Zama Na Jehobah, Alheri ne
“Na Ubangiji muke.”—ROM. 14:8.
1, 2. (a) Wane gata ne muke da shi? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?
AN BA al’ummar Isra’ila gata mai tamani sa’ad da Jehovah ya ce musu: “Sa’annan za ku zama keɓaɓiyar taska a gare ni daga cikin dukan al’umman duniya.” (Fit. 19:5) A yau, waɗanda suke cikin ikilisiyar Kirista suna da ɗaukakar zama na Jehobah. (1 Bit. 2:9; R. Yoh. 7:9, 14, 15) Gata ne da zai amfane mu har abada.
2 Ban da gata, zama na Jehobah hakki ne. Wasu suna iya mamaki: ‘Zan iya yin abin da Jehobah yake bukata a gare ni kuwa? In har na yi zunubi, zai yi watsi da ni ne? Zama na Jehobah zai hana ni ’yanci ne?’ Ya dace mu tattauna irin waɗannan batutuwa. Da farko, da akwai wata tambaya da muke bukatar mu yi tunani sosai a kanta: Waɗanne amfani ne zama na Jehobah zai kawo mana?
Zama na Jehobah Yana Kawo Farin Ciki
3. Yaya zaɓin da Rahab ta yi na bauta wa Jehobah ya amfane ta?
3 Mutane da suka zama na Jehobah suna amfana ne daga yanayin su? Ka yi la’akari da Rahab, wata karuwa wadda take zaune a ƙasar Yariko ta dā. Babu shakka an yi renon ta ta yi bautar ƙazanta na allolin Ka’anan. Duk da haka, sa’ad da ta ji game da nasarorin da Jehobah ya ba Isra’ilawa, ta fahimci cewa Jehobah ne Allah na gaskiya. Saboda haka, ta sa ranta cikin haɗari domin ta kāre mutanen Allah zaɓaɓɓu, kuma ta haka ta saka rayuwarta ta gaba a hannunsu. Litafi Mai Tsarki ya ce: “Haka nan kuma Rahab karuwan nan, da ya ke ta karɓi manzannin, ta sallame su kuma ta wata hanya dabam.” (Yaƙ. 2:25) Ka yi tunanin amfanin da ta samu sa’ad da ta zama ɗaya daga cikin mutanen Allah masu tsabta, mutanen da aka koya wa Dokar Allah a hanyoyin ƙauna da adalci. Babu shakka, ta yi farin ciki sosai cewa ta bar hanyar rayuwarta ta dā! Ta auri Baisra’ile kuma ta haifi ɗanta, Boaz, wanda ya zama fitaccen mutumi na Allah.—Josh. 6:25; Ruth 2:4-12; Mat. 1:5, 6.
4. Ta yaya Ruth ta amfana daga shawarar da ta yi na bauta wa Jehobah?
4 Ruth ’yar ƙasar Mowab ta tsai da shawara ta bauta wa Jehobah. Sa’ad da take yarinya, wataƙila ta bauta wa Chemosh da kuma wasu allolin Mowab, amma ta zo ta san Allah na gaskiya, Jehobah, kuma ta auri Ba’isra’ile wanda ya zo gudun hijira a ƙasarta. (Karanta Ruth 1:1-6.) Bayan haka, sa’ad da Ruth da Orpah da surukuwarsu, Naomi suka kama hanyar komawa Bai’talami, Naomi ta aririci mata biyun su koma gida. Zama a Isra’ila ba zai yi musu sauƙi ba. Orpah “ta koma wurin danginta, da kuma allahnta,” amma Ruth ba ta koma ba. Ta aikata bisa bangaskiyarta kuma ta san wanda take son ta bi. Ta gaya wa Naomi: “Kada ki roƙe ni in rabu da ke, in kuma bar binki: gama inda za ki tafi duka, nan za ni; inda za ki sauka, nan zan sauka: danginki za su zama dangina, Allahnki kuma Allahna.” (Ruth 1:15, 16) Domin ta zaɓi ta bauta wa Jehobah, Ruth ta amfana daga Dokar Allah, wadda ta yi tanadi na musamman ga gwauraye da talakawa da kuma waɗanda ba su da fili. A ƙarƙashin kāriyar Jehobah, Ruth ta samu farin ciki, da kwanciyar hankali.
5. Menene ka gani game da mutanen da suke bauta wa Jehobah da aminci?
5 Wataƙila ka san wasu mutane waɗanda bayan sun keɓe kansu ga Jehobah sun ci gaba da bauta masa da aminci cikin shekaru da yawa. Ka tambaye su yadda suka amfana ta wajen bauta masa. Ko da yake kowa yana da matsaloli, alamar da ke akwai ya tallafa wa kalaman mai zabura sosai: “Masu-farin zuciya ne mutane, waɗanda Ubangiji ne Allahnsu.”—Zab. 144:15.
Jehobah Yana Bukatar Abin da Za Mu Iya Yi
6. Me ya sa ba za mu ji tsoron cewa ba za mu iya yin abin da Jehobah yake bukata a gare mu ba?
6 Mai yiwuwa kana mamaki ko za ka iya yin abin da Jehobah yake bukata a gare ka. Yana da sauƙi mu yi tunanin cewa ba za mu iya zama bayin Allah ba, da yin rayuwar da ta jitu da dokarsa, da kuma yin magana game da sunansa. Alal misali, Musa ya ji bai cancanta ba sa’ad da aka aike shi ya je ya yi magana da Isra’ilawa da kuma sarkin Masar. Amma Allah bai ce Musa ya yi abin da ya fi ƙarfinsa ba. Jehobah ya ‘koya masa abin da zai yi.’ (Karanta Fitowa 3:11; 4:1, 10, 13-15.) Tun da yake Musa ya karɓi taimakon da aka ba shi, ya shaida farin cikin yin nufin Allah. Hakazalika, Jehobah ba ya bukatar mu yi abin da ya fi ƙarfinmu. Ya fahimci cewa mu ajizai ne, kuma yana son ya taimake mu. (Zab. 103:14) Bauta wa Allah ta wajen bin Yesu yana wartsakarwa maimakon gajiyarwa, domin irin wannan tafarkin rayuwa yana sa wasu su amfana kuma yana faranta wa Jehobah rai. Yesu ya ce: “Ku zo gareni . . . ni kuwa in ba ku hutawa. Ku ɗaukar wa kanku karkiyata, ku koya daga wurina; gama ni mai-tawali’u ne, mai-ƙasƙantar zuciya.”—Mat. 11:28, 29.
7. Me ya sa za ka kasance da tabbaci cewa Jehobah zai taimake ka ka yi abin da ya ke bukata a gare ka?
7 Jehobah zai ci gaba da yi mana tanadin ƙarfafawar da muke bukata, muddin mun dogara a gare shi don samun ƙarfi. Alal misali, Irmiya ba mai yin magana da gaba gaɗi ba ne. Saboda haka, sa’ad da Jehobah ya zaɓe shi ya zama annabinsa, Irmiya ya ce: “Ai, Ubangiji Yahweh! ga shi, ni ban iya magana: gama ni yaro ne.” Daga baya ya ce: “Ba ni ƙara faɗin magana cikin sunansa.” (Irm. 1:6; 20:9) Duk da haka, sa’ad da Jehobah ya ƙarfafa shi, Irmiya ya yi wa’azin saƙon da mutane ba sa son su ji har tsawon shekara arba’in. Jehobah ya ci gaba da ƙarfafa shi da waɗannan kalaman: “Ina tare da kai, domin in cece ka, in tsame ka.”—Irm. 1:8, 19; 15:20.
8. Yaya muke nuna cewa mun dogara ga Jehobah?
8 Kamar yadda Jehobah ya ƙarfafa Musa da Irmiya, zai iya taimaka mana mu yi abin da yake bukata daga Kiristoci a yau. Ainihin abin da zai taimaka mana shi ne mu dogara ga Allah. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka, kada ka jingina ga naka fahimi: A cikin dukan al’amuranka ka shaida shi, shi kuma za ya daidaita hanyoyinka.” (Mis. 3:5, 6) Muna nuna cewa mun dogara ga Jehobah sa’ad da muka yi amfani da taimakon da yake tanadinsa ta hanyar Kalmarsa da kuma ikilisiya. Idan muka ƙyale Jehobah ya yi mana ja-gora a rayuwa, babu abin da zai hana mu kasancewa da aminci a gare shi.
Jehobah Yana Kula da Mutanensa Ɗaɗɗaya
9, 10. Wace irin kāriya ce Zabura ta 91 ta yi alkawarinta.
9 Sa’ad da suke tunanin ko su keɓe kansu ga Jehobah, wasu suna iya yin tunanin haɗarin yin zunubi, rashin cancanta, da kuma cewa Jehobah zai ƙi su. Abin farin ciki, Jehobah ya yi tanadin dukan kāriya da muke bukata don mu kāre dangantakarmu mai tamani da shi. Bari mu ga yadda aka furta hakan a Zabura ta 91.
10 Wannan zabura ta soma: “Mai-zama cikin mabuyan Maɗaukaki, za ya dawwama a ƙarƙashin inuwar mai-iko duka. Zan ce da Ubangiji, shi ne mafakata da marayata kuma; Allahna, a gareshi na ke dogara. Gama za ya fishe ka daga tarkon mai-farauta.” (Zab. 91:1-3) Ka lura cewa Allah ya yi alkawarin kāre waɗanda suke ƙaunarsa kuma suka dogara da shi. (Karanta Zabura 91:9, 14.) Wace irin kāriya ce yake nufi? Jehobah ya kāre wasu cikin bayinsa na dā a zahiri, a wasu yanayi don ya kāre zuriya inda Almasihu da aka yi alkawarinsa zai fito. Amma, akwai mutane da yawa masu aminci da aka tsare a fursuna, an gana musu azaba, kuma an kashe su duk a ƙoƙarce-ƙoƙarcen Iblis na hana su kasancewa da aminci ga Allah. (Ibran. 11:34-39) Sun samu gaba gaɗi da suke bukata don su jimre domin Jehobah ya kāre su a ruhaniya daga haɗarin karya amincinsu. Saboda haka, Zabura ta 91 tana nuni ne ga alkawari na kāriya ta ruhaniya.
11. Menene “mabuyan Maɗaukaki,” kuma waye ne Allah yake kārewa a ciki?
11 Saboda haka, “mabuyan Maɗaukaki” da mai zabura ya ambata wuri ne na alama na kāriya ta ruhaniya. A wurin, za a kāre waɗanda suka zauna da Allah a matsayin baƙinsa daga komi ko wani da yake yi wa bangaskiyarsu da kuma ƙaunarsu ga Allah barazana. (Zab. 15:1, 2; 121:5) Maɓuya ne domin marasa bi ba za su iya gane wurin ba. A nan, Jehobah yana kāre mutanen da suka ce: ‘Kai ne Allahna wanda na dogara da shi.’ Idan muka ci gaba da kasancewa a cikin wannan maɓuya, ba ma bukatar mu damu ainun game da rasa amincewar Allah ta wajen faɗa cikin tarkon Shaiɗan, “mai-farauta.”
12. Waɗanne haɗarurruka ne suke yi wa dangantakarmu da Allah barazana?
12 Waɗanne haɗarurruka ne ke yin barazana ga dangantakarmu mai tamani da Allah? Mai zabura ya ambata haɗarurruka masu yawa, a cikinsu akwai “annoban da ke yawo a cikin duhu; [da] halaka wadda ke lalatarwa da tsakar rana.” (Zab. 91:5, 6) “Mai-farauta” ya kama mutane da yawa da sha’awa marar kyau na ’yancin kai. (2 Kor. 11:3) Ya kama wasu ta wajen ɗaukaka haɗama, fahariya, da son abin duniya. Har ila kuma yana yaudarar wasu ta hanyar kishin ƙasa, ra’ayin bayyanau, da addinin ƙarya. (Kol. 2:8) Kuma an kama mutane da yawa cikin tarkon lalata na jima’i. Irin waɗannan ayyuka masu kama da annoba ga ruhaniya sun sa mutane miliyoyi su yi rashin ƙaunarsu ga Allah.—Karanta Zabura 91:7-10; Mat. 24:12.
Ka Kāre Ƙaunarka ga Allah
13. Yaya Jehobah yake kāre mu daga haɗarurruka da ke yi wa zaman lafiyarmu na ruhaniya barazana?
13 Yaya Jehobah yake kāre mutanensa daga waɗannan haɗarurruka na ruhaniya? Mai zabura ya ce: “Za ya ba mala’ikunsa tsaronka, su kiyaye ka cikin tafarkunka duka.” (Zab. 91:11) Mala’iku na samaniya suna yi mana ja-gora kuma suna kāre mu domin mu yi wa’azin bishara. (R. Yoh. 14:6) Ƙari ga mala’iku, dattawa Kirista ta wajen bin Nassosi sosai a koyarwarsu, suna kāre mu don kada a yaudare mu da tunanin ƙarya. Suna iya taimaka wa dukan waɗanda suke fama don su sha kan halaye na duniya. (Tit. 1:9; 1 Bit. 5:2) Kuma “Bawan nan mai-aminci, mai-hikima” yana yin tanadin abinci na ruhaniya don ya kāre mu daga koyarwar ra’ayin bayyanau, sha’awoyin yin lalata, biɗar arziki da yin suna, da sha’awoyi da tasiri da yawa masu lahani. (Mat. 24:45) Menene ya taimaka maka ka ƙi wasu cikin waɗannan haɗarurruka?
14. Ta yaya za mu yi amfani da kāriya da Allah yake tanadinta?
14 Menene za mu yi don mu kasance cikin “mabuyan” kāriya na Allah? Kamar yadda a koyaushe muna kāre kanmu daga abubuwan da za su iya cutar da mu a zahiri, kamar su haɗari, masu aikata laifi, ko cututtuka, dole ne mu riƙa ɗaukan mataki a kai a kai don mu kāre kanmu daga haɗarurruka na ruhaniya. Saboda haka, ya kamata a kowane lokaci mu bi ja-gorancin da Jehobah yake tanadinsa dominmu a cikin littattafanmu da taron ikilisiya da kuma manyan taro. Muna neman shawarar dattawa. Kuma muna amfana daga halaye dabam-dabam da ’yan’uwanmu Kiristoci suke nunawa, ko ba haka ba? Hakika, yin tarayya da ikilisiya yana taimaka mana mu zama masu hikima.—Mis. 13:20; karanta 1 Bitrus 4:10.
15. Me ya sa za ka kasance da tabbaci cewa Jehobah zai iya kāre ka daga duk wani abin da zai sa ka rasa amincewarsa?
15 Ba mu da wani dalilin yin shakkar cewa Jehobah zai iya kāre mu daga duk wani abin da zai sa mu rasa amincewarsa. (Rom. 8:38, 39) Ya kāre ikilisiya daga addinai masu iko da magabta ’yan siyasa waɗanda ba so suke su kashe mu ba amma so suke su ware mu daga Allahnmu mai tsarki. Alkawarin da Jehobah ya yi ya kasance gaskiya: “Babu alatun da aka halitta domin cutarki da za ya yi albarka.”—Isha. 54:17.
Wa Ke Ba Mu ’Yanci?
16. Me ya sa duniya ba za ta iya ba mu ’yanci ba?
16 Zama na Jehobah zai hana mu kasancewa da ’yanci ne? Akasin haka, zama na duniya zai hana mu ’yanci. Duniya tana bāre daga Jehobah kuma azzalumin alla wanda yake sa mutane cikin bauta ne sarkinta. (Yoh. 14:30) Alal misali, tsarin abubuwa na Shaiɗan yana amfani da matsi na tattalin arziki don ya hana mutane ’yancinsu. (Gwada Ru’ya ta Yohanna 13:16, 17.) Zunubi ma yana da ikon sa mutane cikin bauta. (Yoh. 8:34; Ibran. 3:13) Saboda haka, ko da yake marasa bi suna iya yin alkawarin ’yanci sa’ad da suke ɗaukaka hanyar rayuwa da ta saɓa wa koyarwar Jehobah, duk wanda ya saurare su zai sami kansa yana bauta wa salon rayuwa na zunubi da na ƙazanta.—Rom. 1:24-32.
17. Wane ’yanci ne Jehobah yake miƙa mana?
17 A wani ɓangare kuma, Jehobah zai ’yantar da mu daga duk wani abin da zai iya lahanta mu idan muka dogara a gare shi. A wasu hanyoyi, yanayinmu yana kama da mutumin da ya saka ransa a hannun ƙwararren likita mai fiɗa wanda zai iya ’yantar da shi daga rashin lafiyar da za ta iya ɗauke ransa. Mu duka muna cikin yanayin da zai iya ɗauke ranmu, wato, zunubin da muka gāda. Idan muka miƙa kanmu ga Jehobah, bisa hadayar Kristi ne kawai za mu samu begen tsira daga sakamakon zunubi kuma mu rayu har abada. (Yoh. 3:36) Kamar yadda za mu ƙara amincewa da mai fiɗa sa’ad da muka ji cewa ya iya aiki sosai, haka dogarar mu ga Jehobah za ta ƙara ƙaruwa sa’ad da muka ci gaba da koyo game da shi. Saboda haka, za mu ci gaba da nazarin Kalmar Allah sosai domin hakan zai taimaka mana mu ƙaunace shi a hanyar da za ta ƙawar da kowane tsoro da muke ji na zama nasa.—1 Yoh. 4:18.
18. Wane sakamako ne waɗanda suka zama na Jehobah za su samu?
18 Jehobah ya ba dukan mutane ’yancin yin zaɓe. Kalmarsa ta ce: ‘Ka zaɓi rai fa, domin ka rayu, da kai da zuriyarka: garin ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka.’ (K. Sha 30:19, 20) Yana son mu nuna ƙaunarmu a gare shi ta wurin tsai da shawarar bauta masa da kanmu. Maimakon ya hana mu ’yanci, zama na Allah da muke ƙauna babu shakka zai sa mu farin ciki.
19. Me ya sa zama na Jehobah alheri ne da ba mu cancanta ba?
19 A matsayin masu zunubi, ba mu cancanci zama na Allah kamiltacce ba. Alherin Allah ne ya sa hakan ya yiwu. (2 Tim. 1:9) Shi ya sa Bulus ya rubuta: “Ko muna rayuwa, ga Ubangiji muke rayuwa; ko mutuwa muke yi, ga Ubangiji muke mutuwa; ko mu rayu fa, ko mu mutu, na Ubangiji muke.” (Rom. 14:8) Ba za mu taɓa yin da na sani zaɓan zama na Jehobah ba.
Yaya Za Ka Amsa?
• Menene amfanin zama na Jehobah?
• Me ya sa za mu iya yin abin da Allah yake bukata a gare mu?
• Yaya Jehobah yake tanadin kāriya ga bayinsa?
[Hotuna da ke shafi na 8]
Ka tambayi mutane yadda suka amfana ta wajen zama na Jehobah
[Hoton da ke shafi na 10]
A waɗanne hanyoyi ne Jehobah yake tanadin kāriya?