Ku Koyar Da Yaranku
Timothawus Yana Shirye Ya Yi Hidima
“KA shirya?” An taɓa yi maka irin wannan tambayar? Mutumin da ya yi wannan tambayar yana so ya sani ne ko kana shirye. Alal misali, wataƙila mutumin yana nufi ne ko: “Kana tare da littafinka na nazari? Ka karanta darasinka?’ Kamar yadda za mu gani, Timothawus a shirye yake.
Timothawus kuma mai yardar rai ne. Ka san abin da wan nan yake nufi? Sa’ad da aka gayyaci Timothawus ya bauta wa Allah, yana da irin halin wani cikin bayin Allah, wanda ya ce: “Ga ni; Ka aike ni.” (Ishaya 6:8) Domin yana shirye kuma yana so ya yi hidima da yardar ransa, Timothawus ya more rayuwa mai ban sha’awa. Za ka so sa ji labarinsa?
An haifi Timothawus a Urushalima mil mai nisa ƙwarai daga Listira. Kakarsa Lois da mamarsa Eunice, ɗaliban Nassosi ne na kirki. Sa’ad da Timothawus yake ƙarami suka fara koya masa Kalmar Allah.—2 Timothawus 1:5; 3:15.
Wataƙila sa’ad da Timothawus yake matashi ne, manzo Bulus, tare da Barnaba, suka ziyarci Listira a doguwar tafiyarsu ta wa’azi ta farko. Wataƙila a wannan lokacin ne mamar Timothawus da kakarsa suka zama Kiristoci. Za ka so ka ji irin masifa da Bulus da Barnaba suka fuskanta? Mutane da ba sa son Kiristoci suka yi ta jifan Bulus da duwatsu, suka sumar da shi suka ja shi zuwa bayan gari. Suna tsammanin ya riga ya mutu.
Waɗanda suka yarda da abin da Bulus yake koyarwa suka taru a wurinsa, sai ya tashi. Washegari, Bulus da Barnaba suka tafi, amma suka koma Listira nan ba da daɗewa ba. Sa’ad da suka yi haka, Bulus ya ba da jawabi ya gaya wa almajiran: “Sai ta wurin wahala dayawa za mu shiga mulkin Allah.” (Ayyukan Manzanni 14:8-22) Ka san abin da Bulus yake nufi? Abin da yake nufi shi ne wasu za su ba wa waɗanda suke bauta wa Allah wahala. Daga baya Bulus ya rubuta wa Timothawus a wasiƙa: “Dukan waɗanda su ke so su yi rai mai-ibada cikin Kristi Yesu za su sha tsanani.”—2 Timothawus 3:12; Yohanna 15:20.
Bayan da Bulus da Barnaba suka bar Listira sai suka koma garinsu. Bayan ’yan watanni, Bulus ya ɗauki Sila su yi tafiya tare, tare kuma suka tafi su ƙarfafa sababbin almajirai a wuraren da Bulus ya ziyarta da farko. Da suka isa Listira, Timothawus ya yi farin ciki ƙwarai da ya sake ganin Bulus! Farin cikin Timothawus ya ƙaru sosai sa’ad da aka gayyace shi ya bi Bulus da Sila. Timothawus ya yarda. Yana shirye zai bi su da yardar rai.—Ayukan Manzanni 15:40–16:5.
Su ukun suka tafi tare, suka yi tafiyar mil masu yawa, sai suka shiga jirgin ruwa. Bayan da suka isa bakin teku, sai suka taka zuwa Tassalunika. A nan mutane da yawa suka zama Kiristoci. Amma wasu suka yi fushi suka tara taron ’yan banza. Bulus, Sila, da Timothawus suna cikin haɗari saboda haka suka fice, suka tafi Biriya.—Ayukan Manzanni 17:1-10.
Bulus ya damu saboda sababbin almajirai da suke Tassalunika, sai ya aiki Timothawus ya koma wurin. Ka san abin da ya sa? Daga baya Bulus ya yi bayani ga Kiristoci da ke Tassalunika: ‘Domin ya ƙarfafa ku ya yi muku ta’aziyya domin kada kowa ya yi sanyi gwiwa.’ Ka san abin da ya sa Bulus ya aiki saurayi Timothawus zuwa irin wannan aiki mai haɗari? ’Yan hamayyan ba su san Timothawus ba sosai, kuma ya yarda zai je da son ransa. Wannan yana bukatar gaba gaɗi ƙwarai! Yaya sakamakon ziyarar? Sa’ad da Timothawus ya koma wurin Bulus, ya gaya wa Bulus yadda Tassalunikawa suke da aminci. Saboda haka Bulus ya rubuta musu wasiƙa: “Da ƙuncinmu muka ta’azantu a kanku.”—1 Tassalunikawa 3:2-7.
Timothawus ya yi hidima da Bulus shekaru goma da suka biyo baya. Sa’ad da aka saka Bulus a kurkuku a Roma, da kuma Timothawus wanda shi ma kansa ba da daɗewa ba aka sake shi daga kurkuku, ya je wajensa. Sa’ad da yake kurkuku Bulus ya rubuta wasiƙa ga Filibbiyawa, wataƙila Timothawus ne sakatarensa. Bulus ya ce: ‘Ina da niya in aike Timothawus zuwa gareku in an jima kaɗan, domin ba ni da wani da ke da aminci kamarsa da zai yi muku hidima fiye da shi.’—Filibbiyawa 2:19-22; Ibraniyawa 13:23.
Waɗannan kalmomi lalle su faranta wa Timothawus rai! Bulus ya yi ƙaunar Timothawus ƙwarai domin yana shirye ya yi hidima da yardar rai. Muna fata kai ma za ka kasance haka.
Tambayoyi:
○ A ina ne Timothawus ya girma, kuma menene ya faru sa’ad da Bulus ya ziyarci wurin da fari?
○ Menene Timothawus ya yi sa’ad da aka gayyace shi ya tafi tare da Bulus da Sila?
○ Ta yaya Timothawus ya nuna gaba gaɗi, kuma me ya sa Bulus ya ƙaunace shi sosai?
[Hoto a shafi na 18]
Menene ya faru?