Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 4/1 pp. 24-25
  • Josiah Ya Zaɓi Ya Yi Abin da Ya Dace

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Josiah Ya Zaɓi Ya Yi Abin da Ya Dace
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Makamantan Littattafai
  • Josiah Ya Yi Abokan Kirki
    Ku Koyar da Yaranku
  • Josiah Yana Son Dokar Allah
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Sarkin Kirki Na Ƙarshe A Isra’ila
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Matasa, Wane Irin Rayuwa Ne Za Ku Yi?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 4/1 pp. 24-25

Ku Koyar Da Yaranku

Josiah Ya Zaɓi Ya Yi Abin da Ya Dace

KANA ganin yana da wuya a yi abin da ya dace ne?a— Idan ka ce e, mutane da yawa za su yarda da kai. Har ga manya ma, yin abin da suka sani ya dace yana da wuya. Bari mu ga abin da ya sa zai kasance da wuya Josiah ya zaɓi abin da ya dace. Ko ka san shi wanene?—

Josiah ɗan Amon ne, sarkin Yahuda, wanda yana ɗan shekara 16 da haihuwa sa’ad da aka haifi Josiah. Amon mugun mutum ne sosai, kamar ubansa Sarki Manasseh. Hakika, Manasseh mugun sarki ne na shekaru masu yawa. Sai Assuriyawa suka kama shi suka kai shi Babila. Sa’ad da yake cikin kurkuku, Manasseh ya roƙi Jehobah ya gafarta masa, kuma Jehobah ya yi hakan.

Sa’ad da aka saki Manasseh daga kurkuku, ya koma Urushalima kuma ya ci gaba da sarauta. Nan da nan sai ya daina muguntar da yake yi a dā, sai ya taimaki mutanen su bauta wa Jehobah. Ya yi baƙin ciki da ɗansa Amon bai bi misalinsa mai kyau ba. A wannan lokacin ne aka haifi Josiah. Littafi Mai Tsarki bai ambata ko sau nawa Manasseh ya tattauna da jikansa Josiah ba. Amma kana ganin cewa Manasseh zai yi ƙoƙari ya taimake shi ya bauta wa Jehobah?—

Sa’ad da Josiah yake ɗan shekara shida, Manasseh ya rasu, kuma Amon mahaifin Josiah ya zama sarki. Amon ya yi sarauta na shekara biyu ne kawai kafin bayinsa suka kashe shi. Shi ya sa Josiah ya zama sarkin Yahuda sa’ad da yake shekara takwas da haihuwa. (2 Labarbaru, sura 33) Menene kake ganin ya faru a wannan lokaci? Josiah ya zaɓi ya bi mugun misalin mahaifinsa Amon ne, ko kuma misali mai kyau na kakansa da ya tuba Manasseh?—

Ko da yake Josiah yaro ne, ya san cewa yana son ya bauta wa Jehobah. Shi ya sa ya saurari waɗanda suke ƙaunar Jehobah, maimakon abokanan mahaifinsa. Josiah yana ɗan shekara takwas ne kawai, amma ya san cewa ya dace ya saurari mutanen da suke ƙaunar Allah. (2 Labarbaru 34:1, 2) Kana son ka san wani abu game da waɗanda suka shawarci Josiah kuma suka zama abin koyi gare shi?—

Annabi Zephaniah ne ya kafa wa Josiah misali mai kyau. Shi dangin Josiah ne, daga zuriyar mahaifin Manasseh, Sarki Hezekiah mai alheri. A lokacin da Josiah ya soma sarauta, Zephaniah ya rubuta littafin Littafi Mai Tsarki da ke ɗauke da sunansa. Zephaniah ya yi gargaɗi game da miyagun abubuwa da za ta sami waɗanda ba su zaɓi su yi abin da ya dace ba, kuma Josiah ya saurari waɗannan gargaɗin.

Sai kuma Irmiya, wanda wataƙila ka ji labarinsa a dā. Irmiya da Josiah tsara ne kuma sun girma kusa da juna. Jehobah ya huri Irmiya ya rubuta littafin da ke cikin Littafi Mai Tsarki mai ɗauke da sunansa. Sa’ad da aka kashe Josiah a yaƙi, Irmiya ya rubuta waƙa ta musamman da ake kira waƙar makoki don ya nuna baƙin cikinsa. (2 Labarbaru 35:25) Yi tunanin yadda suka ƙarfafa juna don su kasance da aminci ga Jehobah.

Menene kake ganin za ka iya koya daga yin nazari game da Josiah?— Idan mahaifinka ba ya bauta wa Jehobah kamar mahaifin Josiah, akwai wanda zai iya taimakonka ka koyi game da Allah? Wataƙila mahaifiyarka ce, ko kakanninka, ko wani danginka. Wataƙila wani ne da yake bauta wa Jehobah, wani da mahaifiyarka ta yarda ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kai.

Ko da yake Josiah yaro ne, amma ya san cewa ya kamata ya yi abokai da mutanen da suke bauta wa Jehobah. Bari ka yi hakan kuma ka zaɓi ka yi abin da ya dace.

[Hasiya]

a Idan kana karanta wa yaro, wannan alamar fid da ma’ana tana nufin ka dakata, ka ƙarfafa shi ya faɗi ra’ayinsa.

Tambayoyi:

○ Wanene uban Josiah da kuma kakansa, kuma wane irin mutane ne su?

○ Wane gyara ne kakan Josiah ya yi a rayuwarsa?

○ Menene sunayen annabawa guda biyu da suka taimaki Josiah, kuma me ya sa kake ganin yana da muhimmanci a yi abokantaka da mutane kamar su?

[Hotunan da ke shafi na 25]

Ta yaya ne Zephaniah da Irmiya suka taimaki Josiah ya yi abin da ya dace?

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba