Ka Ci Gaba Da Jurewa Kamar Kana Ganin Wanda Ba Shi Ganuwa!
“[Musa] ya jimre, kamar yana ganin wanda ba shi ganuwa.”—IBRANIYAWA 11:27.
1. Wane furci ne na musamman Yesu ya yi game da Allah a Hudubarsa Bisa Dutse?
JEHOVAH Allah ne da ba a gani. Lokacin da Musa ya ce ya ga ɗaukakarsa, Jehovah ya ce: “Ba ka da iko ka ga fuskata: gama mutum ba shi ganina shi rayu.” (Fitowa 33:20) Manzo Yohanna kuma ya rubuta: “Ba wanda ya taɓa ganin Allah ba daɗai.” (Yohanna 1:18) Lokacin da Yesu Kristi mutum ne a duniya, shi ma bai ga Allah ba. Amma a Hudubarsa Bisa Dutse, Yesu ya ce: “Masu-albarka ne masu-tsabtan zuciya: gama su za su ga Allah.” (Matta 5:8) Menene Yesu yake nufi?
2. Me ya sa ba za mu iya ganin Allah ba da idanunmu na zahiri?
2 Nassosi sun nuna cewa Jehovah Ruhu ne da ba a gani. (Yohanna 4:24; Kolossiyawa 1:15; 1 Timothawus 1:17) Saboda haka, Yesu ba cewa yake da gaske za mu iya ganin Jehovah da idanunmu na zahiri ba. A gaskiya, shafaffu Kiristoci za su ga Jehovah Allah a sama bayan an tashe su su zama halittu na ruhu. Amma mutane “masu-tsabtan zuciya” kuma da suke da begen rayuwa har abada a cikin duniya suna iya ‘ganin’ Allah. Yaya wannan zai yiwu?
3. Ta yaya mutane za su gane wasu ingancin Allah?
3 Muna koyon wani abu game da Jehovah ta wajen lura sosai da abubuwa da ya halitta. Da haka ikonsa zai burge mu kuma mu motsa mu amince cewa shi Allah Mahalicci ne. (Ibraniyawa 11:3; Ru’ya ta Yohanna 4:11) Game da wannan, manzo Bulus ya rubuta: “Tun halittar duniya al’amura [na Allah] da ba su ganuwa, watau ikonsa madawwami da allahntakarsa, a sarari a ke ganinsu; ta wurin abubuwa da an halitta ana gane su; har kuwa su rasa hujja.” (Romawa 1:20) Saboda haka, kalmomin Yesu game da ganin Allah ya ƙunshi fahimtar wasu ingancin Jehovah. Irin ganin nan bisa cikakken sani kuma ana gane ta ta ruhaniya ne da ‘idanun zuciya.’ (Afisawa 1:18) Magana da ayyukan Yesu sun bayyana abubuwa da yawa game da Allah. Shi ya sa, Yesu ya ce: “Wanda ya gan ni ya ga Uban.” (Yohanna 14:9) Yesu ya yi kwaikwayon mutumtakar Jehovah daidai. Da haka, sanin rayuwar Yesu da koyarwarsa zai taimaka mana mu gani, ko fahimci wasu inganci na Allah.
Ruhaniya na da Muhimmanci
4. Yaya mutane da yawa a yau suke nuna rashin ruhaniya?
4 Yau bangaskiya da ruhaniya ta gaske na da wuya sosai. “Ba duka ke da imani ba,” in ji Bulus. (2 Tassalunikawa 3:2) Mutane da yawa sun mai da hankali a nema wa na kansu ba su da bangaskiya ga Allah. Halinsu na zunubi da rashin ruhaniya na hana su ganinsa da idanun fahimi, gama manzo Yohanna ya rubuta: “Wanda ya ke aika mugunta ba ya ga Allah ba.” (3 Yohanna 11) Domin irin waɗannan mutane ba sa ganin Allah da idanunsu na zahiri, suna aikata abubuwa kamar ba ya ganin abin da suke yi. (Ezekiel 9:9) Suna raina abubuwa na ruhaniya, da haka ba za su iya “ruski sanin Allah” ba. (Misalai 2:5) Bulus ya rubuta: “Mutum mai-tabi’ar jiki ba shi karɓa al’amura na Ruhun Allah ba: gama wauta su ke a gare shi; ba shi kuwa da iko shi san su, gama ana gwadarsu cikin ruhaniya.”—1 Korinthiyawa 2:14.
5. Wace gaskiya mutane masu ruhaniya suka sani?
5 Amma idan muna mai da hankali ga abubuwa na ruhaniya, kullum za mu san cewa ko da Jehovah ba Allah mai neman laifi ba ne ya san lokacin da muke aikata abubuwa domin munanan tunani da sha’awoyi. Hakika, “al’amuran mutum a gaban Ubangiji su ke, ya kan daidaita dukan tafarkunsa.” (Misalai 5:21) Idan zunubi ya sha kanmu, za mu motsa mu tuba mu nemi gafarar Jehovah domin muna ƙaunarsa kuma ba ma son mu sa shi fushi.—Zabura 78:41; 130:3.
Menene ke Sa Mu Jurewa?
6. Me yake nufi da a jure?
6 Ko da ba ma ganin Jehovah, mu tuna koyaushe cewa yana ganinmu. Sanin cewa yana wanzuwa da kuma tabbacin cewa yana kusa da duk waɗanda suke kira gare shi, zai taimaka mana mu jure—mu tsaya da ƙarfi kuma mu kafu cikin amincinmu gare shi. (Zabura 145:18) Za mu iya zama kamar Musa, wanda Bulus ya rubuta game da shi: “Ta wurin bangaskiya ya bar Masar, ba ya ji tsoron hasalar sarki ba: gama ya jimre, kamar yana ganin wanda ba shi ganuwa.”—Ibraniyawa 11:27.
7, 8. Me ya sa Musa yake da ƙarfin zuciya a gaban Fir’auna?
7 Wajen yin aikin da Allah ya ba shi ya ja-goranci Isra’ilawa su fito daga bauta ta ƙasar Masar, Musa sau da yawa ya bayyana a gaban Fir’auna mai zalunci a fada da ke cike da manya na addini da kuma manyan ’yan siyasa. Wataƙila, bangwayen fadar an zana gumaka. Amma Jehovah, ko da ba shi ganuwa, ya kasance gaskiya ga Musa, ba kamar dukan gumaka da ke wakiltan alloli marasa rai na ƙasar Masar ba. Shi ya sa Musa bai tsorata ba don Fir’auna!
8 Menene ya ba Musa ƙarfin zuciya ya bayyana a gaban Fir’auna a kai a kai? Nassosi sun gaya mana “mutumin nan Musa mai-tawali’u ne ƙwarai, gaba da kowane mutum da ke zaune a bisa fuskar duniya.” (Litafin Lissafi 12:3) A bayyane, ruhaniyarsa mai ƙarfi da tabbaci cewa Allah na tare da shi ya ba Musa ƙarfi da yake bukata ya wakilci ‘Wanda ba shi ganuwa’ a gaban sarki mara tausayi na Masar. Waɗanne hanyoyi ne waɗanda suke ‘ganin’ Allah da ba shi ganuwa suke nuna bangaskiyarsu gare shi a yau?
9. A wace hanya ɗaya ce za mu iya ci gaba da jurewa?
9 Hanya ɗaya da za mu nuna bangaskiya kuma mu ci gaba da jurewa kamar muna ganin Wanda ba shi ganuwa ita ce ta yin wa’azi da gaba gaɗi duk da tsanani. Yesu ya yi wa almajiransa kashedi: “Za ku zama abin ƙi ga dukan mutane sabili da sunana.” (Luka 21:17) Ya kuma gaya musu: “Bawa ba ya fi ubangijinsa girma ba. Idan suka yi mani tsanani, su a yi maku tsanani kuma.” (Yohanna 15:20) Gaskiya ga maganar Yesu, ba da daɗewa ba bayan mutuwarsa, mabiyansa suka sha tsanani a ta hanyar tsoratar da su, tsarewa, da dūka. (Ayukan Manzanni 4:1-3, 18-21; 5:17, 18, 40) Ko da ana tsanani sosai, manzannin Yesu da wasu almajirai suka ci gaba da wa’azin bishara da gaba gaɗi.—Ayukan Manzanni 4:29-31.
10. Ta yaya amincinmu a kula na Jehovah ke taimaka mana a hidima?
10 Kamar Musa, mabiyan Yesu na farko ba su tsorata ba domin magabtansu da yawa da suke gani. Almajiran Yesu suna da aminci ga Allah, a sakamakon haka, sun iya jimre wa tsanani da suka fuskanta. E, sun ci gaba da jurewa kamar suna ganin Wanda ba shi ganuwa. A yau, sanin cewa Jehovah na kula na ƙarfafa mu, yana ba mu ƙarfin zuciya da gaba gaɗi cikin aikinmu na wa’azin Mulki. Maganar Allah ta ce “tsoron mutum ya kan kawo tarko, amma wanda ya sa danganarsa ga Ubangiji za ya zauna lafiya.” (Misalai 29:25) Saboda haka, ba ma ja da baya don tsoron tsanani; ba ma kuma jin kunyar hidimarmu. Bangaskiyarmu na motsa mu mu yi wa’azi da gaba gaɗi ga maƙwabtanmu, abokan aikinmu, abokan makaranta da kuma wasu.—Romawa 1:14-16.
Wanda ba Shi Ganuwa Yana Ja-gorar Mutanensa
11. Bisa ga Bitrus da Yahuda, ta yaya wasu da suke cikin ikilisiyar Kirista suka nuna ba su da ruhaniya?
11 Bangaskiya na taimaka mana mu ga cewa Jehovah ne ke ja-gorar ƙungiyarsa ta duniya. Da haka, muna guje wa zagin waɗanda suke da hakki cikin ikilisiya. Manzo Bitrus da Yahuda ɗan’uwan Yesu sun yi kashedi game da wasu da ba su da ruhaniya waɗanda suke zagin mutane da suke jagabanci tsakanin Kiristoci. (2 Bitrus 2:9-12; Yahuda 8) Irin waɗannan masu neman laifi za su yi magana hakanan a gaban Jehovah idan suna ganinsa a zahiri? Da kyar! Amma domin ba sa ganin Allah, waɗannan mutanen sun manta cewa za su ba da lissafi a gare shi.
12. Wane hali ya kamata mu nuna ga waɗanda suke jagabanci cikin ikilisiya?
12 Gaskiya, mutane ajizai ne suke cikin ikilisiyar Kirista. Waɗanda su dattawa ne suna kuskure da wani lokaci zai shafe mu. Duk da haka, Jehovah yana amfani da irin waɗannan mutane a kiwon garkensa. (1 Bitrus 5:1, 2) Maza da mata masu ruhaniya sun gane cewa wannan hanya ɗaya ce da Jehovah yake ja-gorar mutanensa. Saboda haka, da yake mu Kiristoci ne, mu guji halin zagi, da ƙunƙuni amma mu nuna ladabi ga abin da Allah ya shirya don ya ja-goranci mutanensa. Ta wajen yin biyayya ga waɗanda suke jagabanci tsakaninmu, muna nuna cewa muna ganin Wanda ba shi ganuwa.—Ibraniyawa 13:17.
Ganin Allah Cewa Babba Mai Koya Mana Ne
13, 14. Menene ganin Jehovah Babba Mai Koya mana ke nufi a gare ka?
13 Akwai wani waje da ke bukatar fahimi na ruhaniya. Ishaya ya yi annabci: “Idanunka za su ga mai-koya maka.” (Ishaya 30:20) Yana bukatar bangaskiya mu fahimci cewa Jehovah ne ke koya mana ta wajen ƙungiyarsa ta duniya. (Matta 24:45-47) Ganin Allah cewa Babba ne Mai Koya mana na fiye da riƙe hali mai kyau na nazarin Littafi Mai Tsarki da halartan taron Kirista a kai a kai kawai. Yana nufin yin amfani sosai da tanadi na ruhaniya da Allah yake yi. Alal misali, muna bukatar mu mai da hankali sosai ga ja-gora da Jehovah ya yi tanadinsa ta wurin Yesu don kada mu janye a ruhaniya.—Ibraniyawa 2:1.
14 Wani lokaci yana bukatar ƙoƙari sosai don mu amfana daga abinci na ruhaniya. Alal misali, za mu iya hanzarin karanta wasu labaran Littafi Mai Tsarki da mun iske da wuya mu fahimta. Yayin da muke karatun jaridun Hasumiyar Tsaro da Awake!, wataƙila za mu tsallake wasu talifi domin ba ma son darassin. Ko kuma za mu iya barin zuciyarmu tana yawo a taron Kirista. Amma, za mu iya kasancewa a farke idan muna tunani sosai a kan darassi da ake bincike a kai. Godiyarmu ta ƙwarai ga koyarwa ta ruhaniya da muke samu na nuna mun amince Jehovah ne Babba Mai Koya mana.
