Albarkar Jehovah Za Ta Tarar Da Kai?
“Dukan waɗannan albarka kuma za su zo maka, su tarshe ka, idan ka saurara ga muryar Ubangiji Allahnka.”—KUBAWAR SHARI’A 28:2.
1. Menene zai nuna ko Isra’ilawa za su sami albarka ko la’ana?
KUSAN ƙarshen tafiyarsu ta shekaru 40 cikin daji, Isra’ilawa suka yi zango a Filayen Mowab. Ƙasar Alkawari tana gabansu. Musa ya rubuta littafin Kubawar Shari’a, wanda ya ƙunshi jerin albarka da la’ana. Idan mutanen Isra’ila za su “saurara ga muryar Ubangiji” su yi masa biyayya, albarka za ta ‘tarar da’ su. Jehovah ya ƙaunaci “al’ummarsa keɓaɓɓiya” ya nuna ikonsa dominta. Amma idan ba su saurare sa ba, babu shakka la’ana za ta tarar da su.—Kubawar Shari’a 8:10-14; 26:18; 28:2, 15.
2. Mecece ma’anar aikatau na Ibrananci da aka juya “saurara” da kuma ‘tarar da’ a Kubawar Shari’a 28:2?
2 Aikatau na Ibrananci da aka juya “saurara” a Kubawar Shari’a 28:2 na nufin ci gaba da sauraro. Mutanen Jehovah ba kawai za su saurare shi wani lokaci ba; dole ci gaba da sauraronsa ya zama hanyar rayuwarsu. Sa’an nan ne kawai albarkar Allah za ta tarar da su. Aikatau na Ibrananci da aka fassara ‘tarar da’ an gano cewa furci ne na farauta wanda sau da yawa yana nufin “a kama” ko “a kai ga.”
3. Ta yaya za mu zama kamar Joshua, kuma me ya sa wannan yake da muhimmanci?
3 Shugaban Isra’ilawa Joshua ya zaɓi ya saurari Jehovah ya samu albarka. Joshua ya ce: “Ku zaɓa yau wanda za ku bauta masa . . . amma da ni da gidana, Ubangiji za mu bauta ma.” A jin haka, mutanen suka amsa: “Allah shi sawaƙa mu bar Ubangiji, domin mu bauta ma waɗansu alloli.” (Joshua 24:15, 16) Domin hali mai kyau na Joshua, yana cikin mutane kalilan na tsaransa da suka samu gatar shiga Ƙasar Alkawari. A yau muna bakin shiga mafificiyar Ƙasar Alkawari—aljanna a duniya inda albarka da ta fi ta zamanin Joshua ke jirar dukan waɗanda suka sami yardar Allah. Irin wannan albarka za ta tarar da kai? Za ta tarar da kai idan ka ci gaba da sauraron Jehovah. Don ka ƙarfafa ƙudurinka na yin haka, ka bincika tarihin Isra’ila na dā da misalai masu koyarwa na wasu mutane.—Romawa 15:4.
Albarka ko La’ana?
4. A amsa addu’ar Sulemanu, menene Allah ya ba shi, kuma yaya ya kamata mu ji game da irin wannan albarka?
4 Yawanci a lokacin sarautar Sarki Sulemanu, Isra’ilawa sun samu albarka ƙwarai daga Jehovah. Sun more kwanciyar rai da abubuwa masu kyau a yalwace. (1 Sarakuna 4:25) Arzikin Sulemanu ya zama sananne, ko da yake bai tambayi Allah abin duniya ba. Maimako, yayin da yake matashi kuma ba shi da basira, ya yi addu’a don zuciya mai biyayya—roƙo da Jehovah ya amsa ta wajen ba shi hikima da fahimi. Wannan ya taimake Sulemanu ya yi wa mutanen shari’a da kyau, ya bambance tsakanin nagarta da mugunta. Ko da yake Allah ya ba shi arziki da ɗaukaka, saurayi Sulemanu, ya daraja muhimmancin abubuwa na ruhaniya. (1 Sarakuna 3:9-13) Ko muna da abin duniya da yawa ko babu, za mu yi godiya idan muka samu albarkar Jehovah kuma muna da arziki a ruhaniya!
5. Menene ya faru lokacin da mutanen Isra’ila da Yahuda suka kasa saurarar Jehovah?
5 Isra’ilawan sun kasa nuna godiya ga albarkar Jehovah. Domin ba su ci gaba da sauraronsa ba, la’ana da aka annabta ta tarar da su. Wannan ya sa maƙiyan suka ci su kuma masarautar Isra’ila da ta Yahuda suka je bauta. (Kubawar Shari’a 28:36; 2 Sarakuna 17:22, 23; 2 Labarbaru 36:17-20) Mutanen Allah sun koya daga irin wannan wahala cewa albarkar Allah tana tarar da waɗanda suka ci gaba da saurarar Jehovah ne kawai? Raguwar Yahudawa da suka dawo ƙasarsu a 537 K.Z. suna da zarafi su nuna ko sun samo “zuciya mai-hikima” kuma ko sun ga dalilin su ci gaba da saurarar Allah.—Zabura 90:12.
6. (a) Me ya sa Jehovah ya aiki Haggai da Zechariah su yi annabci ga mutanensa? (b) Wace ƙa’ida ce saƙon Allah ta wurin Haggai ya kwatanta?
6 Yahudawa da aka komar da su suka gina bagadi kuma suka soma aiki a kan haikalin a Urushalima. Amma da hamayya mai tsanani ta taso, himmarsu ta soma raguwa kuma aikin ginin ya tsaya. (Ezra 3:1-3, 10; 4:1-4, 23, 24) Suka kuma soma ɗaukan kayayyakin alatu na rayuwa da muhimmanci. Saboda haka, Allah ya aiki annabi Haggai da Zechariah su sake ta da himmar mutanensa don sujjada ta gaskiya. Ta bakin Haggai, Jehovah ya ce: “Ko lokaci ya yi da ku da kanku za ku zauna cikin sorayenku, wannan gida fa [na bauta] kango ne? . . . Ku lura da al’amuranku. Kun yi shuka dayawa, kun yi girbi kaɗan; kun ci, ba ku ƙoshi ba . . . wanda yana samun albashi yana samu domin ya sa cikin jaka mai-kofaye.” (Haggai 1:4-6) Sadaukar da abubuwa na ruhaniya a biɗan abin duniya ba ya kawo albarkar Jehovah.—Luka 12:15-21.
7. Me ya sa Jehovah ya gaya wa Yahudawa: “Ku lura da al’amuranku”?
7 Domin sun shagala cikin abubuwa na yau da kullum, Yahudawa sun manta cewa albarkatu kamar su ruwan sama da lokacin wadata daga Allah zai tarar da su ne kawai idan suka jimre a tafarkin biyayya ga Allah, har a lokacin da suke fuskantar hamayya. (Haggai 1:9-11) Saboda haka, gargaɗin ya dace: “Lura da al’amuranku.” (Haggai 1:7) Wato, Jehovah yana gaya musu ne: ‘Ku yi tunani! Ku ga fa mahaɗi da ke tsakanin aikinku na wofi a gona da yanayin kango na gidan bauta mini.’ Huraren kalmomi na annabawan Jehovah ya taɓa zukatan masu sauraronsu a ƙarshe, mutanen suka sake soma aikin haikalin, suka gama a 511 K.Z.
8. Wane gargaɗi Jehovah ya ba Yahudawa a zamanin Malachi, kuma me ya sa?
8 Daga baya, a zamanin annabi Malachi, Yahudawan suka soma tantama a ruhaniya kuma, har ma da miƙa hadayu da ba sa karɓuwa ga Allah. (Malachi 1:6-8) Da haka, Jehovah ya gargaɗe su su kawo zakka a cikin ma’ajinsa su gwada shi su ga ko ba zai buɗe musu sakatan sama ba, ya zuba musu albarka har da ba za a sami wurin da za a karɓa ba. (Malachi 3:10) Yahudawa sun yi wauta su yi aiki don abubuwa da Allah zai ba su a yalwace idan za su ci gaba da saurarar muryarsa kawai!—2 Labarbaru 31:10.
9. Za mu bincika rayuwan waɗanne mutane uku ne na tarihin Littafi Mai Tsarki?
9 Ƙari ga ba da tarihin al’ummar Isra’ila, Littafi Mai Tsarki ya ba da tarihin rayuwar mutane da yawa da suka samu albarkar Allah ko kuma la’ana, dangane da ko sun ci gaba da saurarar Jehovah ko babu. Bari mu ga abin da za mu koya daga uku cikinsu—Boaz, Nabal, da Hannatu. Game da wannan, za ka so ka karanta littafin Ruth da kuma 1 Samu’ila 1:1–2:21 da 1 Samu’ila 25:2-42.
Boaz Ya Saurari Allah
10. Waɗanne abubuwa iri ɗaya Boaz da Nabal suke da shi?
10 Ko da yake Boaz da Nabal ba tsara ba ne, suna da wasu abubuwa iri ɗaya. Alal misali, dukansu sun zauna a ƙasar Yahuda. Mawadata ne masu filaye, dukansu kuma sun samu zarafi na musamman su yi alheri ga wani da yake da bukata. A nan ne kamaninsu ya ƙare.
11. Ta yaya Boaz ya nuna cewa ya ci gaba da saurarar Jehovah?
11 Boaz ya rayu a zamanin alƙalai na Isra’ila. Yana daraja wasu, kuma magirbansa suna ba shi daraja ƙwarai. (Ruth 2:4) Cikin biyayya ga Doka, Boaz yana tabbata cewa a gonarsa, ana barin kala da mayunwata da matalauta za su kalace. (Leviticus 19:9, 10) Menene Boaz ya yi lokacin da ya ji game da Ruth da Naomi kuma da ya ga aikin da Ruth take yi sosai domin ta kula da bukatun surukarta da ta tsufa? Ya ji tausayin Ruth musamman, ya umurci mutanensa su bar ta ta yi kala a gonarsa. Ta maganarsa da kuma ayyukansa masu kyau, Boaz ya nuna cewa shi mutum ne mai ruhaniya da yake saurarar Jehovah. Saboda haka ya samu alheri da albarkar Allah.—Leviticus 19:18; Ruth 2:5-16.
12, 13. (a) Ta yaya Boaz ya nuna ya daraja dokar Jehovah ta fansa? (b) Wace albarka ce ta Allah ta tarar da Boaz?
12 Tabbaci na musamman da ya nuna cewa Boaz ya ci gaba da sauraron Jehovah shi ne rashin son kai da ya nuna wajen aikata dokar Allah ta fansa. Boaz ya yi dukan abin da zai iya ya tabbata cewa gadōn danginsa—mijin Naomi da ya mutu, Elimelech—ya kasance cikin iyalinsa. Ta wurin ‘auren ɗan uba,’ gwauruwa za ta auri mai gadōn domin ɗa da za su haifa ya yi gadō. (Kubawar Shari’a 25:5-10; Leviticus 25:47-49) Ruth ta ba da kanta a aura a madadin Naomi, wadda ta wuce haihuwa. Da dangi na kurkusa na Elimelech ya ƙi taimakon Naomi, Boaz ya ɗauki Ruth ta zama matarsa. An ɗauki ɗansu Obed ɗan Noami ne kuma magajin Elimelech.—Ruth 2:19, 20; 4:1, 6, 9, 13-16.
13 Albarka mai yawa ta tarar da Boaz domin rashin son kansa wajen bin dokar Allah. Ta ɗansu Obed, shi da Ruth an albarkace su da gatar zama kakannin Yesu Kristi. (Ruth 2:12; 4:13, 21, 22; Matta 1:1, 5, 6) Daga ayyukan Boaz na rashin son kai, mun koyi cewa albarka tana tarar da waɗanda suke ƙaunar wasu kuma suke aiki cikin jituwa da farillan Allah.
Nabal Bai Saurara Ba
14. Wane irin mutum ne shi Nabal?
14 Ya bambanta da Boaz, Nabal bai saurari Jehovah ba. Ya karya dokar Allah: “Ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka.” (Leviticus 19:18) Nabal ba mutum ba ne mai ruhaniya; “mutumin mai-tankiya ne mai-munanan ayyuka.” Har ma bayinsa sun ɗauke “shi shaƙiyin mutum ne.” Sunansa, Nabal ya dace domin yana nufin “wauta,” ko “wawa.” (1 Samu’ila 25:3, 17, 25) Yaya Nabal zai aikata yayin da yake da zarafi ya yi alheri wa wanda yake cikin bukata—Dauda, wanda Jehovah ya naɗa?—1 Samu’ila 16:13.
15. Yaya Nabal ya bi da Dauda, yaya Abigail ta bambanta daga maigidanta a wannan?
15 Lokacin da suke wajen garken Nabal, Dauda da mutanensa, ba tare da cewa a biya su ba, suka kāre garken daga mahara. Ɗaya cikin makiyayan Nabal ya ce: “Suka zama mana gānuwa dare da rana.” Amma lokacin da manzannin Dauda suka roƙi abinci, Nabal “ya kuwa yi musu furji” suka tafi babu kome. (1 Samu’ila 25:2-16) Matar Nabal, Abigail, nan da nan ta kai wa Dauda abinci. Domin ya fusata, Dauda ya kusa ya halaka Nabal da mutanensa. Abin da Abigail ta yi ya ceci rayukan mutane da yawa kuma ya hana Dauda daga ɗaukan alhakin jini. Amma haɗamar Nabal da tankiyarsa sun yi yawa. Kamar bayan kwana goma, “Ubangiji ya buga Nabal har ya mutu.”—1 Samu’ila 25:18-38.
16. Yaya za mu yi koyi da Boaz mu ƙi hanyoyin Nabal?
16 Da bambanci ƙwarai tsakanin Boaz da Nabal! Yayin da za mu ƙi tankiya da hanyoyi na son kai na Nabal, bari mu yi koyi da alheri da rashin son kai na Boaz. (Ibraniyawa 13:16) Za mu iya hakan ta yin amfani da gargaɗin manzo Bulus: “Yayinda mu ke da dama fa, bari mu aika nagarta zuwa ga dukan mutane, tun ba waɗanda su ke cikin iyalin imani” ba. (Galatiyawa 6:10) A yau “waɗansu tumaki” na Yesu, Kiristoci da suke da begen zama a duniya, suna da gatar yin abu mai kyau ga shafaffu na Jehovah, raguwar 144,000, waɗanda za a ba su rai mara mutuwa a sama. (Yohanna 10:16; 1 Korinthiyawa 15:50-53; Ru’ya ta Yohanna 14:1, 4) Yesu yana ɗaukar irin waɗannan ayyuka masu kyau kamar shi aka yi wa, kuma yin waɗannan abubuwa masu kyau na kawo albarka mai girma na Jehovah.—Matta 25:34-40; 1 Yohanna 3:18.
Gwaji da Kuma Albarkar Hannatu
17. Hannatu ta fuskanci wane gwaji, kuma wane hali ne ta nuna?
17 Albarkar Jehovah ta tarar da mace mai ibada Hannatu. Tana da zama a duwatsu na Ifraimu da mijinta Balawi, Elkanah. Yadda Dokar ta faɗa kuma ta ba da farillai, yana da wata mata—Peninnah. Hannatu ta kasance bakararriya, abin kunya ne ga Ba’isra’iliya, yayin nan kuma Peninnah tana da yara da yawa. (1 Samu’ila 1:1-3; 1 Labarbaru 6:16, 33, 34) Maimakon ta riƙa ƙarfafa Hannatu, Peninnah ta riƙa aikata abubuwa a hanya da ba shi da kyau da ya riƙa sa Hannatu fushi har ta yi hawaye da rashin marmarin abinci. Mafi muni, wannan yana faruwa “shekara a kan shekara,” kowanne lokaci da iyalin suka je gidan Jehovah a Shiloh. (1 Samu’ila 1:4-8) Peninnah mara tausayi ce, gwaji ne kuma ga Hannatu! Duk da haka, Hannatu ba ta ɗaura wa Jehovah laifin ba; ko kuma ta zauna a gida lokacin da maigidanta zai je Shiloh. Saboda haka, a ƙarshe albarka babu shakka za ta tarar da ita.
18. Wane misali ne Hannatu ta bari?
18 Hannatu ta bar misali mai kyau ga mutanen Jehovah a yau, musamman ma waɗanda ƙila bakar magana da wasu suka yi ta ɓata musu rai. A irin wannan yanayi, ware kai ba zai magance matsalar ba. (Misalai 18:1) Hannatu ba ta bar gwajinta ya rage muradinta na kasancewa inda ake koyar da Kalmar Allah ba kuma inda mutanensa suka taru don bauta. Da haka, ta kasance da ƙarfi a ruhaniya. Yadda take da ruhaniya ya bayyana cikin addu’arta mai kyau da ke rubuce a 1 Samu’ila 2:1-10.a
19. Ta yaya za mu nuna godiyarmu don abubuwa na ruhaniya?
19 Mu bayin Jehovah na zamani, ba ma bauta a mazauni. Duk da haka, za mu iya nuna godiyarmu don abubuwa na ruhaniya yadda Hannatu ta yi. Alal misali, za mu iya nuna godiyarmu ga abubuwa na ruhaniya ta kasancewa a taron Kirista kullum, manyan taro, da taron gunduma. Mu yi amfani da waɗannan taron mu ƙarfafa juna a bautar gaskiya ta Jehovah, wanda ya ba mu ‘gatar bauta masa ba tare da tsoro ba, cikin tsarki da adalci.’—Luka 1:74, 75; Ibraniyawa 10:24, 25.
20, 21. Ta yaya aka sakā ma Hannatu don ibadarta?
20 Jehovah ya lura da ibadar Hannatu kuma ya sakā mata a yalwace. A wani tafiyarsu na shekara shekara zuwa Shiloh, Hannatu da hawaye ta yi wa Allah addu’a sosai kuma ta yi wa’adi: “Ya Ubangiji mai-runduna, idan dai ka yarda ka dubi ƙuncin baiwarka, ka tuna da ni, ba ka kuwa manta da baiwarka ba, amma ka ba baiwarka ɗa namiji, ni ma sai in bada shi ga Ubangiji muddar ransa.” (1 Samu’ila 1:9-11) Allah ya ji roƙon Hannatu kuma ya albarkace ta da ɗa, wanda ta sa masa suna Sama’ila. Lokacin da ta yaye shi, ta kai shi Shiloh don ya yi hidima a mazauni.—1 Samu’ila 1:20, 24-28.
21 Hannatu ta nuna tana ƙaunar Allah kuma ta cika wa’adinta gare shi game da Sama’ila. Ka yi tunanin albarka mai yawa da ita da Elkannah suka more domin ɗansu ƙaunacacce ya yi hidima a mazaunin Jehovah! Iyaye Kiristoci da yawa suna da irin wannan farin ciki da albarka domin ’ya’yansu maza da mata suna hidima ta majagaba na cikakken lokaci, suna cikin iyalin Bethel, ko kuma a wasu hanyoyi suna ɗaukaka Jehovah.
Ka Ci Gaba da Sauraron Jehovah!
22, 23. (a) Menene za mu tabbata idan muka ci gaba da saurarar muryar Jehovah? (b) Menene za a bincika a talifi na gaba?
22 Menene za mu tabbata idan muka ci gaba da saurarar Jehovah? Za mu kasance da ruhaniya sosai idan mun nuna muna ƙaunar Allah da dukan zuciyarmu kuma muka cika ƙa’idodin keɓe kanmu gare shi. Idan biɗan irin wannan tafarki zai sa mu jimre gwaji mai tsanani, babu shakka albarkar Jehovah za ta tarar da mu—sau da yawa a hanyoyi da ba za mu yi tsammaninsu ba.—Zabura 37:4; Ibraniyawa 6:10.
23 Mutanen Allah za su samu albarka mai yawa a nan gaba. Don saurarar Jehovah cikin biyayya, za a kāre “taro mai-girma” a “babban tsanani” kuma za su more farin cikin rayuwa cikin sabuwar duniya ta Allah. (Ru’ya ta Yohanna 7:9-14; 2 Bitrus 3:13) A nan Jehovah zai cika muradi mai kyau na dukan mutanensa. (Zabura 145:16) Yadda talifi na gaba zai nuna, a yanzu ma waɗanda suke saurarar muryar Jehovah an albarkace su da ‘kyakkyawar baiwa da cikakkiyar kyauta daga bisa.’—Yaƙub 1:17.
[Hasiya]
a Furcin Hannatu yana da kamani da na budurwa Maryamu, da ta faɗa bayan ta san ita za ta zama uwar Almasihun.—Luka 1:46-55.
Ka Tuna?
• Menene tarihin Isra’ila zai iya koya mana game da albarkar Allah?
• Ta yaya Boaz da Nabal suka bambanta?
• Ta yaya za mu yi koyi da Hannatu?
• Me ya sa ya kamata mu ci gaba da saurarar muryar Jehovah?
[Hoto a shafi na 8]
Sarki Sulemanu ya yi addu’a don zuciya mai biyayya, kuma Jehovah ya albarkace shi da hikima
[Hoto a shafi na 10]
Boaz ya daraja wasu kuma ya yi musu alheri
[Hoto a shafi na 13]
An albarkaci Hannatu don ta dogara ga Jehovah