Shan Tsanani Domin Adalci
“Masu-albarka ne waɗanda an tsanance su saboda adalci.”—MATTA 5:10.
1. Me ya sa aka kai Yesu gaban Bilatus Babunti, me Yesu ya faɗa?
“DOMIN wannan an haife ni, domin wannan kuma na zo cikin duniya, domin in bada shaida ga gaskiya.” (Yohanna 18:37) Sa’ad da Yesu ya faɗi waɗannan kalmomi yana gaban Bilatus Babunti ne, Gwamnar Roma na Yahudiya. Kasancewar Yesu a wajen ba zaɓensa ba ne ko a ce Bilatus ya kira shi ne ba. Maimako, ya kasance wajen domin shugabannin addinin Yahudawa sun tuhume shi cewa mai laifi ne da ya cancanci mutuwa.—Yohanna 18:29-31.
2. Me Yesu ya yi, kuma me ya zama sakamakonsa?
2 Yesu ya sani sarai cewa Bilatus yana da iko ya sake shi ko kuma ya sa a kashe shi. (Yohanna 19:10) Amma wannan bai hana shi yi wa Bilatus magana da gaba gaɗi ba game da Mulkin. Ko da yake ran Yesu na cikin haɗari, ya yi amfani da zarafi ya yi wa’azi wa mafi girma a gwamnati na yankin. Duk da wa’azin, aka hukunta Yesu kuma aka kashe shi, ya mutu don imaninsa a kan gungumen azaba.—Matta 27:24-26; Markus 15:15; Luka 23:24, 25; Yohanna 19:13-16.
Mashaidi ne ko Kuma Wanda Ya Mutu Domin Imaninsa?
3. Mecece kalmar nan (marʹtys) ta Helenanci na lokatan Littafi Mai Tsarki ke nufi, amma me yake nufi a yau?
3 Mutane da yawa a yau suna ɗaukan wanda yake shirye ya mutu domin imaninsa cewa mai wawan bi ne. Mutanen da suke a shirye su mutu domin imaninsu, musamman na addini, ana yawan tuhumarsu da cewa su ’yan ta’adda ne ko kuma haɗari ne ga jama’a. Amma, furcin nan cewa mutum ya mutu domin imaninsa ya fito daga kalmar nan (marʹtys) na Helenanci da yake nufin “shaida,” a lokatan Littafi Mai Tsarki, mutumin da yake ba da shaida wataƙila a kotu, gaskiyar abin da ya gaskata. Daga baya ne furcin ya ɗauki ma’anar nan “wanda ya ba da shaida ta wajen mutuwarsa.”
4. Wace irin mutuwa Yesu ya yi?
4 Yesu ya ba da shaida ta wajen mutuwarsa. Yadda ya gaya wa Bilatus, ya zo “domin [ya] ba da shaida ga gaskiya” ne. Mutane sun nuna halaye dabam dabam ga shaidar da ya ba da. Wasu cikinsu abin da suka ji kuma suka gani ya motsa su su ba da gaskiya ga Yesu. (Yohanna 2:23; 8:30) Jama’a galibi da kuma shugabannin addini musamman sun yi fushi. Yesu ya ce wa danginsa marasa bi: “Duniya ba ta iya ƙinku ba; amma ni ta ke ƙi, domin ni kan shaida ta, ayyukanta miyagu ne.” (Yohanna 7:7) Domin ya ba da gaskiya, shugabannin al’ummar suka yi fushi da Yesu, da ya sa suka kashe shi. Hakika, shi ne “amintaccen mashaidi [marʹtys] mai-gaskiya.”—Ru’ya ta Yohanna 3:14.
“Za Ku Zama Abin Ƙi”
5. A hidimarsa da farko, me Yesu ya ce game da tsanantawa?
5 Ba kawai Yesu kansa ya sha mugun tsanani ba, amma kuma ya yi wa mabiyansa kashedi cewa su ma haka zai faru musu. A hidimarsa da farko, Yesu ya gaya wa masu sauraronsa a Hudubarsa Bisa Dutse: “Masu-albarka ne waɗanda an tsanance su saboda adalci: gama mulkin sama nasu ne. Masu-albarka ne ku lokacinda ana zarginku, ana tsananta muku, da ƙarya kuma ana ambatonku da kowacce irin mugunta, sabili da ni. Ku yi farinciki, ku yi murna ƙwarai: gama ladarku mai-girma ce cikin sama.”—Matta 5:10-12.
6. Wane kashedi Yesu ya bayar sa’ad da yake aika da manzanninsa 12?
6 Daga baya, sa’ad da ya aika da manzanni 12, Yesu ya ce musu: “Amma ku yi hankali da mutane: gama za su bashe ku ga majalisai, cikin majami’unsu kuma za su yi muku bulala; i, kuma a gaban mahukunta da sarakuna za a kawo ku sabili da ni, domin shaida garesu da Al’ummai kuma.” Amma ba masu iko na addini ne kawai za su tsananta wa almajiran ba. Yesu ya ce: “Ɗan’uwa za ya bada ɗan’uwa ga mutuwa, uba kuma za ya bada ɗansa; ’ya’ya za su tasa ma iyayensu, su sa a kashe su. Za ku zama abin ƙi ga dukan mutane sabili da sunana: amma wanda ya jimre har matuƙa, shi ne za ya tsira.” (Matta 10:17, 18, 21, 22) Tarihin wahalar Kiristoci na ƙarni na farko ya nuna gaskiyar waɗannan kalmomi.
Tarihin Masu Aminci da Suka Jimre
7. Me ya sa aka kashe Istifanas?
7 Ba da daɗewa ba bayan mutuwar Yesu, Istifanas ya zama Kirista na farko da ya mutu domin ba da shaidar gaskiya. Ya cika “da alheri da iko, ya aika alamu da al’ajabai masu-girma a wurin mutane.” Magabtansa na addini “ba su da iko su tsaya ma hikima da Ruhu wanda ya ke magana da shi.” (Ayukan Manzanni 6:8, 10) Da kishi ya sha kansu, suka jawo Istifanas zuwa gaban Majalisar, babban kotun Yahudawa, inda ya fuskanci masu tuhumar ƙarya kuma ya ba da shaida ƙwarai. A ƙarshe, magabtan Istifanas suka kashe wannan mashaidi mai aminci.—Ayukan Manzanni 7:59, 60.
8. Menene almajiran da suke Urushalima suka yi game da tsanantawa da ta same su bayan mutuwar Istifanas?
8 Bayan da aka kashe Istifanas, “babban tsanani ya taso ma ikilisiya wadda ke cikin Urushalima; dukansu suka watse cikin iyakar wuraren Yahudiya da Samariya.” (Ayukan Manzanni 8:1) Tsanantawar ta sa a daina wa’azin Kirista ne? Ba haka ba, labarin ya gaya mana cewa “waɗanda suka watse suka yi tafiya ko’ina, suna wa’azin kalmar.” (Ayukan Manzanni 8:4) Lallai suna da ra’ayin manzo Bitrus da ya ce tun farko: “Dole sai mu fi biyayya ga Allah da mutane.” (Ayukan Manzanni 5:29) Duk da tsanantawar, waɗannan almajirai masu aminci masu gaba gaɗi suka ci gaba da aikin ba da shaida ga gaskiya, ko da yake sun sani wannan zai daɗa jawo wahala.—Ayukan Manzanni 11:19-21.
9. Mabiyan Yesu sun ci gaba da fuskantar wace tsanantawa?
9 Hakika kuwa wahalar ba ta ragu ba. Da farko, mun ji cewa Shawulu—mutumin da ya yarda a jejjefe Istifanas—“yana kan [tsananta] kashedi da kisa tukuna bisa masu-bin Ubangiji; ya je wurin babban malamin, ya biɗi takardu a wurinsa zuwa Dimashka, zuwa wurin majami’u, domin idan ya sami waɗanda su ke na Tafarkin, ko maza ko mata, shi zo da su Urushalima a ɗaure.” (Ayukan Manzanni 9:1, 2) Sai kuma, a misalin shekara ta 44 A.Z., “Hirudus sarki ya miƙa hannu garin shi wulakanta waɗansu a cikin ikilisiya. Ya kashe Yaƙub ɗan’uwa Yohanna da takobi.”—Ayukan Manzanni 12:1, 2.
10. Wane tarihin tsanantawa muka gani a cikin Ayukan Manzanni da kuma Ru’ya ta Yohanna?
10 Sauran littafin Ayukan Manzannin na ɗauke da tarihin gwaji, tsare a kurkuku da tsanantawa da masu aminci kamar Bulus suka jimre, wanda dā mai hamayya ne ya zama manzo wanda Daular Roma, Nero ya kashe domin imaninsa a misalin shekara ta 65 A.Z. (2 Korinthiyawa 11:23-27; 2 Timothawus 4:6-8) A ƙarshe, a cikin littafin Ru’ya ta Yohanna, da aka rubuta a ƙarshen ƙarni na farko, mun gani cewa an tsare tsoho manzo Yohanna a tsibirin Batmusa saboda “maganar Allah da shaidar Yesu.” Ru’ya ta Yohanna ta kuma yi maganar “Antibas mashaidina, mai-amincina, wanda aka kashe” a Birgamos.—Ru’ya ta Yohanna 1:9; 2:13.
11. Yaya tafarki da Kiristoci na farko suka bi ya tabbatar da gaskiyar kalmomin Yesu game da tsanantawa?
11 Duka wannan na tabbatar da gaskiyar kalmomin Yesu ne ga almajiransa: “Idan suka yi mini tsanani, su a yi muku tsanani kuma.” (Yohanna 15:20) Kiristoci masu aminci na farko suna shirye su fuskanci gwaji mafi tsanani, mutuwa—ta wurin azaba, ta jefa su wa dabbobi masu kisa, ko kuma a wata hanya—domin su cika aikinsu daga Ubangiji Yesu Kristi: “Za ku zama shaiduna kuma cikin Urushalima da cikin dukan Yahudiya da Samariya, har kuma iyakan duniya.”—Ayukan Manzanni 1:8.
12. Me ya sa tsanantawa da ake yi wa Kiristoci ba a dā ba ne kawai?
12 Idan wani ya yi tunani cewa mugun tsanantawa da aka yi wa mabiyan Yesu a dā ne kawai, lallai ya yi kuskure sosai. Mun ga cewa Bulus ma da ya jimre da nasa wahalar, ya rubuta: “Dukan waɗanda su ke so su yi rai mai-ibada cikin Kristi Yesu za su sha tsanani.” (2 Timothawus 3:12) Game da tsanantawa, Bitrus ya ce: “Gama zuwa wannan aka kiraye ku: gama Kristi kuma ya sha azaba dominku, yana bar muku gurbi, domin ku bi sawunsa.” (1 Bitrus 2:21) Tun lokacin har zuwa waɗannan lokaci na “kwanaki na ƙarshe” na wannan zamani, mutanen Jehovah sun ci gaba da zama abin ƙi da kuma abin hamayya. (2 Timothawus 3:1) A dukan duniya, a ƙarƙashin mulkin kama karya da ƙasashe na dimokuraɗiyya, an tsananta wa Shaidun Jehovah a wasu lokatai, ɗaɗɗaya da kuma rukuninsu.
Me Ya Sa Ake Ƙinsu Kuma Ake Tsananta Musu?
13. Me ya kamata bayin Jehovah na zamani za su tuna da shi game da tsanantawa?
13 Ko da yawancinmu a yau muna da ɗan ’yanci mu yi wa’azi kuma mu yi taro cikin salama, dole mu saurari tunasarwa na Littafi Mai Tsarki cewa “ƙa’idar duniyan nan tana shuɗewa.” (1 Korinthiyawa 7:31) Idan ba mu ƙarfafa azancinmu, jiye-jiyenmu, da ruhaniyarmu ba, zai kasance da sauƙi mu kasala domin abubuwa suna canjawa farat ɗaya. To me za mu yi don mu kāre kanmu? Hanya mai kyau na kāre kanmu ita ce mu tuna abin da ya sa ake ƙi kuma ake tsananta wa Kiristoci masu son salama masu bin doka.
14. Menene Bitrus ya ce shi ne dalilin da ya sa ake tsananta wa Kiristoci?
14 Manzo Bitrus ya yi magana a kan wannan batun a wasiƙarsa ta farko da ya rubuta a misalin shekara ta 62-64 A.Z., sa’ad da Kiristoci a dukan Daular Roma suke fuskantar gwaji da tsanani. Ya ce: “Ƙaunatattu, kada ku ga abin mamaki ne tsanani mai-zafin nan da ke wurinku, wanda ke auko muku domin ya auna ku, sai ka ce wani baƙon al’amari ya same ku.” Domin ya yi bayanin abin da yake maganarsa, Bitrus ya ci gaba: “Kada wani daga cikinku ya sha wuya kamar mai-kisankai, ko kuwa ɓarawo, ko mai-aikin mugunta, ko mai-shishigi: amma idan wani yana shan wuya kamar mai-bin Kristi, kada shi ji kunya; amma sai shi ɗaukaka Allah cikin wannan suna.” Bitrus ya bayyana cewa suna wahala, ba domin wani mugun hali ba, amma domin su Kiristoci ne. Da a ce suna “cikin haukar lalata” na mutane kewaye da su, da an amince da su. Amma suna shan wahala domin suna ƙoƙarin su cika hakkinsu na mabiyan Kristi ne. Yanayin ɗaya ne ma da Kiristoci na gaskiya a yau.—1 Bitrus 4:4, 12, 15, 16.
15. Wace saɓawa ce ake gani a yadda ake bi da Shaidun Jehovah a yau?
15 A ɓangarori da yawa na duniya, ana yaba wa Shaidun Jehovah a fili saboda haɗin kai da suke da shi a taron gundumarsu da aikinsu na gini domin gaskiya da kuma ƙwazo domin ɗabi’arsu da rayuwar iyali mai kyau, har ma domin adonsu mai kyau da kuma hali.a A wata sassa kuma, an hana aikinsu a ƙasashe 28 a lokacin da ake rubuta wannan talifi, kuma Shaidu da yawa sun sha zalunci da kuma rashi domin imaninsu. Me ya sa ake musu haka? Kuma me ya sa Allah ya ƙyale haka?
16. Wane dalili ne musamman ya sa Allah ya ƙyale mutanensa su sha tsanani?
16 Abu mafi muhimmanci, ya kamata mu tuna da kalmomin Misalai 27:11: “Ɗana, ka yi hikima, ka fa faranta zuciyata: domin in mayarda magana ga wanda ya zarge ni.” Hakika, domin tsohon batu na ikon mallakar sararin halitta ne. Duk da tabbaci mai yawa na waɗanda suka kasance da aminci ga Jehovah a dukan tarihin ’yan Adam, Shaiɗan bai daina zargin Jehovah ba yadda ya yi a zamanin Ayuba adali. (Ayuba 1:9-11; 2:4, 5) Babu shakka, Shaiɗan ya fi fushi a ƙoƙarinsa na ƙarshe ya tokara wa da’awarsa, musamman yanzu da aka kafa Mulkin Allah, da talakawansa masu aminci da kuma wakilai da ke kewaye da duniya. Waɗannan za su kasance da aminci ga Allah duk da wahala da ke fāɗa musu? Wannan tambaya ce da kowanne bawan Jehovah dole ya amsa wa kansa.—Ru’ya ta Yohanna 12:12, 17.
17. Menene Yesu yake nufi da kalmomin nan “za ya komo ya zama shaida a kanku”?
17 Da yake gaya wa almajiransa abubuwan da za su faru a “cikar zamani,” Yesu ya nuna wani dalili da ya sa Jehovah ya ƙyale a tsananta wa bayinsa. Ya gaya musu: “[Za a] kawo ku a gaban sarakuna da hakimai sabili da sunana. Wannan za ya komo ya zama shaida a kanku.” (Matta 24:3, 9; Luka 21:12, 13) Yesu kansa ma ya ba da shaida a gaban Hirudus da Bilatus Babunti. An kai manzo Bulus ma a “gaban sarakuna da hakimai.” Da yake Ubangiji Yesu Kristi ya yi masa ja-gora, Bulus ya nemi ya ba da shaida ga sarki mafi iko na lokacinsa, da ya ce: “Na ɗaukaka roƙo zuwa wurin Kaisar.” (Ayukan Manzanni 23:11; 25:8-12) Haka nan ma a yau, yanayi masu wuya sun sa a ba da shaida mai kyau ga ma’aikata da kuma jama’a.b
18, 19. (a) Ta yaya jimre da gwaji zai amfane mu? (b) Waɗanne tambayoyi za a bincika a talifi na gaba?
18 A ƙarshe, jimre da gwaji da wahala zai iya amfane mu. A ta wace hanya? Almajiri Yaƙub ya tunasar da ’yan’uwansa Kiristoci: “ ’Yan’uwana, kadan jarabobi masu-yawa sun same ku, ku maishe shi abin farinciki sarai; kun sani gwadawar bangaskiyarku tana jawo haƙuri.” Hakika, tsanani zai iya kyautata bangaskiyarmu kuma ƙarfafa jimirinmu. Saboda haka, ba ma tsoro ko kuma mu nemi hanya da ba ta Nassi ba mu kawar da tsananin. Maimako, muna bin gargaɗin Yaƙub: “Bari haƙuri shi cika aikinsa, domin ku kamilta, ku cika kuma, ba ragaggu ne cikin kome ba.”—Yaƙub 1:2-4.
19 Ko da yake Kalmar Allah tana taimakonmu mu fahimci dalilin da ya sa ake tsananta wa bayin Allah masu aminci ko kuma da abin da ya sa Jehovah ya ƙyale tsanani, wannan ba ya nufin cewa yana da sauƙi a jimre wa tsanani ba. Me zai ƙarfafa mu mu jimre masa? Me za mu yi idan muka fuskanci tsanani? Za mu bincika waɗannan batu masu muhimmanci a talifi na gaba.
[Hasiya]
a Dubi Watchtower na 15 ga Disamba, 1995, shafofi 27-29 (Turanci); 1 ga Nuwamba, 1994, shafofi 9-10; da kuma Awake! na fitar 22 ga Disamba, 1993, shafofi 6-13, Turanci.
b Dubi Awake! fitar 8 ga Janairu, 2003, shafofi 3-11.
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Wace irin mutuwa Yesu ya yi?
• Yaya tsanani ya shafi Kiristoci na ƙarni na farko?
• Yadda Bitrus ya yi bayani, me ya sa aka tsananta wa Kiristoci na farko?
• Waɗanne dalilai suka sa Jehovah ya ƙyale a tsananta wa bayinsa?
[Hotuna a shafuffuka na 20, 21]
Kiristoci na ƙarni na farko sun wahala ba domin wani mugun hali ba, amma domin su Kiristoci ne
BULUS
YAƘUB
YOHANNA
ANTIBAS
ISTIFANAS