Haske Daga Allah Na Korar Duhu!
“Ubangiji kuma za ya haskaka duhuna.”—2 SAMU’ILA 22:29.
1. Ta yaya haske yake da alaƙa da rai?
“ALLAH ya ce, Bari haske shi kasance: haske kuwa ya kasance.” (Farawa 1:3) Da waɗannan kalmomi na musamman, labarin halitta da ke cikin Farawa ya nuna cewa Jehovah ne tushen haske, da ba tare da haske ba rayuwa a duniya ba za ta yiwu ba. Jehovah ne kuma tushen haske na ruhaniya, da yake da muhimmanci don ja-gorar hanyar rayuwarmu. (Zabura 43:3) Sarki Dauda ya nuna dangantaka ta kusa da ke tsakanin haske na ruhaniya da rai sa’ad da ya rubuta: “A wurinka maɓulɓular rai ta ke: a cikin haskenka za mu ga haske.”—Zabura 36:9.
2. Yadda Bulus ya nuna, haske yana alaƙa da menene?
2 Shekara 1,000 bayan lokacin Dauda, manzo Bulus ya yi maganar labarin halitta. Da yake rubuta wa ikilisiyar Kirista a Koranti, ya ce: “Allah ne, wanda ya ce, Haske daga cikin duhu za ya haskaka.” Sai Bulus ya nuna cewa haske na ruhaniya yana haɗe sosai da sanin Jehovah sa’ad da ya daɗa: “Ya haskaka cikin zukatanmu, domin a bada haske na sanin darajar Allah cikin fuskar Yesu Kristi.” (2 Korinthiyawa 4:6) Ta yaya wannan haske yake zuwa wurinmu?
Littafi Mai Tsarki —Mai Ba da Haske
3. Ta wurin Littafi Mai Tsarki, wane haske Jehovah ya yi tanadinsa?
3 Jehovah yana ba da haske na ruhaniya musamman ta hurariyar Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. Saboda haka, yayin da muke nazarin Littafi Mai Tsarki kuma muke samun ilimi daga Allah, muna barin haskensa ya haskaka wajenmu. Ta wurin Littafi Mai Tsarki, Jehovah yana ba da haske a kan nufe-nufensa kuma yana gaya mana yadda za mu yi nufinsa. Wannan yana ba da ma’ana ga rayuwarmu kuma yana taimaka a biya bukatunmu na ruhaniya. (Mai-Wa’azi 12:1; Matta 5:3) Yesu ya nanata cewa dole ne mu kula da bukatunmu na ruhaniya, sa’ad da ya ɗauko maganar Dokar Musa, ya ce: “An rubuta, ba da abinci kaɗai ba mutum za ya rayu, amma da kowace magana da ke fitowa daga bakin Allah.”—Matta 4:4; Kubawar Shari’a 8:3.
4. A wace hanya ce Yesu ne “hasken duniya”?
4 An san Yesu da haske na ruhaniya. Hakika, ya yi magana game da kansa shi “hasken duniya,” ya ce: “Wanda yana biyona ba za shi yi tafiya cikin duhu ba, amma za ya sami hasken rai.” (Yohanna 8:12) Wannan furcin ya taimaka mana mu fahimci aiki na musamman da Yesu yake da shi a idar da gaskiya ta Jehovah ga mutane. Idan za mu guji duhu kuma mu yi tafiya cikin hasken Allah, dole ne mu saurari dukan abin da Yesu ya faɗa kuma mu bi misalinsa da koyarwarsa yadda suke rubuce cikin Littafi Mai Tsarki.
5. Wane hakki mabiyan Yesu suke da shi bayan mutuwarsa?
5 Kwanaki kaɗan kafin mutuwarsa, Yesu ya nuna kansa haske ne shi, ya gaya wa almajiransa: “Haske yana wurinku tukuna da sauran jimawa kaɗan. Ku yi tafiya tun kuna da haske, domin kada duhu ya ci muku: wanda ya ke tafiya a cikin duhu ba ya san inda ya ke tafiya ba. Tun kuna da haske, ku bada gaskiya ga haske, domin ku zama ’ya’yan haske.” (Yohanna 12:35, 36) Waɗanda suka zama ’ya’yan haske sun koyi “sahihiyan kalmomi” na Littafi Mai Tsarki. (2 Timothawus 1:13, 14) Suna amfani da waɗannan sahihan kalmomi su jawo wasu masu zukatan kirki daga duhu zuwa cikin hasken Allah.
6. Wace gaskiya ce ta musamman game da haske da duhu muka samu a 1 Yohanna 1:5?
6 Manzo Yohanna ya rubuta: “Allah haske ne, a wurinsa kuwa babu duhu ko kaɗan.” (1 Yohanna 1:5) Ka lura da bambanci da ke tsakanin haske da duhu a nan. Haske na ruhaniya daga wurin Jehovah ne, amma ba za a haɗa shi da duhu na ruhaniya ba. To, daga waye ne duhu ya fito?
Tushen Duhu na Ruhaniya
7. Waye ne ke goyon bayan duhu na ruhaniya na duniya, wane tasiri yake da shi?
7 Manzo Bulus ya yi maganar “allah na wannan zamani.” Da wannan furci, yana nufin Shaiɗan Iblis. Ya ci gaba da cewa wannan “ya makantadda hankulan marasa-bada gaskiya, domin kada hasken bisharar darajar Kristi, wanda shi ke surar Allah, ya waye musu.” (2 Korinthiyawa 4:4) Mutane da yawa suna da’awar sun gaskata da Allah; duk da haka, cikinsu adadin waɗanda ba su gaskata da Iblis ba yana ƙaruwa. Me ya sa? Ba sa son su yarda cewa wani mugu, iko mai ƙarfi zai kasance kuma ya shafi yadda suke tunani. Amma, yadda Bulus ya nuna, Iblis yana wanzuwa, yana shafan mutane don kada su ga hasken gaskiya. An ga yadda ikon Shaiɗan ya shafi tunanin mutane a kwatanci na annabci game da shi “mai ruɗin dukan duniya.” (Ru’ya ta Yohanna 12:9) Sakamakon ayyukan Shaiɗan ne, yanayi da annabi Ishaya ya annabta ya shafi dukan mutane amma ban da waɗanda suke bauta wa Jehovah: “Duba, duhu za ya rufe duniya, baƙin duhu kuma za ya rufe al’ummai.”—Ishaya 60:2.
8. A waɗanne hanyoyi ne waɗanda suke cikin duhu na ruhaniya suke nuna cewa sun rikice?
8 A cikin baƙin duhu ba za ka ga kome ba. Yana da sauƙi mutum ya ɓata ko ya rikice. Hakanan ma, waɗanda suke cikin duhu na ruhaniya ba su da fahimta kuma ba da jimawa ba za su rikice a azanci na ruhaniya. Za su iya hasarar iyawarsu ta bambanta gaskiya daga ƙarya, nagarta da mugunta. Annabi Ishaya ya yi maganar waɗanda suke cikin irin wannan duhu sa’ad da ya rubuta: “Kaiton waɗannan da ke ce da mugunta nagarta; nagarta kuma mugunta su ke ce da ita; waɗanda su kan sa duhu maimakon haske, haske kuma maimakon duhu: su sa ɗaci madadin zaƙi, zaƙi kuma madadin ɗaci!” (Ishaya 5:20) Waɗanda suke zama cikin duhu na ruhaniya, allah na duhu ne Shaiɗan Iblis ke rinjayarsu, saboda haka suna ware daga tushen haske da kuma rai.—Afisawa 4:17-19.
Ƙalubalen Barin Duhu Zuwa Haske
9. Ka bayyana yadda masu laifi suke da dangantaka da duhu a zahiri da kuma a azanci na ruhaniya.
9 Ayuba mai aminci ya nuna dangantakar masu laifi da duhu na zahiri sa’ad da ya ce: “Mazinaci kuma ya kan zuba ido yana jiran assubahi, yana rufe fuskarsa, yana cewa; Babu idon da za ya gan ni.” (Ayuba 24:15) Masu aika laifi suna cikin duhu na ruhaniya, kuma irin wannan duhu yana iya zama da iko ƙwarai. Manzo Bulus ya ce lalata, sata, haɗama, maye, alfasha, da ƙwace sun zama ruwan dare tsakanin waɗanda suke cikin duhu. Amma kowanne da ya shigo cikin hasken Kalmar Allah zai iya canjawa. Bulus ya bayyana sarai cewa za a iya irin wannan canji a wasiƙarsa ga Korinthiyawa. Kiristocin Koranti da yawa suna ayyuka na duhu, amma Bulus ya gaya musu: “Amma aka wanke ku, amma aka tsarkake ku, amma aka baratadda ku cikin sunan Ubangiji Yesu Kristi, cikin Ruhun Allahnmu kuma.”—1 Korinthiyawa 6:9-11.
10, 11. Ta yaya Yesu ya girmama wani mutum da ya mai da wa ido? (b) Me ya sa mutane da yawa ba sa zaɓan haske?
10 Sa’ad da mutum ya fito daga baƙin duhu zuwa haske, zai ɗauki ɗan lokaci kafin idanunsa su daidaita da haske. A Baitsaida, Yesu ya warkar da wani makaho amma ya yi hakan da kaɗan kaɗan. “Ya kama hannun makaho, ya kawo shi daga bayan ƙauye; kuma ya yi ma idanunsa tofi, ya ɗibiya masa hannuwansa, kāna ya tambaye shi, Kana ganin kome? Ya duba bisa, ya ce, Ina duban mutane; gama ina ganinsu kamar itatuwa; suna yawo. Sa’annan ya sake ɗibiya hannuwa bisa idanunsa; shi ma ya kafa ido, aka warkadda shi, ya ga komi sarai.” (Markus 8:23-25) Hakika, Yesu ya mai da wa mutumin idanu a hankali domin mutumin ya iya daidaita kansa da hasken rana. Babu shakka mutumin ya yi farin ciki sosai sa’ad da ya ga gari.
11 Amma, farin cikin waɗanda aka taimaka musu su fito, a hankali daga duhu na ruhaniya zuwa hasken gaskiya ya fi farin cikin wannan mutumin. Yayin da muka ga farin cikinsu, za mu yi mamakin abin da ya sa hasken bai jawo ƙari ƙarin mutane da yawa ba. Yesu ya ba da dalilin: “Shari’a fa ke nan, haske ya zo cikin duniya, amma mutane suka fi son duhu da haske; domin ayyukansu miyagu ne. Gama kowanene wanda ya ke aika mugunta ƙin haske ya ke yi, kuma ba shi zuwa wurin haske, domin kada ayyukansa su tonu.” (Yohanna 3:19, 20) Hakika, mutane da yawa suna son ‘aikata mugunta’—kamar su lalata, zalunci, ƙarya, zamba, da sata—kuma duhu na ruhaniya na Shaiɗan wuri ne mai kyau sosai na yin yadda suke so.
Ci Gaba Cikin Haske
12. A waɗanne hanyoyi ne muka amfana a sanin haske?
12 Tun da muka zo ga sanin haske, waɗanne canje-canje muka gani game da mu kanmu? Wani lokaci yana da kyau mu tuna kuma mu bincika ci gaba da muka yi a ruhaniya. Waɗanne halaye muka daina da ba su da kyau? Wace matsala a rayuwarmu muka iya gyarawa? Ta yaya shirinmu don nan gaba ya canja? Cikin ƙarfin Jehovah da taimako na ruhunsa mai tsarki, za mu ci gaba da yin canje-canje a mutuntaka da yadda muke tunani da za su nuna muna saurarar hasken. (Afisawa 4:23, 24) Bulus ya furta shi haka: “Dā ku duhu ne, amma yanzu haske ne cikin Ubangiji: ku yi tafiya kamar ’ya’yan haske gama amfanin haske yana cikin dukan nagarta da adalci da gaskiya.” (Afisawa 5:8, 9) Barin hasken Jehovah ya yi mana ja-gora, yana ba mu bege mai ma’ana kuma na kyautata rayuwar waɗanda suke gewaye da mu. Kuma yin irin waɗannan canje-canje na faranta zuciyar Jehovah!—Misalai 27:11.
13. Ta yaya za mu nuna godiyarmu ga hasken Jehovah, me ake bukata don wannan tafarkin?
13 Muna nuna godiya don rayuwa ta farin cikin da muke morewa ta wajen nuna hasken Jehovah—gaya wa waɗanda suke cikin iyalinmu, abokai, da kuma maƙwabta abin da muka koya daga Littafi Mai Tsarki. (Matta 5:12-16; 24:14) Ga waɗanda suka ƙi su saurara, wa’azi da muke yi da tafarkin rayuwa na Kirista mai kyau zai zama abin gyara. Bulus ya yi bayani: “Kuna gwada abin da ke na yarda ga Ubangiji; kuma kada ku yi tarayya da ayyukan duhu marasa-amfani, amma har tone su za a yi.” (Afisawa 5:10, 11) Taimakon wasu su bar duhu su zaɓi haske ya bukaci gaba gaɗi a gare mu. Mafi muhimmanci, yana bukatar juyayi da damuwa game da wasu da son mu gaya musu hasken gaskiya don madawwamin amfaninsu daga zuciya.—Matta 28:19, 20.
Ka Mai da Hankali da Haske na Ƙarya!
14. Game da haske, wane kashedi ya kamata mu bi?
14 Ga waɗanda suke cikin teku daddare, kowane haske yana da kyau. Dā, ana saka wuta a kan tuddai na duwatsu a Ingila don a nuna inda za a samu mafaka daga hadari. Matuƙan jirgin ruwa suna godiya domin wannan wuta ya ja-gorance su zuwa matsayar jiragen teku. Amma wasu wutan tarko ne. Maimakon samun masauƙi, ana yaudarar jirage da yawa kuma suka lalace a bakin teku, inda ake satar kayansu. A wannan duniya mai ruɗu, dole ne mu mai da hankali kada a jawo mu zuwa hasken ƙarya da zai rinjaye mu zuwa haɗari na ruhaniya. An gaya mana, “Shaiɗan da kansa ya kan mayar da kansa kamar mala’ika na haske.” Hakanan, bayinsa, haɗe da ’yan ridda, “masu-ƙaryan manzanci” ne da suke “mayarda kansu masu-hidiman adalci.” Idan mun karɓi tunanin ƙarya na irin waɗannan, amincinmu ga Kalmar gaskiya ta Jehovah, Littafi Mai Tsarki, zai raunana kuma bangaskiyarmu za ta mutu.—2 Korinthiyawa 11:13-15; 1 Timothawus 1:19.
15. Menene zai taimake mu mu tsaya a kan hanya wadda ta nufa wajen rai?
15 Mai Zabura ya rubuta: “Maganarka fitila ce ga sawayena, haske ne kuma a tafarkina.” (Zabura 119:105) Hakika, Allahnmu mai ƙauna, Jehovah, “wanda ya ke nufi dukan mutane su tsira, kuma su kawo ga sanin gaskiya” ne ke haskaka ‘matsatsiyar hanya da ta nufa wajen rai.’ (Matta 7:14; 1 Timothawus 2:4) Yin amfani da umurnin Littafi Mai Tsarki zai hana mu fita daga matsatsiyar hanya zuwa cikin hanyar duhu. Bulus ya rubuta: “Kowane nassi hurare daga wurin Allah mai-amfani ne ga koyarwa, ga tsautawa, ga kwaɓewa, ga horo kuma da ke cikin adalci.” (2 Timothawus 3:16) Yayin da muke girma a ruhaniya, ana koyar da mu a Kalmar Allah. Za mu iya, ta wurin hasken Kalmar Allah, tsauta wa kanmu ko, idan da bukata makiyaya masu ƙauna cikin ikilisiya su tsauta mana. Hakanan, za mu iya daidaita al’amura kuma cikin tawali’u mu karɓi horo cikin adalci mu ci gaba da tafiya a kan hanyar rai.
Tafiya Cikin Haske da Godiya
16. Ta yaya za mu nuna godiya ga tanadin Jehovah na haske mai ban al’ajabi?
16 Ta yaya za mu nuna godiya don tanadin Jehovah na haske na ban al’ajabi? Yohanna sura 9 ta gaya mana cewa lokacin da Yesu ya warkar da mutum da aka haife shi makaho, mutumin ya yi godiya. Ta yaya? Ya ba da gaskiya ga Yesu Ɗan Allah kuma ya ambaci hakan a fili cewa “annabi” ne. Bugu da ƙari, ya yi magana da gaba gaɗi ga waɗanda suke ƙoƙari su kushe mu’ujizar Yesu. (Yohanna 9:17, 30-34) Manzo Bitrus ya kira waɗanda su shafaffu ne cikin ikilisiyar Kirista “jama’a abin mulki.” Me ya sa? Domin suna da halin godiya kamar mutum da aka haife shi makaho kuma aka warkar da shi. Suna nuna godiya ga Jehovah, Mai Amfane su, ta ‘sanar da mafifitan al’amura wanda ya kirawo su daga cikin duhu suka shiga maɗaukakin haskensa.’ (1 Bitrus 2:9; Kolossiyawa 1:13) Waɗanda suke da begen zama a duniya suna da irin wannan halin godiya, suna tallafa wa ’yan’uwansu shafaffu a sanar da “mafifitan al’amura” na Jehovah a fili. Lallai wannan gata ce mafi girma da Allah ya ba mutane ajizai!
17, 18. (a) Menene hakkin kowannenmu? (b) A yin koyi da Timothawus, menene aka ƙarfafa kowane Kirista ya guje wa?
17 Kasancewa da godiya daga zuciya don haske na gaskiya na da muhimmanci. Ka tuna, babu wani cikinmu da aka haifa da sanin gaskiya. Wasu sun koye ta bayan da suka girma, kuma nan da nan suka ga cewa haske ya fi duhu kyau. Wasu suna da gata mai girma da iyaye masu tsoron Allah ne suka yi renonsu. Ga irin waɗannan, da sauƙi ba za su ɗauki haske da muhimmanci ba. Wata Mashaidiya, wadda iyayenta suke bauta wa Jehovah kafin a haife ta, ta yarda cewa ya ɗauki lokaci mai yawa da ƙoƙari ta fahimci muhimmancin gaskiya da aka koya mata tun tana jaririya. (2 Timothawus 3:15) Yara ko manya, kowannenmu na bukatar mu yi godiya sosai don gaskiya da Jehovah ya bayyana.
18 Saurayi Timothawus an koya masa “littattafai masu-tsarki” tun yana jariri, amma sai kawai ta wajen mazakuta kansa a hidimarsa ya zama Kirista da ya manyanta. (2 Timothawus 3:15) Sai ya kasance a matsayi da ya taimaki manzo Bulus, wanda ya yi masa gargaɗi: “Ka yi ƙoƙari ka miƙa kanka yardaje ga Allah, ma’aikaci wanda babu dalilin kunya gareshi, kana rarrabe kalmar gaskiya sosai.” Bari dukanmu, kamar Timothawus, mu guje yin abu da zai sa mu kunya—ko sa Jehovah ya ji kunyarmu!—2 Timothawus 2:15.
19. (a) Kamar Dauda, menene dukanmu muke da dalilin mu faɗa? (b) Menene za a tattauna a talifi na gaba?
19 Muna da dalilai mu yabi Jehovah, wanda ya ba mu hasken gaskiyarsa. Kamar Sarki Dauda, mu ce: “Kai ne fitilata, ya Ubangiji, Ubangiji kuma za ya haskaka duhuna.” (2 Samu’ila 22:29) Duk da haka, kada mu kasance da halin ba ruwanmu, domin wannan zai sa mu koma mu faɗa cikin duhu da aka cece mu. Saboda haka, talifi na gaba zai taimaka mana mu bincika muhimmanci da muke bai wa gaskiya ta Allah a rayuwarmu.
Me Ka Koya?
• Ta yaya Jehovah ya yi tanadin wayewa ta ruhaniya?
• Wane ƙalubale ne duhu na ruhaniya da ya gewaye mu ke kawowa?
• Wane haɗari ne dole mu guje wa?
• Ta yaya za mu iya nuna godiyarmu ga haske na gaskiya?
[Hoto a shafi na 19]
Jehovah ne tushen haske na zahiri da na ruhaniya
[Hoto a shafi na 21]
Yadda Yesu ya warkar da makaho a hankali, yana taimaka mana mu fito daga duhu na ruhaniya
[Hoto a shafi na 22]
Ƙyale hasken ƙarya na Shaiɗan ya yaudare mu zai kawo haɗari na ruhaniya