Za Mu Kawo Lissafin Kanmu
15. Ta yaya wasu suke yi kamar Jehovah ba ya ganinsu?
15 Musamman ma domin mugunta na ko’ina a wannan “kwanakin ƙarshe,” bangaskiya ga Wanda ba shi ganuwa tana da muhimmanci. (Daniel 12:4) Rashin gaskiya da lalata na ko’ina. Hakika, yana da kyau mu tuna cewa Jehovah yana lura da ayyukanmu ko da mutane ba sa iya ganinmu. Wasu sun manta da wannan gaskiyar. Lokacin da wasu ba sa ganinsu, suna iya sa hannu cikin hali da ba na Nassi ba. Alal misali, wasu ba su tsayayya wa jarabar kallon nishaɗi mai lahani da hotunan tsirarun mutane a Intane, telibijin, da wasu fasaha na zamani. Tun da yake za a iya sa hannu cikin irin waɗannan abubuwa a ɓoye, wasu suna yi kamar Jehovah ba ya ganin halinsu.
16. Menene zai taimaka mana mu bi mizanan Jehovah mai girma?
16 Yana da kyau mu tuna da kalmomin manzo Bulus: “Kowane ɗayanmu fa za ya kawo lissafin kansa ga Allah.” (Romawa 14:12) Muna bukatar mu sani cewa kowanne lokaci da muka yi zunubi, muna zunubi ne ga Jehovah. Sanin wannan ya kamata ya taimaka mana mu bi mizanansa mai girma mu kuma guje wa halin da ba shi da tsabta. Littafi Mai Tsarki ya tunasar da mu: “Babu wani abu mai-rai kuma da ba a bayyane a gabansa ba: amma abubuwa duka a tsiraice su ke, buɗaɗu kuma gaban idanun wannan wanda mu ke gareshi.” (Ibraniyawa 4:13) Hakika, dole ne za mu kawo lissafi ga Allah, amma babu shakka ƙaunarmu mai zurfi ga Jehovah ita ce dalilin da ya sa muke yin nufinsa kuma muke yin biyayya ga mizanansa na adalci. Saboda haka, bari mu nuna hikima a zaɓan nishaɗi da halinmu wajen kishiyar jinsi.
17. Wane irin damuwa Jehovah yake da shi game da mu?
17 Jehovah yana damuwa sosai da mu, amma wannan ba ya nufin cewa yana jira mu yi kuskure don ya hore mu ba. Maimako, yana lura da mu da kulawa mai kyau, kamar na uba da yake so ya sāka wa yaransa masu biyayya. Abin ƙarfafa ne mu sani cewa bangaskiyarmu tana faranta wa Ubanmu na sama rai kuma shi “mai-sākawa ne ga waɗanda ke biɗarsa”! (Ibraniyawa 11:6) Bari mu ba da cikakkiyar gaskiya ga Jehovah kuma mu “bauta masa da sahihiyar zuciya.”—1 Labarbaru 28:9.
18. Domin Jehovah yana kallonmu da kuma lura da amincinmu, wane tabbaci muka samu daga Nassosi?
18 Misalai 15:3 ta ce: “Idanun Ubangiji suna cikin kowane wuri, suna tsaron miyagu da nagargaru.” Hakika, Allah yana tsaron miyagu kuma yana bi da su daidai da halinsu. Amma, idan muna cikin “nagargaru,” za mu tabbata cewa Jehovah yana lura da ayyukanmu na aminci. Abin ƙarfafa bangaskiya ne mu sani cewa ‘wahalarmu ba banza ta ke ba cikin Ubangiji’ kuma cewa wanda ba shi ganuwa ba zai ‘manta da aikinmu da ƙauna wadda muka nuna ga sunansa’ ba!—1 Korinthiyawa 15:58; Ibraniyawa 6:10.
Gayyaci Jehovah Ya Bincike Mu
19. Waɗanne fa’idodi ne suke zuwa daga bangaskiya mai ƙarfi ga Jehovah?
19 Da yake mu bayin Jehovah ne masu aminci, muna da tamani gare shi. (Matta 10:29-31) Ko da ba a ganinsa, zai kasance da gaske a gare mu, za mu iya daraja dangantakarmu mai tamani da shi. Kasancewa da irin wannan hali game da Ubanmu na sama yana kawo mana fa’idodi da yawa. Bangaskiyarmu mai ƙarfi tana taimaka mana mu kasance da zuciya mai tsabta da lamiri mai kyau a gaban Jehovah. Bangaskiya mara riya tana hana mu yin rayuwa mai fuska biyu. (1 Timothawus 1:5, 18, 19) Bangaskiya mara jijjiga ga Allah na kafa misali mai kyau kuma za ta iya zama ƙarfafa ga waɗanda suka kewaye mu. (1 Timothawus 4:12) Ƙari ga haka, irin bangaskiyar tana gabatar da hali na ibada, yana faranta wa Jehovah rai.—Misalai 27:11.
20, 21. (a) Me ya sa yake da kyau Jehovah yana tsaronmu? (b) Ta yaya za mu yi amfani da Zabura 139:23, 24 wa kanmu?
20 Idan mu masu hikima ne, muna farin ciki cewa Jehovah yana tsaronmu. Ba kawai muna son ya gan mu ba amma muna son ya bincika tunaninmu da ayyukanmu sosai. Cikin addu’a, zai yi kyau mu ce wa Jehovah ya bincike mu ya gani ko muna da wani nufi da bai dace ba. Babu shakka zai taimaka mana mu jimre da matsalolinmu kuma mu yi kowane gyare-gyare da ake bukata. Daidai, mai Zabura Dauda ya rera: “Ka yi bincikena, ya Ubangiji, ka san zuciyata: Ka auna ni, ka san tunanina: Ka duba ko da wata hanyar mugunta daga cikina, ka bishe ni cikin tafarki na har abada.”—Zabura 139:23, 24.
21 Dauda ya roƙi Jehovah ya bincika shi ya gani ko da akwai wata “hanyar mugunta” a cikinsa. Kamar mai zabura, ba ma son Allah ya bincika zuciyarmu ya gani ko muna da wani nufi da bai dace ba? Cikin bangaskiya, mu gaya wa Jehovah ya bincike mu. Amma idan muna damuwa da ɗawainiya don wasu kuskure ko kuma akwai wani abu da ba shi da kyau cikinmu? Bari mu ci gaba da addu’a ga Allah mai ƙauna, Jehovah, kuma mu yi biyayya cikin tawali’u ga ja-gorar ruhunsa mai tsarki da gargaɗin Kalmarsa. Za mu kasance da gaba gaɗi cewa zai taimaka mana mu biɗi tafarki da zai kai ga rai madawwami.—Zabura 40:11-13.
22. Me ya kamata ya zama aniyyarmu game da Wanda ba shi ganuwa?
22 E, Jehovah zai albarkace mu da rai madawwami idan muka cika farillansa. Babu shakka, dole ne mu amince da ikonsa da matsayi, har ma yadda manzo Bulus ya yi lokacin da ya rubuta: “Ga Sarki na zamanu, mara-mutuwa, mara-ganuwa, Allah makaɗaici, girma da ɗaukaka su tabbata har zuwa zamanun zamanai. Amin.” (1 Timothawus 1:17) Bari ko yaushe mu nuna irin wannan tsoro daga zuciya ga Jehovah. Ko menene ya faru, kada mu yi shakka cikin aniyyarmu mu ci gaba da jurewa kamar muna ganin Wanda ba shi ganuwa.
Yaya Za Ka Amsa?
• Ta yaya zai yiwu mutane su ga Allah?
• Idan Jehovah da gaske yake a garemu, yaya za mu aikata abubuwa yayin da ake tsananta mana?
• Menene yake nufi mu ga Jehovah cewa Babba ne Mai Koya mana?
• Me ya sa za mu so Jehovah ya bincike mu?
[Hoto a shafi na 12]
Musa, bai tsorata ba don Fir’auna, ya aikata abubuwa kamar yana ganin Jehovah, Allah da ba shi ganuwa
[Hoto a shafi na 15]
Kada mu aikata abubuwa kamar Jehovah ba zai iya taɓa ganin abin da muke yi ba
[Hoto a shafi na 17]
Muna biɗan sani na Allah sosai domin muna ganin shi Babba ne Mai Koya mana