Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 11/15 pp. 7-11
  • Ka Kyautata Addu’o’inka Ta Wurin Nazarin Littafi Mai Tsarki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Kyautata Addu’o’inka Ta Wurin Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Biɗi Kuma Ka Bi Ja-gorar Allah
  • Addu’a Tana Taimaka Mana Mu Rage Damuwa
  • Ka Yi Addu’ar Samun Hikima
  • Ka Yi Addu’a Daga Zuciya
  • Yadda Zabura za ta Iya Kyautata Addu’o’inka
  • Ka Yi Addu’a da Bangaskiya
  • Ka Tuna Yin Yabo da Godiya
  • Ka Roƙi Allah da Daraja
  • Ka Ci Gaba da Kyautata Addu’o’inka
  • Ka Kusaci Allah Cikin Addu’a
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Menene Addu’o’inka Suke Nunawa Game Da Kai?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Gatan da Muke da Shi Na Yin Addu’a
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Ka Rika Yin Addu’a don Ka Kusaci Allah
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 11/15 pp. 7-11

Ka Kyautata Addu’o’inka Ta Wurin Nazarin Littafi Mai Tsarki

“Ya Ubangiji, ina roƙonka, ka bar kunnenka yanzu shi saurari addu’ar bawanka.”—NEH. 1:11.

1, 2. Me ya sa zai kasance da amfani mu bincika wasu addu’o’i da ke rubuce a cikin Littafi Mai Tsarki?

ADDU’A da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki fannoni ne masu muhimmanci a bauta ta gaskiya. (1 Tas. 5:17; 2 Tim. 3:16, 17) Hakika, Littafi Mai Tsarki ba littafin addu’a ba ne. Duk da haka, ya ƙunshi addu’o’i masu yawa, har da waɗanda suke cikin littafin Zabura.

2 Yayin da kake karatu da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki, za ka samu addu’o’i da suka yi daidai da yanayin da kake fuskanta. Hakika, haɗa kalamai na addu’o’in da ke rubuce cikin Nassosi a cikin addu’o’inka zai kyautata su. Menene za ka iya koya daga waɗanda aka amsa roƙe-roƙensu na taimako da kuma abubuwan da suka faɗa a cikin addu’o’insu?

Ka Biɗi Kuma Ka Bi Ja-gorar Allah

3, 4. Wane aiki ne aka ba bawan Ibrahim, kuma menene za mu iya koya daga sakamakon da Jehobah ya ba da?

3 A nazarin da ka yi na Littafi Mai Tsarki, ka koyi cewa ya kamata a koyaushe ka riƙa yin addu’ar samun ja-gorar Allah. Ka yi la’akari da abin da ya faru sa’ad da Ibrahim uban iyali ya aiki babban bawansa, wataƙila Eliezer zuwa Mesopotamia don ya samo wa Ishaƙu mata mai jin tsoron Allah. Sa’ad da mata suke ɗiban ruwa a wata rijiya, bawan ya yi addu’a: “Ya Ubangiji, . . . in ka yarda, budurwa wadda zan ce mata, Ki sauke tulunki, ina roƙonki, domin in sha; ita kuwa ta ce, Sha, in ba raƙumanka kuma su sha; bari ya zama ita ke wanda ka sanya domin bawanka Ishaƙu; haka nan kuwa zan sani ka gwada alheri ga ubangidana.”—Far. 24:12-14.

4 An amsa addu’ar bawan Ibrahim sa’ad da Rifkatu ta ba raƙumansa ruwa. Ba da daɗewa ba ta bi shi zuwa Ka’anan kuma ta zama ƙaunatacciyar matar Ishaƙu. Hakika, kada ka yi tsammanin cewa Allah zai ba ka wata alama ta musamman. Duk da haka, zai yi maka ja-gora a rayuwa idan ka yi addu’a kuma ka ƙudurta cewa kana son ruhunsa ya yi maka ja-gora.—Gal. 5:18.

Addu’a Tana Taimaka Mana Mu Rage Damuwa

5, 6. Menene abu na musamman a addu’ar da Yakubu ya yi sa’ad da yake son ya sadu da Isuwa?

5 Addu’a tana iya rage damuwa. Da yake yana jin tsoron cewa Isuwa, tagwayensa zai iya yi masa lahani, Yakubu ya yi addu’a: “Ya Ubangiji . . . ni ban isa mafi ƙaramta a cikin dukan jiyejiyanƙanka, da dukan gaskiya, waɗanda ka nuna wa bawanka ba . . . Ina roƙonka, ka cece ni daga hannun ɗan’uwana, daga hannun Isuwa: gama ina jin tsoronsa, kada ya zo ya buge ni, uwa da ’ya’ya. Kai kuwa ka ce, hakika zan yi maka alheri, in maida zuriyanka kamar yashi na teku, wanda ba shi lissaftuwa domin yawa.”—Far. 32:9-12.

6 Bayan ya yi addu’a, Yakubu ya ɗauki matakai don ya kāre iyalinsa, kuma an amsa addu’arsa sa’ad da shi da Isuwa suka sulhunta. (Far. 33:1-4) Ka karanta wannan roƙon da kyau, kuma za ka ga cewa Yakubu bai yi roƙon samun taimako kawai ba. Ya nuna bangaskiya a Zuriyar da aka yi alkawarinsa kuma ya nuna godiya ga alherin Allah. Kana da “tsorace-tsorace” a zuciyarka? (2 Kor. 7:5) Idan haka ne, roƙon da Yakubu ya yi zai iya tuna maka cewa addu’o’i za su iya rage damuwa. Amma, ya kamata su ƙunshi roƙo da kuma furcin bangaskiya.

Ka Yi Addu’ar Samun Hikima

7. Me ya sa Musa ya yi addu’ar sanin tafarkun Jehobah?

7 Ya kamata muradin faranta wa Jehobah rai ya motsa ka ka yi addu’a don hikima. Musa ya yi addu’ar sanin tafarkun Allah. Ya yi roƙo: “Ka gani kai [Jehobah] kana ce mani, Ka ɗauki wannan mutane [daga Masar] . . . Yanzu fa, ina roƙonka, idan na sami tagomashi a idonka, ka koya mani tafarkunka . . . domin in sami tagomashi a gare ka.” (Fit. 33:12, 13) Allah ya amsa roƙon da Musa ya yi ta wajen ba shi ƙarin sani game da tafarkunsa, abin da yake bukata idan zai shugabanci mutanen Jehobah.

8. Ta yaya za ka amfana wajen yin bimbini a kan 1 Sarakuna 3:7-14?

8 Dauda ya kuma yi addu’a: “Ya Ubangiji, ka nuna mini tafarkunka.” (Zab. 25:4) Sulemanu, ɗan Dauda ya roƙi Allah ya ba shi hikimar da yake bukata don ya cika hakkokinsa na yin sarauta a Isra’ila. Addu’ar Sulemanu ta faranta wa Jehobah rai, wadda hakan ta sa ya ba shi abin da ya roƙa kuma ya ba shi arziki da ɗaukaka. (Karanta 1 Sarakuna 3:7-14.) Idan aka ba ka gatan yin hidima wanda kamar yana da wuya sosai, ka yi addu’ar samun hikima kuma ka kasance da tawali’u. Allah zai taimaka maka ka samu sani kuma ya sa ka aikata da hikimar da ake bukata don ka kula da hakkinka a hanyar da ta dace da kuma cikin ƙauna.

Ka Yi Addu’a Daga Zuciya

9, 10. Wane abu mai muhimmanci ka lura da shi game da yadda Sulemanu ya yi nuni ga zuciya a cikin addu’arsa ta keɓe haikali?

9 Don a ji addu’armu, dole ne mu yi ta daga zuciya. Sulemanu ya yi addu’a da dukan zuciyarsa, wadda aka rubuta a 1 Sarakuna sura ta 8, a gaban jama’ar da suka taru a Urushalima don keɓe haikalin Jehobah a shekara ta 1026 K.Z. Bayan da aka saka sunduƙin alkawari a Wuri Mafi Tsarki kuma gajimare na Jehobah ya cika haikalin, Sulemanu ya yabi Allah.

10 Ka yi nazarin addu’ar Sulemanu kuma ka lura da yadda ta yi nuni ga zuciya. Sulemanu ya amince cewa Jehobah ne kaɗai ya san zuciyar mutum. (1 Sar. 8:38, 39) Wannan addu’ar ta nuna cewa akwai bege ga mai zunubin da ya ‘koma ga Allah da dukan zuciyarsa.’ Idan maƙiyi ya kama mutanen Allah, Jehobah zai ji roƙonsu idan suka bauta masa da zuciya ɗaya. (1 Sar. 8:48, 58, 61) Babu shakka, ya kamata ka yi addu’o’inka da dukan zuciyarka.

Yadda Zabura za ta Iya Kyautata Addu’o’inka

11, 12. Menene ka koya daga kalaman addu’a na wani Balawi wanda bai sami damar zuwa haikalin Allah ba har tsawon wani lokaci?

11 Yin nazarin Zabura za ta iya kyautata addu’o’inka kuma ta taimaka maka ka jira Allah ya amsa su. Ka yi la’akari da haƙurin wani Balawi da aka kai zaman bauta. Ko da yake ya kasa zuwa haikalin Jehobah har tsawon wani lokaci, ya rera: “Don menene ka ke tagumi, ya raina? Don menene ka ke alhini a cikina? Ka kafa bege ga Allah: gama duk da haka zan yabe shi saboda taimakon fuskarsa.”—Zab. 42:5, 11; 43:5.

12 Menene za ka iya koya daga wannan Balawi? Idan an jefa ka kurkuku don adalci kuma hakan ya hana ka taruwa da ’yan’uwa masu bi a wurin bautarsu har tsawon wani lokaci, ka jira Allah cikin haƙuri domin ya aikata dominka. (Zab. 37:5) Ka yi bimbini a kan farin cikin da ka shaida a dā a hidimar Allah, kuma ka yi addu’a don ka jimre yayin da kake “kafa bege ga Allah” ya sa ka soma tarayya kuma da mutanensa.

Ka Yi Addu’a da Bangaskiya

13. Cikin jituwa da Yaƙub 1:5-8, me ya sa za ka yi addu’a da bangaskiya?

13 Ko da menene yanayinka, ka yi addu’a da bangaskiya a koyaushe. Idan kana fuskantar gwajin amincinka, ka bi shawarar almajiri Yaƙub. Ka yi addu’a ga Jehobah, kuma kada ka yi shakkar cewa zai ba ka hikimar da kake bukata don ka jimre da gwajinka. (Karanta Yaƙub 1:5-8.) Allah ya san dukan abubuwan da ke damunka, kuma zai yi maka ja-gora kuma ya ƙarfafa ka ta hanyar ruhunsa. Ka gaya masa yadda kake ji da cikakkiyar bangaskiya, “ba da shakkar komi ba,” kuma ka amince da ja-gorar ruhunsa da kuma shawarar da ke cikin Kalmarsa.

14, 15. Me ya sa za a ce Hannatu ta yi addu’a kuma ta aikata da bangaskiya?

14 Hannatu, ɗaya daga cikin mata biyu na Elkanah Balawi, ta yi addu’a kuma ta aikata da bangaskiya. Ɗayan matar, Peninnah, wadda take da yara da yawa, tana ta yi wa Hannatu dariya domin ba ta haihu ba. A mazauni, Hannatu ta yi alkawari cewa idan ta haifi ɗa, za ta ba da shi ga Jehobah. Domin leɓunanta suna motsi sa’ad da take addu’a, Eli, Babban Firist ya soma tunanin cewa ta yi maye. Da ya san ba hakan ba ne, sai ya ce: “Allah kuwa na Isra’ila shi ba ki roƙonki.” Ko da yake Hannatu ba ta san yadda sakamakon zai kasance ba, tana da bangaskiya cewa za a amsa addu’arta. Saboda haka, “fuskarta ba ta ƙara nuna baƙinciki ba.” Ba ta ƙara yin baƙin ciki ko kuma karai ba.—1 Sam. 1:9-18.

15 Bayan haihuwar Sama’ila da kuma yaye shi, Hannatu ta ba da shi ga Jehobah don ya yi hidima mai tsarki a mazauni. (1 Sam. 1:19-28) Yin bimbini sosai a kan addu’arta a wannan lokaci yana iya kyautata addu’o’inka kuma ya taimaka maka ka ga cewa za ka iya sha kan baƙin ciki game da wata matsala idan ka yi addu’a cikin bangaskiya cewa Jehobah zai amsa addu’arka.—1 Sam. 2:1-10.

16, 17. Menene ya faru domin Nehemiya ya yi addu’a kuma ya aikata da bangaskiya?

16 Nehemiya mutum mai aminci a ƙarni na biyar K.Z., ya yi addu’a kuma ya aikata da bangaskiya. Ya yi roƙo: “Ya Ubangiji, ina roƙonka, ka bar kunnenka yanzu shi saurari addu’ar bawanka, da addu’ar bayinka, waɗanda su ke da farinciki wajen jin tsoron sunanka: Ina roƙonka kuma ka ba bawanka nasara yau, ka yarda kuma ya sami tagomashi a wurin mutumin nan.” Wanene “mutumin nan”? Artaxerxes ne Sarkin Farisa, wanda Nehemiya yake wa hidima a matsayin mai ɗaukan ƙoƙo.—Neh. 1:11.

17 Nehemiya ya yi addu’a da bangaskiya kwanaki da yawa sa’ad da ya ji cewa Yahudawa da aka ’yanta daga bauta a Babila “suna cikin wahala da shan zargi sosai: [kuma] ganuwar Urushalima ta rushe.” (Neh. 1:3, 4) An amsa addu’o’in Nehemiya fiye da yadda yake tsammani sa’ad da Sarki Artaxerxes ya ƙyale shi ya tafi Urushalima don ya sake gina ganuwarta. (Neh. 2:1-8) An sake gina ganuwar cikin ɗan ƙanƙanin lokaci. An amsa addu’o’in Nehemiya domin ya mai da hankali ne ga bauta ta gaskiya kuma ya yi su da bangaskiya. Hakan ne kake yin addu’o’inka?

Ka Tuna Yin Yabo da Godiya

18, 19. Domin waɗanne dalilai ne ya kamata bawan Jehobah ya yabe shi kuma yi masa godiya?

18 Sa’ad da kake yin addu’a, ka tuna ka yabi Jehobah kuma ka yi masa godiya. Da akwai dalilai da yawa na yin hakan! Alal misali, Dauda yana ɗokin ya yabi sarautar Jehobah. (Karanta Zabura 145:10-13.) Addu’o’inka suna nuna cewa kana daraja gatar shelar Mulkin Jehobah kuwa? Kalaman masu zabura suna iya taimaka maka ka yi godiya ga Allah a cikin addu’arka da dukan zuciyarka domin taron Kirista, manyan taro, da kuma taron gunduma.—Zab. 27:4; 122:1.

19 Yin godiya don dangantakarka mai tamani da Allah yana iya motsa ka ka yi addu’a da dukan zuciyarka da kalamai kamar waɗannan: “Zan yi maka godiya, ya Ubangiji, a cikin dangogi: Zan raira yabbai gareka a cikin al’ummai. Gama jinƙanka mai-girma ne har sama, gaskiyarka kuma har sararin sammai. Ka ɗaukaka, ya Allah, bisa sammai; bari darajarka ta ɗaukaka bisa dukan duniya.” (Zab. 57:9-11) Waɗannan kalamai ne masu ƙarfafawa! Ka yarda cewa irin waɗannan kalamai masu ban ƙarfafa daga Zabura za su iya shafan addu’arka kuma su kyautata su?

Ka Roƙi Allah da Daraja

20. Ta yaya Maryamu ta furta ibadarta ga Allah?

20 Ya kamata addu’o’inka su nuna cewa kana daraja Allah. Kalaman daraja da Maryamu ta furta bayan ta san cewa za ta zama mamar Almasihu sun yi kama da irin waɗanda Hannatu ta furta sa’ad da take miƙa Sama’ila don ya yi hidima a mazauni. Darajar da Maryamu take yi wa Allah sun bayyana a kalamanta: “Raina yana girmama Ubangiji, ruhuna kuwa ya yi murna cikin Allah Mai-cetona.” (Luk 1:46, 47) Za ka iya kyautata addu’o’inka ta wajen furta irin waɗannan kalaman? Shi ya sa aka zaɓi Maryamu mai ibada ta zama mamar Yesu Almasihu!

21. Ta yaya addu’o’in Yesu suka nuna tabbacin daraja da kuma bangaskiya?

21 Yesu ya yi addu’a da cikakkiyar bangaskiya. Alal misali, kafin ya ta da Li’azaru daga matattu, “Yesu kuwa ya tada idanunsa bisa, ya ce, ya Uba, na gode maka da ka ji ni. Ko dā ma na sani kana jina kullum.” (Yoh. 11:41, 42) Addu’o’inka suna nuna irin wannan darajar da kuma bangaskiya? Ka yi nazarin addu’ar misali na Yesu, kuma za ka ga cewa fannoninta na musamman su ne tsarkake sunan Jehobah, zuwan Mulkinsa, da kuma cikar nufinsa. (Mat. 6:9, 10) Ka yi tunani game da addu’o’inka. Suna nuna cewa kana son Mulkin Jehobah sosai, kana son yin nufinsa, da kuma tsarkake sunansa mai tsarki? Ya kamata ya kasance hakan.

22. Me ya sa za ka kasance da tabbaci cewa Jehobah zai ba ka gaba gaɗi don ka sanar da bishara?

22 Saboda tsanantawa ko wani gwaji, sau da yawa addu’a tana haɗa da roƙe-roƙen samun taimako don mu bauta wa Jehobah da gaba gaɗi. Sa’ad da ’yan Majalisa suka umurci Bitrus da Yohanna su daina ‘koyarwa cikin sunan Yesu,’ da gaba gaɗi waɗannan manzanni sun ƙi yin hakan. (A. M. 4:18-20) Bayan da aka sake su, sun gaya wa ’yan’uwa masu bi abin da ya faru. Sa’an nan dukan waɗanda suke wajen suka roƙi Allah ya taimaka musu su faɗi kalmarsa da gaba gaɗi. Babu shakka, sun yi farin ciki sosai sa’ad da aka amsa wannan addu’ar, domin “suka cika da ruhu mai-tsarki, suka faɗi maganar Allah da ƙarfinzuciya.” (Karanta A. M. 4:24-31.) Saboda haka, mutane da yawa suka zama masu bauta wa Jehobah. Addu’a za ta iya ƙarfafa ka ka sanar da bishara da gaba gaɗi.

Ka Ci Gaba da Kyautata Addu’o’inka

23, 24. (a) Ka ambata wasu misalai da suka nuna cewa nazarin Littafi Mai Tsarki zai iya kyautata addu’o’inka. (b) Menene za ka yi don ka kyautata addu’o’inka?

23 Za a iya ambata wasu misalai don a nuna cewa karatun Littafi Mai Tsarki da nazari suna iya kyautata addu’o’inka. Alal misali kamar Yunana, sa’ad da kake addu’a kana iya amince cewa “ceto na Ubangiji ne.” (Yun. 2:1-10) Idan kana damuwa don wani zunubi mai tsanani da ka yi kuma ka nemi taimakon dattawa, kalaman Dauda za su iya taimaka maka ka furta tubanka a lokacin da kake yin addu’a. (Zab. 51:1-12) Sa’ad da kake wasu addu’o’i, kana iya yabawa Jehobah kamar yadda Irmiya ya yi. (Irm. 32:16-19) Idan kana neman abokiyar aure, yin nazarin addu’ar da ke cikin Ezra sura ta 9, tare da yin roƙo, za su iya ƙarfafa ƙudurinka na yin biyayya ga Allah ta wajen yin ‘aure sai dai cikin Ubangiji.’—1 Kor. 7:39; Ezra 9:6, 10-15.

24 Ka ci gaba da yin karatu, nazari, da kuma bincika Littafi Mai Tsarki. Ka nemi kalamai da za ka haɗa cikin addu’o’inka. Kana iya yin amfani da irin waɗannan kalamai na Nassosi cikin roƙe-roƙenka da addu’o’inka na godiya da kuma yabo. Ka tabbata cewa za ka kusaci Jehobah Allah yayin da kake kyautata addu’o’inka ta wurin nazarin Littafi Mai Tsarki.

Yaya Za Ka Amsa?

• Me ya sa za mu nemi kuma mu bi ja-gorar Allah?

• Menene ya kamata ya motsa mu mu yi addu’a don hikima?

• Ta yaya littafin Zabura zai kyautata addu’o’inmu?

• Me ya sa za mu yi addu’a da bangaskiya da kuma daraja?

[Hotunan da ke shafi na 8]

Bawan Ibrahim ya yi addu’a don ja-gorar Allah. Kana yin hakan?

[Hotunan da ke shafi na 10]

Bauta ta Iyali za ta iya kyautata addu’o’inka

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba