Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 1/1 pp. 12-17
  • ‘Zai Kusace Ka’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Zai Kusace Ka’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Kyauta Daga Jehovah
  • “Ubangiji Yana Kiyayarda  Dukan Waɗanda Ke Ƙaunarsa”
  • Hanyar Kusantar “Mai-Jin Addu’a”
  • Jehovah Yana Sāka wa Bayinsa
  • ‘Ka Kusaci Allah’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Za Ka Iya ‘Kusantar Allah’ da Gaske Kuwa?
    Ka Kusaci Jehobah
  • Jehovah Yana Kula Da Kai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • ‘Ka Yi Kusa da Allah, Shi Kuwa Zai Yi Kusa da Kai’
    Ka Kusaci Jehobah
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 1/1 pp. 12-17

‘Zai Kusace Ka’

“[Allah] ba shi da nisa da kowane ɗayanmu ba.”—AYUKAN MANZANNI 17:27.

1, 2. (a) Sa’ad da muka ɗaga idanunmu muka kalli taurari, wace tambaya za mu yi game da Mahalicci? (b) Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa mutane suna da muhimmanci a idanun Jehovah?

KA TAƁA ɗaga idanunka cikin dare ka ga taurari kuma ka cika da mamaki? Yawan taurari da faɗin sarari na da ban mamaki. A wannan sararin samaniya mai girma, duniya ɗan ɗigo ne kawai. Wannan yana nufi ne cewa Mahalicci, “Maɗaukaki bisa dukan duniya,” yana da girma ainu da ba zai damu da mutane ba ko kuma yana da nisa ainun da ya fi gaban a san shi?—Zabura 83:18.

2 Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa mutane suna da muhimmanci a idanun Jehovah. Hakika, Kalmar Allah ta ƙarfafa mu mu neme shi, tana cewa: “Ba shi da nisa da kowane ɗayanmu ba.” (Ayukan Manzanni 17:27; 1 Labarbaru 28:9) Hakika, idan mun ɗauki matakai mu kusaci Allah, zai yi wa ƙoƙarinmu albarka. A wace hanya? Kalmomin jigon shekara ta 2003 sun ba da amsar nan mai daɗaɗa zuciya: ‘Zai kusace ku.’ (Yaƙub 4:8) Bari mu tattauna wasu albarka masu girma da Jehovah yake bai wa waɗanda suka kusace shi.

Kyauta Daga Jehovah

3. Wace kyauta ce Jehovah yake ba wa waɗanda suka kusace shi?

3 Na farko, bayin Jehovah suna da kyauta mai tamani da ya ajiye wa mutanensa. Dukan iko, dukiya, da ilimi da wannan zamani ke da shi ba sa iya ba da wannan kyautar ba. Kyauta ce da Jehovah yake bai wa waɗanda suka kusace shi. Mecece kyautar? Kalmar Allah ta amsa: “Idan . . . ka tada muryarka garin neman fahimi: Idan ka neme ta kamar azurfa, ka biɗe ta kamar da a ke biɗan ɓoyayyun dukiya: Sa’annan za ka gane tsoron Ubangiji, ka ruski sanin Allah. Gama Ubangiji yana bada hikima.” (Misalai 2:3-6) Ka yi tunani cewa mutane ajizai suna iya samun “sanin Allah”! Wannan kyautar—sanin da ake samu cikin Kalmar Allah—an gwada ta da “ɓoyayyun dukiya.” Me ya sa?

4, 5. Me ya sa za a kwatanta “sanin Allah” da “ɓoyayyun dukiya”? Ka ba da misali.

4 Abu ɗaya, sani na Allah yana da amfani mai girma. Albarkarsa mafi tamani ita ce begen rai madawwami. (Yohanna 17:3) Amma wannan sanin na kyautata rayuwarmu yanzu ma. Alal misali, domin nazarin Kalmar Allah sosai, mun san amsar tambayoyi masu muhimmanci kamar su: Menene sunan Allah? (Zabura 83:18) Yaya yanayin matattu yake da gaske? (Mai-Wa’azi 9:5, 10) Menene nufin Allah game da duniya da ’yan Adam? (Ishaya 45:18) Mun kuma zo ga sanin cewa hanyar rayuwa da ta fi kyau ita ce yin amfani da gargaɗin Littafi Mai Tsarki. (Ishaya 30:20, 21; 48:17, 18) Da haka, mun samu lafiyayyar ja-gora da ta taimaka mana mu jimre da alhini na rayuwa kuma mu biɗi hanyar rayuwa da ke kawo farin ciki da gamsuwa. Mafi muhimmanci, nazarin Kalmar Allah ya taimaka mana mu zo ga sanin halayen Jehovah masu ban al’ajabi kuma mu kusace shi. Menene ya fi dangataka ta kusa da Jehovah da ke da tushe da “sanin Allah” tamani?

5 Akwai wani dalilin da ya sa za a kwatanta sani na Allah da “ɓoyayyun dukiya.” Kamar dukiya da yawa, da ƙyar a gan ta a wannan duniya. A cikin mazauna biliyan shida na duniya, wasu miliyan shida masu bauta wa Jehovah, ko kuma misalin 1 cikin 1,000 sun sami “sanin Allah.” Domin a kwatanta yadda sanin gaskiyar Kalmar Allah take gata ce mai wuyar samu, ka yi la’akari da tambayar Littafi Mai Tsarki guda kawai: Menene yake faruwa da mutane bayan sun mutu? Daga Nassosi mun sani cewa kurwa tana mutuwa kuma matattu ba su san kome ba. (Ezekiel 18:4) Duk da haka, yawancin addinan duniya sun yi imanin ƙarya ta cewa wani abu cikin mutum yana ci gaba da rayuwa bayan mutum ya mutu. Sashen koyarwa ne na musamman na addinan Kiristendam. Haka yake a Buddhanci, Hindunci, Musulunci, Jaininci, Yahudanci, Shintunci, Sikhinci, da To’isanci. Ka yi tunani—an ruɗi mutane biliyoyi da wannan koyarwar ƙarya!

6, 7. (a) Su waye ne kawai za su iya samun “sanin Allah”? (b) Wane misali ne ya nuna cewa Jehovah ya ba mu fahimi da “masu-hikima masu-fahimi” da yawa ba su da shi?

6 Me ya sa ba mutane da yawa ba ne suka sami “sanin Allah.” Domin idan ba tare da taimakonsa ba, mutum ba zai iya fahimtar ma’anar Kalmar Allah ba. Ka tuna, wannan sanin kyauta ce. Jehovah yana ba wa waɗanda suke so su bincika Kalmarsa da gaske cikin tawali’u. Irin waɗannan mutane ƙila ba “masu-hikima . . . ga zancen jiki ba.” (1 Korinthiyawa 1:26) Ana iya ɗaukan da yawa cikinsu “mutane marasa-karatu” ne a mizanan duniya. (Ayukan Manzanni 4:13) Duk da haka, wannan ba abin damuwa ba ne. Jehovah yana yi mana albarka da “sanin Allah” domin halayen da ya gani a zuciyarmu.

7 Yi la’akari da wannan misali. Manazarta da yawa cikin Kiristendam sun buga littattafai game da Littafi Mai Tsarki. Irin waɗannan littattafan bincike za su iya ba da tarihi, da kuma ma’anar kalmomi na Ibrananci da na Helenanci, da sauransu. Duk da iliminsu, irin waɗannan manazarta sun sami “sanin Allah” ne da gaske? Sun fahimci jigon Littafi Mai Tsarki—kunita ikon mallakar Jehovah ta wurin Mulkinsa na samaniya? Sun sani cewa Jehovah Allah ba Allah-Uku-Cikin-Ɗaya ba ne? Mu muna da cikakken fahimi na wannan batun. Me ya sa? Jehovah ya ba mu fahimi wajen gaskiya ta ruhaniya da “masu-hikima da masu-fahimi” da yawa ba su da shi. (Matta 11:25) Lallai Jehovah yana yi wa waɗanda suka kusace shi albarka!

“Ubangiji Yana Kiyayarda  Dukan Waɗanda Ke Ƙaunarsa”

8, 9. (a) Yaya Dauda ya kwatanta wata albarka domin waɗanda suke kusa da Jehovah? (b) Me ya sa Kiristoci na gaskiya suke bukatar kāriya ta Allah?

8 Waɗanda suka kusaci Jehovah suna more wata albarka—kāriyar Allah. Mai Zabura Dauda, wanda ya ji da matsaloli da yawa, ya rubuta: “Ubangiji yana kusa da dukan waɗanda su ke kira bisa gareshi, ga dukan waɗanda su ke kira gareshi da gaskiya. Za ya biya muradin waɗanda ke tsoronsa; Za ya kuma ji kukansu, ya cece su. Ubangiji yana kiyayarda dukan waɗanda ke ƙaunarsa.” (Zabura 145:18-20) Hakika, Jehovah yana kusa da waɗanda suke ƙaunarsa da haka yana saurarar kukansu na taimako da sauri.

9 Me ya sa muke bukatar kāriyar Allah? Ƙari ga ji da sakamakon zama a waɗannan “miyagun zamanu,” Kiristoci na gaskiya su ne abin fako na babban Magabcin Jehovah, Shaiɗan Iblis. (2 Timothawus 3:1) Wannan magabci mai kissa ya yi niyya ya “cinye” mu. (1 Bitrus 5:8) Shaiɗan yana tsananta mana, yana matsa mana, kuma yana jaraba mu. Yana neman halaye na azanci da zuciya da zai yi amfani da su. Yana da nufi: ya raunana bangaskiyarmu kuma ya halaka ruhaniyarmu. (Ru’ya ta Yohanna 12:12, 17) Tun da muna fama da irin wannan abokin gaba mai ƙarfi, ba abin ƙarfafa ba ne mu sani cewa “Ubangiji yana kiyayarda dukan waɗanda ke ƙaunarsa”?

10. (a) Ta yaya Jehovah yake kāre mutanensa? (b) Wace kāriya ce ta fi muhimmanci, kuma me ya sa?

10 Amma, ta yaya Jehovah yake kāre mutanensa? Alkawarinsa na kāriya ba zai sa mu yi rayuwa da babu wahala a wannan zamani ba; ba ya kuwa nufin cewa wajibi ne ya yi mu’ujiza dominmu. Duk da haka, Jehovah yana ba da kāriya ta zahiri wa rukunin mutanensa. Ballantana ma, ba zai taɓa ƙyale Iblis ya shafe masu bauta ta gaskiya daga duniya ba! (2 Bitrus 2:9) Musamman ma, Jehovah yana kāre mu a ruhaniya. Yana shirya mu da abin da muke bukata mu jimre gwaji kuma mu kāre dangantakarmu da shi. A ƙarshe, kāriya ta ruhaniya ita ce ta fi muhimmanci. Me ya sa? Muddin muna da dangantaka da Jehovah, babu abin da zai iya yi mana lahani na dindindin—har ma mutuwa.—Matta 10:28.

11. Wane tanadi Jehovah ya yi don kāriya ta ruhaniya na mutanensa?

11 Jehovah ya yi tanadin abubuwa da yawa don kāriya ta ruhaniya na waɗanda suke kusa da shi. Ta wajen Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki, ya ba mu hikima da za mu bi da gwaji dabam dabam. (Yaƙub 1:2-5) Yin amfani da gargaɗi mai amfani da ke cikin Nassosi kāriya ce ma. Ban da wannan, Jehovah yana ba da “ruhu Mai-tsarki ga waɗanda suke roƙonsa?” (Luka 11:13) Wannan ruhun shi ne iko mafi ƙarfi a sararin samaniya, saboda haka za ta iya shirya mu mu bi da kowane gwaji ko jaraba da za mu fuskanta. Ta wajen Kristi, Jehovah ya ba da “kyauta ga mutane.” (Afisawa 4:8) Waɗannan mutane ƙwararru a ruhaniya suna ƙoƙari su nuna juyayi mai zurfi na Jehovah sa’ad da suka taimaka wa ’yan’uwa masu bi.—Yaƙub 5:14, 15.

12, 13. (a) Ta yaya Jehovah yake ba mu abinci na ruhaniya a lotonsa? (b) Yaya kake ji game da tanadin Jehovah don lafiyarmu ta ruhaniya?

12 Jehovah yana tanadin wani abu don ya kāre mu: abinci na ruhaniya a lotonsa. (Matta 24:45) Ta wurin littattafai da aka buga haɗe da jaridun Hasumiyar Tsaro da na Awake!, da kuma taro, babban taro, taron gunduma, Jehovah yana ba mu abin da muke bukata sa’ad da muke bukatarta. Ka tuna lokacin da ka ji wani abu a taron Kirista, babban taro, ko taron gunduma da ya taɓa zuciyarka, ya ƙarfafa ka ko kuma ya yi maka ta’aziyya? Ka taɓa karanta wani talifi a jaridu da aka ambata a baya kuma ka ji kamar dominka aka rubuta?

13 Ɗaya cikin abubuwan da Shaiɗan ya fi amfani da ita kasala ce, kuma ba a kāre muke ba daga lahaninta. Ya sani cewa kasancewa cikin yanayi mai ban tausayi na dogon lokaci zai ci ƙarfinmu, ya sa mu faɗi. (Misalai 24:10) Domin Shaiɗan yana ƙoƙari ya yi amfani da inda muka kasala, muna bukatar taimako. Jaridun Hasumiyar Tsaro da Awake! wani lokaci na ɗauke da talifofi da ke taimaka mana mu yaƙi kasala. Game da irin wannan talifi, wata ’yar’uwa Kirista ta rubuta: “Ina karanta talifin kusan kowacce rana, kuma hawaye har ila suna zuba daga idanuna. Na ajiye kusa da gadona don in riƙa karanta shi duk lokacin da na ji na kasala. Ta wajen talifofi kamar wannan, ina jin Jehovah yana runguma ta da hannunsa na kāriya.”a Ba mu gode wa Jehovah ba ne da yake ba mu abinci na ruhaniya a kan kari? Ka tuna, tanadinsa don lafiyarmu ta ruhaniya tabbaci ne cewa yana kusa da mu kuma muna ƙarƙashin kāriyarsa.

Hanyar Kusantar “Mai-Jin Addu’a”

14, 15. (a) Wace albarka Jehovah ya bai wa waɗanda suka yi kusa da shi? (b) Me ya sa ’yancin kusantar Jehovah cikin addu’a baiwa ce mai girma?

14 Ka lura cewa sa’ad da mutane suka samu iko, waɗanda suke ƙarƙashinsu ba sa kusa da su? Jehovah Allah kuma fa? Ya yi nisa ainun ya ji furci da mutane suke yi ne? A’a! Kyautar addu’a albarka ce da Jehovah ya bai wa waɗanda suke kusa da shi. Da yake an ba mu ’yancin kusantar “mai-jin addu’a” wannan baiwa ce mai girma. (Zabura 65:2) Me ya sa?

15 Alal misali: Shugaban wani kamfani yana da hakki da yawa. Ya tsai da shawarar abubuwa da zai yi da kansa da waɗanda zai ba wasu su yi. Haka nan ma, Mamallakin dukan halitta yana da ikon zaɓan al’amura da zai sa hannu da kuma wanda zai ba wasu. Ka yi la’akari da dukan abin da Jehovah ya ba ƙaunataccen Ɗansa, Yesu. An ba Ɗan “iko da za shi hukunta shari’a.” (Yohanna 5:27) An sarayar da mala’iku “ƙarƙashinsa.” (1 Bitrus 3:22) An ba Yesu ikon ruhu mai tsarki na Jehovah ya taimake shi ya ja-goranci almajiransa a duniya. (Yohanna 15:26; 16:7) Saboda haka, Yesu ya ce: “Dukan hukunci a cikin sama da ƙasa an bayar gareni.” (Matta 28:18) Duk da haka, in ya zo ga addu’armu, Jehovah ya zaɓa ya sa kansa. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya gaya mana mu yi addu’armu ga Jehovah kaɗai, mu yi haka cikin sunan Yesu.—Zabura 69:13; Yohanna 14:6, 13.

16. Me ya sa za mu kasance da tabbaci cewa Jehovah yana jin addu’a?

16 Jehovah yana saurarar addu’armu kuwa? Idan ba ya damuwa da mu, ba zai aririce mu mu “lizima cikin addu’a” ko kuma mu zuba damuwarmu da alhininmu a hannunsa ba. (Romawa 12:12; Zabura 55:22; 1 Bitrus 5:7) Bayi masu aminci a lokatan Littafi Mai Tsarki suna da cikakken tabbaci cewa Jehovah yana jin addu’a. (1 Yohanna 5:14) Saboda haka, mai zabura Dauda ya ce: “[Jehovah] ya kuwa ji muryata.” (Zabura 55:17) Mu ma muna da kyakkyawar dalili mu kasance da gaba gaɗi cewa Jehovah yana kusa, yana shirye ya ji kowacce damuwarmu da alhini.

Jehovah Yana Sāka wa Bayinsa

17, 18. (a) Yaya Jehovah yake ɗaukan hidima da aminci da halittunsa masu basira suke yi? (b) Ka ba da bayanin yadda Misalai 19:17 ta nuna cewa Jehovah yana lura da ayyukanmu na jinƙai.

17 Abin da mutane suka yi ko suka ƙi su yi bai shafi matsayin Jehovah na Mamallakin Dukan Halitta ba. Duk da haka, Jehovah, Allah ne da yake a shirye ya nuna godiyarsa. Hakika, yana daraja—kuma yana son hidima da aminci da halittunsa masu basira suke yi. (Zabura 147:11) Wannan shi ne wani amfani da waɗanda suka yi kusa da Jehovah suke morewa: Yana saka wa bayinsa.—Ibraniyawa 11:6.

18 Littafi Mai Tsarki ya nuna sarai cewa Jehovah yana daraja abin da bayinsa suke yi. Alal misali, mun karanta: “Mai-jin tausayin fakirai yana bada rance ga Ubangiji, kuma za ya sāka masa da alherinsa.” (Misalai 19:17) Yadda Jehovah yake la’akari da matalauta cikin jinƙai an nuna a cikin Dokar Musa. (Leviticus 14:21; 19:15) Yaya Jehovah yake ji sa’anda muka yi koyi da jinƙansa a yadda muke bi da matalauta? Sa’ad da muka bai wa matalauta abu, ban da zaton za su biya mu ba, Jehovah yana ɗaukan wannan rance muka ba shi. Jehovah ya yi alkawari zai biya wannan bashi da alheri da albarka. (Misalai 10:22; Matta 6:3, 4; Luka 14:12-14) Hakika, sa’ad da muka nuna juyayi ga ’yan’uwa masu bi da suke da bukata, yana taɓa zuciyar Jehovah. Muna farin cikin sanin cewa Ubanmu na samaniya yana lura da ayyukanmu na jinƙai!—Matta 5:7.

19. (a) Me ya sa za mu tabbata cewa Jehovah yana daraja abin da muke yi a aikin wa’azi da almajirantarwa? (b) Ta yaya Jehovah yake saka wa ayyukan hidima da aka yi wajen tallafa wa Mulkinsa?

19 Jehovah musamman yana daraja abin da muke yi domin Mulkinsa. Sa’ad da muka yi kusa da Jehovah, muna son mu yi amfani da lokacinmu, kuzari, da kuma dukiya mu saka hannu yadda zai yiwu a aikin wa’azin Mulki da almajirantarwa. (Matta 28:19, 20) Wani lokaci, za mu ji cewa abin da muke cim ma bai taka kara ya karya ba. Zuciyarmu ajiza za ta iya sa mu damu ko Jehovah yana farin ciki da ƙoƙarin da muke yi. (1 Yohanna 3:19, 20) Amma Jehovah yana ɗaukan kowacce kyauta da tamani komen ƙanƙantarta da ta fito daga zuciya da ƙauna ce ta motsa ta. (Markus 12:41-44) Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa: “Allah ba marar-adalci ba ne da za shi manta da aikinku da ƙauna wadda kuka nuna ga sunansa.” (Ibraniyawa 6:10) Hakika, Jehovah yana tunawa kuma yana saka wa ayyukan hidima mafi ƙanƙanta da aka yi don tallafa wa Mulkinsa. Ƙari ga albarka ta ruhaniya mai yawa a yanzu, za mu saurari farin ciki na rayuwa a sabuwar duniya, inda Jehovah zai buɗe hannunsa ya cika sha’awoyi na adalci na dukan waɗanda suka kusace shi!—Zabura 145:16; 2 Bitrus 3:13.

20. A cikin shekara ta 2003, ta yaya za mu riƙa tuna da kalmomin jigonmu na shekara, kuma wane sakamako hakan zai kawo?

20 A cikin shekara ta 2003, mu tambayi kanmu ko muna ci gaba da ƙoƙari mu kusaci Ubanmu na samaniya. Idan muna yin haka, za mu tabbata cewa zai yi yadda ya yi alkawari. Ballantana, “Allah . . . ba shi iya yin ƙarya.” (Titus 1:2) Idan ka kusace shi, zai kusace ka. (Yaƙub 4:8) Kuma me zai zama sakamakon haka? Albarka mai yawa yanzu da begen matsawa kusa da Jehovah a dukan fil azal!

[Hasiya]

a Magana game da talifin nan ne “Jehovah Ya Fi Zuciyarmu Girma” Hasumiyar Tsaro fitar 1 ga Mayu, 2000 shafofi 28-31 a Turanci.

Ka Tuna?

• Wace kyauta ce Jehovah yake bai wa waɗanda suke kusa da shi?

• Wane tanadi Jehovah ya yi don kāriya ta ruhaniya na mutanensa?

• Me ya sa ’yancin addu’a ga Jehovah baiwa ce mai girma?

• Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehovah yana godiya da hidima ta aminci da halittunsa masu basira suke yi?

[Hoto a shafi na 13]

Jehovah ya yi mana albarka da fahimi na gaskiya ta ruhaniya

[Hotuna a shafuffuka na 14, 15]

Jehovah yana tanadin kāriya ta ruhaniya

[Hoto a shafi na 17]

Jehovah yana kusa, a shirye ya saurara ga kowacce addu’armu

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba