Ka Koyar Da Zuciyarka Ta Ji Tsoron Jehovah
“Da ma da wannan irin zuciya a cikinsu da za su ji tsorona, su kiyaye dukan dokokina kullum.”—KUBAWAR SHARI’A 5:29.
1. Me ya sa za mu tabbata cewa wata rana mutane za su more ’yanci daga tsoro?
TSORO ya kama mutane a ƙarnuka da yawa. Tsoron yunwa, cuta, yin laifi, ko kuma yaƙi ya ta da wa miliyoyin mutane hankali. Domin wannan gabatarwa Universal Declaration of Human Rights ya furta muradin kawo duniya inda dukan ’yan Adam za su more ’yanci daga tsoro.a Abin farin ciki, Allah da kansa ya tabbatar mana cewa irin wannan duniyar za ta zo—ko da yake ba daga ƙoƙarin mutane ba ne. Ta bakin annabinsa Mikah, Jehovah ya yi mana alkawari cewa a sabuwar duniyarsa ta adalci, ‘ba kuwa wani mai tsoratar da mutanensa ba.’—Mikah 4:4.
2. (a) Ta yaya Nassosi suka aririce mu mu ji tsoron Allah? (b) Waɗanne tambayoyi za su taso idan muka bincika wajibinmu mu ji tsoron Allah?
2 A wani ɓangare kuma, tsoro zai iya kasancewa abin kirki. A cikin Nassosi, an aririci bayin Allah a kai a kai su ji tsoron Jehovah. Musa ya gaya wa Isra’ilawa: “Za ka ji tsoron Ubangiji Allahnka; shi ne za ka bauta masa.” (Kubawar Shari’a 6:13) Ƙarnuka daga baya Sulemanu ya rubuta: “Ji tsoron Allah, ka kiyaye dokokinsa; gama wannan kaɗai ne wajibin mutum.” (Mai-Wa’azi 12:13) Ta wajen aikinmu na wa’azi, da ake yi a ƙarƙashin ja-gorar mala’iku, mu ma muna ariritar dukan mutane su ‘ji tsoron Allah, su ba shi daraja.’ (Ru’ya ta Yohanna 14:6, 7) Ƙari ga tsoron Jehovah, Kiristoci dole ne su ƙaunace shi da dukan zukatansu. (Matta 22:37, 38) Ta yaya za mu ji tsoron Allah kuma har ila mu ƙaunace shi? Me ya sa ya wajaba mu ji tsoron Allah mai ƙauna? Wane amfani muke samu daga koyon tsoro irin na ibada? Domin mu amsa waɗannan tambayoyin, dole ne da farko mu fahimci abin da tsoron Allah yake nufi kuma yadda irin wannan tsoron yake zama tushen dangantakarmu da Jehovah.
Fargaba, Girmamawa, da Tsoro
3. Menene tsoron Allah yake nufi?
3 Tsoron Allah yadda Kiristoci ya kamata su ji ne game da Mahaliccinsu. Bayanin wannan tsoron shi ne “fargaba da kuma girmama Mahalicci sosai tare da razana na baƙanta masa rai.” Saboda haka, tsoron Allah yana rinjayar ɓangarori biyu na rayuwarmu: halinmu ga Allah da kuma halinmu ga ayyuka da yake ƙyama. Babu shakka, duka suna da muhimmanci kuma sun cancanci mu bincika su a hankali. Kamar yadda Expository Dictionary of New Testament Words na Vine ya nuna, ga Kiristoci wannan tsoro na girmamawa ‘yana ja-gorar nufi a rayuwa, a batutuwa na ruhaniya da kuma na ɗabi’a.’
4. Ta yaya za mu koyi fargaba da kuma girmama Mahaliccinmu?
4 Ta yaya za mu koyi fargaba da kuma girmama Mahaliccinmu? Muna mamaki idan muka ga kyakkyawan fili, mafaɗar ruwa mai ban sha’awa, ko kuma faɗuwar rana mai kyan gani. Wannan mamakin sai ya ƙaru idan muka fahimci, da idanunmu na bangaskiya, Allah ne ya yi waɗannan ayyuka. Bugu da ƙari, kamar Sarki Dauda, sai mu fahimci ƙanƙancinmu idan aka gwada mu da halittu masu ban mamaki na Jehovah. “Sa’anda ina lura da sammanka, aikin yatsotsinka, wata kuma da taurari waɗanda ka sanya; wane abu ne mutum, da ka ke tuna da shi?” (Zabura 8:3, 4) Wannan fargaba mai tsanani take kai ga girmamawa, take motsa mu mu yi godiya kuma mu ɗaukaka Jehovah domin dukan abin da ya yi dominmu. Dauda kuma ya rubuta: “Zan yi godiya gareka; gama ƙirata abin ban tsoro ce, abin al’ajabi ce kuwa: ayyukanka suna da ban al’ajabi; wannan ma raina ya sani sarai.”—Zabura 139:14.
5. Me ya sa ya kamata mu ji tsoron Jehovah, kuma wane misali ne mai kyau muke da shi a wannan batu?
5 Fargaba da kuma girmamawa na kawo tsoron daraja na ikon Allah don shi ne Mahalicci kuma da ikonsa da ya dace na Mai Mallakar dukan halitta. A wahayi da manzo Yohanna ya gani, “waɗanda suka taho masu-nasara da bisan, da gunkinsa”—shafaffun mabiyan Kristi a matsayinsu a samaniya—suna shela: “Ayyukanka masu-girma ne, masu-ban al’ajabi, ya Ubangiji Allah, Mai-iko duka; halullukanka kuma masu-adalci ne, masu-gaskiya kuma, ya Sarkin zamanai. Wanene za ya rasa jin tsoro, ya rasa ɗaukaka sunanka, ya Ubangiji?” (Ru’ya ta Yohanna 15:2-4) Tsoron Allah, da ya zo daga girmamawa ƙwarai domin ɗaukakar, ya kai waɗannan abokan sarautar Kristi a Mulkinsa na samaniya su daraja Allah domin shi ne mai iko duka. Idan mun bincika dukan abin da Jehovah ya cim ma da kuma hanya ta adalci da yake shugabancin dukan halitta, muna da dalilai na jin tsoronsa ne?—Zabura 2:11; Irmiya 10:7.
6. Me ya sa ya kamata mu kasance da razana na kada mu baƙanta wa Jehovah rai?
6 Duk da haka, ƙari ga fargaba da girmamawa, tsoron Allah dole ya ƙunshi razana don kada a baƙanta masa rai ko kuma a yi masa rashin biyayya. Me ya sa? Domin ko da yake Jehovah “mai-alheri kuma, mai-jinkirin fushi,” dole ne mu tuna cewa ‘ba shi kuɓutar da mai-laifi ko kaɗan.’ (Fitowa 34:6, 7) Ko da yake mai ƙauna ne kuma mai jinƙai, Jehovah ba ya ƙyale rashin adalci da kuma laifi da gangan. (Zabura 5:4, 5; Habakkuk 1:13) Waɗanda suke yin abin da yake mugu a idanun Jehovah da gangan kuma ba sa tuba kuma waɗanda suke yin adawa da shi ba za su yi haka ba babu horo ba. Kamar yadda manzo Bulus ya ce, “abin ban tsoro ne a fāɗa cikin hannuwan Allah mai-rai.” Razana kada mu faɗa cikin irin wannan yanayin kāriya ce mai girma a gare mu.—Ibraniyawa 10:31.
“Ku Manne Masa”
7. Waɗanne dalilai muke da su na dogara ga ikon ceto na Jehovah?
7 Tsoron Allah na girmamawa da kuma sanin ikonsa mai ban fargaba su ne mafarin yarda da kuma dogara ga Jehovah. Kamar yadda yaro zai ji yana kāre idan ubansa na kusa, haka muke jin muna da kwanciyar hankali da kuma tabbaci cikin hannun Jehovah mai ja-gora. Ka lura da abin da Isra’ilawa suka yi bayan Jehovah ya fito da su daga ƙasar Masar: “Isra’ila kuma suka ga babban aikin da Ubangiji ya aika bisa Masarawa, mutanen kuwa suka ji tsoron Ubangiji: suka bada gaskiya ga Ubangiji.” (Fitowa 14:31) Abin da Elisha ya fuskanta ma ya tabbatar da haka ‘mala’ikan Ubangiji yana kafa sansani a kewaye da masu-tsoronsa, yana tsirar da su kuma.’ (Zabura 34:7; 2 Sarakuna 6:15-17) Tarihin zamani na mutanen Jehovah da kuma abin da kai kanka wataƙila ka fuskanta ya tabbatar da cewa Jehovah yana nuna ikonsa domin waɗanda suke bauta masa. (2 Labarbaru 16:9) Saboda mun zo ga fahimtar cewa, “cikin tsoron Ubangiji akwai sakankancewa mai-ƙarfi.”—Misalai 14:26.
8. (a) Me ya sa tsoron Allah yake motsa mu mu yi tafiya cikin hanyoyinsa? (b) Ka yi bayanin abin da ya sa ya kamata mu “manne” wa Jehovah.
8 Tsoron Allah ba kawai yana ƙarfafa yarda da kuma dogara a gare shi ba amma kuma yana motsa mu mu yi tafiya cikin hanyoyinsa. Sa’ad da Sulemanu ya keɓe haikali, ya yi addu’a ga Jehovah: “Domin [Isra’ila] su ji tsoronka, su yi tafiya cikin hanyarka, muddar ransu a cikin ƙasa wadda ka ba ubaninmu.” (2 Labarbaru 6:31) Da farko, Musa ya aririci Isra’ilawa: “Za ku bi Ubangiji Allahnku, ku ji tsoronsa, ku kiyaye dokokinsa, ku ji muryatasa, za ku bauta masa kuma, ku manne masa.” (Kubawar Shari’a 13:4) Kamar yadda wannan ayar ta nuna sarai, muradin tafiya cikin hanyoyin Jehovah da kuma “manne” masa yana zuwa ne daga yarda da kuma dogara ga Allah. Hakika, tsoro irin na ibada yana kai mu ga biyayya ga Jehovah, mu bauta masa, kuma mu manne masa, kamar yadda ɗan yaro a zahiri yake manne wa ubansa wanda ya yarda da shi kuma ya dogara a gare shi.—Zabura 63:8; Ishaya 41:13.
A Ƙaunaci Allah Yana Nufin a Ji Tsoronsa
9. Wace alaƙa ke tsakanin ƙauna da kuma tsoron Allah?
9 A ra’ayin Nassi, tsoron Allah bai hana ƙaunar Allah ba a kowacce hanya. Akasin haka, an umurci Isra’ilawa su ‘ji tsoron Ubangiji Allahnsu, su yi tafiya cikin dukan tafarkunsa, su ƙaunace shi.’ (Kubawar Shari’a 10:12) Saboda haka, tsoron Allah da ƙaunar Allah suna haɗe kusa. Tsoron Allah yana motsa mu mu yi tafiya cikin hanyoyinsa, kuma wannan yana tabbatar da ƙaunarmu gare shi. (1 Yohanna 5:3) Wannan daidai ne domin idan muna ƙaunar mutum, muna tsoron mu ɓata masa rai. Ta tawayensu, Isra’ilawa suka ɓata wa Jehovah rai a cikin daji. Babu shakka ba za mu so mu yi abin da zai baƙanta wa Ubanmu na samaniya rai ba. (Zabura 78:40, 41) A wani ɓangare kuma, tun da “Ubangiji yana jin daɗin waɗanda ke tsoronsa,” biyayyarmu da kuma bangaskiya suna faranta masa rai. (Zabura 147:11; Misalai 27:11) Ƙaunar Allah tana motsa mu mu faranta masa rai kuma tsoron Allah yana hana mu ɓata masa rai. Halayen, suna taimaka wa juna ne, ba saɓa wa juna suke yi ba.
10. Ta yaya Yesu ya nuna yana farin ciki a jin tsoron Jehovah?
10 Rayuwar Yesu Kristi ta ba da misali ƙwarai na yadda za mu ƙaunaci kuma har ila mu ji tsoron Allah. Game da Yesu, annabi Ishaya ya rubuta: “Ruhun Ubangiji za ya zauna bisansa, ruhun ilimi da na ganewa, ruhun shawara da iko, ruhun sani da na tsoron Ubangiji: jin daɗinsa kuma za ya kasance a cikin tsoron Ubangiji.” (Ishaya 11:2, 3) In ji wannan annabcin, ruhun Allah ya motsa Yesu ya ji tsoron Ubansa na samaniya. Ƙari ga haka, mun lura cewa tsoronsa, ya wuce kaya, tushen farin ciki ne. Yesu yana farin ciki wajen yin nufin Allah da kuma faranta masa rai, har a yanayi mai wuya ƙwarai. Lokacin da yake fuskantar mutuwa a gungumen azaba, ya gaya wa Jehovah: “Ba nawa nufi za a bi ba, sai naka.” (Matta 26:39) Domin tsoronsa na ibada, Jehovah ya amsa roƙonsa, ya ƙarfafa shi, kuma ya cece shi daga mutuwa.—Ibraniyawa 5:7.
Koya Jin Tsoron Jehovah
11, 12. (a) Me ya sa za mu koya mu ji tsoron Allah? (b) Ta yaya Yesu ya koya mana tsoron Jehovah?
11 Ba kamar mamaki da muke yi sa’ad da muka ga iko da kuma ɗaukakar abin da Allah ya halitta, tsoron Allah ba ya zuwa haka. Saboda haka ne Dauda Mafi Girma, Yesu Kristi, cikin annabci ya gayyace mu: “Ku zo, ku yara, ku kasa kunne gareni: ni koya muku tsoron Ubangiji.” (Zabura 34:11) Ta yaya za mu koya daga wurin Yesu tsoron Jehovah?
12 Yesu ya koya mana tsoron Jehovah ta wajen taimakonmu mu fahimci mutuntaka mai ban sha’awa na Ubanmu na samaniya. (Yohanna 1:18) Misalin Yesu ya nuna yadda Allah yake tunani da kuma yadda yake bi da wasu, domin Yesu ya nuna mutuntakar Ubansa daidai. (Yohanna 14:9, 10) Ƙari ga haka, ta wajen hadayar Yesu, mun samu hanyar zuwa ga Jehovah sa’ad da muka roƙi gafara domin zunubanmu. Wannan shahararren nuna jinƙai na Allah ma ƙaƙƙarfan dalili ne na jin tsoronsa. Mai Zabura ya rubuta: “Akwai gafara a wurinka, domin a ji tsoronka.”—Zabura 130:4.
13. Menene littafin Misalai ya zana daki-daki da zai taimake mu mu ji tsoron Jehovah?
13 Littafin Misalai ya zana daki-dakin abin da zai taimake mu mu koyi tsoro na ibada. “Ɗana, idan ka karɓi zantattukana, ka ɓoye dokokina a wurinka: har da za ka karkata kunnenka ga hikima, ka maida zuciyarka ga fahimi: I, idan ka nace bin ganewa, ka tada muryarka garin neman fahimi: . . . Sa’annan za ka gane tsoron Ubangiji, ka ruski sanin Allah.” (Misalai 2:1-5) Domin mu ji tsoron Allah, to, dole ne mu yi nazarin Kalmarsa, mu yi ƙoƙari mu fahimci umurnansa, sai kuma mu mai da hankalinmu sosai ga gargaɗinsa.
14. Ta yaya za mu bi umurni da aka bai wa sarakunan Isra’ila?
14 Kowanne sarki na Isra’ila ta dā an umurce shi ya Kofe Dokar kuma ya ‘riƙa karantawa daga cikin dukan kwanakin ransa: domin shi koya shi ji tsoron Ubangiji Allahnsa, shi kiyaye dukan zantattukan dokar.’ (Kubawar Shari’a 17:18, 19) Karatun Littafi Mai Tsarki da kuma nazari suna da muhimmanci a gare mu idan za mu koyi mu ji tsoron Jehovah. Sa’ad da muke yin amfani da mizanan Littafi Mai Tsarki a rayuwarmu, a hankali za mu samu hikima da kuma ilimi na Allah. Za mu zo ga ‘fahimtar tsoron Jehovah’ domin mun ga sakamako mai kyau da ya kawo a rayuwarmu, kuma za mu daraja dangantakarmu da Allah. Bugu kan ƙari, ta wajen taruwa a kai a kai da ’yan’uwa masu bi, manya da yara za su saurari koyarwa ta Allah, su koyi su ji tsoron Allah, kuma su yi tafiya cikin hanyoyinsa.—Kubawar Shari’a 31:12.
Mai Farin Ciki ne Duk Waɗanda Yake Tsoron Jehovah
15. A wace hanya ce tsoron Allah yake haɗe da bautarmu gare shi?
15 Daga abin da muka bari a baya, za mu ga cewa tsoron Allah hali ne mai kyau da dukanmu ya kamata mu koya, tun da tushen bautarmu ne ga Jehovah. Yana kai mu ga dogara ƙwarai a gare shi, mu yi tafiya cikin hanyoyinsa, kuma mu manne masa. Kamar yadda ya kasance hakika ga Yesu Kristi, tsoron Allah zai iya motsa mu mu cika alkawarin keɓe kanmu yanzu da kuma har abada abadin.
16. Me ya sa Jehovah ya ƙarfafa mu mu ji tsoronsa?
16 Tsoro irin na ibada ba firgita ba ce ko kuma ba ya ba da sukuni. “Mai-albarka ne kowane mutum mai-tsoron Ubangiji, mai-takawa cikin tafarkunsa,” yadda Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana. (Zabura 128:1) Jehovah ya ƙarfafa mu mu ji tsoronsa domin ya san cewa wannan halin zai kāre mu. Mun lura da damuwarsa ta ƙauna cikin kalmominsa ga Musa: “Da ma da wannan irin zuciya a cikinsu da za su ji tsorona, su kiyaye dukan dokokina kullum, domin su zauna lafiya, duk da ’ya’yansu har abada!”—Kubawar Shari’a 5:29.
17. (a) Wane amfani muke samu daga jin tsoron Allah? (b) Wane ɓangaren tsoro irin na ibada za mu bincika a talifi na gaba?
17 Hakazalika, idan muka koyar da zuciyarmu ta ji tsoron Allah, kome zai tafi daidai a garemu. A waɗanne hanyoyi? Na farko, irin wannan hali zai faranta wa Allah rai kuma zai sa mu kusace shi. Dauda ya sani daga abin da ya koya cewa ‘za ya biya muradin waɗanda ke tsoronsa; za ya kuma ji kukarsu, ya cece su.’ (Zabura 145:19) Na biyu, tsoro irin na ibada zai amfane mu domin zai taɓa halinmu game da abin da yake mugu. (Misalai 3:7) Talifi na gaba zai bincika yadda wannan tsoron zai kāre mu daga haɗari na ruhaniya, kuma zai maimaita misalai na mutane waɗanda suka ji tsoron Allah suka guje wa mugunta.
[Hasiya]
a Babban Taro na Majalisar Ɗinkin Duniya sun karɓi Universal Declaration of Human Rights a ranar 10 ga Disamba, 1948.
Za Ka Iya Amsa Waɗannan?
• Menene tsoron Allah yake nufi, kuma ta yaya ya shafe mu?
• Wace alaƙa ke tsakanin tsoron Allah da tafiya tare da shi?
• Ta yaya misalin Yesu ya nuna cewa tsoron Allah yana da alaƙa da ƙaunar Allah?
• A wace hanya ce za mu iya koyar da zuciyarmu ta ji tsoron Jehovah?
[Hoto a shafi na 23]
Sarakunan Isra’ilawa an umurce su su kofe Doka kuma su riƙa karatunta kowacce rana
[Hoto a shafi na 24]
Tsoron Jehovah yana kai mu ga dogara a gareshi kamar yadda yaro yake dogara ga ubansa
[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 21]
Stars: Photo by Malin, © IAC/RGO 1991