurin’ mutane, ra’ayinsa game da mutane bai canja ba. (Yohanna 1:14) Menene ya taimake kamilcaccen Ɗan Allah da ya riƙe ra’ayi mai kyau haka game da iyalin ’yan Adam masu zunubi?
7 Da farko, Yesu ya daidaita a abin da yake tsammani wa kansa da kuma ga wasu. Ya san cewa ba zai juya duniya ba. (Matta 10:32-39) Saboda haka, yana farin ciki idan ko mutum ɗaya ne ya yi na’am da saƙon Mulkin. Ko da yake ayyuka da kuma halayen almajiransa wasu lokatai ba sa gamsarwa, amma Yesu ya sani cewa a zuciyarsu da gaske suna son yin nufin Allah, domin haka yana ƙaunarsu. (Luka 9:46; 22:24, 28-32, 60-62) Musamman, a cikin addu’a ga Ubansa na sama, Yesu ya taƙaita tafarki mai kyau da almajiransa suka bi har lokacin: “Sun kuwa kiyaye maganarka.”—Yohanna 17:6.
8. Ka ambata wasu hanyoyi da za mu iya bin misalin Jehovah da Yesu yayin da ya zo ga batun riƙe farin cikinmu.
8 Babu shakka, dukanmu za mu amfana daga bincika a hankali misalin da Jehovah Allah da Kristi Yesu suka nuna a batun nan. Za mu iya bin misalin Jehovah sosai, ƙila ta ƙin mu damu ainu yayin da abubuwa ba su faru yadda muke tsammani ba? Za mu iya bin sawun Yesu sosai ta wurin kasancewa da ra’ayi mai kyau game da yanayinmu na yanzu, da kasancewa da daidaita game da abubuwan da muke tsammani wa kanmu da kuma wasu? Bari mu ga yadda za a iya yin amfani da waɗannan ƙa’idodi a hali mai kyau da ke da muhimmanci ga zukatan Kiristoci masu himma a ko’ina—hidimar fage.
Kasancewa da Ra’ayi Mai Kyau Game da Hidimar Fage
9. Ta yaya Irmiya ya sake samun farin cikinsa, ta yaya misalinsa zai iya taimaka mana?
9 Jehovah yana son mu yi farin ciki cikin hidimarsa. Bai kamata farin cikinmu ya dangana ga sakamakon da muke samu ba. (Luka 10:17, 20) Annabi Irmiya ya yi wa’azi shekaru da yawa a yanki da ba ya ba da ’ya’ya. Yayin da ya mai da hankalinsa ga halin mutanen, ya yi rashin farin cikinsa. (Irmiya 20:8) Amma yayin da ya yi bimbini a kan kyan saƙon, ya sake samun farin cikinsa. Irmiya ya ce wa Jehovah: “Aka iske maganarka, na kuwa ci su: zantattukanka sun zama mini murna da farinciki na zuciyata: gama an kira ni da sunanka, ya Ubangiji.” (Irmiya 15:16) Hakika, Irmiya ya yi farin ciki da gatarsa na yin wa’azin maganar Allah. Mu ma za mu iya yin haka.
10. Ta yaya za mu riƙe farin cikinmu cikin hidima ko idan yankinmu a yanzu ba ta ba da amfani?
10 Ko idan yawancin mutane sun ƙi su yi na’am da bisharar, muna da dalili mai girma na yin farin ciki da muke shaƙu cikin hidimar fage. Ka tuna cewa Jehovah ya yi gaba gaɗi cewa zai sami wasu mutane da za su motsa su bauta masa. Kamar Jehovah, ya kamata kada mu yi rashin bege cewa wasu za su fahimci batun nan kuma su amshi saƙon Mulkin. Kada mu manta cewa yanayin mutane yakan canja. Yayin da muka fuskanci wasu rashi ko kuma tarzoma, ko mutane da suke da kome ma za su fara tunani sosai game da ma’anar rai. Za ka kasance a wurin domin ka taimaka wa irin mutumin nan yayin da yake ‘tunanin bukatarsa ta ruhaniya’? (Matta 5:3) Hakika, wataƙila wani a yankinka zai so ya ji bisharar wata rana da za ka sake zuwa wurinsa!
11, 12. Menene ya faru a wani gari, kuma menene za mu iya koya daga ciki?
11 Yanayin yankinmu zai iya canjawa. Ga misali. A wani ƙaramin gari, da akwai wasu rukunin matasa masu aure tare da yaransu. Yayin da Shaidun Jehovah sun kai ƙofarsu, sai a ba su amsa iri ɗaya, “Ba ma so!” Idan wani ya nuna yana son saƙon Mulkin, maƙwabtan babu ɓata lokaci za su tabbata mutumin ba zai ƙara ganin Shaidun ba. Lalle kam, yin wa’azi a wajen kalubale ne. Duk da haka, Shaidun ba su yi sanyi ba; sun ci gaba da yin wa’azi. Da wane sakamako?
