Tambayoyi Daga Masu Karatu
Ya dace da Yakubu ya yi kamar shi ne Isuwa, kamar yadda aka rubuta a Farawa 27:18, 19?
Wataƙila ka san wannan labarin sosai. A lokacin da Ishaƙu ya tsufa ya gaya wa Isuwa ya je ya farauto masa nama, yana cewa: “In ci raina kuma ya albarkace ka tun ban mutu ba.” Sa’ad da ta ji abin da maigidanta ya ce, Rifkatu ta shirya soye mai daɗi kuma ta umurci Yakubu: “Za ka kai [abincin] wurin ubanka kuma, domin ya ci, ya albarkace ka kuma, tun ba ya mutu ba.” Bayan ta yafa wa Yakubu tufafin Isuwa kuma ta sa fatun awaki a wuyansa da hannuwansa, sai ya tafi wurin ubansa da soyen mai daɗi. Sa’ad da Ishaƙu ya tambaye shi “Wanene kai, ɗana?” Yakubu ya ce: “Ni ne Isuwa ɗan farinka.” Ishaƙu ya yarda da abin da ya ce kuma ya albarkace shi.—Farawa 27:1-29.
Littafi Mai Tsarki bai gaya mana dukan dalilan da ya sa Rifkatu da Ishaƙu suka yi haka ba, ko da yake ya nuna cewa yanayin ya taso ne ba za to ba tsammani. Ya kamata mu san cewa Kalmar Allah ba ta amince ko kuwa haramta abin da Rifkatu da Yakubu suka yi ba, kuma wannan labarin bai ba da hujjar yin ƙarya da ruɗi ba. Amma, Littafi Mai Tsarki ya ba da ƙarin haske a kan yanayin.
Na farko, labarin ya bayyana dalla-dalla cewa Yakubu ya cancanci ya sami albarkar babansa; amma Isuwa bai cancanta ba. A dā, Yakubu ya sayi damar ɗan fari daga ɗan’uwansa marar godiya, wanda ya sayar da damar domin yunwar da yake ji. Isuwa ya wulakanta “gādonsa na haifuwa.” (Farawa 25:29-34) Saboda haka, sa’ad da ya je wajen babansa, Yakubu yana neman albarka wadda tasa ce.
Na biyu, sa’ad da Ishaƙu ya gane cewa ya riga ya albarkaci Yakubu, bai nemi ya canja abin da ya riga ya yi ba. Wataƙila ya tuna abin da Jehobah ya gaya wa Rifkatu kafin ta haifi ’yan biyun: “Babban kuma za ya bauta ma ƙaramin.” (Farawa 25:23) Ya kamata mu tuna cewa sa’ad da Yakubu yake son ya tafi Haran, Ishaƙu ya daɗa albarkar da ya yi masa a dā.—Farawa 28:1-4.
A ƙarshe, ya kamata a tuna cewa Jehobah yana sane kuma yana sha’awar dukan abubuwan da ke faruwa. Albarkar da Ishaƙu ya yi ta jitu ne da alkawarin da Allah ya yi wa Ibrahim. (Farawa 12:2, 3) Da a ce Allah ba ya son Yakubu ya sami wannan albarkar, da ya ɗauki mataki. Maimakon haka, Jehobah ya tabbatar da batun ga Yakubu, yana cewa: “Cikin zuriyanka dukan kabilan duniya za su sami albarka.”—Farawa 28:10-15.