Me Ya Sa Za Mu Yi Addu’a Ba Fasawa?
“Ku yi addu’a ba fasawa; cikin kowanne abu a bada godiya.”—1 Tassalunikawa 5:17, 18.
1, 2. Ta yaya Daniel ya nuna cewa yana daraja gatar yin addu’a, kuma yaya wannan ya shafi dangantakarsa da Allah?
AL’ADAR annabi Daniel ne ya yi addu’a ga Allah sau uku a rana. Yana durƙusawa a tagar da ke gidansa, wadda take fuskantar birnin Urushalima, ya yi ta addu’arsa. (1 Sarakuna 8:46-49; Daniel 6:10) Ko sa’ad da aka ba da doka da ta hana addu’a ga kowa sai Dariyus, sarkin Midiya, Daniel bai daina addu’arsa ba ko na ɗan lokaci ma. Ko ransa yana cikin haɗari ko babu, wannan mutumi mai addu’a ya ci gaba da yi wa Jehovah addu’a ba fasawa.
2 Yaya Jehovah yake ganin Daniel? Sa’ad da mala’ika Jibra’ilu ya zo ya amsa ɗaya cikin addu’o’in Daniel, ya kwatanta annabin cewa “ƙaunatacce ne ƙwarai.” (Daniel 9:20-23) Cikin annabcin Ezekiel, Jehovah ya ce Daniel adali ne. (Ezekiel 14:14, 20) A zamaninsa, addu’o’in Daniel sun sa shi ya kasance da dangantaka ta kud da kud da Allahnsa, abin da Dariyus ma ya sani.—Daniel 6:16.
3. Yadda labarin wani mai wa’azi a ƙasashen waje ya nuna, yaya addu’a za ta taimake mu mu riƙe aminci?
3 Addu’a a kai a kai zai taimake mu mu jimre gwaji mai tsanani. Alal misali, ka yi la’akari da Harold King mai wa’azi a ƙasashen waje da yake Sin da aka tsare shi a kaɗaice na shekara biyar. Ɗan’uwa King ya ba da labarinsa haka: “Ana iya ware ni daga mutane, amma ba wanda zai iya ware ni daga Allah. . . . Saboda haka, ina durƙusawa sau uku a rana ina addu’a da murya, waɗanda suke wucewa suna iya ganina, ina tunawa da Daniel wanda Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da shi. . . . Kamar ruhun Allah ne ke ja-gorar zuciyata ga al’amura mafi amfani a lokatan nan kuma na sami kwanciyar rai. Lallai addu’a ta sa na sami ƙarfi na ruhaniya da ta’aziyya!”
4. Waɗanne tambayoyi game da addu’a za mu bincika a wannan talifin?
4 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku yi addu’a ba fasawa; cikin kowanne abu a bada godiya.” (1 Tassalunikawa 5:17, 18) Game da wannan gargaɗi, bari mu yi la’akari da tambayoyi na gaba: Me ya sa za mu mai da hankali ga addu’o’inmu? Waɗanne dalilai muke da su na kusantar Jehovah kullum? Me ya kamata mu yi idan muna ji ba mu cancanci yi wa Allah addu’a domin kasawarmu ba?
Ka Ƙulla Abota ta Wurin Addu’a
5. Wace abota ta musamman addu’a take taimakonmu mu more?
5 Za ka so Jehovah ya ce kai abokinsa ne? Haka ya faɗa game da uban iyali Ibrahim. (Ishaya 41:8; Yaƙub 2:23) Jehovah yana son mu ƙulla irin abotar nan da shi. Ya gayyace mu mu kusace shi. (Yaƙub 4:8) Bai kamata wannan gayya ta sa mu yi tunani sosai game da tanadi na musamman na addu’a ba? Yana da wuya ƙwarai a samu yin magana da wani babban ma’aikacin gwamnati, ballantana ma a zama abokinsa! Amma, Mahaliccin sararin halitta yana ƙarfafa mu mu kusace shi cikin addu’a, duk lokacin da muke so ko kuma muke bukatar yin haka. (Zabura 37:5) Yin addu’a ba fasawa na taimakonmu mu kasance da abota ta kusa da Jehovah.
6. Menene misalin Yesu ya koya mana game da bukatar yin “addu’a [kullum]”?
6 Amma yana da sauƙi mu ƙyale yin addu’a! Bi da matsi na rayuwar yau da kullum na iya janye hankalinmu da ba za mu yi ƙoƙarin yi wa Allah addu’a ba. Yesu ya ƙarfafa almajiransa su yi “addu’a [kullum],” shi ma ya yi haka. (Matta 26:41) Ko da yake ya taƙure daga safe zuwa dare, ya nemi lokaci ya yi magana da Ubansa na samaniya. A wasu lokatai kuma Yesu yakan tashi “da assusuba” domin ya yi addu’a. (Markus 1:35) A wasu lokatai kuma, yana zuwan wajen da babu kowa, bayan ya tashi aiki don ya yi magana da Jehovah. (Matta 14:23) Yesu kullum yana shirya lokacin yin addu’a, haka ya kamata mu yi mu ma.—1 Bitrus 2:21.
7. Waɗanne yanayi ya kamata ya motsa mu mu yi magana da Ubanmu na samaniya kullum?
7 Akwai lokatai da yawa da sun dace don yin addu’a na kanmu kowacce rana sa’ad da muke fuskantar matsaloli, gwaji, da kuma tsai da shawarwari. (Afisawa 6:18) Sa’ad da muka nemi ja-gorar Allah a dukan fannonin rayuwa, abutarmu da shi babu shakka za ta ƙaru. Idan abokai biyu suna kokawa da matsala tare, abutarsu ba za ta daɗa ƙarfi ba ne? (Misalai 17:17) Haka ma yake sa’ad da muka dogara ga Jehovah kuma sami taimakonsa.—2 Labarbaru 14:11.
8. Me muka koya game da tsawon addu’o’inmu a misalin Nehemiah, Yesu, da kuma Hannatu?
8 Abin farin ciki ne cewa Allah bai sa iyaka a yawan lokaci da za mu yi masa addu’a ba! Nehemiah ya yi sauri ya yi addu’a a zuciya kafin ya nemi izini daga sarkin Pasiya. (Nehemiah 2:4, 5) Yesu ma ya yi gajeriyar addu’a sa’ad da ya roƙi Allah ya ba shi iko ya ta da Li’azaru. (Yohanna 11:41, 42) Hannatu kuma ta “jima tana addu’a a gaban Ubangiji” sa’ad da take gaya masa dukan zuciyarta. (1 Samu’ila 1:12, 15, 16) Muna iya yin gajeriyar addu’a ko kuma doguwa yadda bukata da yanayi ya kama.
9. Me ya sa ya kamata addu’o’inmu su haɗa da yabo da godiya ga dukan abubuwa da Jehovah ke mana?
9 Addu’o’i da yawa cikin Littafi Mai Tsarki suna furta godiya ga mafificin matsayin Jehovah da kuma ayyukansa masu ban al’ajabi. (Fitowa 15:1-19; 1 Labarbaru 16:7-36; Zabura 145) A cikin wahayi, manzo Yohanna ya ga dattawa 24—cikakken adadin Kiristoci shafaffu a matsayinsu na samaniya—suna yabon Jehovah, cewa: “Kai ne mai-isa ka karɓi ɗaukaka da daraja da iko, ya Ubangijinmu da Allahnmu: gama kai ka halicci dukan abu, saboda nufinka kuma suka kasance, saboda nufinka aka halicce su.” (Ru’ya ta Yohanna 4:10, 11) Mu ma muna da dalili na yabon Mahalicci a kai a kai. Iyaye suna farin ciki sa’ad da yaronsu ya gode musu don abin da suka yi masa daga zuciya! Yin tunani a kan alherin Jehovah da furta godiyarmu dominsu hanya mai kyau ce ta kyautata addu’o’inmu.
Me Ya Sa Za a Yi “Addu’a ba Fasawa?”
10. Wane hakki addu’a take da shi a ƙarfafa bangaskiyarmu?
10 Addu’a a kai a kai tana da muhimmanci ga bangaskiyarmu. Bayan ya ba da misalin bukatar “a riƙa yin addu’a, kada a suma,” Yesu ya yi tambaya: “Sa’anda Ɗan mutum ya zo, za ya sami imani bisa duniya?” (Luka 18:1-8) Addu’a mai ma’ana daga zuciya tana ƙarfafa bangaskiya. Sa’ad da uban iyali Ibrahim yake tsufa kuma bai samu ɗa ba, ya gaya wa Allah batun. A amsawa, Jehovah ya ce masa ya dubi sama kuma ya ƙirga taurari, idan zai iya. Sai kuma Allah ya ba Ibrahim wannan tabbaci: “Hakanan zuriyarka za ta yi.” Menene sakamakon? Ibrahim “ya fa bada gaskiya ga Ubangiji; shi kuma ya lissafta wannan adalci ne gareshi.” (Farawa 15:5, 6) Idan mun gaya wa Jehovah zuciyarmu cikin addu’a, muka amince da tabbacinsa daga Littafi Mai Tsarki, muka yi masa biyayya, zai ƙarfafa bangaskiyarmu.
11. Ta yaya addu’a za ta taimake mu mu bi da matsaloli?
11 Addu’a ma za ta iya taimakonmu mu bi da matsalolinmu. Rayuwarka ta cika da damuwa kuma yanayinka mai wuyan jimrewa ne? Littafi Mai Tsarki ya gaya mana: “Ka zuba nawayarka bisa Ubangiji, shi kuma za ya agaje ka: Ba za ya yarda a jijjige masu-adalci ba daɗai.” (Zabura 55:22) Sa’ad da muke son mu tsai da shawara mai wuya, za mu iya koyi da misalin Yesu. Ya yi addu’a dukan dare kafin ya zaɓi manzanninsa 12. (Luka 6:12-16) Kuma daddare kafin ya mutu, Yesu ya yi addu’a sosai da “jiɓinsa kuma ya zama kamar manyan ɗararasa na jini, sun[a] fāɗuwa a ƙasa.” (Luka 22:44) Menene sakamakon? “Aka amsa masa kuma saboda tsoronsa mai-ibada.” (Ibraniyawa 5:7) Addu’o’inmu na ƙwarai ba fasawa za su taimake mu mu bi da matsaloli.
12. Ta yaya addu’a ta nuna yadda Jehovah yake damuwa da mu?
12 Wani dalili na matsa kusa da Jehovah ta wurin addu’a shi ne, shi ma ya matso kusa da mu. (Yaƙub 4:8) Sa’ad da muka gaya wa Jehovah zuciyarmu cikin addu’a, ba ma jin yana biyan bukatunmu kuma yana kulawa da kyau? Muna shaida ƙaunar Allah a hanya ta musamman. Jehovah bai ba kowa hakkin saurarar kowacce addu’a da bayinsu suke masa shi Ubansu na samaniya ba. (Zabura 66:19, 20; Luka 11:2) Kuma yana gayyatarmu mu ‘zuba dukan alhininmu a bisansa, domin yana kula da mu.’—1 Bitrus 5:6, 7.
13, 14. Waɗanne dalilai muke da su na yin addu’a ba fasawa?
13 Addu’a tana motsa mu mu daɗa himma a hidimar fage kuma tana ƙarfafa mu sa’ad da muke ji mu daina aikin don rashin son saƙon ko hamayya. (Ayukan Manzanni 4:23-31) Addu’a tana kuma kāre mu daga “dabarun Shaiɗan.” (Afisawa 6:11, 17, 18) Sa’ad da muke kokawa mu jimre da gwaji na kullum, za mu iya roƙon Allah ya ƙarfafa mu. Addu’ar misali ta Yesu ta haɗa da roƙon cewa Jehovah ya “cece mu daga Mugun,” Shaiɗan Iblis.—Matta 6:13.
14 Idan mun ci gaba da addu’a don taimako mu sarrafa halinmu na zunubi, za mu samu taimakon Jehovah. Muna da wannan tabbacin: “Allah mai-aminci ne, da ba za ya bari a yi muku jaraba wadda ta fi ƙarfinku ba; amma tare da jaraba za ya yi muku hanyar tsira, da za ku iya jimrewa.” (1 Korinthiyawa 10:13) Manzo Bulus shi ma ya shaida ƙarfafawar Jehovah a yanayi dabam dabam. Ya ce: “Na iya yin abu duka a cikin wannan da ya ke ƙarfafata.”—Filibbiyawa 4:13; 2 Korinthiyawa 11:23-29.
Ka Lizima Cikin Addu’a Duk da Kasawa
15. Menene zai iya faruwa sa’ad da halinmu ya kasa cika mizanan Allah?
15 Domin a ji addu’o’inmu dole mu amince da gargaɗin Kalmar Allah. Manzo Yohanna ya rubuta: “Dukan iyakar abin da mu ke roƙa kuma, muna karɓa daga wurinsa, domin muna kiyaye dokokinsa, muna yin abubuwa da sun gamshe shi.” (1 Yohanna 3:22) Amma me zai iya faruwa idan halinmu ya kasa cika mizanan Allah? Adamu da Hauwa’u sun ɓoye kansu bayan da suka yi zunubi a gonar Adnin. Mu ma za mu so mu ɓuya “daga fuskar Ubangiji” mu daina yin addu’a. (Farawa 3:8) Klaus mai kula mai ziyara da ya ƙware ya ce: “Na lura cewa mataki na farko da ba daidai ba da waɗanda suka bijire daga Jehovah da ƙungiyarsa suke bi shi ne suna daina yin addu’a.” (Ibraniyawa 2:1) Haka ya faru wa José Ángel. Ya ce: “Kusan shekara takwas, da kyar na yi addu’a ga Jehovah. Na ji ban cancanci na yi masa magana ko da har ila ina ɗaukansa Ubana na samaniya.”
16, 17. Ka ba da misalai yadda addu’a a kai a kai za ta taimake mu mu sha kan raunana ta ruhaniya.
16 Wasunmu za mu iya jin ba mu cancanci yin addu’a ba domin raunana ta ruhaniya ko kuma don mun yi wani laifi. Amma wannan ne musamman lokaci da muke bukatar yin amfani sosai da tanadin addu’a. Yunana ya gudu daga aikinsa. Amma cikin ‘ƙuncinsa Yunana ya kira ga Ubangiji. Ya kuwa amsa masa; daga cikin cikin Sheol Yunana ya yi kira, Jehovah kuwa ya ji muryarsa.’ (Yunana 2:2) Yunana ya yi addu’a, Jehovah ya amsa addu’arsa, kuma Yunana ya farfaɗo a ruhaniya.
17 José Ángel ma ya yi addu’a don taimako. Ya tuna: “Na gaya wa Allah zuciyata kuma na roƙe shi ya gafarce ni. Kuma da gaske ya taimake ni. Ban tsammani da na komo gaskiya ba ba tare da taimakon addu’a ba. Yanzu ina addu’a a kai a kai kowacce rana, kuma nakan yi fatan lokacin nan.” Ya kamata mu kasance a sake koyaushe mu gaya wa Allah game da kuskurenmu kuma cikin tawali’u mu nemi gafararsa. Sa’ad da Sarki Dauda ya faɗi laifinsa, Jehovah ya gafarta masa zunubansa. (Zabura 32:3-5) Jehovah yana son ya taimake mu, ba ya hukunta mu. (1 Yohanna 3:19, 20) Addu’o’in dattawan ikilisiya na iya taimakonmu a ruhaniya, irin waɗannan addu’o’i suna da “iko dayawa.”—Yaƙub 5:13-16.
18. Wane tabbaci bayin Allah suke da shi ko idan ma sun bijire?
18 Wane uba zai ƙi da ɗa wanda cikin tawali’u ya nemi taimako da shawara bayan ya yi kuskure? Almarar ɗa mubazzari ta nuna cewa ko yaya muka bijire, Ubanmu na samaniya yana farin ciki sa’ad da muka komo wurinsa. (Luka 15:21, 22, 32) Jehovah ya aririce dukan waɗanda suka bijire su yi addu’a gare shi, “gama za ya yi gafara a yalwace.” (Ishaya 55:6, 7) Ko da Dauda ya yi zunubai masu tsanani da yawa, ya yi addu’a ga Jehovah, yana cewa: “Ka kasa kunne ga addu’ata, ya Allah; Kada ka ɓuya ga roƙona.” Ya kuma ce: “Maraice da safiya da tsakiyar rana, zan kai ƙara, in yi nishi: [Jehovah] za ya kuwa ji muryata.” (Zabura 55:1, 17) Wannan yana tabbatarwa sosai!
19. Me ya sa bai kamata mu kammala cewa addu’o’i da kamar ba a amsa ba tabbacin rashin amincewar Allah ne ba?
19 Idan ba a amsa addu’armu nan da nan ba fa? Saboda haka, dole mu tabbata cewa roƙonmu ya jitu da nufin Jehovah kuma an yi roƙon cikin sunan Yesu. (Yohanna 16:23; 1 Yohanna 5:14) Almajiri Yaƙub ya yi maganar wasu Kiristoci waɗanda ba a amsa addu’o’insu ba domin suna “roƙa a karkace.” (Yaƙub 4:3) A wata sassa, bai kamata mu yi saurin kammala cewa addu’o’i da ba a amsa ba tabbacin rashin amincewar Allah ne. A wasu lokatai, Jehovah yana iya ƙyale masu bauta da aminci su ci gaba da addu’a game da wani batu na ɗan lokaci kafin ya amsa. Yesu ya ce: “Ku roƙa, za a ba ku.” (Matta 7:7) Saboda haka, muna bukata mu “lizima cikin addu’a.”—Romawa 12:12.
Ka Yi Addu’a a Kai a Kai
20, 21. (a) Me ya sa muke bukatar yin addu’a ba fasawa a waɗannan “kwanaki na ƙarshe”? (b) Menene za mu samu sa’ad da muka je gaban kursiyin Jehovah na alheri?
20 Matsi da matsaloli suna ƙaruwa a waɗannan “kwanaki na ƙarshe,” na “miyagun zamanu.” (2 Timothawus 3:1) Ba shi da wuya gwaji su taƙure zukatanmu ba. Addu’o’inmu ba fasawa za su taimake mu mu bi da rayuwarmu a tafarki na ruhaniya duk da nacewar matsaloli, gwaji, da sanyin gwiwa. Addu’o’inmu na kullum ga Jehovah na ba mu ƙarfi da muke bukata.
21 Jehovah “mai-jin addu’a,” bai shagala ba da ba zai iya jin mu ba. (Zabura 65:2) Kada mu shagala da ba za mu iya magana da shi ba. Abutarmu da Allah ita ce mallaka mafi tamani da muke da ita. Bari kada mu yi wasa da ita. “Bari mu guso fa gaba gaɗi zuwa kursiyi na alheri, domin mu karɓi jinƙai, mu sami alheri kuma mai-taimakonmu cikin lotun bukata.”—Ibraniyawa 4:16.
Yaya Za Ka Amsa?
• Menene muka koya daga annabi Daniel game da muhimmancin addu’a?
• Yaya za mu ƙarfafa abutarmu da Jehovah?
• Me ya sa za mu yi addu’a ba fasawa?
• Me ya sa jin ba mu cancanta ba ba zai hana mu daga yi wa Jehovah addu’a ba?
[Hoto a shafi na 14]
Nehemiah ya yi gajeriyar addu’a a zuciya kafin ya yi wa sarkin magana
[Hoto a shafi na 15]
Hannatu ta “jima tana addu’a a gaban Ubangiji”
[Hotuna a shafi na 16]
Yesu ya yi addu’a dukan dare kafin ya zaɓi manzanninsa 12
[Hotuna a shafi na 18]
Muna samun zarafin addu’a kowacce rana