12 A kwana a tashi, yara da yawa da suke garin suka yi girma kuma yi aure, suka yi nasu iyalin a wajen. Da suka gane cewa hanyar rayuwarsu ba ta kawo musu farin ciki ba, wasu cikin waɗannan matasan suka fara neman gaskiya. Sun same ta yayin da suka yi na’am da bisharar da Shaidun suka sanar. Saboda haka, bayan shekaru da yawa ne, ƙaramar ikilisiyar ta fara girma. Ka yi tunanin farin cikin masu shelar Mulkin da ba su yi sanyi ba! Bari naciya a yaɗa saƙon Mulki mai darajar nan ta kawo mana farin ciki mu ma!
’Yan’uwa Masu Bi Za Su Toƙara Maka
13. Ga wanene za mu iya juyawa yayin da muke sanyin gwiwa?
13 Yayin da ka fuskanci matsi mai yawa ko kuma masifa ta same ka, ina za ka juya don ƙarfafa? Miliyoyin bayin Jehovah da suka keɓe kai sukan juya da farko ga Jehovah cikin addu’a, sai kuma ga ’yan’uwansu Kiristoci. Yayin da yake duniya, Yesu kansa ya daraja toƙarawar almajiransa. A dare kafin mutuwarsa, ya yi magana game da su cewa ‘waɗanda sun lizimce ni a cikin jarabtuwana.’ (Luka 22:28) Hakika, waɗannan almajiran ba kamiltattu ba ne, amma amincinsu ya ta’azantar da Ɗan Allah. Mu ma za mu iya samun ƙarfi daga abokai da muke bauta tare da su.
14, 15. Menene ya taimaki wata mata da mijinta su jimre wa mutuwar ɗansu, me muka koya daga abin da ya faru da su?
14 Wata mata da mijinta Kirista da sunansu Michel da Diane suka ga yadda toƙarawa daga ’yan’uwa take da amfani sosai. Ɗansu Jonathan, shekararsa 20, Kirista ne lafiyayye cike da zato sosai, aka gwada shi aka ga yana da ƙari a ƙwaƙwalwa. Likitoci sun jarumtaka wajen neman su cece shi, amma yanayin jikin Jonathan ya daɗa muni har ya kai wani yamma da ya mutu. Michel da Diane sun gigita. Sun sani cewa Taron Hidima na ranar, an kusan a gama. Duk da haka, domin suna son su sami ta’aziyya, suka gaya wa dattijon da yake tare da su ya raka su zuwa Majami’ar Mulki. Suna kaiwa ikilisiyar ana sanar da mutuwar Jonathan. Bayan taron, ’yan’uwa suka kewaya iyayen nan da suke kuka, suka rungume su kuma suka yi masu ta’aziyya. Diane ta tuna: “Muka isa majami’ar raunanu, amma mun sami ta’aziyya sosai daga ’yan’uwa—sun ƙarfafa mu! Ko da yake ba su iya cire azabarmu ba, amma sun taimaka mana mu jure da shi!”—Romawa 1:11, 12; 1 Korinthiyawa 12:21-26.
15 Wahala ta sa Michel da Diane suka matsa kurkusa da ’yan’uwansu. Ta kuma sa su matso kurkusa da juna. Michel ya ce: “Na koyi na ƙaunaci ƙaunatacciyar matata sosai. A lokacin sanyin gwiwa haka, mukan yi taɗi da juna a kan zancen gaskiyar Littafi Mai Tsarki da kuma yadda Jehovah yake kiyaye mu.” Diane ta daɗa: “Yanzu begen Mulkin yana da muhimmanci a gareni fiye da dā.”
16. Me ya sa yake da muhimmanci mu ɗauki mataki na gaya wa ’yan’uwanmu bukatunmu?
16 Gaskiya ne, ’yan’uwanmu Kiristoci suna mana “ta’aziyya” cikin lokatai masu wuya kuma suna taimakonmu mu riƙe farin cikinmu. (Kolossiyawa 4:11) Babu shakka, ba su san zuciyarmu ba. Saboda haka, idan muna bukatar a toƙara mana, zai yi kyau mu gaya musu. Ta haka, za mu iya yin godiya ta gaske ga dukan ta’aziyya da ’yan’uwanmu suka iya bayarwa, muna ɗaukan haka na fitowa daga wurin Jehovah.—Misalai 12:25; 17:17.
Dubi Cikin Ikilisiyarku
17. Waɗanne matsaloli wata uwa gwauruwa ta fuskanta, ta yaya za mu aza mutane kamarta?
17 Idan ka dubi ’yan’uwa masu bi sosai, za ka koyi ka so su kuma ka sami farin ciki a yin tarayya da su. Ka duba cikin ikilisiyarku. Me ka gani? Da akwai uwa gwauruwa da take faman ta yi renon yaranta a hanyar gaskiya? Ka yi tunanin misali mai kyau da take nunawa kuwa? Ka ƙaga irin matsalolin da take fuskanta. Wata uwa gwauruwa mai suna Jeanine ta ambata wasu cikinsu: kaɗaici, soyayya da ba a so daga maza a wajen aiki, da kuma lura da yadda mutum zai yi maƙo da kuɗi. Amma matsala mafi wuya ciki duka, in ji ta, ya haɗa da kula da bukatun jiye-jiye na yaranta, tun da yake kowanne yaro dabam yake. Jeanine ta zaro wata matsala kuma: “Kalubale ne ƙwarai na ƙi ba da aikin zama shugaban gida wa yaro domin ya cika gurbin da maigidan ya bari. Ina da ’ya, da ƙyar na tuna cewa ’yata ce kada na dame ta da zantattuka na asiri.” Kamar dubban waɗanda su iyaye gwauraye ne masu tsoron Allah, Jeanine tana aiki na cikakken lokaci kuma tana kula da iyali. Tana kuma nazarin Littafi Mai Tsarki tare da yaranta, ta koyar da su cikin hidimar fage, kuma ta kawo su taron ikilisiya. (Afisawa 6:4) Lalle Jehovah zai yi farin ciki sosai ya ga ƙoƙarin wannan iyalin don su riƙe aminci! Ba ma murna ne a ganin irin waɗannan a tsakaninmu? Hakika kuwa.
18, 19. Ka ba da misalin yadda za mu iya zurfafa ƙaunarmu ga waɗanda suke cikin ikilisiya.
18 Ka sake duba cikin ikilisiyarku. Za ka ga gwauraye mata ko maza da ba sa “rabuwa” da taro. (Luka 2:37) Suna jin kaɗaici kuwa a wasu lokatai? Haka yake. Suna tunanin rashin abokan aurensu sosai! Amma hidimar Jehovah ta taƙura su kuma suna kasancewa da marmari wajen wasu. Halinsu mai kyau na cin gaba yana daɗa ga farin ciki na ikilisiyar! Wata Kirista da ta yi hidima ta cikakken lokaci na fiye da shekara 30 ta ce: “Farin cikina ɗaya shi ne ganin ’yan’uwa tsofaffi da suka jimre da gwaji har ila yau suna bauta wa Jehovah cikin aminci!” Hakika kam, Kiristoci tsofaffi tsakaninmu ƙarfafa ce ga matasa.
19 Sababbi da a baya bayan nan ne suka fara tarayya da ikilisiyar fa? Ba ya motsa mu ne yayin da sun furta bangaskiyarsu a cikin taro? Ka yi tunanin ci gaba da suka yi tun lokacin da suka fara nazarin Littafi Mai Tsarki. Lalle Jehovah yana farin ciki da su sosai. Muna haka? Muna furta farin cikinmu, muna yaba wa ƙoƙarce-ƙoƙarcensu?
20. Me ya sa za a iya cewa kowanne cikin ikilisiya yana da aiki mai muhimmanci cikin ikilisiya?
20 Kai mai aure ne, mara aure, iyaye gwauraye? Kai maraya ne mara uba (ko uwa), gwauruwa ko gwauro? Ka yi shekaru da yawa kana tarayya da ikilisiya ko kuma dai a baya bayan nan ne ka fara? Ka tabbata cewa misalin amincinka yana ƙarfafa dukanmu. Yayin da ka sa baƙi a rera waƙar Mulkin, yayin da ka yi furci ko ka gabatar da wani aiki a Makarantar Hidima ta Allah, yana daɗawa ga farin cikinmu. Mafi muhimmanci kuma, yana sa Jehovah farin ciki.
21. Dalilai da yawa na yin menene muke da su, amma waɗanne tambayoyi ne akwai?
21 Hakika, ko a cikin waɗannan lokatai masu wuya, za mu iya yin farin ciki a bauta wa Allahnmu mai farin ciki. Muna da dalilai masu yawa mu yi na’am ga ƙarfafar Bulus: “Ku zauna lafiya. . . . Allah kuwa na ƙauna da na salama za ya zauna tare da ku.” (2 Korinthiyawa 13:11) Me za mu yi idan bala’i ya same mu, tsanani, ko kuma tattalin arziki ya yi wuya? Yana yiwuwa mu riƙe farin cikinmu cikin irin yanayin nan? Ka ba da taka amsar bayan ka bincika talifi na biye.
[Hasiya]
a Duba Littafi na 2 na Insight on the Scriptures, shafi na 119, wanda Shaidun Jehovah suka buga.
Za Ka Iya Amsawa?
• Ta yaya aka kwatanta farin ciki?
• Ta yaya riƙe hali mai kyau zai taimake mu kasancewa da farin ciki?
• Menene zai taimake mu kasancewa da ra’ayi mai kyau game da yanki na ikilisiyarmu?
• A waɗanne hanyoyi ne ka ke son ’yan’uwa da suke cikin ikilisiyarku?
[Hotuna a shafi na 22]
Mutane da suke yankinmu suna iya canjawa
[Hoto a shafi na 24]
Waɗanne matsaloli waɗanda suke cikin ikilisiyarku suke fuskanta?