Na Shagala Sosai A Ƙungiyar Jehobah
Vernon Zubko ne ya ba da labarin
AN RENE ni a wata gona da ke kusa da Stenen, wani ƙauye da ke lardin Saskatchewan, Kanada. Iyayena, Fred da Adella, sun yi aiki tuƙuru don su yi wa yayata, Aurellia, da ni da kuma ƙannena, Alvin, Allegra, da Daryl tanadi na ruhaniya da na zahiri. Har yau, muna godiya ga iyayenmu don gaskiya da suka koya mana.
Mahaifina Kirista ne shafaffe kuma yana wa’azi da gaba gaɗi. Ya yi aiki tuƙuru don ya yi mana tanadi, amma ya kuma sa kowa su san cewa shi Mashaidi ne. Yana magana game da gaskiya kuma. Ba zan taɓa mantawa da ƙwazo da kuma gaba gaɗinsa ba. Yana yawan gaya mini, “Idan ka shagala a ƙungiyar Jehobah za ka kauce wa matsaloli da yawa.”
Sau da yawa, muna yin wa’azi a titin Stenen da kewayenta. Hakan bai kasance mini da sauƙi ba. Kowane gari yana da nasa azzalumai waɗanda za su zo wurinmu matasa suna yi mana ba’a. Sa’ad da nake ɗan shekara takwas, na tsaya a wani ɓangare da Hasumiyar Tsaro da Awake! sai matasa da yawa suka kewaye ni. Suka ƙwace sabon hular da na saka kuma suka rataye shi a kan wata doguwar sanda da ke kusa da ni. Abin farin ciki, wani ɗan’uwa da ya fi ni girma da ke kula da ni ya ga abin da ke faruwa. Sai ya zo wurin ya ce, “Vern, akwai wata matsala ne?” Sai duk yaran suka watse. Ko da abin da ya faru ya ɓata mini rai kaɗan, amma ya koya mini cewa sa’ad da nake wa’azi a kan titi, ya dace na ci gaba da yin tafiya kada na tsaya a wuri ɗaya. Irin wannan koyarwar a lokacin da nake girma ya sa na samu gaba gaɗin yin wa’azi daga kofa zuwa kofa.
Ni da Alvin mun yi baftisma a watan Mayu a shekara ta 1951. Ina ɗan shekara sha uku a lokacin. Amma na tuna cewa Ɗan’uwa Jack Nathan, wanda ya ba da jawabin baftismar, ya aririce mu cewa kada mu taɓa ƙyale wata ɗaya ta wuce ba tare da mun yi magana game da Jehobah ba.a A iyalinmu, muna ɗaukan hidimar majagaba kamar abu mafi kyau da mutum ya kamata ya yi. Saboda haka a shekara ta 1958, bayan na gama makaranta, na ƙaura zuwa birnin Winnipeg, Manitoba, don yin hidimar majagaba. Ko da Babana ya yi farin ciki sosai don aikin gyaran katako da nake yi tare da shi, shi da Mamata sun ƙarfafa ni na yi aikin hidima ta cikakken lokaci kuma sun tallafa mini na ƙaura.
Sabon Gida da Sabuwar Abokiyar Aiki
A shekara ta 1959, ofishin reshe ya gayyaci kowa da zai iya ya ƙaura zuwa lardin Quebec, inda ake bukatar masu hidima sosai. Na yi hidimar majagaba a birnin Montreal. Wannan canji ne na musamman! Hakan ya yi dabam da abin da na taɓa yi a dā, domin ina koyon yaren Faransa kuma ina neman sabawa da wata al’ada dabam. Mai kula da da’irarmu ya gaya mini, “Kada ka ce, ‘Haka ne muke yi a gida.’” Wannan shawara ce mai kyau.—1 Kor. 9:22, 23.
Ba ni da aboki da muke aikin majagaba tare sa’ad da na ƙaura zuwa lardin Quebec. Amma, wata ’yar’uwa matashiya mai suna Shirley Turcotte, wadda na sadu da ita da farko a birnin Winnipeg, ta zama abokiyar aikina na dindindin sa’ad da muka yi aure a watan Fabrairu na shekara ta 1961. Ita ma ta zo daga iyalin da suke ƙaunar Jehobah. Ko da yake a lokacin ban san cewa za ta zama mini abin ƙarfafa sosai a shekaru da yawa ba.
Tafiye-Tafiyen Wa’azi a Birnin Gaspé
An naɗa mu majagaba na musamman a birnin Rimouski, Quebec shekaru biyu bayan aurenmu. A lokacin bazara na gaba, ofishin reshe suka ce mu yi tafiye-tafiyen wa’azi a wurare da yawa a birnin Gaspé da ke kusa da teku a gabashin Kanada. Aikinmu shi ne mu yi wa’azi sosai yadda ya yiwu. (M. Wa. 11:6) Muka cika motarmu da mujallu fiye da 1,000 da littattafai kusan 400, da kuma abinci da tufafi, kuma muka yi wa’azi na wata guda. Muka yi wa’azi sosai a dukan ƙananan ƙauyuka da ke birnin Gaspé. Tashar rediyo da ke ƙauyen suka yi kashedi cewa Shaidun suna nan tafe kuma suka gaya wa mutanen cewa kada su karɓi littattafanmu. Amma, yawancin mutanen ba su fahimci sanarwar ba kuma suka yi tsammani cewa suna tallar littattafanmu, saboda haka suka karɓi littattafan.
Bai daɗe ba da aka ba da ’yancin yin wa’azi a wasu ɓangarorin lardin Quebec a waɗannan shekarun, saboda haka, ba abin mamaki ba ne idan ’yan sanda suka tsayar da mu. Hakan ya faru a wani birni da muke ba da littattafai a kusan kowace ƙofa. Wani ɗan sanda ya ce mana mu bi shi zuwa ofishinsu, kuma muka bi shi. Na gano cewa lauyan da ke birnin ya ba da umurni a sa mu daina wa’azi. Tun da yake shugaban ’yan sandan ya yi tafiya a ranar, na nuna wa lauyan wasiƙar da aka rubuta daga ofishin reshe da ke birnin Toronto da ya bayyana hakkinmu na yin wa’azi. Bayan ya karanta wasiƙar, lauyan ya ce da sauri: “Kun ga, ba na son matsala. Firist ne ya gaya mini na sa ku daina.” Tun da yake muna son mutane da ke yankin su san cewa wa’azin da muke yi bisa doka ne, nan da nan muka koma wurin da ɗan sandan ya tsayar da mu kuma muka soma hidimarmu.
Washegari da safe sa’ad da muka koma mu ga shugaban ’yan sanda, ya yi fushi da ya ji cewa an ce mu daina wa’azin. Ya yi fushi sosai da lauyan sa’ad da yake magana da shi a waya. Ɗan sandan ya gaya mana cewa idan muna da wata matsala, mu zo mu same shi zai magance matsalar. Ko da yake mu baƙi ne kuma ba mu iya Faransanci sosai ba, mutanen sun nuna mana alheri da karimci. Amma, mun yi mamaki, ‘Za su taɓa sanin gaskiya kuwa?’ Mun sami amsar bayan shekaru da yawa sa’ad da muka koma don mu gina Majami’un Mulki a dukan birnin Gaspé. Mun ga cewa mutane da yawa da muka taɓa yi wa wa’azi ’yan’uwanmu ne yanzu. Hakika, Jehobah ne ke ba da amfani.—1 Kor. 3:6, 7.
Mun Samu Gado
An haifi ’yarmu Lisa a shekara ta 1970. Wannan gado daga wurin Jehobah ya daɗa mana farin ciki a rayuwa. Shirley da Lisa sun yi aiki tare da ni a aikin gine-gine na Majami’ar Mulki. Bayan Lisa ta gama makaranta, sai ta ce: “To, Mama da Baba, tun da yake ni ce na sa ku bar hidima ta cikakken lokaci na ɗan lokaci, zan biya ku ta wajen zama majagaba.” Shekaru 20 bayan hakan, Lisa ta ci gaba da hidimar majagaba, amma yanzu tare da mijinta, Sylvain. Suna da gatar yin aikin gine-gine masu yawa a wasu ƙasashe tare. Makasudinmu a matsayin iyali shi ne mu sauƙaƙa rayuwarmu kuma mu ba da kanmu don hidimar Jehobah. Ban taɓa mantawa da kalaman Lisa sa’ad da ta soma majagaba ba. Hakika, ta motsa ni na koma hidima ta cikakken lokaci a shekara ta 2001, kuma ina aikin majagaba tun lokacin. Hidimar majagaba ta ci gaba da koya mini na dogara ga Jehobah a dukan abubuwan da nake yi kuma na sauƙaƙa rayuwata kuma na samu gamsuwa da farin ciki a rayuwa.
Aikin Gine-Gine na Bukatar Ƙauna da Aminci
Jehobah ya koya mini cewa idan muka ba da kanmu kuma muka karɓi kowane aikin da ya ba mu, za mu samu albarka mai yawa. Yin hidima na Kwamitin Gini na Yanki, da kuma aikin gine-gine tare da ’yan’uwana maza da mata a dukan lardin Quebec da wasu wurare gata ce mai tamani.
Ko da yake wasu da suka ba da kansu ba za su iya ba da jawabai na musamman a kan dakalin yin magana ba, amma sun ƙware a aikinsu na gina Majami’ar Mulki sosai. Waɗannan ƙaunatattu suna yin aikin da dukan zuciyarsu, kuma ana ganin iyawarsu. Sakamakon shi ne kyakkyawan gini da za a yi amfani da shi a bautar Jehobah.
An tambaye ni, “Waɗanne halaye mafi muhimmanci ne ake bukatan daga wanda ya ba da kansa a aikin gina Majami’ar Mulki?” Daga abin da na shaida, dole ne mutum ya fara ƙaunar Jehobah da Ɗansa da kuma dukan ’yan’uwanci. (1 Kor. 16:14) Na biyu, ana bukatar aminci. Sa’ad da abubuwa ba su faru yadda muke so ba, kuma hakan zai faru, mutum mai aminci zai bi ja-gorancin ƙungiyar nan. Aminci zai motsa shi ya ba da kansa don ayyuka na nan gaba.
Godiya ga Jehobah
Ko da yake babana ya mutu a shekara ta 1985, na ci gaba da tunawa da shawarar da ya ba ni cewa in shagala a ƙungiyar Jehobah. Kamar wasu da suka samu ladarsu a sashen ƙungiyar Jehobah na samaniya, babu shakka ya shagala. (R. Yoh. 14:13) Yanzu Mamata tana da shekaru 97. Domin ciwon gazawar jiki, ba ta iya yin magana yadda take yi ba, duk da haka ta san Littafi Mai Tsarki. Tana yin ƙaulin nassosi a cikin wasiƙunta kuma tana ƙarfafa mu mu ci gaba da bauta wa Jehobah da aminci. Dukanmu yara muna godiya don samun irin waɗannan iyaye masu ƙauna!
Ina kuma godiya ga Jehobah don Shirley, matata abokiya mai aminci da ya ba ni. Tana bin shawarar da mamarta ta ba ta, “Vern zai shagala da aiki a cikin gaskiya, kuma za ki ƙyale wasu ma su amfana daga wurinsa.” Sa’ad da muka yi aure shekaru 49 da suka wuce, mun ƙuduri aniya za mu yi tsufa tare, muna bauta wa Jehobah, kuma idan dukanmu muka tsira daga wannan zamanin, za mu sake zama matasa tare kuma mu ci gaba da bauta masa har abada. Hakika, mun “yawaita cikin aikin Ubangiji.” (1 Kor. 15:58) Jehobah ya kula da mu kuma ya tabbata cewa ba mu taɓa yin rashin komi mai kyau ba.
[Hasiya]
a Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Satumba, 1990, na Turanci, shafuffuka na 10-14 don labarin Jack Halliday Nathan.
[Hoton da ke shafi na 31]
“Makasudinmu a matsayin iyali shi ne mu sauƙaƙa rayuwarmu kuma mu ba da kanmu don hidimar Jehobah”