Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 4/1 pp. 21-26
  • Ya Koyi Gafartawa Daga Wurin Ubangijinsa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ya Koyi Gafartawa Daga Wurin Ubangijinsa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Mutum da ke da Abubuwa da Yawa da Zai Koya
  • Ƙarin Bukatar Gafartawa
  • Kuskuren Bitrus Mafi Tsanani
  • Shin Kuskuren Bitrus Ya Wuce a Gafarta Masa Kuwa?
  • Ƙarin Tabbaci na Gafartawa
  • Ya Koyi Gafartawa Daga Wurin Ubangijinsa
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Ya Kasance da Aminci a Lokacin Gwaji
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Ya Shawo Kan Tsoro da Kuma Shakka
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Za Ka Iya Ci Gaba da Yin Kokari Kamar Bitrus
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 4/1 pp. 21-26

Ka Yi Koyi Da Imaninsu

Ya Koyi Gafartawa Daga Wurin Ubangijinsa

BITRUS ba zai taɓa mance da takaicin da ya ji ba sa’ad da idanunsu ya haɗu. Shin kallon da Yesu ya yi masa ya nuna baƙin ciki ne ko kunya? Ba za mu iya sani ba, abin da hurarren labarin ya ce kawai shi ne “Ubangiji ya waiwaya, ya dubi Bitrus.” (Luka 22:61) Amma a kallon nan guda, Bitrus ya ga tsananin kuskurensa. Ya fahimci cewa ya yi ainihin abin da Yesu ya annabta, abin da Bitrus ya nanata cewa ba zai taɓa yi ba, ya ƙi Ubangijinsa. Lokaci ne mafi takaici a rayuwar Bitrus, wataƙila lokaci da rana mafi tsanani a rayuwarsa.

Wannan ba shike nan ba ne ga Bitrus. Saboda Bitrus mutumi ne mai imani sosai, yana da sauran zarafi na warwarewa daga kurakurensa kuma ya koyi ɗaya cikin darussan mafi girma na Yesu. Hakan ya shafi gafartawa. Kowannenmu muna bukata mu koyi irin wannan darasin, bari mu ga yadda Bitrus ya koyi wannan darassi mai wuya.

Mutum da ke da Abubuwa da Yawa da Zai Koya

Kusan watanni shida kafin wannan aukuwar a garinsu a Kafarnahum, Bitrus ya je wurin Yesu kuma ya tambaye shi: “Ubangiji, so nawa ɗan’uwana za ya yi mani zunubi, in gafarta masa? har so bakwai? Bitrus yana tunanin cewa ta yin hakan yana da kirki sosai. Ga shi ma malaman addinin zamanin sun koyar cewa mutum ya gafarta sau uku kawai! Yesu ya ce masa, Ban ce maka, Har so bakwai ba; amma, Har bakwai bakwai so saba’in.”—Matta 18:21, 22.

Shin Yesu yana ce wa Bitrus ne ya dinga rubuta sau nawa aka yi masa laifi kuwa? A’a, maimakon hakan, ta mai da bakwai ɗin Bitrus zuwa saba’in da bakwai, yana nufin cewa babu iyaka ga gafartawa. Yesu ya nuna cewa taurin zuciya da halin rashin gafartawa wanda gama gari ne a lokacin ya rinjayi Bitrus, wanda yake sa ake lissafa kurakuran mutum kamar ana lissafa bashi. Amma dai, gafartawa da ke bisa ƙa’idodin Allah kyauta ce.

Bitrus bai yi musu da Yesu ba. Amma shin darasin Yesu ya taɓa zuciyar Bitrus kuwa? A wasu lokatai muna koya gafartawa sosai idan mu ma muna bukatar gafara. Yanzu bari mu koma aukuwar da ya faru zuwa mutuwar Yesu. A waɗannan sa’o’in masu wuya, Bitrus ya ba Ubangijinsa abubuwa da yawa da zai gafarta.

Ƙarin Bukatar Gafartawa

Muhimmiyar yamma ce, daren ƙarshe na rayuwar Yesu a duniya. Yesu yana da ƙarin abubuwa da yawa da zai koya wa almajiransa, alal misali, game da tawali’u. Yesu ya kafa misali ta wanke ƙafafunsu cikin tawali’u, aikin da bayi suke yi. Da farko, Bitrus ya ƙalubanci abin da Yesu ya yi. Sai ya ƙi yarda a wanke ƙafafunsa. Sai ya kuma nace cewa Yesu ya wanke ƙafafunsa hannayensa da kansa! Yesu bai yi fushi ba, amma ya bayyana muhimmancin da ma’anar abin da ya yi cikin natsuwa.—Yohanna 13:1-17.

Jim kaɗan bayan hakan, almajiran suka soma musu game da wanda ya fi girma cikinsu. Bitrus ma yana cikin waɗanda suke yin wannan abin kunya, wato nuna girman kai. Amma dai, Yesu ya daidaita su cikin tawali’u har ma ya ƙarfafa su don halinsu mai kyau na manne wa Ubangijinsu. Amma ya annabta cewa dukansu za su yashe shi. Bitrus ya amsa cewa zai kasance tare da Yesu ko a gaban mutuwa. Yesu ya annabta cewa Bitrus zai musunci Ubangijinsa sau uku a daren kafin zakara ta yi cara sau biyu. Bitrus bai musunci abin da Yesu ya ce kaɗai ba amma ya cika baki cewa zai fi dukan sauran almajiran kasancewa da aminci!—Matta 26:31-35; Markus 14:27-31; Luka 22:24-28.

Shin Yesu ya yi fushi da Bitrus ne? Hakika, cikin dukan wannan mawuyacin lokaci, Yesu ya ci gaba da neman hali mai kyau a waɗannan almajiransa ajizai. Ya san cewa Bitrus zai yashe shi, amma duk da haka ya ce: “Na yi maka addu’a kada bangaskiyarka ta kāsa: kai ma lokacin da ka sāke juyowa, sai ka ƙarfafa ’yan’uwanka.” (Luka 22:32) Yesu ya nuna yardarsa cewa Bitrus zai waiwaya ya sake soma amintattun ayyuka. Wannan halin gafartawa ne sosai!

Daga baya, a lambun Jathsaimani, Bitrus yana bukatar gyara fiye da sau ɗaya. Yesu ya ce masa, da Yaƙub da Yohanna, su yi tsaro yayin da Yake yin addu’a. Yesu yana cikin azaba na motsin rai kuma yana bukatar taimako, amma Bitrus da sauran sun yi barci sau da yawa. Yesu ya furta waɗannan kalamai da suka nuna tausayi da gafartawarsa: “Gaskiya ruhu ya yarda, amma jiki rarrauna ne.”—Markus 14:32-38.

Ba da daɗewa ba, taron ’yan iska suka taho, suna riƙe da tocila da takuba da kulki. Yanzu lokaci ne na aikatawa da hankali. Duk da haka, Bitrus ya ɗauki mataki, ya miƙa takobi bisa kan Malchus, bawan babban firist, sai ya datse kunnensa guda. Yesu ya yi wa Bitrus gyara cikin tawali’u, ya warkar da ciwon, sai ya bayyana ƙa’idar ƙin yin faɗa wanda ke ja-goranci mabiyansa har yau. (Matta 26:47-55; Luka 22:47-51; Yohanna 18:10, 11) Bitrus ya riga ya yi kurakure da yawa da yake bukata Ubangijinsa ya gafarta masa. Labarinsa zai iya tuna mana cewa “dukanmu mu kan yi tuntuɓe.” (Yaƙub 3:2) Wanene cikinmu ba ya bukatar Allah ya gafarta masa kowanne rana? Ga Bitrus kuwa, abubuwa da yawa za su faru a daren. Abu mafi tsanani zai faru.

Kuskuren Bitrus Mafi Tsanani

Yesu ya tattauna da ’yan iskan cewa idan shi suke nema, su ƙyale almajiransa su tafi. Bitrus ya kalli ba tare da iya yin komi ba sa’ad da ’yan iskan suka kama Yesu. Bayan hakan sai Bitrus ya gudu, yadda sauran almajiran suka yi.

Bitrus da Yohanna suka daina guduwan, wataƙila kusa da gidan Babban Firist na dā Hananiya, inda aka soma kai Yesu. Sa’ad da aka fitar da Yesu daga wurin, Bitrus da Yohanna suka bi shi amma “daga nesa nesa.” (Matta 26:58; Yohanna 18:12, 13) Bitrus ba matsoraci ba ne. Babu shakka, yana bukatan gaba gaɗi sosai ya bi shi. ’Yan iskan suna riƙe da makamai, kuma Bitrus ya riga ya ji wa ɗayansu rauni. Duk da haka, ba mu iya tsammani a misalin Bitrus irin ƙaunar da shi da kansa yake da shi ba, ya yarda ya mutu tare da Ubangijinsa idan bukata ta kama.—Markus 14:31.

Kamar Bitrus, mutane da yawa a yau suna son su bi Kristi “daga nesa nesa,” don kada kowa ya san cewa suna binsa. Amma daga baya Bitrus da kansa ya rubuta cewa, hanya kaɗai da za mu iya bin Kristi sosai shi ne kusantarsa iya ƙarfinmu, bin misalinsa a dukan abubuwa, ko da menene yanayinmu.—1 Bitrus 2:21.

Bitrus ya bi waɗanda suka kama Yesu a hankali har suka isa ƙofar wata gida mafi kyau a Urushalima. Gidan Kayafa ne, babban firist mai wadata da iko. Akan gina irin waɗannan gidajen kewaye da farfajiya, da ƙofa a gabanta. Bitrus ya isa ƙofar kuma ba a yarda ya shi ba. Yohanna da ya riga ya shi ciki, ya fito ya ce wa mai gadin ya ƙyale Bitrus ya shi. Kamar Bitrus bai tsaya kusa da Yohanna ba; kuma bai shiga cikin gidan ba don ya tsaya kusa da Ubangijinsa. Ya zauna a farfajiyar, inda wasu barori da dogaran haikalin suke wucewa ta gaban wuta da daddaren, suna kallo yadda ake gwada Yesu a ciki.—Markus 14:54-57; Yohanna 18:15, 16, 18.

Da taimakon hasken wutan, yarinyar da ta ƙyale Bitrus ya shiga ta samu ganinsa sosai. Ta waye shi. Ta tuhume shi: “Kai kuma dā kana tare da Yesu Ba-galilin nan!” Ba zata ba tsammani, Bitrus ya musunci sanin Yesu, ko kuma fahimtar abin da yarinyar take faɗa. Sai ya koma ya tsaya kusa da ƙofar, don kada a waye shi, amma sai wata yarinya ta waye shi sai ta nuna shi ta ce: “Wannan mutum kuma dā yana tare da Yesu Ba-nazarat.” Bitrus ya rantse: “Ban san mutumin ba.” (Matta 26:69-72) Wataƙila bayan wannan musu na biyu da Bitrus ya yi ne zakara ya yi cara, amma bai maida hankali ga annabcin da Yesu ya furta ɗazun ba.

Bayan hakan, Bitrus ya ci gaba da yin ƙoƙari don kada a waye shi. Amma rukunin mutanen da ke tsaye a farfajiyar suka matso kusa. Ɗaya cikinsu ɗan’uwan Malchus ne, wannan bawan da Bitrus ya ji ma rauni. Ya ce wa Bitrus: “Ko ban gan ka a cikin gona tare da shi ba?” Bitrus ya nemi ya sa su yarda cewa ba haka ba ne. Sai ya rantse game da zancen, ya ce la’ana ta same shi idan ƙarya yake yi. Kalaman suna fitowa daga bakinsa sai zakara ya yi cara, na biyu kenan da Bitrus ya ji a daren.—Yohanna 18:26, 27; Markus 14:71, 72.

Yesu ya shigo cikin fafarandan ne, yana kallon farfajiyar. A lokacin, kamar yadda aka faɗa da farko ne idanunsa suka haɗe da na Bitrus. Bitrus ya ankara cewa ya yi wa Ubangijinsa laifi mai tsanani. Bitrus ya fita daga farfajiyar cike da takaici saboda kuskurensa. Ya nufa cikin gari, hasken wata kuma ta cika ko’ina. Idanunsa suka kumbura. Hawaye suka soma zubo masa. Ya yi kuka mai zafi.—Markus 14:72; Luka 22:61, 62.

Bayan ya ankara tsananin irin wannan kuskuren, yana da sauƙi mutum ya yi tunani cewa ba za a iya gafarta masa ba. Wataƙila Bitrus ya yi tunanin hakan. Za a iya gafarta masa kuwa?

Shin Kuskuren Bitrus Ya Wuce a Gafarta Masa Kuwa?

Yana da wuya mu fahimci yadda Bitrus ya ji sa’ad da gari ya waye kuma aukuwar ranar suka soma faruwa. Babu shakka ya tsauta wa kansa sosai sa’ad da Yesu ya mutu da ranan bayan sa’o’in azaba! Wataƙila Bitrus ya ji azaba duk lokacin da ya yi tunani game da yadda ya ɓata ran Ubangijinsa a daren ƙarshe na rayuwarsa a matsayin mutum. Duk da tsananin baƙin cikin da ya ji, Bitrus bai yi sanyin gwiwa ba. Mun san da hakan domin ba da daɗewa ba ya sake soma tarayya da sauran ’yan’uwansa. (Luka 24:33) Babu shakka dukan almajiran sun yi baƙin ciki game da yadda suka aikata a wannan daren mai wuya, kuma sun ƙarfafa junansu.

A nan mun gan Bitrus yana yanka shawara mafi kyau. Yayin da bawan Allah ya ƙasa, abu mai muhimmanci ba zurfin ƙasawarsa ba amma ƙudurinsa na sake tashi, ya daidaita komai. (Misalai 24:16) Bitrus ya nuna tabbataciyar imani ta tattara ’yan’uwansa duk da ƙasawarsa. Idan mutum yana cike da baƙin ciki ko nadama, zai so ya kaɗaita amma hakan bai dace ba. (Misalai 18:1) Abu mafi kyau shi ne ya zauna tare da ’yan’uwansa kuma ya samu ƙarfafa na ruhaniya.—Ibraniyawa 10:24, 25.

Domin yana tare da ’yan’uwansa na ruhaniya, Bitrus ya samu labari mai tayar da hankali cewa an ɗauki gawar Yesu daga kabarin. Bitrus da Yohanna suka gudu zuwa kabarin da aka binne Yesu kuma aka rufe ƙofar. Yohanna, wataƙila ya fi Bitrus ƙarami, ya fara isa wurin. Da ya tarar da ƙofar a buɗe, sai ya dakata. Amma Bitrus bai yi hakan ba. Ko da ya gaji don gudun da ya yi, ya shiga cikin. Babu komi a ciki!—Yohanna 20:3-9.

Shin Bitrus ya amince cewa Yesu ya tashi daga matattu kuwa? Hakan bai faru da farko ba, ko da mata amintattu sun sanar cewa mala’iku sun bayana musu don sanar cewa Yesu ya tashi daga matattu. (Luka 23:55–24:11) Amma a ƙarshen ranar, dukan baƙin ciki da shakka da ke zuciyar Bitrus sun riga sun ɓace. Yanzu Yesu yana da rai, a matsayin ruhu mai iko! Ya bayana wa dukan manzanninsa. Amma da farko ya soma yin wani abu dabam, ko da yake asiri ne. Manzanni sun ce a ranar “Hakika Ubangiji ya tashi, ya kuwa bayyana ga Siman.” (Luka 24:34) Akasin hakan, manzo Bulus daga baya ya rubuta game da wannan rana mai ban al’ajabi da Yesu ya ‘bayyana ga Kefas; sannan ga su goma sha biyu.’ (1 Korintiyawa 15:5) Kefas da Siman wasu sunayen da ake kiran Bitrus ne. Yesu ya bayyana masa a ranar, wataƙila sa’ad da yake shi kaɗai.

Littafi Mai Tsarki bai bayyana dalla-dalla abin da ya faru sa’ad da Yesu da Bitrus suka sake saduwa ba. Amma dai za mu iya tunani yadda Bitrus ya ji sa’ad da ya ga ƙaunataccen Ubangijinsa ya sake rayuwa kuma ya samu zarafin nuna baƙin cikinsa da neman gafara. Abu mafi muhimmanci da yake bukata shi ne gafara. Wanene zai iya musunci cewa Yesu ya gafarta masa a yalwace? Kiristoci a yau da suka faɗa cikin zunubi suna bukatar su tuna da labarin Bitrus. Kada mu taɓa tunani cewa mun wuce Allah ya gafarta mana. Yesu yana wakiltar Ubansa sarai, wanda ke “gafara a yalwace.”—Ishaya 55:7.

Ƙarin Tabbaci na Gafartawa

Yesu ya gaya wa almajiransa su je Galili, inda za su sake saduwa da shi. Sa’ad da suka isa wurin, Bitrus ya tafi Tekun Galili don sū. Da yawa cikin sauran suka raka shi. Bitrus ya sake ganin kansa a tafkin da yake yawan kasancewa shekaru da yawa da suka gabata. Babu shakka, Bitrus ya tuna da karan tafiyar jirgin, na raƙumin ruwan da yadda yake riƙe tarunsa. Shin ya yi mamaki da daddaren yadda ya kamata ya dinga rayuwa yanzu da Yesu ya kusan gama hidimarsa a duniya? Shin ya yi sha’awar rayuwar masu sū marar yawan matsaloli? Ko yaya dai, ba su kama kifi daddaren ba.—Matta 26:32; Yohanna 21:1-3.

Amma da sassafe, wani ya kira su daga bakin tekun kuma ya umurce su su saka tarunsu cikin wancan ɓangaren jirgin. Suka yi hakan kuma suka kama kifaye guda ɗari da hamsin da uku! Bitrus ya san kowanene wannan mutum. Ya yi tsalle daga jirgin zuwa bakin takun. A bakin tekun, Yesu ya ba su kifin da aka gasa da wutan gawayi. Ya mai da hankali ga Bitrus.

Yesu ya tambayi Bitrus in yana ƙaunar Ubangijinsa ‘fiye da wannan,’ babu shakka ya miƙa hannu ga kifin da suka kama. A zuciyar Bitrus, shin ƙaunar da yake da shi ga aikin sū ya fi wanda yake wa Yesu kuwa? Kamar dai yadda Bitrus ya musunci Ubangijinsa sau uku, Yesu ya ba shi zarafi ya nuna zurfin ƙaunarsa sau uku a gaban mabiyinsa. Sa’ad da Bitrus ya yi hakan, Yesu ya faɗar masa yadda zai nuna wannan ƙaunar, ta saƙa tsarkakkar ayyuka gaba da kowacce irin aiki, yin kiwon tumakin Kristi, wato, amintattun mabiyinsa.—Yohanna 21:4-17.

Da haka, Yesu ya nuna cewa har ila Bitrus yana da amfani gare shi da Ubansa. Bitrus zai ɗauki matsayi mai tamani a ikilisiyar da ke ƙarƙashin ja-gorancin Kristi. Wannan tabbacin cikakken gafartawar Yesu ne! Babu shakka wannan halin jin ƙai ya taɓa Bitrus, kuma hakan ya shafe shi.

Bitrus ya yi hidimarsa cikin aminci a shekaru da yawa. Ya ƙarfafa ’yan’uwansa, kamar yadda Yesu ya umurce shi a daren ƙarshe kafin mutuwarsa. Bitrus yana kiwon mabiyin Kristi cikin haƙuri da tawali’u. Mutumin nan Siman ya cika sunan da Yesu ya ba sa, wato, Bitrus, ko Dutse ta zaman mai ƙarfi da kuma abin ƙarfafa ga ikilisiyar. Muna da ƙarin tabbacin hakan ta wasiƙun ƙauna biyu da Bitrus ya rubuta da suka zama littattafan a Littafi Mai Tsarki. Waɗannan wasiƙun sun nuna cewa Bitrus bai taɓa manta da darasin da ya koya daga gafartawar Yesu ba.—1 Bitrus 3:8, 9; 4:8.

Bari mu ma mu koyi wannan darasin. Shin muna neman gafarar Allah kullum don kurakuranmu kuwa? Shin muna karɓar gafarar kuma mu amince cewa zai tsarkaka mu? Kuma shin muna gafarta wa waɗanda suke tare da mu kuwa? Idan mun yi hakan, za mu yi koyi da imanin Bitrus, da kuma jin ƙan Ubangijinsa.

[Bayanin da ke shafi na 22]

Bitrus ya ba Ubangijinsa abubuwa da yawa da zai gafarta, amma wanene cikinmu ba ya bukatar gafartawa kullum?

[Hoton da ke shafi na 23]

“Ubangiji ya waiwaya, ya dubi Bitrus”

[Hoton da ke shafi na 24]

“Ubangiji ya . . . bayyana ga Siman.”

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba