Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 1/1 pp. 27-32
  • “Ku Yi Tsaro”!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ku Yi Tsaro”!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Ku Yi Tsaro, Ku Tsaya da Ƙarfi”
  • Manzanni Uku da Ba Su Iya Yin Tsaro Ba
  • Muhimman Halaye Uku
  • “Riƙe Abin da Ka Ke da Shi da Kyau”
  • Me Ya Sa Ya Wajaba Mu Ci Gaba da ‘Yin Tsaro’?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • “Ku Zauna A Faɗake”—Lokacin Hukunci Ya Yi!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • ‘Ku Ci Gaba Da Yin Tsaro’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ka Kasance A Shirye Domin Ranar Jehovah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 1/1 pp. 27-32

“Ku Yi Tsaro”!

“Abin da ni ke ce muku ina ce ma duka, Ku yi tsaro.”—MARKUS 13:37.

1, 2. (a) Wane darasi ne wani mutum ya koya game da gadin kayansa? (b) Me muka koya daga misalin da Yesu ya bayar game da ɓarawo a batun yin tsaro?

JUAN ya yi ajiyar kayansa masu tamani a gida. Ya ajiye su a ƙarƙashin gado—a tsammaninsa ba za a iya sace su ba a wannan wajen a gidansa. Amma, wata rana cikin dare sa’ad da shi da matarsa suke barci, ɓarawo ya shiga ɗakin. A bayyane yake cewa ɓarawon ya san daidai inda za shi. Cikin sukuni ya kwashe dukan kayayyaki masu tamani da suke ƙarƙashin gadon har da kuɗin da Juan ya ajiye cikin wata darowa na teburin da ke kusa da gadon. Washegari, Juan ya ga satar da aka yi masa. Zai daɗe yana tuna darasin da ya koya daga wannan: Mutumin da yake barci ba zai iya gadin kayansa ba.

2 Haka wannan yake a ruhaniya. Ba za mu iya tsare begenmu da kuma bangaskiyarmu ba idan mun yi barci a ruhaniya. Saboda haka, Bulus ya yi gargaɗi: “Kada fa mu yi barci, kamar sauran mutane, amma mu yi zamanmu ba barci ba maye.” (1 Tassalunikawa 5:6) Yesu ya yi amfani da misalin ɓarawo domin ya nuna muhimmancin kasancewa a faɗake. Ya kwatanta aukuwa da zai kammala sa’ad da ya zo zuwan Alƙali, sai ya yi kashedi: “Ku yi tsaro fa: gama ba ku sani ba cikin ko wace rana Ubangijinku ke zuwa. Amma ku san wannan, da ubangijin gida ya san cikin ko wane tsaro ɓarawo ke zuwa, da ya yi tsaro, da ba ya bari a huda masa gida ba. Ku fa ku zama da shiri: gama cikin sa’an da ba ku sa tsammani ba Ɗan mutum yana zuwa.” (Matta 24:42-44) Ɓarawo ba ya sanar da lokacin da zai zo. Nufinsa ne ya isa lokacin da ba wanda ke tsammaninsa. Haka nan, ƙarshen wannan zamanin zai zo a ‘sa’a da ba mu yi tsammani ba’ kamar yadda Yesu ya ce.

“Ku Yi Tsaro, Ku Tsaya da Ƙarfi”

3. Ta yaya yadda Yesu ya yi amfani da misalin bayi da suke jirar uban ɗakinsu ya dawo daga bikin aure ya nuna muhimmancin kasancewa a faɗake?

3 A cikin kalmomin da ke labarin Lingilar Luka, Yesu ya kwatanta Kiristoci da bayi da suke jirar uban gidansu ya dawo daga bikin aure. Suna bukatar su yi tsaro saboda sa’ad da ya dawo suna a faɗake su marabce shi. Saboda haka ne Yesu ya ce: “Cikin sa’a da ba ku sa tsammani ba, Ɗan mutum yana zuwa.” (Luka 12:40) Wasu da sun bauta wa Jehovah na shekaru da yawa za su iya sanyin jiki game da azancin gaggawa na lokatai da muke ciki. Suna iya kammala cewa ƙarshen yana can gaba da nisa. Hakika irin tunanin nan zai iya sa mu juya hankali daga abubuwa na ruhaniya zuwa abin duniya, abubuwan kwashe hankali da za su sa mu yi gyangyaɗi a ruhaniyarmu.—Luka 8:14; 21:34, 35.

4. Wane tabbaci ne zai motsa mu mu yi tsaro, kuma ta yaya Yesu ya nuna wannan?

4 Za mu iya samun wani darasi daga misalin Yesu kuma. Ko da yake bayin ba su san sa’ar da uban ɗakinsu zai dawo ba, sun san dai a daren zai zo. Zai yi wuya su kasance a faɗake duk dare idan suka yi tunanin cewa uban ɗakinsu zai dawo cikin wani dare ne dabam. Amma sun san daren da zai dawo, kuma wannan ya ba su dalili na kasancewa a faɗake. A wata hanya makamancinta, annabcin Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa muna cikin kwanaki na ƙarshe; amma ba su gaya mana rana ko kuma sa’a ta ƙarshe ba. (Matta 24:36) Imaninmu a kan cewa ƙarshen yana zuwa yana taimakonmu mu kasance a faɗake, amma idan mun tabbata cewa da gaske ne ranar Jehovah ta kusa, za mu samu dalili mai ƙarfi na yin tsaro.—Zephaniah 1:14.

5. Ta yaya za mu yi game da gargaɗin Bulus mu “yi tsaro”?

5 Da Bulus ya rubuta wa Korantiyawa wasiƙa, ya aririce su: “Ku yi tsaro, ku tsaya da ƙarfi cikin imani.” (1 Korinthiyawa 16:13) Hakika, yin tsaro yana haɗe da kasancewa da ƙarfi cikin imanin Kirista. Ta yaya za mu iya yin tsaro? Ta samun sani mai zurfi na Kalmar Allah. (2 Timothawus 3:14, 15) Hali mai kyau na nazari da kuma na halartan taro a kai a kai zai taimaka a ƙarfafa bangaskiyarmu da kuma tuna da ranar Jehovah muhimmin ɓangare ne na bangaskiyarmu. Saboda haka, idan lokaci-lokaci muna bincike tabbaci na Nassi cewa muna kusa da ƙarshen wannan zamanin zai taimake mu, ba za mu manta ba da muhimman gaskiya game da ƙarshen da ke zuwa.a Yana da kyau mu lura aukuwa da ke faruwa a duniya da suke cika annabcin Littafi Mai Tsarki. Wani ɗan’uwa a Jamus ya rubuta: “Duk lokacin da nake saurarar labarai—yaƙe-yaƙe, girgizar ƙasa, nuna ƙarfi, da kuma gurɓata mahalli—suna nanata mini cewa ƙarshe ya yi kusa.”

6. A wace hanya ce Yesu ya misalta yadda yake yiwuwa a manta da bukatar yin tsaro na ruhaniya da shigewar lokaci?

6 A Markus sura 13, da akwai wani labarin Yesu na gargaɗi ga mabiyansa su yi tsaro. Bisa ga wannan surar, Yesu ya kwatanta yanayinsu da na mai gadi da yake jirar uban ɗakinsa ya dawo daga tafiyarsa ƙasar waje. Mai gadin bai san sa’ar da uban ɗakinsa zai dawo ba. Amma yana bukatar ya ci gaba da yin tsaro. Yesu ya ambata sa’o’i dabam dabam da uban ɗakin zai iya dawowa. Sa’a ta huɗu tana somawa ne daga ƙarfe uku na asuba har fitowar rana. A lokacin sa’ar nan ta ƙarshe, yana da sauƙi mai gadin ya yi gyangyaɗi. Yadda aka ce, sojoji sun ga cewa sa’ar nan kafin wayewar gari shi ne lokaci mafi kyau na kama magabci ba tsammani. Haka nan kuma, a wannan lokaci na ƙarshe, da duniya da ta kewaye mu take share barci na ruhaniya, ya kamata mu dage mu yi tsaro. (Romawa 13:11, 12) Saboda haka, a cikin misalinsa, sau da yawa Yesu ya aririta: “Ku yi lura, ku yi tsaro, . . . Ku yi tsaro fa . . . Abin da ni ke ce muku ina ce ma duka, Ku yi tsaro.”—Markus 13:32-37.

7. Wane haɗari ne ke akwai da gaske, tunawa da wannan, wace ƙarfafa ce muke karantawa sau da yawa cikin Littafi Mai Tsarki?

7 Sau da yawa lokacin hidimarsa da kuma bayan tashinsa daga matattu, Yesu ya aririta a yi tsaro. Hakika, kusan duk lokacin da Nassi yake zancen ƙarshen zamanin nan, muna samun wannan faɗakar cewa mu kasance a faɗake ko kuma mu yi tsaro.b (Luka 12:38, 40; Ru’ya ta Yohanna 3:2; 16:14-16) A bayyane yake, gyangyaɗi a ruhaniya haɗari ne na gaske. Dukanmu na bukatar waɗannan gargaɗin!—1 Korinthiyawa 10:12; 1 Tassalunikawa 5:2, 6.

Manzanni Uku da Ba Su Iya Yin Tsaro Ba

8. A lambun Jathsaimani, menene manzannin Yesu uku suka yi game da roƙon da ya yi musu su yi tsaro?

8 Yin tsaro ya ƙunshi fiye da mutum yana da nagarin nufi kawai, yadda muka gani daga misalan Bitrus, Yaƙub, da kuma Yohanna. Waɗannan mutane uku masu ruhaniya ne, da sun bi Yesu da aminci kuma suna ƙaunarsa da gaske. Amma, a daren 14 ga Nisan na shekara ta 33 A.Z., sun kasa yin tsaro. Bayan sun fita daga ɗakin gidan bene da suka yi bikin Faskar, manzannin uku suka bi Yesu zuwa lambun Jathsaimani. A wurin, Yesu ya ce musu: “Raina ya yi baƙi ƙwarai, har ya kai ga mutuwa: ku zauna daganan, ku yi tsaro tare da ni.” (Matta 26:38) Sau uku Yesu ya yi addu’a daga zuci ga Ubansa a samaniya, kuma sau uku ya koma wurin abokansa, amma sai ya tarar suna barci.—Matta 26:40, 43, 45.

9. Me wataƙila ya sa manzanni suka yi gyangyaɗi?

9 Me ya sa waɗannan maza masu aminci suka kunyatar da Yesu a wannan daren? Wani dalili shi ne sun gaji. Dare ne, ƙila ma cikin dare, “idanunsu sun yi nauyi” da barci. (Matta 26:43) Duk da haka, Yesu ya ce: “Ku yi tsaro, ku yi addu’a, kada ku shiga cikin jarraba: ruhu lallai ya yarda, amma jiki rarrauna ne.”—Matta 26:41.

10, 11. (a) Duk da gajiyarsa, menene ya taimaki Yesu ya yi tsaro a lambun Jathsaimani? (b) Menene za mu koya daga abin da ya faru da manzanni uku lokacin da Yesu ya ce su yi tsaro?

10 Hakika, Yesu shi ma ya gaji a daren nan na musamman. Amma maimakon ya yi barci, ya ba da muhimman ’yan sa’o’in nan na ƙarshe cikin addu’a. ’Yan kwanaki kafin lokacin, ya aririce mabiyansa su yi addu’a, yana cewa: “Amma a kowane loto sai ku yi tsaro, kuna yin roƙo ku sami ikon da za ku tsere ma dukan waɗannan al’amuran da za su faru, ku tsaya kuma a gaban Ɗan mutum.” (Luka 21:36; Afisawa 6:18) Idan muka saurari gargaɗin Yesu kuma muka bi nagarin misalinsa a batun addu’a, roƙonmu daga zuci ga Jehovah zai taimake mu mu yi tsaro a ruhaniya.

11 Yesu ya fahimci—ko da yake almajiransa ba su fahimta ba lokacin—cewa za a tsare shi ba da daɗewa ba kuma a yi masa hukuncin kisa. Gwajinsa zai yi tsanani ƙwarai a kan gungumen azaba. Yesu ya faɗakar da manzanninsa game da waɗannan abubuwa, amma ba su fahimci abin da yake faɗa ba. Saboda haka, suka yi barci shi kuma yana faɗake yana addu’a. (Markus 14:27-31; Luka 22:15-18) Yadda yake ga manzannin, mu ma jikunanmu raunannu ne kuma akwai abubuwa da ba mu fahimta ba tukuna. Hakika, idan ba mu fahimci gaggawar lokacin da muke ciki ba, za mu iya yin barci a ruhaniya. Sai fa muna shirye za mu iya yin tsaro.

Muhimman Halaye Uku

12. Waɗanne halaye uku ne Bulus ya haɗa da mai da hankalinmu?

12 Ta yaya za mu riƙe halinmu na gaggawa? Mun riga mun ga muhimmancin addu’a da kuma bukatar tunawa da ranar Jehovah. Bugu da ƙari, Bulus ya ambaci muhimman halaye uku da ya kamata mu biɗa. Ya ce: “Da shi ke na rana ne mu, mu yi natsuwa, muna yafe da sulke na bangaskiya da ƙauna; kuma da bege na ceto, kwalkwali ke nan.” (1 Tassalunikawa 5:8) Bari mu yi la’akari da aikin bangaskiya, bege, da kuma ƙauna wajen kasancewa a faɗake a ruhaniya.

13. Wane matsayi bangaskiya take da shi a kasancewarmu a faɗake?

13 Dole ne mu kasance da bangaskiya mai ƙarfi cewa Jehovah yana nan kuma “shi mai-sākawa ne ga waɗanda ke biɗarsa.” (Ibraniyawa 11:6) Cikar farko na annabcin Yesu na ƙarni na farko game da ƙarshen yana ƙarfafa bangaskiyarmu a cikarsa mai girma a zamaninmu. Bangaskiyarmu ce take sa mu saurari ranar Jehovah, da tabbacin cewa “[wahayin annabci] lallai za ta zo, ba za ta yi jinkiri ba.”—Habakkuk 2:3.

14. Ta yaya bege yake da muhimmanci idan za mu kasance a faɗake?

14 Begenmu da ke da tabbaci da kama ‘anga ta rai’ da take taimakonmu mu jimre wa wahala ko idan yana bukatar mu jira wata cikar alkawarin Allah. (Ibraniyawa 6:18, 19) Margaret, wata ’yar’uwa ’yar shekara 90 shafaffiya, wadda ta yi baftisma shekaru 70 da suka shige, ta ce: “Lokacin da mijina ya mutu domin ciwon daji a shekara ta 1963, na ji kamar zai fi kyau idan ƙarshen ya zo da sauri. Amma yanzu na fahimci cewa ina tunanin son kaina ne lokacin. A lokacin ba mu san iyakar yadda aikin zai faɗaɗa ba a dukan duniya. Har yanzu ma, da akwai wuraren da yanzu ne aikin ya isa wurin. Domin haka ina godiya da Jehovah ya yi haƙuri.” Manzo Bulus ya tabbatar mana: “Haƙuri [tana kawo] gwadawa; gwadawa kuma, bege: bege kuma ba ya kunyatarwa.”—Romawa 5:3-5.

15. Yaya ne ƙauna za ta motsa mu ko da mun daɗe muna jira?

15 Ƙauna ta Kirista hali ne na musamman domin ita ce muhimmiyar dalilin dukan abin da muke yi. Muna bauta wa Jehovah domin muna ƙaunarsa, ko da yaya ma’ajin lokacinsa yake. Ƙaunar maƙwabci na motsa mu mu yi wa’azin bisharar Mulki, ko yaya ne Allah ya nufi mu daɗe muna yi kuma ko da sau nawa ne muke zuwa gidajen da muka saba zuwa. Kamar yadda Bulus ya rubuta, “bangaskiya, da bege, da ƙauna sun tabbata, su uku; amma mafi girmansu ƙauna ce.” (1 Korinthiyawa 13:13) Ƙauna tana taimaka mana mu jimre kuma tana taimaka mana mu kasance a faɗake. “[Ƙauna] tana kafa bege ga abu duka, tana daurewa da abu duka. Ƙauna ba ta ƙarewa daɗai.”—1 Korinthiyawa 13:7, 8.

“Riƙe Abin da Ka Ke da Shi da Kyau”

16. Maimakon mu yi sanyin gwiwa, wane hali ya kamata mu biɗa?

16 Muna zama ne a lokatai da abubuwa da suke faruwa a duniya suna tuna mana cewa muna cikin kammala kwanaki na ƙarshe. (2 Timothawus 3:1-5) Yanzu ba lokaci ba ne da za mu yi sanyin jiki amma mu ‘ci gaba da riƙe abin da muke da shi da kyau.’ (Ru’ya ta Yohanna 3:11) Ta wurin kasancewa “rai shimfiɗe zuwa ga addu’a” da kuma biɗan bangaskiya, bege, da kuma ƙauna, muna nuna kanmu a shirye domin sa’a ta gwadi. (1 Bitrus 4:7) Muna da aikin Ubangiji da yawa da za mu yi. Idan muka shagala a yin ayyuka na ibada zai taimake mu kasancewa a faɗake sosai.—2 Bitrus 3:11.

17. (a) Me ya sa ba za mu yi sanyin gwiwa ba domin wasu kunya da muke sha? (Dubi akwati a shafi na 21.) (b) Ta yaya za mu yi koyi da Jehovah, kuma wace albarka ke jiran waɗanda suka yi?

17 Irmiya ya rubuta: “Ubangiji rabona ne, . . . zan fa sa begena gareshi. Ubangiji yana da alheri ga waɗanda ke sauraronsa, ga ran wanda ke biɗarsa. Abu mai-kyau ne mutum shi yi bege, shi saurari ceton Ubangiji a natse.” (Makoki 3:24-26) Wasu cikinmu suna jira na ɗan lokaci ne kawai. Wasu sun jira na shekaru da yawa su ga ceton Jehovah. Amma wannan lokacin jirar kaɗan ne idan aka gwada da dawwama da ke a nan gaba! (2 Korinthiyawa 4:16-18) Yayin da muke jiran ayanannen lokaci na Jehovah, za mu iya gina muhimman halaye na Kirista kuma mu taimaki wasu su yi amfani da wannan lokaci na haƙurin Jehovah kuma su amshi gaskiya. Bari dukanmu fa mu yi tsaro. Mu yi koyi da Jehovah mu kasance da haƙuri, muna godiya domin begen da ya ba mu. Yayin da muke ci gaba da kasancewa a faɗake, bari mu ci gaba da riƙe begen rai na har abada gam. Ta haka ne waɗannan alkawura za su cika a kanmu: “[Jehovah] za ya ɗaukake ka ka gaji ƙasar: lokacinda an datse miyagu, ka gani.”—Zabura 37:34.

[Hasiya]

a Zai kasance da taimako ƙwarai idan muka maimaita tabbaci guda shida da aka jera a shafofi 6-7, a Hasumiyar Tsaro fitar 1 ga Fabrairu, 2000, da suke nuna cewa muna rayuwa cikin “kwanaki na ƙarshe.”—2 Timothawus 3:1.

b Da yake zance game da aikatau na Helenanci da aka fassara “yi tsaro,” mawallafin ƙamus W. E. Vine ya bayyana cewa a zahiri yana nufin ‘a kori barci,’ kuma “ba ya nufin a buɗe idanu kawai, amma a mai da hankali a kan abin da ake fako.”

Yaya Za Ka Amsa?

• Ta yaya za mu ƙarfafa tabbacinmu cewa ƙarshen wannan zamani ya kusa?

• Me za a iya koya daga misalan Bitrus, Yaƙub, da kuma Yohanna?

• Waɗanne halaye uku ne za su taimake mu mu ci gaba da kasancewa a faɗake a ruhaniya?

• Me ya sa wannan ne lokaci na ‘ci gaba da riƙe abin da muke da shi da kyau’?

[Box/Hoto a shafi na 31]

‘Mai Farin Ciki ne Wanda Yake Tsammani’—Daniel 12:12

Ka yi tunanin cewa mai gadi yana tsammanin ɓarawo yana neman ya shiga inda yake gadi. Idan dare ya yi, mai gadin zai kasa kunne ya ji motsin da zai sa ya san ko mai fashi yana neman shiga. Koyaushe yana kasa kunnensa yana duddubawa ko zai ga wani abu. Yana da sauƙi motsin wani abu ya ruɗe shi—iska da ke motsa ganyayen itatuwa ko kuma ƙyanwa da ta taka wani abu.—Luka 12:39, 40.

Makamancin wannan zai iya faru da waɗanda suke “jiran bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Kristi.” (1 Korinthiyawa 1:7) Manzannin sun yi tsammanin cewa Yesu zai ‘mai da mulkin ga Isra’ila’ nan da nan bayan tashinsa daga matattu. (Ayukan Manzanni 1:6) Shekaru da yawa daga baya, an tunasar da Kiristoci a Tassalunika cewa bayyanuwar Yesu a nan gaba ne. (2 Tassalunikawa 2:3, 8) Duk da haka, tsammanin da bai cika ba game da ranar Jehovah bai sa mabiyan Yesu na farko su bar tafarkin da ke kai wa ga rai ba.—Matta 7:13.

A zamaninmu, bai kamata yadda muke jin cewa zuwan ƙarshen wannan zamanin ta makara ya sa mu daina tsaro ba. Mai gadi da yake a shirye, motsin zai iya ruɗarsa, amma zai fi idan ya ci gaba da yin tsaro! Aikinsa ke nan. Haka ma yake ga Kiristoci.

[Hoto a shafi na 28]

Ka tabbata cewa ranar Jehovah ta yi kusa?

[Hotuna a shafi na 29]

Taro, addu’a, da kuma hali mai kyau na nazari za su taimake mu mu ci gaba da yin tsaro

[Hoto a shafi na 32]

Bari mu kasance da haƙuri kamar Margaret kuma mu ci gaba da yin tsaro sosai

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba