Mata Kiristoci Masu Aminci—Masu Bauta Wa Allah Ne Masu Tamani
“Tagomashi yana da rikici, jamali kuma abin banza ne: Amma mace mai-tsoron Ubangiji za a yabe ta.”—MISALAI 31:30.
1. Yaya Jehovah yake ɗaukan kyau idan aka gwada da yadda duniya take ɗaukanta?
GANIN waje ne ya fi muhimmanci wa duniya, musamman ma a batun mata. Amma Jehovah yana damuwa musamman da mutum na ciki, da yake daɗa kyau a tsufa ma. (Misalai 16:31) Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya yi wa mata gargaɗi: “Kada adonku ya zama ado na waje, watau su kitson gashi, da sa ado na zinariya, ko yafa tufafi masu ƙawa; amma ya zama ɓoyayyen mutum na zuciya, cikin tufafi waɗanda ba su lalacewa, na ruhu mai-ladabi mai-lafiya, abin da ke da tamani mai-girma a gaban Allah.”—1 Bitrus 3:3, 4.
2, 3. Ta yaya mata suka tallafa wa ci gaban bishara cikin ƙarni na farko, kuma yaya aka annabta wannan?
2 Mata da yawa da aka ambata cikin Littafi Mai Tsarki sun nuna irin hali da ya isa yabon nan. A ƙarni na farko, waɗansu daga cikin waɗannan sun sami gatar yi wa Yesu da manzanninsa hidima. (Luka 8:1-3) Daga baya, mata Kiristoci sun zama masu bishara; wasu suna tallafa wa maza Kiristoci da suke shugabanci, har da manzo Bulus; kuma wasu sun nuna hali na karimci, har sun yarda a yi taron ikilisiya a gidajensu.
3 An annabta cikin Nassosi cewa Jehovah zai yi amfani da mata a hanya mai girma a cika ƙudurinsa. Alal misali, Joel 2:28, 29 ta annabta cewa mata da maza, ƙanana da manya za su sami ruhu mai tsarki kuma su sa hannu a yin shelar bisharar Mulkin. Annabcin nan ya soma cikarsa a Fentakos shekara ta 33 A.Z. (Ayukan Manzanni 2:1-4, 16-18) An ba wa wasu mata shafaffu kyauta ta mu’ujiza, kamar su kyautar annabci. (Ayukan Manzanni 21:8, 9) Ta wurin ƙwazonsu a hidimar, waɗannan rundunan ’yan’uwa mata masu aminci sun haɗa a yaɗa Kiristanci a ƙarni na farko. Hakika, a shekara ta 60 A.Z., manzo Bulus ya rubuta cewa an ‘yi wa’azin bishara cikin dukan halitta da ke ƙarƙashin sama.’—Kolossiyawa 1:23.
An Yaba Musu Saboda Gaba Gaɗinsu, Himma da Kuma Karimci
4. Me ya sa Bulus yake da dalili mai kyau na yaba wa mata da yawa a ikilisiyar Kirista a ƙarni na farko?
4 Shi manzo Bulus, ya nuna godiya ga hidimar da wasu mata musamman suka yi masa—yadda Kiristoci masu kula a yau suke godiya ga hidima da mata masu himma suke yi. Mata da Bulus ya ambata sunansu su ne “Farifaina da Tarifusa, waɗanda su ke aiki cikin Ubangiji,” da kuma ‘Barsisa ƙaunatacciya, wadda ta yi aiki dayawa cikin Ubangiji.’ (Romawa 16:12) Bulus ya rubuta cewa, Afodiya da Sintiki, sun “yi aiki tare da [shi] cikin bishara.” (Filibbiyawa 4:2, 3) Biriskilla, tare da mijinta, Akila, ma sun yi aiki tare da Bulus. Har ita da Akila suka “miƙa wuyansu” domin Bulus, da ya sa ya rubuta: “Ba ni kaɗai ni ke gode musu ba, amma har da dukan ikilisiyoyi na Al’ummai.”—Romawa 16:3, 4; Ayukan Manzanni 18:2.
5, 6. A waɗanne hanyoyi ne Biriskilla ta bar misali mai kyau domin ’yan’uwa mata a yau?
5 Menene ya daɗa ga himmar Biriskilla da kuma gaba gaɗinta? Ɗan labarin yana cikin Ayukan Manzanni 18:24-26, inda muka karanta cewa ta goyi bayan mijinta a taimaka wa Afolos, wanda yake da baiwar iya magana, suka taimake shi ya fahimci gaskiya yadda take. A bayyane yake cewa Biriskilla ɗalibar kirki ce ta Kalmar Allah kuma na koyarwar manzanni. Saboda haka, ta iya koyon halaye masu kyau da ya sa ta zama da tamani ga Allah, ga mijinta, wadda take cikin ikilisiya ta farko. Haka ma ’yan’uwa mata Kiristoci masu aiki tuƙuru da suke nazarin Littafi Mai Tsarki sosai kuma suna cin abinci na ruhaniya da Jehovah yake tanadinsa ta wurin “wakili mai-aminci.”—Luka 12:42.
6 Akila da Biriskilla masu karimci ne musamman. Bulus ya zauna a gidansu lokacin da yake aikin kafa rumfa tare da su a Koranti. (Ayukan Manzanni 18:1-3) Lokacin da ma’auratan suka ƙaura daga Afisas zuwa Roma, sun ci gaba da nuna karimci na Kirista, har ma suna ba da gidansu don a yi taron ikilisiya. (Ayukan Manzanni 18:18, 19; 1 Korinthiyawa 16:8, 19) Nimfa da kuma Maryamu mamar Yohanna Markus ma sun yarda a yi amfani da gidajensu don taron ikilisiya.—Ayukan Manzanni 12:12; Kolossiyawa 4:15.
Abu Mai Tamani a Yau
7, 8. Wane labari mai kyau ne na tsarkakan hidima, mata Kirista na zamanin yau suke da shi, kuma za mu tabbata da menene?
7 Kamar yadda yake a ƙarni na farko, mata Kiristoci masu aminci a yau suna da aiki na musamman a cikar ƙudurin Allah, musamman a aikin bisharanci. Lallai kuwa waɗannan ’yan’uwa mata suna da sunan kirki! Ga misalin Gwen, da ta bauta wa Jehovah na shekaru fiye da 50 har mutuwarta a shekara ta 2002. “Himmar Gwen a bisharanci kusan dukan birnin sun sani,” in ji mijinta. A gare ta, kowanne mutum, wanda ya dace ne ya sami ƙaunar Jehovah da kuma alkawuransa. Amincinta ga Allah, ƙungiyarsa, da kuma iyalinmu—balle ma yadda take ba da ƙarfafa sa’ad da mun gamu da abin sanyin gwiwa—goyon baya na ƙwarai gare ni kuma ga yaranmu abin ƙarfafa ne a rayuwarmu. Mun yi rashinta ƙwarai.” Gwen da mijinta sun yi aure na shekara 61.
8 Dubban mata Kiristoci, marasa aure da masu aure, suna hidimar majagaba da kuma hidima a ƙasashen waje, sun gamsu da bukatu na rayuwa sa’ad da suke yaɗa saƙon Mulkin a yankuna da birane ne ko waɗanda suke a ware. (Ayukan Manzanni 1:8) Wasu da yawa sun ƙyale batun samun gidan kansu ko haihuwar yara domin su bauta wa Jehovah sosai. Da akwai wasu da suke tallafa wa mazansu da suke hidima na masu kula masu ziyara, wasu dubban mata kuma suna hidima a gidajen Bethel a kewaye da duniya. Babu shakka, waɗannan mata masu sadaukar da kai suna cikin “muradin dukan dangogi” da suka cika gidan Jehovah da ɗaukaka.—Haggai 2:7.
9, 10. Ta yaya wasu cikin iyali suka furta godiyarsu ga misalai masu kyau na mata da kuma uwaye Kiristoci?
9 Hakika, mata Kiristoci da yawa suna da hakki na iyali da suke kula da shi; duk da haka, suna sa Mulkin da farko. (Matta 6:33) Wata majagaba marasa aure ta rubuta: “Domin mamata tana da ƙarfafar bangaskiya da kuma misalinta na kirki, ta sa na zama majagaba na kullum. Gaskiya kam, tana ɗaya cikin abuyata mafi kusa na aikin wa’azi.” Wani maigida ya ce game da matarsa, wadda uwar yara mata biyar ce: “Gidanmu yana da tsabta kuma a tsare. Bonnie tana shirya shi da sauƙi babu yawan kaya saboda iyalinmu ta iya biɗan abubuwa na ruhaniya. Yadda take tallafawa kuma take bi da kuɗinmu ya sa na iya aiki na rabin rana na shekaru 32, ya taimake ni na ba da ƙarin lokaci wa iyalinmu da kuma batu na ruhaniya. Matata ta koya wa yaran darajar aiki tuƙuru kuma. Babu shakka ta cancanci na yabe ta.” A yau mata da mijin suna hidima a hedkwatar Shaidun Jehovah.
10 Wani maigida ya rubuta game da matarsa, uwar yara da sun yi girma: “Halin da na fi so wurin Susan shi ne ƙaunarta na ƙwarai ga Allah da kuma mutanensa, da fahiminta, jinƙai, da kuma yin gaskiya. Tana da ra’ayin nan kullum cewa Jehovah ya cancanci bauta mafi kyau da za mu iya yi—ƙa’idar da ya kamata ta bi ne na baiwar Allah kuma domin ita uwa ce.” Ta wurin tallafawar matansa, wannan maigidan ya iya kula da hakki masu yawa na ruhaniya, har da hidima na dattijo, majagaba, mataimakin mai kula da da’ira, da kuma ɗaya cikin Kwamitin Hulɗa da Asibitoci. Lallai waɗannan mata suna da tamani wajen mazansu, ga ’yan’uwa Kirista, mafi muhimmanci kuma wajen Jehovah!—Misalai 31:28, 30.
Mata Masu Tamani da Ba Su da Magidanta
11. (a) Ta yaya Jehovah ya bayyana yadda yake damuwa game da mata masu aminci, musamman ma gwauraye? (b) Game da menene gwauraye Kiristoci da wasu ’yan’uwa mata masu aminci da ba su da magidanta za su tabbata?
11 Sau da yawa Jehovah yana furta yadda ya damu game da lafiyar gwauraye. (Kubawar Shari’a 27:19; Zabura 68:5; Ishaya 10:1, 2) Bai canja ba. Har yanzu yana damuwa sosai ba game da gwauraye kawai ba amma kuma game da mahaifiya ɗaya da kuma mata marasa aure waɗanda domin sun zaɓi haka ne ko kuma saboda ba su sami miji da Kirista ne da ya dace ba. (Malachi 3:6; Yaƙub 1:27) Idan kina cikin waɗanda suke bauta wa Jehovah da aminci ba tare da goyon bayan abokin aure Kirista ba, ki tabbata cewa kina da tamani a idanun Allah.
12. (a) Yaya wasu ’yan’uwa mata Kiristoci suke nuna amincinsu ga Jehovah? (b) Menene wasu ’yan’uwanmu mata suke jurewa?
12 Alal misali, yi la’akari da ’yan’uwa mata Kiristoci da ba su yi aure ba saboda suna biyayya ga gargaɗin Jehovah na su yi aure “sai dai cikin Ubangiji.” (1 Korinthiyawa 7:39; Misalai 3:1) Kalmar Allah ta tabbatar da su: “Ga mai aminci za ka nuna kai mai aminci ne.” (2 Samu’ila 22:26, NW ) Amma, wasu da yawa cikinsu kasancewa babu aure kaluɓale ne. Wata ’yar’uwa ta ce: “Na shawarta na yi aure cikin Ubangiji, amma ina kuka sa’ad da na ga abokaina suna auren maza Kirista ni kuma ina nan babu kowa.” Wata ’yar’uwa kuma ta ce: “Yanzu na bauta wa Jehovah na shekara 25. Na shawarta zan ci gaba da aminci gare shi, amma sau da yawa ina baƙin cikin kaɗaici.” Ta daɗa haka: “ ’Yan’uwa kamar ni suna bukatar ƙarfafa.” Ta yaya za mu iya taimakon irin waɗannan masu aminci?
13. (a) Me muka koya daga misalin waɗanda suka ziyarci ’yar Jehpthah? (b) A waɗanne hanyoyi kuma za mu nuna mun damu game da ’yan’uwa mata marasa aure cikin ikilisiyarmu?
13 Ga hanya ɗaya cikin misali na zamanin dā. Lokacin da ’yar Jehpthah ta ƙyale zarafinta na yin aure, mutane sun fahimci cewa tana sadaukar da kai ne. Me aka yi don a ƙarfafa ta? ‘ ’Yan matan Isra’ila su kan fita kowacce shekara su yi kukan ɗiyar Jephthah Bagileadi kwana huɗu cikin kowacce shekara.’ (Alƙalawa 11:30-40) Haka nan ma, ya kamata mu yaba ma ’yan’uwa mata marasa aure da zuciya ɗaya da suke biyayya da dokar Allah cikin aminci.a A wace hanya ce kuma za mu iya nuna damuwarmu? A cikin addu’o’inmu ya kamata mu roƙi Jehovah ya toƙara wa waɗannan ƙaunatattu, ’yan’uwa masu aminci su ci gaba da hidimarsu. Sun wajaba a tabbatar da su cewa Jehovah da kuma dukan ikilisiyar Kirista na ƙaunarsu kuma suna sonsu.—Zabura 37:28.
Yadda Mahaifiya Ɗaya Suke Nasara
14, 15. (a) Me ya sa mata Kiristoci da su kaɗai ne za su nemi taimakon Jehovah? (b) Ta yaya mata da su kaɗai ne za su aikata daidai da addu’o’insu?
14 Mata Kiristoci da su kaɗai ne ma suna fuskantar kaluɓale da yawa. Amma za su iya juya wajen Jehovah don taimako na yin renon yara da ya jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Hakika, idan ke ce kaɗai mahaifiya, yana da wuya ki cika hakkin uwa da kuma uba a dukan fasalolinsu. Duk da haka, Jehovah zai taimake ku ku kula da hakkinku masu yawa kuma idan kuka kira gare shi cikin bangaskiya. Ga misali: A ce kina ɗauke da kaya mai nauyi zuwa gidanki da yake kan tudu. Idan akwai mota da za ta ɗauki kayan, za ki ƙi ne, ki yi kokawar hawa da kayan ke kaɗai? A’a! Haka nan ma, kada ku yi ƙoƙarin ɗaukan nauyin kaya ku kaɗai tun da za ku iya samun taimakon Jehovah. Hakika, yana gayyatar ku ku biɗe shi. Zabura 68:19 ta ce: ‘Albarka ga Ubangiji, wanda yana ɗauke da nauwayarmu kowace rana.’ Haka ma, 1 Bitrus 5:7 ta gayyace ku ku zuba dukan alhininku bisa Jehovah “domin yana kula da ku.” Saboda haka, sa’ad da matsaloli da kuma alhini sun danna ki, ki sauƙe a kan Ubanmu na samaniya, kina yin haka “ba fasawa.”—1 Tassalunikawa 5:17; Zabura 18:6; 55:22.
15 Alal misali, idan ke uwa ce, babu shakka kina damuwa game da matsi na tsara da yaranki za su fuskanta a makaranta ko kuma gwaji na aminci. (1 Korinthiyawa 15:33) Damuwa ce da ta dace. Amma kuma batu ne na addu’a. To, me ya sa ba za ki yi addu’a game da irin batun nan tare da yaranki kafin su tafi makaranta ba, wataƙila bayan kun bincika nassi na yini tare? Addu’a daga zuciya da ainihi ne tana motsa yara. Ban da haka ma, kina biɗan albarkar Jehovah ne sa’ad da cikin haƙuri kina ƙoƙarin ki sahinta Kalmarsa cikin zukatan yaranki. (Kubawar Shari’a 6:6, 7; Misalai 22:6) Ki tuna cewa “idanun Ubangiji suna bisa masu-adalci, kunnuwansa kuma suna buɗe ga jin roƙonsu.”—1 Bitrus 3:12; Filibbiyawa 4:6, 7.
16, 17. (a) Menene wani ɗa ya faɗa game da ƙaunar da uwarsa ta nuna masa? (b) Ta yaya ruhaniyar mamar ta shafi yaranta?
16 Ga misalin Olivia uwa mai yara shida. Mijinta da ba mai bi ba ya wasar da iyalin bayan an haifi ’yar autar, amma ta ɗauki hakkin yin renon yaran a hanyar Allah. Ɗan Olivia, Darren yanzu shekararsa 31 yana hidimar Kirista dattijo kuma majagaba, shekararsa 5 a lokacin. Abin da ya daɗa alhinin Olivia shi ne, Darren ya yi ciwo mai tsanani da ke damunsa har yanzu. Da yake tunanin lokacin yarantakarsa, Darren ya rubuta: “Ina tunanin lokacin da nake zaune a kan gadona a asibiti, ina jiran mama. Takan zauna kusa da ni ta karanta mini Littafi Mai Tsarki kowacce rana. Sai kuma ta rera waƙar Mulki ‘Mun Gode Maka Jehovah.’b Har yanzu, wannan ce waƙar Mulki da na fi so.”
17 Dogarar Olivia ga Jehovah da kuma ƙaunarsa ta taimake ta mahaifiya kaɗai ta yi nasara. (Misalai 3:5, 6) Halinta mai kyau ya bayyana a makasudi da ta kafa wa yaranta. “Koyaushe mama tana ƙarfafa mu mu yi hidima ta cikakken lokaci,” in ji Darren. “Saboda haka, ’yan’uwana mata biyar sun shiga aikin hidima ta cikakken lokaci. Amma, mama ba ta fahariyar waɗannan abubuwa ba ga wasu. Ina ƙoƙari sosai na yi koyi da halayenta masu kyau.” Hakika, ba dukan yara ne suke girma su bauta wa Allah yadda na Olivia suka yi ba. Amma idan uwa ta yi iyakacin ƙoƙarinta ta bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki, za ta iya dogara ga kāriyar Jehovah da kuma goyon bayansa mai kyau.—Zabura 32:8.
18. Ta yaya za mu nuna cewa muna godiya ga tanadin Jehovah na ikilisiyar Kirista?
18 Yawancin goyon bayan da Allah yake bayarwa ta wurin ikilisiyar Kirista ce, da tsarin ciyarwa ta ruhaniya a kai a kai, ’yan’uwanci na Kirista, da kuma “kyauta ga mutane” na maza da suka ƙware a ruhaniya. (Afisawa 4:8) Dattawa masu aminci suna aiki tuƙuru su ƙarfafa duka a cikin ikilisiya, suna mai da hankali musamman ga bukatun “marayu da gwauraye cikin ƙuncinsu.” (Yaƙub 1:27) Saboda haka, ku kasance kusa da mutanen Allah, kada ku ware kanku.—Misalai 18:1; Romawa 14:7.
Kyaun Halin Biyayya
19. Me ya sa yin biyayyar mata ba ta nufin ita ƙarama ce ba, kuma wane misalin Littafi Mai Tsarki ya goyi bayan wannan?
19 Jehovah ya halicce mace ta zama mataimakiyar namiji. (Farawa 2:18) Shi ya sa, biyayyar mata ga mijinta ba ta nufin ita ƙarama ba ce sam. Maimako, tana daraja mace, tana sa ta yi amfani da baiwa da kuma tamani masu yawa da take da su daidai da nufin Allah. Misalai sura 31 ta kwatanta girman ayyuka na mata da ta ƙware a Isra’ila ta dā. Tana taimaka wa mabukata, tana dasa inabi, kuma tana sayan fage. Hakika, “zuciyar mijinta tana dogara gareta, ba kuwa za shi rasa riba ba.”—Ayoyi na 11, 16, 20.
20. (a) Yaya ya kamata mata Kirista za ta yi amfani da iyawar da Allah ya ba ta ko kuma baiwa? (b) Waɗanne halaye masu kyau ne Esther ta nuna, kuma yaya Jehovah ya yi amfani da ita domin wannan?
20 Mata mai tsoron Allah mai filako ba ta ɗaga kanta ko kuma ta yi gasa da mijinta ba. (Misalai 16:18) Ba ta biɗan gamsar da kanta wajen abin duniya kawai ba amma tana amfani da kyauta da Allah ya ba ta ta yi wa wasu hidima—iyalinta, ’yan’uwa Kirista, maƙwabta, mafi kyau kuma, ga Jehovah. (Galatiyawa 6:10; Titus 2:3-5) Ka yi la’akari da misalin Sarauniya Esther na Littafi Mai Tsarki. Ko da yake kyakkyawa ce, tana filako kuma da biyayya. (Esther 2:13, 15) Sa’ad da ta yi aure, ta nuna biyayya ƙwarai ga mijinta, Sarki Ahasuerus, ba kamar Vashti ba matar sarkin ta dā. (Esther 1:10-12; 2:16, 17) Esther kuma cikin biyayya ta saurari yayanta, Mordekai, a batutuwa da suka dace—har ma bayan da ta zama sarauniya. Amma ita ba raunanniya ba ce! Da gaba gaɗi ta fallasa Haman, wani mai iko mai rashin hankali da ya ƙulla ya halaka Yahudawa. Jehovah ya yi amfani da Esther a hanya mai girma a cetar da mutanensa.—Esther 3:8–4:17; 7:1-10; 9:13.
21. Ta yaya mata Kirista za ta ci gaba da zama da ƙarin tamani ga Jehovah?
21 A bayyane yake, a dā da kuma a yanzu, mata masu ibada sun nuna bautarsu ta kaɗai ga Jehovah. Saboda haka, mata masu tsoron Allah suna da tamani a gaban Jehovah. ’Yan’uwa mata Kiristoci, ku ƙyale Jehovah ya ci gaba da mulmula ku ta wurin ruhu mai tsarki nasa ku zama “santali,” mai daraja wanda “shiryayye zuwa kowane kyakkyawan aiki.” (2 Timothawus 2:21; Romawa 12:2) Game da irin waɗannan masu bauta masu tamani, Kalmar Allah ta ce: “A ba ta daga cikin amfanin hannuwanta: Bari kuma ayyukanta su yabe ta a cikin ƙofofi.” (Misalai 31:31) Bari wannan ya zama haka a kan kowannenku.
[Hasiya]
a Domin sanin yadda za mu yaba musu, dubi Hasumiyar Tsaro na 15 ga Maris, 2002, (Turanci) shafofi na 26-28.
b Waƙa ta 212 cikin Sing Praises to Jehovah, da Shaidun Jehovah suka buga.
Ka Tuna?
• Ta yaya wasu mata Kiristoci na ƙarni na farko suka nuna suna da tamani a gaban Jehovah?
• Ta yaya ’yan’uwa mata da yawa a zamaninmu suke nuna suna da tamani ga Allah?
• A waɗanne hanyoyi ne Jehovah yake goyon bayan mata da su kaɗai ne da kuma ’yan’uwa mata marasa aure?
• Ta yaya mata za ta nuna biyayya ta ƙwarai ga tsari na shugabancin gida?
[Akwati a shafi na 29]
Misalai Da Za A Yi Tunani A Kansu
Za ka so ka ƙara bincika wasu misalan mata masu aminci da aka ambata cikin Littafi Mai Tsarki? Idan kana so, sai ka karanta nassosi da aka nuna a ƙasan nan. Sa’ad da kake bimbini a kan kowannensu da aka jera a nan, ka yi ƙoƙarin fahimtar ƙa’idar da za ka iya amfani da ita a rayuwarka.—Romawa 15:4.
◆ Saratu: Farawa 12:1, 5; 13:18a; 21:9-12; 1 Bitrus 3:5, 6.
◆ Mata Isra’ilawa masu karimci: Fitowa 35:5, 22, 25, 26; 36:3-7; Luka 21:1-4.
◆ Deborah: Alƙalawa 4:1–5:31.
◆ Ruth: Ruth 1:4, 5, 16, 17; 2:2, 3, 11-13; 4:15.
◆ Mata ’yar Shunem: 2 Sarakuna 4:8-37.
◆ Mata ’yar Finikiya: Matta 15:22-28.
◆ Martha da Maryamu: Markus 14:3-9; Luka 10:38-42; Yohanna 11:17-29; 12:1-8.
◆ Tabita: Ayukan Manzanni 9:36-41.
◆ ’Ya’ya mata na Filibbus: Ayukan Manzanni 21:9.
◆ Fibi: Romawa 16:1, 2.
[Hoto a shafi na 27]
Kana yaba wa ’yan’uwa mata marasa aure da suke aminci a yin biyayya da dokar Allah?
[Hoto a shafi na 28]
Waɗanne irin roƙo za a iya yi ainihi cikin addu’a kafin yara su tafi makaranta?