Yadda Zantattukan Yesu Ke Kawo Albarka
“[Yesu] ya hau cikin dutse . . . almajiransa suka zo wurinsa . . . ya yi ta koya musu.”—MAT. 5:1, 2.
1, 2. (a) A wane yanayi ne Yesu ya ba da Huɗubarsa na kan Dutse? (b) Ta yaya Yesu ya soma jawabinsa?
ASHEKARA ta 31 A.Z. Yesu ya ɗan dakatar da aikinsa na wa’azi a Galili don ya kiyaye Idin Ƙetarewa a Urushalima. (Yoh. 5:1) Da ya koma Galili, ya yi addu’a dukan dare don Allah ya yi masa ja-gora wajen zaɓan manzanni 12. Washegari, jama’a suka taru yayin da Yesu yake warkar da marasa lafiya. Tare da almajiransa da wasu da suke wajen, ya zauna a kan dutse kuma ya fara koyar da su.—Mat. 4:23–5:2; Luk 6:12-19.
2 Yesu ya soma jawabinsa, wato, Huɗuba a kan Dutse ta wajen nuna cewa mutum zai yi farin ciki ne idan yana da dangantaka mai kyau da Allah. (Karanta Matta 5:1-12.) Farin ciki ‘yanayi ne na zaman lafiya da ake samu ta wajen gamsuwa da kuma murna.’a Albarkatu tara da Yesu ya tattauna sun nanata dalilin da ya sa Kiristoci suke farin ciki, kuma suna da amfani a yau kamar yadda suke kusan shekaru 2,000 da suka shige. Bari yanzu mu tattauna kowannensu.
“Masu-Ladabia Ruhu”
3. Menene kasancewa masu ladabi a ruhu yake nufi?
3 “Masu-albarka ne masu-ladabi a ruhu: gama mulkin sama nasu ne.” (Mat. 5:3) “Masu-ladabi a ruhu” sun fahimci cewa suna bukatar ja-gorar Allah da kuma jin ƙansa.
4, 5. (a) Me ya sa masu albarka ne masu ladabi a ruhu? (b) Ta yaya za mu gamsar da bukatunmu na ruhaniya?
4 Masu albarka ne masu ladabi a ruhu, tun da “mulkin sama nasu ne.” Amincewa da Yesu a matsayin Almasihu ya ba almajiransa na farko zarafin yin sarauta da shi a Mulkin Allah na samaniya. (Luk 22:28-30) Idan muna da begen zama abokan gado da Kristi a sama ko kuma muna da begen samun rai madawwami a cikin aljanna a duniya a lokacin sarautar Mulki, za mu zama masu albarka idan da gaske mun san bukatarmu ta ruhaniya kuma mun fahinci cewa muna bukatar mu dogara da Allah.
5 Ba dukan mutane ba ne suka fahimci cewa suna da bukata ta ruhaniya, domin yawanci ba su da bangaskiya kuma ba sa son abubuwa masu tsarki. (2 Tas. 3:1, 2; Ibran. 12:16) Hanyoyin da za mu biya bukatunmu na ruhaniya sun ƙunshi yin nazarin Littafi Mai Tsarki sosai, nuna ƙwazo a aikin almajirantarwa, da kuma halartar taron Kirista a kai a kai.—Mat. 28:19, 20; Ibran. 10:23-25.
Masu Ɓacin Zuciya da Suke da “Albarka”
6. Su waye ne masu “ɓacin zuciya,” kuma me ya sa suke samun “albarka”?
6 “Masu albarka ne waɗanda su ke da ɓacin zuciya: gama za a yi masu ta’aziya.” (Mat. 5:4) Masu “ɓacin zuciya” da “masu-ladabi a ruhu” duk mutane iri ɗaya ne. Ba sa ɓacin zuciya don wahalar da suke fuskanta a rayuwa. Suna ɓacin zuciya ne domin yanayinsu na zunubi da kuma yanayin da ake ciki domin ajizancin ’yan adam. Me ya sa “albarka” ta tabbata ga irin waɗannan mutane masu ɓacin zuciya? Domin sun ba da gaskiya ga Allah da kuma Kristi kuma suna samun ƙarfafa ta wajen kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah.—Yoh. 3:36.
7. Menene ya kamata ya zama ra’ayinmu game da duniyar Shaiɗan?
7 Kowannenmu yana ɓacin zuciya domin rashin adalci da ke ko’ina a duniyar Shaiɗan? Yaya muke ji game da abin da wannan duniyar za ta bayar? Manzo Yohanna ya rubuta: “Dukan abin da ke cikin duniya, da kwaɗayin jiki, da sha’awar idanu, da darajar rai ta wofi, ba na Uba ba ne.” (1 Yoh. 2:16) Menene ya kamata mu yi idan muka fahimci cewa “ruhun duniya” wato, ikon da ke rinjayar mutanen da suke bare daga Allah, ya soma shafan ruhaniyarmu? Ya kamata mu yi addu’a sosai, mu yi nazarin Kalmar Allah, kuma mu nemi taimakon dattawa. Yayin da muka kusaci Jehobah, za mu sami ‘ta’aziyya,’ ko da menene ke sa mu baƙin ciki.—1 Kor. 2:12; Zab. 119:52; Yaƙ. 5:14, 15.
Yadda Albarka ta Tabbata ga “Masu-Tawali’u”
8, 9. Menene kasancewa da tawali’u yake nufi, kuma me ya sa irin waɗannan mutanen suke farin ciki?
8 “Masu-albarka ne masu-tawali’u: gama su za su gāji duniya.” (Mat. 5:5) “Sauƙin hali,” ko kuma tawali’u, ba yana nufin kasawa ko kuma nuna hankali a munafunce. (1 Tim. 6:11) Idan mu masu sauƙin hali ne, za mu nuna tawali’u ta wajen yin nufin Jehobah, mu kuma amince da ja-gorarsa. Za a ga cewa mu masu sauƙin hali ne a yadda muke bi da ’yan’uwa masu bi da kuma sauran mutane. Irin wannan tawali’un ya jitu da gargaɗin da manzo Bulus ya bayar.—Karanta Romawa 12:17-19.
9 Me ya sa albarka ta tabbata ga masu tawali’u? Domin “za su gāji duniya,” in ji Yesu wanda shi ma mai tawali’u ne. Shi ne magajin duniya na musamman. (Zab. 2:8; Mat. 11:29; Ibran. 2:8, 9) Amma, “masu-tarayyan gado da Kristi” waɗanda masu tawali’u ne, su ma za su gaji duniya tare da shi. (Rom. 8:16, 17) A ɓangaren duniya na Mulkin Yesu, mutane da yawa masu tawali’u za su more rai madawwami.—Zab. 37:10, 11.
10. Ta yaya rashin tawali’u zai shafi gatanmu na hidima da kuma dangantakarmu da mutane?
10 Kamar Yesu, ya kamata mu zama masu tawali’u. Amma, idan an san mu da halin son yin faɗa kuma fa? Irin wannan halin son faɗa da husuma za su iya sa mutane su guje mu. Idan ɗan’uwa ne da yake burin samun hakki a cikin ikilisiya, wannan halin zai sa ba zai cancanta ba. (1 Tim. 3:1, 3) Bulus ya gaya wa Titus ya ci gaba da tuna wa Kiristoci a Karita “su kasance marasa-faɗa, masu-laushin hali, suna nuna iyakacin tawali’u ga dukan mutane.” (Tit. 3:1, 2) Irin wannan tawali’u albarka ne ga mutane!
Suna Yunwa don “Adalci”
11-13. (a) Menene jin yunwa da ƙishirwa na adalci yake nufi? (b) Ta yaya za a ƙosar da waɗanda suke yunwa da ƙishirwa na adalci?
11 “Masu-albarka ne waɗanda suke yunwata suna ƙishirta zuwa adalci: gama za a ƙosaɗda su.” (Mat. 5:6) “Adalci” da Yesu yake nufi shi ne halin yin abin da yake da kyau ta wajen aikata daidai da nufin Allah da kuma dokokinsa. Mai zabura ya ce “ya karai saboda marmarin” hukuncin adalci na Allah. (Zab. 119:20) Muna ɗaukan adalci da tamani kuwa da har za mu yi marmarinta sosai?
12 Yesu ya ce waɗanda suke marmarin adalci za su yi farin ciki domin za a ‘ƙosar da su.’ Hakan ya yiwu bayan Fentakos na shekara ta 33 A.Z., domin ruhu mai tsarki na Jehobah a wannan lokacin ya soma “kāda duniya a kan . . . adalci.” (Yoh. 16:8) Ta wurin ruhu mai tsarki, Allah ya hure mutane su rubuta Nassosin Helenanci na Kirista, waɗanda suke da amfani “ga horo kuma da ke cikin adalci.” (2 Tim. 3:16) Ruhun Allah yana taimakonmu mu “yafa sabon mutum, wanda an halitta shi bisa ga Allah cikin adalci da tsarkin gaskiya.” (Afis. 4:24) Yana da ban ƙarfafa cewa waɗanda suka tuba kuma suka nemi gafarar zunubansu bisa hadayar fansa na Yesu suna iya samun adalci a gaban Allah.—Karanta Romawa 3:23, 24.
13 Ga yawancinmu, za a ƙosar da yunwa da ƙishirwa da muke ji sa’ad da muka samu rai madawwami a yanayi na adalci a duniya. Kafin lokacin, bari mu ƙuduri aniya mu yi rayuwa da ta jitu da mizanan Jehobah. Yesu ya ce: ‘Ku fara biɗan mulki, da adalcin [Allah].’ (Mat. 6:33) Yin hakan zai sa mu shagala da ayyukan da suka shafi bautar Allah kuma mu cika zuciyarmu da farin ciki.—1 Kor. 15:58.
Abin da Ya Sa Albarka ta Tabbata ga “Masu-Jinƙai”
14, 15. Ta yaya za mu nuna jin ƙai, kuma me ya sa albarka ta tabbata ga “masu-jin ƙai?
14 “Masu-albarka ne masu-jinƙai: gama su za su sami jinƙai.” (Mat. 5:7) Juyayi da tausayi ga mutane ne ke motsa “masu-jinƙai.” Ta mu’ujiza Yesu ya sauƙaƙa wahalar da mutane da yawa suke sha domin ya ji tausayinsu. (Mat. 14:14) Ana nuna jin ƙai a azanci na shari’a sa’ad da mutane suka gafarta wa waɗanda suka yi musu laifi, yadda Jehobah cikin jin ƙai yake gafarta wa waɗanda suka tuba. (Fit. 34:6, 7; Zab. 103:10) Muna iya nuna jin ƙai kamar haka da kuma kalamanmu da ayyuka na alheri da ke kawo sauƙi ga tsiyayyu. Hanya mai kyau na nuna jin ƙai ita ce ta gaya wa mutane gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Domin ya ji tausayin taron, Yesu ya “fara koya musu abubuwa da yawa.”—Mar. 6:34.
15 Muna da dalilin amincewa da furcin Yesu: “Masu-albarka ne masu-jinƙai: gama su za su sami jinƙai.” Idan muka nuna wa mutane jin ƙai, su ma za su yi mana hakan. Za mu ga cewa jin ƙai da muka nuna wa mutane zai sa ƙila Allah ba zai yi mana hukunci mai tsanani ba a lokacin hukuncinsa. (Yaƙ. 2:13) Masu jin ƙai ne kawai za a gafarta wa zunubansu kuma za su sami rai madawwami.—Mat. 6:15.
Abin da Ya Sa “Masu-Tsabtan Zuciya” Suke da Albarka
16. Menene kasancewa da “tsabtan zuciya” yake nufi, ta yaya waɗanda suke da wannan halin suke ‘ganin Allah’?
16 “Masu-albarka ne masu-tsabtan zuciya: gama su za su ga Allah.” (Mat. 5:8) Idan mu “masu-tsabtan zuciya” ne za a lura cewa dangantakarmu, sha’awoyinmu, da muradinmu za su kasance masu tsabta. Za mu nuna ‘ƙauna mai-fitowa daga zuciya mai-tsabta.’ (1 Tim. 1:5) Da yake zuciyarmu tana da tsabta, za mu ‘ga Allah.” Wannan ba ya nufin za mu ga Jehobah ido da ido, domin ‘mutum ba shi ganin [Allah] shi rayu.’ (Fit. 33:20) Amma, domin ya nuna halin Allah sarai, Yesu ya faɗi cewa: “Wanda ya gan ni ya ga Uban.” (Yoh. 14:7-9) A matsayin masu bauta wa Jehobah a duniya, muna iya ‘ganin’ Allah ta wajen barin ya aikata dominmu. (Ayu. 42:5) Ga shafaffu Kiristoci, za su ga Allah ido da ido sa’ad da aka tashe su zuwa rai ta ruhu kuma su ga Ubansu na samaniya.—1 Yoh. 3:2.
17. Ta yaya kasancewa da zuciya mai tsabta zai shafe mu?
17 Domin zuciya mai tsabta tana da tsabta a ɗabi’a da kuma ruhaniya, ba ta mai da hankali a kan abubuwa da ba su da tsabta a gaban Jehobah. (1 Laba. 28:9; Isha. 52:11) Idan muna da zuciya mai tsabta, abin da muka faɗa kuma muka yi zai kasance da tsabta, kuma munafunci ba zai kasance a hidimarmu ga Jehobah ba.
“Masu-Sada Zumunta” Sun Zama ’Ya’yan Allah
18, 19. Ta yaya “masu-sada zumunta” suke aikatawa?
18 “Masu-albarka ne masu-sada zumunta: gama za a ce da su ’ya’yan Allah.” (Mat. 5:9) Ana sanin “masu-sada zumunta” ta abin da za su yi da abin da ba za su yi ba. Idan mu irin mutane ne da Yesu yake magana, mu masu sada zumunta ne kuma ba za mu ‘saka ma wani mugunta da mugunta’ ba. Maimakon haka, a koyaushe za mu ‘biɗi abin da ke nagari ga dukan mutane.’—1 Tas. 5:15.
19 Kalmar Helenanci da aka fassara “sada-zumunta” a Matta 5:9 a zahiri tana nufin “masu son zaman lafiya.” Don mu kasance a cikin masu sada zumunta, dole ne mu zama masu son zaman lafiya. Masu ƙulla zumunci ba sa yin duk wani abin da zai ‘raba abokan gaske.’ (Mis. 16:28) A matsayin masu sada zumunta, muna ɗaukan matakai mu “nemi salama da dukan mutane.”—Ibran. 12:14.
20. Su wanene yanzu “ya’yan Allah,” kuma waye daga baya zai zama ɗan Allah?
20 Masu sada zumunta suna farin ciki domin “za a ce da su ’ya’yan Allah.” Jehobah ya zaɓi shafaffu Kiristoci masu aminci kuma su “’ya’yan Allah” ne. Sun riga sun ƙulla dangantaka na kud da kud da Jehobah a matsayin yaransa domin sun ba da gaskiya ga Kristi kuma suna bauta wa ‘Allah na ƙauna da na salama’ da dukan zuciyarsu. (2 Kor. 13:11; Yoh. 1:12) “Waɗansu tumaki” na Yesu masu sada zumunta fa? Yesu zai zama musu “Uba madawwami” a lokacin Sarautarsa ta Shekara Dubu, amma a ƙarshensa zai miƙa kansa ga Jehobah kuma za su zama ’ya’yan Allah.—Yoh. 10:16; Isha. 9:6; Rom. 8:21; 1 Kor. 15:27, 28.
21. Ta yaya za mu aikata idan muna “rayuwa bisa ga ruhu”?
21 Idan muna “rayuwa bisa ga Ruhu,” salama za ta zama ɗaya cikin halayenmu da mutane suke gani. Ba za mu riƙa “cakuna juna” ba. (Gal. 5:22-26) Maimakon haka, za mu yi ƙoƙari mu “[zauna] lafiya da dukan mutane.”—Rom. 12:18.
Farin Ciki Duk da Tsanantawa
22-24. (a) Menene ya sa waɗanda aka tsananta musu saboda adalci suka zama masu albarka? (b) Menene za mu tattauna a talifofi biyu na gaba?
22 “Masu-albarka ne waɗanda an tsanance su saboda adalci: gama mulkin sama nasu ne.” (Mat. 5:10) Sa’ad da yake ƙara ba da bayani a kan wannan, Yesu ya daɗa: “Masu-albarka ne ku lokacinda ana zarginku, ana tsananta muku, da ƙarya kuma ana ambatonku da kowacce irin mugunta, sabili da ni. Ku yi farinciki, ku yi murna ƙwarai: gama ladarku mai-girma ce cikin sama: gama hakanan suka tsananta ma annabawan da suka rigaye ku.”—Mat. 5:11, 12.
23 Kamar annabawa na dā na Allah, Kiristoci sun san za a zage su, za a tsananta musu, kuma a ƙaga musu kowace irin mugunta “saboda adalci.” Ta wajen jimre wa gwaji cikin aminci, muna samun gamsuwa na faranta wa Jehobah rai da kuma daraja shi. (1 Bit. 2:19-21) Wahalar da muke sha ba zai rage farin cikinmu ba wajen bauta wa Jehobah yanzu da kuma nan gaba. Ba zai rage farin cikin yin sarauta tare da Kristi a Mulki na samaniya ba ko kuma farin cikin samun rai madawwami a matsayin talakawa na duniya na wannan mulkin. Irin wannan albarka tabbaci ne na amincewar Allah, nagartansa, da kuma alherinsa.
24 Da ƙarin abubuwa da za a koya daga Huɗuba na kan Dutse. Za a tattauna darussa dabam dabam a talifofi biyu na gaba. Bari mu ga yadda za mu yi amfani da waɗannan koyarwa na Yesu Kristi.
[Hasiya]
a Kalmar Helenanci da ke nufin “farin ciki,” sau da yawa an fassara ta “albarka” a cikin Litafi Mai-Tsarki. Saboda haka, a wannan talifin, za mu bi ta juyin Litafi Mai-Tsarki wadda take nufin “farin ciki” a yare na asali.
Yaya Za Ka Amsa?
• Me ya sa “masu-ladabi a ruhu” suke da albarka?
• Me ya sa “masu-tawali’u” za su samu albarka?
• Me ya sa Kiristoci suke samun albarka duk da cewa ana tsananta musu?
• Wace albarka ce da Yesu ya sanar ta fi burge ka?
[Hotunan da ke shafi na 7]
Albarkatu tara da Yesu ya tattauna suna da amfani a yau kamar yadda suke a dā
[Hotunan da ke shafi na 8]
Hanya mai kyau na nuna jin ƙai ita ce koya wa mutane gaskiyar Littafi Mai Tsarki