Ka Kafa Idanunka Bisa Ladan
“Ina nace bi har zuwa ga goal, in kai ga ladan.”—FILIB. 3:14.
1. Wane lada ne aka miƙa wa manzo Bulus?
MANZO Bulus, da ake kira Shawulu na Tarsus, ya fito ne daga sanannen iyali. Gamaliel, wanda sananne ne wajen koyar da Shari’a, shi ne ya koyar da shi bisa addinin kakanninsa. (A. M. 22:3) Bulus yana da abin da ake ganin zarafi ne mai kyau, duk da haka ya bar addininsa kuma ya zama Kirista. Ya mai a hankalinsa ga ladan rai madawwami da aka miƙa masa, wato, na zama sarki da firist da ba ya mutuwa a Mulkin samaniya na Allah. Wannan Mulkin zai yi sarauta bisa aljanna a duniya.—Mat. 6:10; R. Yoh. 7:4; 20:6.
2, 3. Yaya ladan rai a sama yake da tamani ga Bulus?
2 Don ya nuna yadda yake ɗaukan wannan ladan da tamani, Bulus ya ce: “Abubuwan da su ke ribobi a gareni, waɗannan na lissafa su hasara sabili da Kristi. I, hakika, ina lissafa dukan abu hasara kuma bisa ga fifikon sanin Kristi Yesu Ubangijina: wanda na sha hasarar dukan abu sabili da shi, kamar najasa kuwa ni ke maishe su.” (Filib. 3:7, 8) Abubuwan da yawancin mutane suke ɗauka da muhimmanci, kamar matsayi, arziki, aiki, da suna, Bulus ya ɗauke su najasa bayan ya koyi gaskiya game da nufin Jehobah don ’yan adam.
3 Tun daga lokacin, ainihin abin da ya fi muhimmanci ga Bulus shi ne sani mai tamani na Jehobah da Kristi, wanda Yesu ya ambata sa’ad da yake addu’a ga Allah, ya ce: “Rai na har abada ke nan, su san ka, Allah makaɗaici mai-gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Kristi.” (Yoh. 17:3) Muradin Bulus na samun rai na har abada ya bayyana a kalmominsa da aka rubuta a Filibiyawa 3:14: “Ina nace bi har zuwa ga goal, in kai ga ladan nasara na maɗaukakiyar kira ta Allah cikin Kristi Yesu.” Hakika, ya kafa idanunsa a kan ladan samun rai madawwami a sama a Mulkin Allah.
Rayuwa Har Abada a Duniya
4, 5. Wane lada ne aka miƙa wa miliyoyin mutanen da suke yin nufin Allah a yau?
4 Ga yawancin waɗanda suka zaɓi yin nufin Allah, ladan da ya kamata mu ƙoƙarta mu samu shi ne rai madawwami a sabuwar duniya ta Allah. (Zab. 37:11, 29) Yesu ya nuna cewa wannan begen tabbatacce ne. Ya ce: “Masu-albarka ne masu-tawali’u: gama su za su gāji duniya.” (Mat. 5:5) Yesu ne musamman zai gaji duniyarmu, kamar yadda Zabura 2:8 ta nuna, kuma mutane 144,000 ne za su yi sarauta da shi a sama. (Dan. 7:13, 14, 22, 27) Mutane masu kama da tumaki da za su zauna a duniya za su “gaji” sashen duniya na Mulkin da aka ‘shirya dominsu tun kafawar duniya.’ (Mat. 25:34, 46) Kuma mun tabbata cewa hakan zai faru domin Allah, wanda ya yi alkawarin, “ba shi iya yin ƙarya.” (Tit. 1:2) Za mu iya kasance da irin tabbacin da Joshua yake da shi cewa alkawuran Allah za su cika sa’ad da ya gaya wa Isra’ilawa cewa: “Babu wani abu ɗaya ya sare daga cikin dukan alherai waɗanda Ubangiji Allahnku ya ambace su a kanku: dukansu sun tabbata a gareku, babu wani abu ɗaya ya sare daga ciki.”—Josh. 23:14.
5 Rayuwa a sabuwar duniya ta Allah ba za ta kasance marar gamsuwa kamar ta yau ba. Za ta kasance dabam: babu yaƙi, mugunta, talauci, rashin adalci, ciwo, da kuma mutuwa. A lokacin mutane za su samu cikakkiyar lafiya, kuma za su zauna a duniya da aka mai da aljanna. Irin wannan rayuwar za ta kasance mai gamsuwa fiye da yadda muke zato. Hakika, kowace rana za ta zama na farin ciki. Wannan lada ne mai girma!
6, 7. (a) Ta yaya Yesu ya kwatanta abin da zai faru a sabuwar duniya ta Allah? (b) Ta yaya za a sa matattu su soma sabuwar rayuwa?
6 Sa’ad da Yesu yake duniya, Allah ya ba shi iko ta ruhunsa mai tsarki don ya nuna irin abubuwa masu ban al’ajabi da za su faru a ko’ina a sabuwar duniya. Alal misali, Yesu ya gaya wa wani mutumin da jikinsa ya shanye na shekaru talatin da takwas ya yi tafiya. Littafi Mai Tsarki ya faɗi cewa mutumin ya yi hakan. (Karanta Yohanna 5:5-9.) A wani lokaci, Yesu ya ga “wani mutum wanda shi ke makafo tun ran da aka haife shi.” Daga baya, an tambayi mutumin da makaho ne a dā game da wanda ya warkar da shi, kuma ya amsa: “Tun farkon duniya ba a taɓa jin labari wani ya buɗe idanun mutum wanda aka haife shi da makanta ba. Da mutumin nan ba daga wurin Allah ba ne, da ba ya iya yin kome ba.” (Yoh. 9: 1, 6, 7, 32, 33) Yesu ya yi dukan waɗannan abubuwa ne domin Allah ya ba shi iko. Duk inda ya tafi, Yesu ya warkar da “waɗanda su ke bukatar warkaswa.”—Luk 9:11.
7 Yesu ya warkar da marasa lafiya da guragu, ya kuma ta da matattu. Alal misali, wata yarinya ’yar shekara 12 ta rasu, kuma hakan ya jawo baƙin ciki sosai ga iyayenta. Amma Yesu ya ce: “Yarinya, ina ce maki, Ki tashi.” Kuma ta tashi! Ka yi tunanin yadda iyayen da kuma mutanen da suke wajen suka ji! (Karanta Markus 5:38-42.) A sabuwar duniya ta Allah, za a yi “mamaki mai-girma” sa’ad da aka ta da mutane masu yawa daga matattu, don “za a yi tashin matattu, na masu-adalci da na marasa-adalci.” (A. M. 24:15; Yoh. 5:28, 29) Za a sa waɗannan su soma sabuwar rayuwa da begen rayuwa har abada.
8, 9. (a) A lokacin Sarautar Kristi ta Shekara Dubu, menene zai faru da zunubi da aka gada daga Adamu? (b) Bisa menene za a yi wa matattu shari’a?
8 Waɗanda aka ta da daga matattu za su samu damar yin rayuwa har abada. Ba za a yi wa waɗanda aka ta da daga matattu shari’a bisa zunubai da suka yi kafin su mutu ba. (Rom. 6:7) Sa’ad da aka yi amfani da fa’idodin hadayar fansa a lokacin sarautar Kristi na Shekara Dubu, a hankali talakawan Mulki masu biyayya za su zama kamiltattu, daga baya za su samu ’yanci gabaki ɗaya daga dukan sakamakon zunubin Adamu. (Rom. 8:21) Jehobah zai “haɗiye mutuwa har abada: Ubangiji Yahweh za ya shafe hawaye daga dukan fuskoki.” (Isha. 25:8) Kalmar Allah ta kuma ce za a “buɗe littattafai,” hakan ya nuna cewa za a ba waɗanda suke rayuwa a lokacin sabon umurni. (R. Yoh. 20:12) Sa’ad da aka mai da duniya ta zama aljanna, “mazaunan duniya su kan koyi adalci.”—Isha. 26:9.
9 Za a yi wa waɗanda aka ta da daga matattu shari’a, ba domin zunubi da suka gada daga Adamu ba, amma don abin da su da kansu suka zaɓa su yi. Ru’ya ta Yohanna 20:12 ta ce: “Aka yi ma matattu shari’a kuma bisa ga abin da aka rubuta cikin littattafai, gwargwadon ayyukansu,” wato, ayyukansu bayan sun tashi daga matattu. Wannan misali ne mai kyau na adalcin Jehobah, jin ƙai, da kuma ƙaunarsa! Ƙari ga haka, ba za su tuna abubuwa masu ban ciwo na rayuwarsu ta dā a wannan tsohuwar duniya ba, “ba kuwa za su shiga zuciya ba.” (Isha. 65:17) Da yake suna da sabon umurni mai ƙarfafawa da rayuwa da ke cike da abubuwa masu kyau, ba za su ƙara damuwa ba game da mugayen abubuwa na dā. Za su mance da waɗannan abubuwa da suka fuskanta a dā. (R. Yoh. 21:4) Hakan zai faru da “taro mai-girma,” waɗanda suka tsira daga Armageddon.—R. Yoh. 7:9, 10, 14.
10. (a) Yaya rayuwa za ta zama a sabuwar duniya ta Allah? (b) Menene za ka yi da zai taimake ka ka kafa idanunka bisa ladan?
10 A sabuwar duniya ta Allah, mutane za su yi rayuwa babu ciwo da mutuwa. “Wanda ya ke zaune a ciki ba za ya ce, Ina ciwo ba.” (Isha. 33:24) A ƙarshe, mazauna sabuwar duniya za su tashi kowane safe da koshin lafiya, suna farin cikin ganin wata safiya mai ban al’ajabi. Za su yi aiki mai gamsarwa, kuma za su yi cuɗanya da mutanen da suke ƙaunar su. Hakika, irin wannan rayuwa lada ne mai ban al’ajabi! Ga wata shawara, ka ɗauki lokaci ka karanta annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki da ke cikin Ishaya 33:24 da 35:5-7. Ka sa kanka cikin yanayin. Hakan zai taimake ka ka mai da hankalinka ga ladan.
Wasu da Ba Su Kafa Idanunsu Bisa Ladan Ba
11. Ka kwatanta yadda Sulemanu ya soma sarautarsa da kyau.
11 Muddin muka koya game da ladan, muna bukatar mu yi aiki tuƙuru don mu ci gaba da kafa idanunmu bisa ladan domin muna iya daina yin hakan. Alal misali, sa’ad da Sulemanu ya zama sarkin Isra’ila ta dā, ya yi addu’a ga Allah don ya ba shi fahimi da hikima don ya yi wa mutanensa shari’a da kyau. (Karanta 1 Sarakuna 3:6-12.) Saboda haka, Littafi Mai Tsarki ya ce, “Allah ya ba Solomon hikima da ganewa ƙwarai da gaske.” Hakika, “hikimar Solomon fa ta fi hikimar dukan mutanen gabas, da dukan hikimar Masar.”—1 Sar. 4:29-32.
12. Wane gargaɗi ne Jehobah ya ba waɗanda za su zama sarakuna a Isra’ila?
12 Amma, da farko Jehobah ya ba da gargaɗi cewa duk wanda ya zama sarki “ba za ya tara ma kansa dawakai ba,” kuma “ba kuwa za ya tara ma kansa mata ba, domin kada zuciyatasa ta karkata.” (K. Sha 17:14-17) Tara dawakai zai nuna cewa sarkin ya dogara ga ƙarfin rundunarsa don su kāre al’ummar maimakon ya dogara ga Jehobah, Mai kāriya. Kuma tara mata zai kasance da haɗari domin mai yiwuwa wasu daga cikinsu ’yan al’ummai ne masu bautar ƙarya da suka kewaye su, kuma waɗannan mata suna iya juya sarkin daga bauta ta gaskiya na Jehobah.
13. Ta yaya Sulemanu ya yi rashin abin da aka ba shi?
13 Sulemanu bai bi waɗannan gargaɗin ba. Maimakon haka, ya yi ainihin abubuwan da Jehobah ya ce kada sarakuna su yi. Ya tara dawakai dubbai da kuma mahaya. (1 Sar. 4:26) Ya kuma auri mata 700 da ƙwaraƙwarai 300, yawancinsu sun fito ne daga al’ummai arna da ke kusa. Waɗannan mata “suka juyadda zuciyatasa zuwa bin waɗansu alloli; zuciyatasa ba ta kamilta zuwa ga Ubangiji Allahnsa.” Sulemanu ya soma bautar ƙarya mai ban ƙyama na al’ummai arna da matansa suka koya masa. Saboda haka, Jehobah ya ce zai ‘fizge mulkin’ daga hannun Sulemanu.—1 Sar. 11:1-6, 11.
14. Menene sakamakon rashin biyayyar Sulemanu da kuma al’ummar Isra’ila?
14 Sulemanu ya daina mai da hankali ga gata mai tamani da yake da shi na wakiltan Allah na gaskiya. Sarkin ya shaƙu sosai da bautar ƙarya. Da shigewar lokaci, al’ummar gabaki ɗaya ta yi ridda, kuma hakan ya sa aka halaka ta a shekara ta 607 K.Z. Ko da yake daga baya Yahudawa sun mai do da bauta ta gaskiya, bayan ƙarnuka da yawa, Yesu ya ce: “Za a amshe muku mulkin Allah, za a bayar ga al’umma mai-fitowa da ’ya’yansa.” Abin da ya faru ke nan. Yesu ya sanar: “Ga shi, an bar muku gidanku kango.” (Mat. 21:43; 23:37, 38) Saboda rashin amincinta, al’ummar ta yi hasarar gata mai girma na wakiltan Allah na gaskiya. A shekara ta 70 A.Z., sojojin Roma suka halaka Urushalima da haikalinta, kuma Yahudawa da yawa da suka rage suka zama bayi.
15. Ka ba da misalai na mutanen da suka daina mai da hankali ga abin da ke da muhimmanci.
15 Yahuda Iskariyoti yana cikin manzannin Yesu goma sha biyu. Yahuda ya ji koyarwar Yesu masu ban al’ajabi, kuma ya ga mu’ujizai da ya yi da taimakon ruhu mai tsarki na Allah. Duk da haka, Yahuda bai tsare zuciyarsa ba. An ba shi ajiyar akwatin kuɗi da ke ɗauke da kuɗin Yesu da na manzanninsa goma sha biyu. Amma “domin shi ɓarawo ne, kuma da shi ke jikka tana wurinsa ya kan ɗiba abin da a ke sa ciki.” (Yoh. 12:6) Saboda irin muguwar haɗamar da yake da ita, ya ƙulla da manyan firistoci masu riya kuma ya ci amanar Yesu a kan azurfa talatin. (Mat. 26:14-16) Wani kuma da ya dai na mai da hankali shi ne na Dimas, wanda abokin tafiyar manzo Bulus ne. Dimas bai tsare zuciyarsa ba. Bulus ya ce: “Dimas ya yashe ni, yana ƙaunar wannan zamani na yanzu.”—2 Tim. 4:10; karanta Misalai 4:23.
Darussa Don Kowannenmu
16, 17. (a) Ta yaya hamayyar da muke fuskanta take da iko? (b) Menene zai taimake mu mu jimre kowane gwaji da Shaiɗan zai kawo mana?
16 Ya kamata dukan bayin Allah su yi tunani sosai a kan misalan da ke cikin Littafi Mai Tsarki, don an gaya mana: “Waɗannan al’amura dai suka same su watau misali ne; kuma aka rubuta su domin gargaɗi garemu, mu waɗanda matuƙan zamanu sun zo a kanmu.” (1 Kor. 10:11) A yau, muna zaune a kwanaki na ƙarshe na wannan mugun zamani.—2 Tim. 3:1, 13.
17 Shaiɗan Iblis, “allah na wannan zamani” ya san “sauran zarafinsa kaɗan ne.” (2 Kor. 4:4; R. Yoh. 12:12) Zai yi duk iyakar ƙoƙarinsa don ya rinjayi bayin Jehobah su daina bin ƙa’idodi na Kirista. Shaiɗan yana mallakar wannan duniya, har da hanyarta na watsa labarai. Amma, mutanen Jehobah suna da abin da ya fi ƙarfi, wato, “mafificin girman iko.” (2 Kor. 4:7) Za mu iya dogara ga wannan ikon daga Allah don ya taimake mu mu jimre duk wani gwajin da Shaiɗan ya kawo mana. Saboda haka, an aririce mu mu yi addu’a a kai a kai, domin muna da tabbaci cewa Jehobah zai “bada Ruhu Mai-tsarki ga waɗanda su ke roƙonsa.”—Luk 11:13.
18. Yaya ya kamata mu ɗauki wannan duniya?
18 An ƙarfafa mu da sanin cewa ba da daɗewa ba za a halaka dukan duniyar Shaiɗan amma Kiristoci na gaskiya za su tsira. “Duniya ma tana wucewa, duk da sha’awatata: amma wanda ya aika nufin Allah ya zauna har abada.” (1 Yoh. 2:17) Saboda haka, ba zai dace ba wani cikin bayin Allah ya yi tunanin cewa da akwai wani abu a wannan zamanin da ya fi dangantakarsa da Jehobah tamani! Wannan duniya da Shaiɗan yake mallaka tana shuɗewa, amma Jehobah ya yi tanadin ikilisiyar Kirista da za ta taimaka wajen kāre bayinsa masu aminci. Yayin da suke son su shiga sabuwar duniya, za su iya kasancewa da tabbaci da wannan alkawarin: “Za a datse masu-aika mugunta: amma waɗanda ke sauraro ga Ubangiji, su ne za su gāji duniya.” (Zab. 37:9) Saboda haka, ka mai da hankalinka ga wannan lada mai ban al’ajabi!
Ka Tuna?
• Yaya Bulus yake ji game da ladan da aka miƙa masa?
• Bisa menene za a yi wa waɗanda za su yi rayuwa har abada a duniya shari’a?
• Wane tafarki na hikima ne za ka ɗauka yanzu?
[Hotunan da ke shafi na 13]
Kana ganin kanka wajen samun ladan sa’ad da kake karanta labarun da ke cikin Littafi Mai Tsarki?