Ka Kasance Da Ra’ayin Nassi Wajen Kula Da Lafiyarka
“Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan . . . azancinka, da dukan ƙarfinka.”—MARKUS 12:30.
1. Menene ainihin nufin Allah ga ’yan Adam?
CIWO da mutuwa ba sa cikin abubuwan da Jehobah Allah ya nufa ga halittunsa ’yan Adam. An saka Adamu da Hauwa’u a gonar Adnin, ko kuma ‘aljanna,’ su “kiyaye ta” ba na shekara 70 ko 80 ba, amma har abada. (Far. 2:8, 15; Zab. 90:10) Da a ce sun kasance da aminci ga Jehobah kuma suka miƙa kai ga mulkin mallakarsa na ƙauna, da ba za su taɓa sanin ciwo ba, tsufa da mutuwa.
2, 3. (a) Ta yaya aka kwatanta tsufa a littafin Mai-Wa’azi? (b) Wanene ya jawo mutuwar ’yan Adam, kuma ta yaya za a kawar da ita?
2 Littafin Mai Wa’azi sura ta 12 ta kwatanta “mugayen kwanaki” da ’yan Adam ajizai suke shaidawa sa’ad da suka tsufa. (Karanta Mai Wa’azi 12:1-7.) An kwatanta furfura da “itacen alboma.” An kwatanta ƙafafuwa da “majiya-ƙarfi” da yanzu sun raunana. Mata masu leƙe ta taga don samun haske amma sun duhunta, kwatanci ne mai kyau na idanun da ba sa gani sosai domin tsufa. Tun da yake tsofaffi za su rasa wasu haƙora, an kwatanta hakan da ‘masu-niƙa da suka daina aiki, domin ba su da yawa.’
3 Ainihi, ba nufin Allah ba ne mutane su tsufa su kasance da ƙafafu marasa ƙarfi, duhuntar idanu, da kuma rashin haƙora. Ƙari ga haka, mutuwar da muka gada daga Adamu, tana ɗaya daga cikin “aikin Iblis” da Ɗan Allah zai kawar ta wajen Mulkin Almasihu. Manzo Yohanna ya rubuta: “Dalilin bayyanuwar Ɗan Allah ke nan, shi halaka ayyukan Shaiɗan.”—1 Yoh. 3:8.
Ba Laifi Ba ne a Nuna Damuwa Daidai wa Daida
4. Me ya sa bayin Jehobah suke damuwa daidai wa daida game da lafiyarsu, amma menene suke sane da shi?
4 A yanzu, wasu a cikin bayin Jehobah suna fuskantar matsaloli na rashin lafiya da kuma tsufa da mutane masu zunubi suke fuskanta. Damuwa daidai wa daida game da lafiyarmu a irin waɗannan yanayi daidai ne kuma yana da amfani. Muna so mu bauta wa Jehobah da ‘dukan ƙarfinmu.’ (Mar. 12:30) Amma kuma, sa’ad da muke so mu kasance da koshin lafiya, ya kamata mu fahimci cewa babu abin da za mu iya yi da zai hana mu tsufa ko kuma mu guje wa dukan cututtuka.
5. Wane darasi ne za mu iya koya daga yadda amintattun bayin Allah suka jimre da rashin lafiya?
5 Amintattun bayin Jehobah masu yawa suna fama da rashin lafiya. Abafaroditas yana ɗaya daga cikinsu. (Filib. 2:25-27) Abokin tafiyar manzo Bulus, Timoti, yana yawan ciwon ciki, kuma Bulus ya shawarce shi ya riƙa shan “ruwan inabi kaɗan.” (1 Tim. 5:23) Bulus da kansa ya jimre da “masuki,” wataƙila ciwon ido ko wani ciwon da babu maganinsa a lokacin. (2 Kor. 12:7; Gal. 4:15; 6:11) Game da wannan “masuki,” da ke jikinsa, Bulus ya roƙi Jehobah sosai ya cire masa shi. (Karanta 2 Korantiyawa 12:8-10.) Allah bai cire wa Bulus ‘masukin cikin jikinsa’ ba ta hanyar mu’ujiza. Maimakon haka, Allah ya ƙarfafa shi ya jimre. Ƙarfin Jehobah ya bayyana a raunanar Bulus. Za mu iya koyan darasi daga wannan misalin kuwa?
Ka Guji Yawan Damuwa Game da Neman Magani
6, 7. Me ya sa za mu guji yawan damuwa da lafiyar mu?
6 Kamar yadda kuka sani, Shaidun Jehobah suna karɓan magunguna dabam-dabam don kasancewa da koshin lafiya. Sau da yawa jaridar Awake! tana ɗauke da talifofi game da lafiyar jiki. Ko da yake ba ma faɗin irin maganin da za a sha, muna godiya ga taimako da kuma haɗin kai na ƙwararrun masu kiwon lafiya. Hakika, mun san cewa ba zai yiwu a sami cikakkiyar lafiya ba. Saboda haka, kada mu ƙyale neman magani don samun lafiya ya ɗauke mana hankali. Ya kamata halinmu ya bambanta da na mutanen da ba su da “bege,” waɗanda suke tunanin cewa wannan rayuwar ita ce kawai kuma za su iya neman kowane irin magani domin su warkar da kansu. (Afis. 2:2, 12) Mun ƙuduri aniyar ba za mu yi hasarar amincewar Jehobah ba domin mu ceci ranmu na yanzu, muna da tabbaci cewa idan muka kasance da aminci ga Allah, za mu “riƙi rai wanda yake na hakika,” wato, rai madawwami a sabuwar duniya wadda Allah ya yi alkawari.—1 Tim. 6:12, 19; 2 Bit. 3:13.
7 Muna guje wa damuwa da yawa game da lafiyar mu domin wani dalili kuma. Yawan damuwa game da lafiyar mu za ta iya kai ga son kai. Bulus ya yi gargaɗi game da wannan haɗarin sa’ad da ya aririci Filibiyawa kada su ‘lura da na su abu, amma kowane a cikinsu ya lura da na waɗansu.’ (Filib. 2:4) Daidai ne mu kula da kanmu iyaka gwargwado, amma kuma kula da ’yan’uwanmu da kuma mutanen da muke yi wa “bisharan nan ta Mulkin” zai hana mu damuwa da yawa da lafiyarmu ta zahiri.—Mat. 24: 14.
8. Menene yawan damuwa game da lafiyar mu za ta iya sa mu yi?
8 Damuwa da lafiyar jiki za ta iya sa Kirista ya mai da al’amuran Mulki su kasance na biyu a rayuwarsa. Yawan damuwa da lafiyar jiki za ta iya sa mu cusa ra’ayoyinmu ga wasu game da muhimmancin wasu irin hanyoyin magani da kuma abinci. Game da wannan batun, ka yi la’akari da mizanan da ke cikin kalmomin Bulus: “Ku gwada mafifitan al’amura; domin ku zama sahihai da marasa-abin tuntuɓe kuma zuwa ranar Kristi.”—Filib. 1:10.
Menene Ya Fi Muhimmanci?
9. Menene ɗaya daga cikin abubuwa mafi muhimmanci da bai kamata mu yi watsi da shi ba, me ya sa?
9 Idan muna mai da hankali ga abubuwa mafi muhimmanci, za mu saka hannu sosai a aikin taimaka wa mutane su kasance da dangantaka mai kyau da Allah. Ana cim ma hakan ne ta wajen wa’azi da koyar da Kalmar Allah. Waɗannan ayyuka suna amfanar mu da kuma waɗanda muka koyar. (Mis. 17:22; 1 Tim. 4:15, 16) Jifa-jifa, Hasumiyar Tsaro da kuma Awake! suna ƙunshe da talifofi game da ’yan’uwanmu maza da mata na ruhaniya da suke mugun rashin lafiya. Waɗannan labaran a wasu lokatai sun bayyana yadda suka jimre matsalolinsu ko kuma yadda suka mance da matsalolin na ɗan lokaci, ta wajen neman zarafi su taimaki mutane su san Jehobah da kuma alkawuransa masu ban sha’awa.a
10. Me ya sa irin maganin da muka zaɓa yake da muhimmanci?
10 Sa’ad da muke fuskantar matsala ta rashin lafiya, kowanne Kirista da ya balaga “za ya ɗauki kayan kansa” na hakkin zaɓan irin maganin da za a yi masa. (Gal. 6: 5) Amma kuma ya kamata mu tuna cewa irin maganin da muka zaɓa yana da muhimmanci ga Jehobah. Kamar yadda daraja mizanan Littafi Mai Tsarki yake motsa mu mu guje wa “jini,” hakanan ma, daraja Kalmar Allah ya kamata ta motsa mu mu guje wa yin magani da zai yi wa ruhaniyarmu lahani ko kuma ya shafi dangantakarmu da Jehobah. (A. M. 15:20) Wasu hanyoyin suna amfani ne da mugun magani da yi daidai da sihiri. Jehobah ya ƙi Isra’ilawan da suka yi ridda suka juya ga sihiri. Ya ce: “Kada ku ƙara kawo hadayu na banza; turare abin ƙyama ne a gareni: tsayawar wata da assabbat, da kiran taron jama’a: ai! ba na iya jimrewa da su, mugunta ne, i, har da taro mai-saduda.” (Isha. 1:13) Lokacin rashin lafiya ba lokaci ba ne da ya kamata mu yi abin da zai hana Allah ya saurari addu’armu da kuma abin da zai ɓata dangantakarmu da shi.—Mak. 3: 44.
“Hankali” Yana da Muhimmanci
11, 12. Ta yaya za mu yi amfani da “hankali” sa’ad da muke zaɓan irin maganin da muke so?
11 Sa’ad da ba mu da lafiya, kada mu yi tsammanin cewa Jehobah zai warkar da mu ta hanyar mu’ujiza, amma muna iya yin addu’a mu roƙi hikima domin mu zaɓi maganin da ya dace. Ya kamata mizanan Littafi Mai Tsarki da kuma tunanin kirki su taimake mu mu zaɓi magani mai kyau. Idan ciwon mai tsanani ne, hikima ce mu tuntuɓi masana da yawa, cikin jituwa da abin da Misalai 15:22 ta ce: “Wurinda babu shawara, nufe nufe su kan warware: Amma cikin taron masu-shawara su kan tabbata.” Manzo Bulus ya aririci ’yan’uwa masu bi su “rayu da hankali da adalci da ibada cikin wannan zamani na yanzu.”—Tit. 2:12.
12 Yanayin mutane da yawa a yau ya yi daidai da ta wata mace marar lafiya a zamanin Yesu. A Markus 5:25, 26, mun karanta: “Wata mace kuma, wadda ta shekara goma sha biyu tana zuba jini, ta sha wahala dayawa kuwa ga hannuwan masu-magani dayawa, ta ɓatasda dukan abin da ke wurinta, ba ta amfana komi ba, amma cuta ta riƙa daɗuwa.” Yesu ya warkar da wannan matar kuma ya tausaya mata. (Mar. 5:27-34) Domin damuwa, wasu Kiristoci za su ji kamar su zaɓi hanyoyin magani da suka saɓa wa mizanan bauta mai tsarki.
13, 14. (a) Ta yaya Shaiɗan zai iya yin amfani da hanyar magani da muka zaɓa ya karya amincinmu? (b) Me ya sa ya kamata mu ƙi duk wani abin da ke da ɗigon sihiri?
13 Shaiɗan zai yi amfani da kowace hanya don ya rinjaye mu daga bauta ta gaskiya. Kamar yadda yake amfani da lalata da kuma abin duniya don ya sa wasu su yi tuntuɓe, yana ƙoƙarin ya lalata amincin wasu ta wajen yin amfani da hanyoyin magani da suka yi daidai da yin amfani da sihiri. Muna yin addu’a ga Jehobah ya “cece mu daga Mugun” da kuma dukan “zunubi.” Kada mu ba da kanmu ga Shaiɗan ta wajen saka hannu cikin dukan wani abin da ya shafi sihiri.—Mat. 6:13; Tit. 2:14.
14 Jehobah ya hana Isra’ilawa yin duba da dabo. (K. Sha 18:10-12) Bulus ya lissafa “sihiri” a cikin “ayyukan jiki.” (Gal. 5:19, 20) Bugu da ƙari, “masu-sihiri” ba za su gaji sabuwar duniya ta Jehobah ba. (R. Yoh. 21:8) A bayyane yake cewa dukan wani abu da ke da ɗigon sihiri abin ƙyama ne a gun Jehobah.
“Bari Jimrewarku Ta Sanu”
15, 16. Me ya sa muke bukatar hikima yayin da muke neman magani, kuma wace shawara mai kyau ce hukumar mulki na ƙarni na farko ta bayar?
15 Saboda abubuwan da muka ambata a baya, idan muna shakkar wata hanyar magani, guje mata shi ya fi. Amma, domin ba za mu iya bayyana yadda wata hanyar magani take aiki ba, hakan ba ya nufin cewa maganin ya ƙunshi sihiri. Kasancewa da ra’ayin Nassi game da kula da lafiyar jiki yana bukatar hikima ta Allah da kuma tunanin kirki daga gare mu. A Misalai sura ta 3, mun sami wannan umurnin: “Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka, kada ka jingina ga naka fahimi: A cikin dukan al’amuranka ka shaida shi, shi kuma za ya daidaita hanyoyinka. . . . Ka kiyaye sahihiyar hikima da hankali kuma: Da haka za su zama rai ga ruhunka.”—Mis. 3:5, 6, 21, 22.
16 Sa’ad da muke ƙoƙarin mu kasance da koshin lafiya, dole ne mu mai da hankali kada mu yi rashin tagomashin Allah yayin da muke jimre rashin lafiya ko kuma tsufa. Wajen al’amarin magani, kamar yadda yake a kowane al’amari, ya kamata mu bari ‘jimrewarmu ta sanu ga dukan mutane’ ta wajen yin rayuwar da ta jitu da mizanan Littafi Mai Tsarki. (Filib. 4:5) A cikin wata wasiƙa mai muhimmanci, hukumar mulki na ƙarni na farko ta umurci Kiristoci su guje wa bautar gumaka, jini, da kuma fasikanci. Wannan wasiƙar ta haɗa da wannan tabbaci: “In kun tsare kanku daga waɗannan, za ku zauna lafiya.” (A. M. 15:28, 29, Littafi Mai Tsarki.) Ta wace hanya?
Kula da Lafiya Daidai wa Daida Yayin da Kuke Jiran Koshin Lafiya a Nan Gaba
17. Ta yaya muka amfana a zahiri ta wajen bin mizanan Littafi Mai Tsarki?
17 Ya kamata kowannenmu ya tambayi kansa, ‘Na fahimci kuwa sosai yadda na sami zaman lafiya domin ina bin mizanan Littafi Mai Tsarki game da jini da kuma fasikanci?’ Ka yi kuma tunanin irin amfanin da muka samu domin ƙoƙarin da muke yi na “tsarkake kanmu daga dukan irin ƙazamtar jiki da ta ruhu.” (2 Kor. 7:1) Ta wajen bin mizanan Littafi Mai Tsarki game da tsabta, muna samun kāriya daga cututtuka masu yawa. Mun sami zaman lafiya domin mun guje wa shan taba sigari da kuma miyagun ƙwayoyi da ke ƙazamtar da jiki da ruhu. Ka kuma yi tunanin lafiyar da muka samu daga ci da sha daidai wa daida. (Karanta Misalai 23:20; Titus 2:2, 3.) Ko da yake samun isashen hutu da kuma motsa jiki suna kyautata lafiyarmu, hakika, mun sami zaman lafiya a zahiri da kuma a ruhaniya ne domin mun bi umurnin Nassosi.
18. Me ya kamata ya zama ainihin damuwarmu, kuma wane annabci game da lafiya ne ya kamata mu jira cikarsa?
18 Fiye da kome, ya kamata mu kula da lafiyarmu ta ruhaniya kuma mu ƙarfafa dangantakarmu mai tamani da Ubanmu na samaniya, wanda shi ne Tushen ‘ranmu na yanzu, da mai zuwa’ a sabuwar duniya da ya yi alkawari. (1 Tim. 4:8; Zab. 36:9) A sabuwar duniya ta Allah, za a sami cikakkiyar lafiya ta ruhaniya da ta zahiri ta wurin gafarar zunubi bisa hadayar fansa ta Yesu. Ɗan ragon Allah, Yesu Kristi, zai yi mana ja-gora zuwa “maɓulɓulan ruwaye na rai,” kuma Allah zai ‘share dukan hawaye daga idanunmu.’ (R. Yoh. 7:14-17; 22:1, 2) A lokacin, za mu shaida cikar wannan annabcin mai ban sha’awa: “Wanda ya ke zaune a ciki ba za ya ce, Ina ciwo ba.”—Isha. 33:24.
19. Yayin da muke kula da lafiyar mu daidai wa daida, wane tabbaci ne muke da shi?
19 Muna da tabbaci cewa cetonmu ya yi kusa, kuma muna jiran ranar da Jehobah zai dakatar da ciwo da mutuwa. Amma a yanzu, muna da tabbaci cewa Ubanmu mai ƙauna zai taimake mu mu jimre azabobi da matsalolinmu domin ‘yana kula da mu.’ (1 Bit. 5:7) Saboda haka, bari mu ci gaba da kula da lafiyar jikinmu cikin jituwa da umurnin da ke rubuce cikin Kalmar Allah hurarriya!
[Hasiya]
a Za ka sami jerin irin waɗannan talifofi a akwatin da ke shafi na 17 na Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Satumba, 2003 na Turanci.
Domin Maimaitawa
• Wanene ya jawo rashin lafiya, kuma wanene zai cire sakamakon zunubi?
• Ko da yake daidai ne mu damu da lafiyar mu, me ya kamata mu ƙi?
• Me ya sa maganin da muka zaɓa yake da muhimmanci ga Jehobah?
• Game da lafiyar mu, ta yaya za mu amfana daga mizanan Littafi Mai Tsarki?
[Hoto a shafi na 23]
Ba a halicci ’yan Adam don su fuskanci ciwo da tsufa ba
[Hoto a shafi na 25]
Duk da matsaloli na rashin lafiya, mutanen Jehobah suna samun farin ciki a hidima