Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 10/1 pp. 26-30
  • Ka Yi Sauraron Jehobah Da Bege Da Gaba Gaɗi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Sauraron Jehobah Da Bege Da Gaba Gaɗi
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka “Yalwata Cikin Bege” Kuwa?
  • Bege Yana da Muhimmanci ga Bangaskiya
  • “Kuna Murna Cikin Bege”
  • “Daɗai Ba Ni Tauye Maka Ba”
  • “Ka Yi Sauraro ga Ubangiji”
  • “Fansarku ta Kusa”
  • Ka Ci Gaba da Karfafa Begenka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Abin da Kake Sa Zuciya a Kai Zai Tabbata
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Ka Yi Farin Ciki Don Begenmu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Me Zai Taimaka Mana Mu Kasance da Halin Sa Zuciya ko Bege?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 10/1 pp. 26-30

Ka Yi Sauraron Jehobah Da Bege Da Gaba Gaɗi

“Ka yi sauraro ga Ubangiji: Ka ƙarfafa, ka bar zuciyarka ta ɗauki ƙarfin rai; I, ka yi sauraro ga Ubangiji.”—ZABURA 27:14.

1. Yaya muhimmancin bege, kuma yaya aka yi amfani da wannan kalma a cikin Nassosi?

TABATTACEN bege yana kama da fitowar rana. Yana taimakonmu fiye da jarrabobin da muke fuskanta yanzu kuma mu fuskance su da gaba gaɗi da farin ciki. Jehobah ne kaɗai zai ba mu tabbataccen bege, kuma yana yin haka ta hurarriyar Kalmarsa. (2 Timothawus 3:16) Kalmar nan “bege” ta bayyana sau da yawa a cikin Littafi Mai Tsarki kuma tana nuni ga sauraron wani abu mai kyau da kuma abin da ake sauraronsa.a Irin wannan begen ba fata ba ne kawai, da ba shi da tushe ko kuwa wanda ba zai cika ba.

2. Ta yaya bege ya shafi rayuwar Yesu?

2 Sa’ad da yake fuskantar gwaji da wahala, Yesu ya zuba ido ga gaba kuma ya yi bege ga Jehobah. “Ya jimre da giciye domin farin zuciya da aka sa gabansa, yana rena kunya, ya kuwa zauna ga hannun dama na al’arshen Allah.” (Ibraniyawa 12:2) Domin Yesu ya mai da hankali ga kunita ikon mallakar Jehobah da kuma tsarkake sunansa, bai taɓa janyewa daga tafarkinsa na yin biyayya ga Allah ko da menene zai jimre.

3. Wane hakki ne bege yake da shi a rayuwar bayin Allah?

3 Sarki Dauda ya ambata nasabar da ke tsakanin bege da gaba gaɗi, yana cewa: “Ka yi sauraro ga Ubangiji: Ka ƙarfafa, ka bar zuciyarka ta ɗauki ƙarfin rai; I, ka yi sauraro ga Ubangiji.” (Zabura 27:14) Idan muna son mu kasance da bege mai ƙarfi, ba za mu bar begenmu ya zama fata ko abu marar tabbaci ba amma koyaushe mu ɗauke shi da tamani. Yin haka zai taimake mu mu yi koyi da Yesu wajen nuna gaba gaɗi da himma sa’ad da muke aikin da ya ce almajiransa su yi. (Matta 24:14; 28:19, 20) Hakika, da yake an ambata bege cikin Littafi Mai Tsarki tare da bangaskiya da ƙauna, wannan ya nuna cewa hali ne mai muhimmanci da ya kamata bayin Allah su riƙa nunawa sosai a rayuwarsu.—1 Korinthiyawa 13:13.

Ka “Yalwata Cikin Bege” Kuwa?

4. Menene Kiristoci shafaffu da abokansu “waɗansu tumaki” suke sauraro?

4 Mutanen Allah suna da bege mai ban al’ajabi a gabansu. Shafaffun Kiristoci suna jiran yin hidima da Kristi a sama, “waɗansu tumaki” kuma suna da begen “tsira daga bautar ɓacewa zuwa cikin ’yanci na darajar ’ya’yan Allah [na duniya].” (Yohanna 10:16; Romawa 8:19-21; Filibbiyawa 3:20) Wannan “ ’yanci na daraja” ya ƙunshi ceto daga zunubi da mugun sakamakonsa. Hakika, Jehobah mai ba da “kowacce kyakkyawar baiwa, da kowacce cikakkiyar kyauta” zai ba masu aminci a gare shi abu mafi kyau.—Yaƙub 1:17; Ishaya 25:8.

5. Ta yaya muke “yalwata cikin bege”?

5 Wane hakki ne bege yake da shi a rayuwarmu? Romawa 15:13 ta ce: ‘Allah kuwa na bege ya cika ku da dukan farin zuciya da salama cikin bada gaskiya, domin ku yalwata cikin bege, cikin ikon Ruhu Mai-tsarki.’ Hakika, ba za a kwatanta bege da kyandir da ke haskaka duhu ba, amma da haske na fitowar rana, da ke sa mutum ya kasance da salama, farin ciki, manufa, da gaba gaɗi a rayuwa. Muna “yalwata cikin bege” sa’ad da muka gaskata da Kalmar Allah kuma muka sami ruhunsa mai tsarki. Romawa 15:4 ta ce: “Iyakar abin da aka rubuta a dā aka rubuta su domin koyarwarmu, domin ta wurin haƙuri da ta’aziyyar littattafai mu zama da bege.” Saboda haka, ka tambayi kanka: ‘Ina sa bege na ya yi haske ta wajen karanta Littafi Mai Tsarki kullum? Ina addu’a koyaushe don ruhun Allah?’—Luka 11:13.

6. Don begenmu ya yi haske, menene za mu guje wa?

6 Kalmar Allah ce ta ƙarfafa Yesu wanda muke bin Misalinsa. Ta wajen bin misalinsa sosai, za mu kauce wa ‘gajiya da yin suwu cikin rayukanmu.’ (Ibraniyawa 12:3) Ya kamata mu tuna cewa idan muka daina kasancewa da bege ga Allah ko kuma wasu abubuwa suka janye hankalinmu, wataƙila abubuwan mallaka ko kuma makasudai na duniya, ba da daɗewa ba gajiya na ruhaniya zai sha kanmu, daga baya za mu yi hasarar ƙarfi da gaba gaɗi na yin rayuwa bisa ƙa’idodi na ɗabi’a. Idan muna da irin wannan halin muna iya ‘lalata’ imaninmu. (1 Timothawus 1:19) A wani sassa kuma, bege na gaskiya na ƙarfafa bangaskiyarmu.

Bege Yana da Muhimmanci ga Bangaskiya

7. Yaya bege yake da muhimmanci ga bangaskiya?

7 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Bangaskiya fa ainin abin da mu ke begensa ne, tabbatawar al’amuran da ba a gani ba.” (Ibraniyawa 11:1) Saboda haka, bege ba ƙaramin abu ne kawai ga bangaskiya ba, sashe ne mai muhimmanci na bangaskiya. Ga misalin Ibrahim. A ra’ayin ɗan adam, sa’ad da Jehobah ya yi musu alkawarin magāji, da shi da matarsa Saratu sun wuce shekarun haihuwa. (Farawa 17:15-17) Yaya Ibrahim ya aikata? ‘Shi wannan bisa ga kafa bege ya bada gaskiya saɓanin tsammani, da za ya zama uban al’ummai dayawa.’ (Romawa 4:18) Hakika, begensa ga Allah ya ƙarfafa bangaskiyar Ibrahim cewa zai sami ɗa. Bangaskiyarsa kuma ta haskaka da kuma ƙarfafa begensa. Ibrahim da Saratu sun kasance da gaba gaɗin barin gidansu da danginsu kuma su yi sauran rayuwarsu a tanti a wata ƙasa!

8. Ta yaya jimrewa cikin aminci yake ƙarfafa begenmu?

8 Ibrahim ya ƙarfafa begensa ta yin biyayya ga Jehobah ƙwarai, ko sa’ad da yin haka yake da wuya. (Farawa 22:2, 12) Hakanan ma, ta wajen biyayyarmu da jimrewarmu a hidimar Jehobah, muna da tabbaci cewa za mu sami lada. Bulus ya rubuta cewa “haƙuri” na kawo “gwadawa” da ke sa a kasance da bege, “bege kuma ba ya kunyatarwa.” (Romawa 5:4, 5) Shi ya sa kuma Bulus ya rubuta: ‘Muna kuwa so kowane ɗayanku shi nuna wannan ƙwazo zuwa ga tabbatawar bege har ƙarshe.’ (Ibraniyawa 6:11) Irin wannan ra’ayi mai kyau, da ke bisa dangantaka na kud da kud da Jehobah zai taimake mu mu fuskanci kowace matsala da gaba gaɗi da farin ciki.

“Kuna Murna Cikin Bege”

9. Yin menene a kai a kai zai taimake mu mu yi “murna cikin bege”?

9 Begen da Allah ya yi mana alkawarinsa ya fi kome da duniya za ta ba mu. Zabura 37:34 ta ce: “Ka yi sauraro ga Ubangiji, ka kiyaye tafarkinsa, shi kuma za ya ɗaukake ka ka gaji ƙasar: lokacinda an datse miyagu, ka gani.” Hakika, muna da dalilin “murna cikin bege.” (Romawa 12:12) Amma, domin mu yi hakan, dole ne mu ci gaba da tunani game da begenmu. Kana tunani game da begen da Allah ya yi maka alkawarinsa a kai a kai kuwa? Kana ganin kanka cikin Aljanna da koshin lafiya, ba ka alhini, mutanen da kake ƙauna sun kewaye ka, kuna aiki mai gamsarwa tare? Kana bimbini game da hotunan Aljanna da suke cikin littattafanmu? Ana iya kwatanta yin irin wannan bimbini a kai a kai da share taga da yake sa ya riƙa haske. Idan ba mu goge madubin ba, ba da daɗewa ba datti zai hana mu ganin yanayin masu kyau. Wasu abubuwa za su janye hankalinmu. Kada mu ƙyale hakan ya faru!

10. Me ya sa sauraron lada zai sa dangantakarmu da Jehobah ya yi kyau?

10 Hakika, ƙaunar da muke masa ne ainihin dalilin da ya sa muke bauta wa Jehobah. (Markus 12:30) Duk da haka, ya kamata mu saurari ladar. Jehobah yana son mu yi hakan! Ibraniyawa 11:6 ta ce: “Ba shi kuwa yiwuwa a gamshe shi ba sai tare da bangaskiya: gama mai-zuwa wurin Allah sai shi bada gaskiya akwai shi, kuma shi mai-sākawa ne ga waɗanda ke biɗarsa.” Me ya sa Jehobah yake so mu ɗauke shi Mai Sakawa? Idan mun yi hakan, muna nuna mun san Ubanmu na samaniya da kyau. Shi mai alheri ne kuma yana ƙaunar yaransa. Ba za mu yi farin ciki ba kuma za mu riƙa sanyin gwiwa da sauri idan ba mu da “bege mai-kyau.”—Irmiya 29:11.

11. Ta yaya begensa ga Allah ya taimaki Musa ya tsai da shawara mai kyau?

11 Musa fitaccen misali ne na wanda ya manne wa begensa ga Allah. Da yake shi “ɗan ɗiyar Fir’auna” ne Musa yana da iko, matsayi, da kuma arzikin Masar. Zai biɗi waɗannan abubuwa ne, ko kuwa zai bauta wa Jehobah? Musa da gaba gaɗi ya zaɓi ya bauta wa Jehobah. Me ya sa? Domin ‘yana sauraron sakamakon.’ (Ibraniyawa 11:24-26) Hakika, Musa bai yi sakaci game da begen da Jehobah ya kafa a gabansa ba.

12. Me ya sa begen Kirista yake kamar kwalkwali?

12 Manzo Bulus ya kwatanta bege da kwalkwali. Kwalkwalinmu na alama yana kāre hankalinmu, yana taimakonmu mu tsai da shawara mai kyau, mu sa abubuwa masu kyau da suka fi muhimmanci a gaba, kuma mu riƙe aminci. (1 Tassalunikawa 5:8) Kana sanya kwalkwalinka na alama koyaushe? Idan kana hakan, kamar Musa da Bulus ba za ka kafa begenka “bisa wadata marar-tsayawa, amma bisa Allah, wanda ke ba mu kome a yalwace mu ji daɗinsu.” Hakika, ƙin biɗe-biɗe na son kai da ke ko’ina a duniya na bukatar kasancewa da gaba gaɗi, amma kwalliya ce da ta biya kuɗin sabulu! Ballantana ma, ba abin da za a gwada da “hakikanin rai” da ke jiran waɗanda suke bege ga Jehobah kuma suna ƙaunarsa.—1 Timothawus 6:17, 19.

“Daɗai Ba Ni Tauye Maka Ba”

13. Wane tabbaci ne Jehobah ya ba bayinsa masu aminci?

13 Dole ne mutane da suka kafa begensu a kan wannan zamani su yi tunani sosai game da mugun abin da ke jiransu yayin da ‘wahalar’ wannan duniya take ƙaruwa. (Matta 24:8) Amma waɗanda suke bege ga Jehobah ba sa jin irin wannan tsoron. Za su ci gaba da zama “rai a kwance, ba tsoron masifa ba.” (Misalai 1:33) Domin ba su kafa begensu a kan wannan zamani ba, suna biyayya da gargaɗin Bulus da farin ciki: “Ku kawarda hankalinku daga ƙaunar kuɗi; ku haƙura da abin da ku ke da shi: gama shi da kansa ya ce, daɗai ba ni tauye maka ba, daɗai kuwa ba ni yashe ka ba.”—Ibraniyawa 13:5.

14. Me ya sa bai kamata Kiristoci su yi alhini ainun game da bukatunsu na rayuwa ba?

14 Wannan furci “daɗai” ya nuna sarai cewa Allah zai kula da mu. Yesu ya kuma tabbatar mana cewa Allah yana damuwa da mu, yana cewa: “Ku fara biɗan mulkinsa, da adalcinsa; waɗannan abu duka fa [abin biyan bukatar rayuwa] za a ƙara muku su. Kada fa ku yi alhini a kan gobe: gama gobe za ya yi alhini don kansa.” (Matta 6:33, 34) Jehobah ya san cewa yana da wuya mu kasance da himma don Mulkinsa kuma mu ɗauki hakkin biyan bukatunmu na zahiri. Saboda haka bari mu amince da iyawarsa da sha’awarsa na son ya biya bukatunmu.—Matta 6:25-32; 11:28-30.

15. Ta yaya Kiristoci suke sa idonsu ya zama “sosai”?

15 Muna nuna mun dogara ga Jehobah sa’ad da muka sa ‘idonmu sosai.’ (Matta 6:22, 23) Mutum da idonsa sosai ne yana faɗan gaskiya, yana da ra’ayi mai kyau, ba ya hadama da biɗan buri na son kai. Amma kasancewa da ido da ke sosai ba ya nufin rayuwar talauci mai tsanani ko kuma yin ƙyaliya game da kula da ayyukan ikilisiya. Maimakon haka, yana nufin ‘horon’ kanmu yayin da muke saka hidimar Jehobah farko.—2 Timothawus 1:7.

16. Me ya sa muke bukatar bangaskiya da gaba gaɗi don idonmu ya kasance sosai?

16 Kasancewa da ido da ke sosai na bukatar bangaskiya da gaba gaɗi. Alal misali, idan shugaban aikinka ya nace ka riƙa aiki a lokacin taron Kirista, za ka manne wa abubuwa na ruhaniya da ka sa a gaba da gaba gaɗi? Idan mutum yana shakka cewa Jehobah zai cika alkawarinsa na kula da bayinsa, Shaiɗan zai ƙara matsin kuma irin wannan mutumin yana iya daina halartan taro gabaki ɗaya. Hakika, idan mun yi rashin bangaskiya Shaiɗan zai riƙa kafa mana abubuwa da suka fi muhimmanci, ba Jehobah ba. Wannan zai zama bala’i!—2 Korinthiyawa 13:5.

“Ka Yi Sauraro ga Ubangiji”

17. Ta yaya ake yi wa waɗanda suka dogara ga Jehobah albarka yanzu?

17 A kai a kai Nassosi sun nuna cewa waɗanda suke da bege kuma suke dogara ga Jehobah ba sa rashi. (Misalai 3:5, 6; Irmiya 17:7) Hakika, wani lokaci suna rashin abin biyan bukata, amma wannan ba kome ba ne idan aka gwada da albarka da ke jiransu nan gaba. Da haka sun nuna cewa suna “sauraro ga Ubangiji” kuma suna da tabbaci cewa zai biya muradin zuciyar amintattunsa. (Zabura 37:4, 34) Shi ya sa, suke farin ciki da gaske. “Begen masu-adilci za ya zama farin zuciya: Amma gurin miyagu za ya lalace.”—Misalai 10:28.

18, 19. (a) Wane tabbaci ne Jehobah ya ba mu? (b) Ta yaya muke sa Jehobah a ‘hannun damanmu’?

18 Sa’ad da ƙaramin yaro yake tafiya da babansa yana riƙe da hannunsa, ba ya jin tsoro. Haka muke ji yayin da muke tafiya da Ubanmu na samaniya. Jehobah ya gaya wa Isra’ilawa, “kada ka ji tsoro; gama ina tare da kai, . . . ni taimake ka. . . . Gama ni Ubangiji Allahnka zan riƙe hannun damanka, in ce maka, kada ka ji tsoro, ni taimake ka.”—Ishaya 41:10, 13.

19 Kwatanci ne mai kyau a ce Jehobah yana riƙe hannun mutum. Dauda ya rubuta: “Na sa Ubangiji a gabana tuttur: Da shi ke yana ga hannun damana ba zan jijjigu ba.” (Zabura 16:8) Ta yaya muke sa Jehobah a ‘hannun damanmu’? Muna haka ta hanyoyi biyu. Na ɗaya, muna barin Kalmarsa ta yi mana ja-gora a kowane fanni na rayuwa, na biyu, muna mai da hankali ga lada mai tamani da Jehobah ya kafa a gabanmu. Mai zabura Asaph ya rera waƙa yana cewa: “Duk da haka kullum ina tare da kai: ka riƙe ni a hannuna na dama. Za ka bishe ni da shawararka, bayan wannan kuma za ka karɓe ni zuwa daraja.” (Zabura 73:23, 24) Da irin wannan tabbaci, za mu fuskanci nan gaba da gaba gaɗi.

“Fansarku ta Kusa”

20, 21. Menene ke jiran waɗanda suke da bege ga Jehobah?

20 Da shigewar kowace rana, yana daɗa zama da gaggawa mu sa Jehobah a hannunmu na dama. Ba da daɗewa ba, za a soma halaka addinin ƙarya, duniyar Shaiɗan za ta fuskanci ƙunci da ba a taɓa yi ba. (Matta 24:21) Tsoro zai kama ’yan adam marasa bangaskiya. Duk da haka a wannan lokaci na ruɗewa, bayin Jehobah masu gaba gaɗi za su yi murna cikin bege! Yesu ya ce: “Sa’anda waɗannan al’amura sun soma faruwa, ku duba bisa, ku tada kanku; gama fansarku ta kusa.”—Luka 21:28.

21 Saboda haka, bari mu yi farin ciki a begenmu ga Allah kuma kada mu ƙyale abubuwan janye hankali na Shaiɗan su ruɗe mu ko kuma su gwada mu. Yayin nan kuma, bari mu yi aiki tuƙuru mu kasance da bangaskiya, ƙauna, da tsoron Allah. Ta yin haka, za mu kasance da gaba gaɗi mu yi biyayya ga Jehobah a dukan yanayi kuma mu yi tsayayya da Iblis. (Yaƙub 4:7, 8) Hakika, “ku ƙarfafa, bari zuciyarku ta yi gaba gaɗi, dukanku masu-sauraro ga Ubangiji.”—Zabura 31:24.

[Hasiya]

a Ko a cikin Nassosin Kirista na Helenanci sau da yawa an yi amfani da kalmar nan “bege” ga shafaffu Kiristoci da za su sami ladar zama a sama, a wannan talifin an tattauna bege da ya shafi kowa.

Za Ka Iya Amsawa?

• Ta yaya begen Yesu ya sa ya kasance da gaba gaɗi?

• Ta yaya bangaskiya da bege suke da nasaba da juna?

• Ta yaya bege tare da bangaskiya za su sa Kirista ya kasance da gaba gaɗi don ya kafa abubuwa masu kyau da suka fi muhimmanci a rayuwa?

• Me ya sa waɗanda suke ‘sauraro ga Ubangiji’ suke jiran nan gaba da gaba gaɗi?

[Hoto a shafi na 28]

Ko kai yaro ne ko babba, kana ganin kanka cikin Aljanna?

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba