Fansa Ta Ɗaukaka Adalcin Allah
BAYAN tawayen Adamu da Hauwa’u, Jehobah ya faɗi nufinsa na kawo wata Zuriya da za a ƙuje diddigensa. (Farawa 3:15) Wannan ya faru sa’ad da abokan gaban Allah suka kashe Yesu Kristi a kan gungumen gana azaba. (Galatiyawa 3:13, 16) Yesu ba shi da zunubi da yake budurwa ce cikin mu’ujiza ta ɗauki cikinsa ta ikon ruhu mai tsarki. Saboda haka, za a iya yin amfani da jininsa da aka zubar a biya fansa da za a ceci ’yan adam, waɗanda suka gaji zunubi da mutuwa daga Adamu.—Romawa 5:12, 19.
Babu abin da zai hana Jehobah Allah mai iko duka cika nufinsa. Saboda haka, bayan da mutum ya faɗa cikin zunubi, a wurin Jehobah kamar an riga an biya fansa ne, kuma ya yi sha’ani da waɗanda suka ba da gaskiya cewa zai cika alkawuransa. Wannan ya taimaki ’ya’yan Adamu masu zunubi, kamar su Anuhu, Nuhu, Ibrahim, su bi Allah kuma su yi abota da shi ba tare da dushe tsarkakarsa ba.—Farawa 5:24; 6:9; Yakubu 2:23.
Wasu mutane da suka ba da gaskiya ga Jehobah sun yi zunubi mai tsanani. Sarki Dauda misali ne. ‘Ta yaya,’ wataƙila ka yi tambaya, ‘Jehobah zai ci gaba da yi wa Sarki Dauda albarka bayan ya yi zina da Batsheba kuma ya sa aka kashe mijinta, Uriya?’ Wani abu mai muhimmanci shi ne tuba ta gaskiya ta Dauda da kuma bangaskiyarsa. (2 Sama’ila 11:1-17; 12:1-14) Bisa ga hadaya da Yesu Kristi zai miƙa, Allah zai iya yafe wa Dauda da ya tuba zunubansa kuma ya kasance da shari’arsa da kuma adalci. (Zabura 32:1, 2) Domin ya tabbatar da haka, Littafi Mai Tsarki ya yi bayani cewa abu mafi ban sha’awa da fansar Yesu ya cim ma shi ne “domin [Allah] ya nuna adalcinsa ne, domin dā saboda haƙurinsa ya jingine zunuban . . . a wannan zamani.”—Romawa 3:25, 26.
Hakika, ’yan adam sun sami albarka mai yawa domin tamanin jinin Yesu. Bisa ga fansar, ’yan adam masu zunubi da suka tuba za su iya more dangantaka na kud da kud da Allah. Bugu da ƙari, ta fansar za a yi tashin matattu a sabuwar duniya ta Allah. Za a haɗa da bayin Allah masu aminci da suka mutu kafin Yesu ya biya fansa, har da yawanci da suka mutu cikin jahilci kuma ba su bauta masa ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Za a ta da matattu, masu adalci da marasa adalci duka.” (Ayyukan Manzanni 24:15) Bisa ga fansar, a lokacin Jehobah zai ba mutane masu biyayya rai madawwami. (Yahaya 3:36) Yesu kansa ya yi bayani: ‘Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya halaka, sai dai ya sami rai madawwami.’ (Yahaya 3:16) ’Yan adam za su sami dukan waɗannan albarkatu domin Allah ya yi tanadin hadayar fansa.
Abu mafi ban sha’awa na fansar ba albarkatu da aka samu domin ta ba ne. Amfani mafi muhimmanci shi ne abin da fansar Kristi take wa sunan Jehobah. Ta tabbata cewa Jehobah Allah ne mai cikakken adalci mai hulɗa da ’yan adam kuma duk da haka ya kasance da cikakkiyar tsarkaka. Idan ba domin Allah ya nufa ya yi tanadin fansa ba, babu ɗan adam, har da Anuhu da Nuhu, da Ibrahim, da zai iya tafiya da Jehobah ko kuma ya zama abokinsa. Fahimtar haka ya sa mai zabura ya rubuta: “Idan kana yin lissafin zunubanmu, wa zai kuɓuta daga hukunci?” (Zabura 130:3) Ya kamata mu kasance masu godiya ga Jehobah domin aiko da Ɗansa zuwa duniya cikin ƙauna da kuma Yesu domin ba da ransa fansa gare mu da son rai!—Markus 10:45.