Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 11/15 pp. 12-16
  • Matasa, Me Za Ku Yi Da Rayuwarku?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Matasa, Me Za Ku Yi Da Rayuwarku?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Waɗanne Irin Maƙasudai Ne Za Ku Iya Kafawa?
  • Cim ma Maƙasudin Yin Baftisma
  • Yaya Za Ku Cim ma Maƙasudanku?
  • Yara da Matasa, Ku Kafa Makasudai a Bautarku
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Yadda Za Mu Iya Kafa da Kuma Cim ma Makasudai a Hidimarmu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Ka Ci Gaba da Karfafa Dangantakarka da Jehobah
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 11/15 pp. 12-16

Matasa, Me Za Ku Yi Da Rayuwarku?

“Haka ni ke yin dambe kuma, ba kamar mai-naushen sarari ba.”—1 COR. 9:26.

1, 2. Don ku yi nasara yayin da kuke girma ku zama manya, mene ne kuke bukatan ku samu?

A CE za ku wani wuri da ba ku sani ba. Amma kuna tare da wani wanda kuka amince da shi kuma wanda ya san wurin sosai. Shi ne zai yi muku ja-gora. Idan kun ƙi bin shawarar mutumin nan za ku iya ɓatawa. Idan kun bi umurninsa, ba za ku ɓata ba.

2 Kuna fuskantar irin wannan yanayin yayin da kuke girma ku zama manya. Kuna da abu mai kyau da zai yi muku ja-gora. Littafi Mai Tsarki ne zai taimaka muku ku san tafarkin da za ku zaɓa. (Mis. 3:5, 6) Idan kuka koyar da lamirinku sosai, zai iya zama abin taimako sosai wajen bin tafarki mai kyau. (Rom. 2:15) Zai iya zama abin da zai yi muku ja-gora. Amma, don ku yi nasara a rayuwa, kuna kuma bukatar ku san inda kuke nufa. Kuna bukatan ku kafa maƙasudai da za su yiwu.

3. Waɗanne amfanin kafa maƙasudai ne Bulus ya yi nuni ga a 1 Korintiyawa 9:26?

3 Manzo Bulus ya taƙaita amfanin kafa maƙasudai da kuma yin ƙoƙari a cim ma su sa’ad da ya rubuta: “Haka fa ni ke yin tsere, ba kamar da shakka ba; haka ni ke yin dambe kuma, ba kamar mai-naushen sarari ba.” (1 Kor. 9:26) Idan kuna da maƙasudai, za ku yi gudu da tabbaci. Ba da daɗewa ba za ku tsai da shawarwari masu muhimmanci game da bauta, aiki, aure da iyali, da kuma sauransu. A wani lokaci za ku ji kamar kuna fuskantar zaɓi masu yawa da suke rikitar da ku. Amma idan kun tsara tafarkinku tun da wuri, kuma kuka tsai da shawarwarinku bisa ga gaskiya da ƙa’idodi da ke cikin Kalmar Allah, ba za ku fuskanci gwajin bin mummunar tafarki ba.—2 Tim. 4:4, 5.

4, 5. (a) Mene ne zai iya faruwa idan ba ku kafa wa kanku maƙasudai ba? (b) Me ya sa ya kamata son faranta wa Allah rai ya yi wa zaɓinku ja-gora?

4 Idan ba ku kafa wa kanku maƙasudai ba, tsaranku da malamanku za su rinjaye ku ku yi abin da suke gani ya yi muku daidai. Hakika, ko da kun kafa ainihin maƙasudai, har ila wasu suna iya ba da ra’ayinsu. Sa’ad da kuke sauraron shawarwarinsu, ku tambayi kanku, ‘Shin maƙasudai da suka ambata za su taimaka mini na tuna Mahaliccina a lokacin ƙuruciyata ko kuma za su raba hankalina daga yin hakan?’—Karanta Mai-Wa’azi 12:1.

5 Me ya sa ya kamata son ku faranta wa Allah rai ya ja-goranci zaɓin ku a rayuwa? Dalili ɗaya shi ne cewa Jehobah ne ya ba mu kowane abu mai kyau da muke da shi. (Yaƙ. 1:17) Hakika, ya kamata kowa ya nuna godiya ga Jehobah. (R. Yoh. 4:11) Ba hanyar da ta fi kyau da za ku nuna godiyarku ga Jehobah fiye da tuna da shi sa’ad da kuke kafa maƙasudai. Bari mu yi la’akari da maƙasudai da sun cancanci cim ma wa da kuma abin da dole ne ku yi don ku cim ma su.

Waɗanne Irin Maƙasudai Ne Za Ku Iya Kafawa?

6. Wane maƙasudi mai muhimmanci ne za ku iya kafawa, kuma me ya sa?

6 Kamar yadda aka ambata a talifin da ya gabata, maƙasudi na musamman da za ku iya kafawa shi ne ku tabbatar wa kanku cewa abin da aka faɗa cikin Littafi Mai Tsarki gaskiya ne. (Rom. 12:2; 2 Kor. 13:5) Tsaranku suna iya yin imani da ra’ayin bayyanau ko kuma koyarwar addinan ƙarya dabam dabam domin wasu sun gaya musu cewa abin da ya kamata su yi imani da shi ke nan. Amma, bai kamata ku gaskata da abu domin kawai wasu suna son ku gaskata hakan ba. Ku tuna, Jehobah yana son ku bauta masa da dukan zuciyarku. (Karanta Matta 22:36, 37.) Ubanmu na samaniya yana son ku kafa bangaskiyarku a kan tabbaci.—Ibran. 11:1.

7, 8. (a) Kafa waɗanne maƙasudai na ɗan lokaci ne zai taimaka muku ku ƙarfafa bangaskiyarku? (b) Mene ne za ku shaida yayin da kuka cim ma wasu cikin maƙasudanku na ɗan lokaci?

7 Don ku ƙarfafa bangaskiyarku, ku kafa maƙasudai da za ku iya cim ma wa a cikin ɗan lokaci. Ɗaya cikin maƙasudan zai iya zama yin addu’a kullum. Don addu’o’inku su kasance takamammu kuma wanda ba ku cika maimaitawa, kuna iya tuna ko kuma rubuta takamammun abubuwa da suka faru a ranar da kuke son ku haɗa a cikin addu’o’inku. Ku tabbata cewa kun ambata abubuwa da kuka ji daɗinsu a ranar ba kawai ƙalubale da kuka fuskanta ba. (Filib. 4:6) Wani maƙasudi kuma shi ne karanta Littafi Mai Tsarki a kowace rana. Shin kun san cewa idan kuka karanta aƙalla shafuffuka huɗu a kowace rana, za ku karance dukan Littafi Mai Tsarki a cikin shekara guda kawai?a Zabura 1:1, 2 ta ce: “Mai-albarka ne mutum wanda . . . marmarinsa cikin shari’a ta Ubangiji ya ke; kuma a cikin shari’arsa ya kan riƙa tunani dare da rana.”

8 Maƙasudi na uku da za ku iya cim ma wa a cikin ɗan lokaci shi ne shirya yin kalami a kowane taron ikilisiya. Da farko, za ku iya so ku karanta kalamin ko kuma wani nassi. Daga baya, kuna iya kafa maƙasudin yin kalami a naku kalmomi. Hakika, kowane lokaci da kuka yi kalami, kuna miƙa kyauta ga Jehobah. (Ibran. 13:15) Muddin kun cim ma wasu cikin waɗannan maƙasudai, za ku ƙara kasancewa da tabbaci, za ku daɗa nuna godiya ga Jehobah, kuma za ku kasance a shirye ku kafa maƙasudai na dogon lokaci.

9. Idan ba ku zama masu shelar Mulki tukuna ba, waɗanne maƙasudai na dogon lokaci ne za ku iya kafa wa kanku?

9 Waɗanne maƙasudai na dogon lokaci ne za ku iya kafa wa kanku? Idan ba ku soma shelarta bishara ga jama’a ba tukun, maƙasudinku na dogon lokaci shi ne ku zama masu shelar Mulki. Muddin kun cim ma wannan maƙasudi mai ɗaukaka, za ku so ku riƙa fita hidima a kai a kai kuma ku ƙware wajen yin hakan, kada ku ƙyale kowane wata ya wuce ba ku fita hidima ba. Za ku kuma so ku koya yin amfani da Littafi Mai Tsarki a hidima. Yayin da kuke haka, wataƙila za ku gano cewa za ku fi jin daɗin aikin. Za ku ƙara lokacin da kuke yi a hidimar gida gida ko kuma ku yi ƙoƙari ku gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki. A matsayin masu shela da ba su yi baftisma ba, maƙasudi ne mai muhimmanci ku cancanci yin baftisma kuma ku zama Shaidun Jehobah Allah da suka keɓe kansu kuma suka yi baftisma.

10, 11. Waɗanne maƙasudai na dogon lokaci ne matasa da suka yi baftisma za su iya kafa wa kansu?

10 Idan ku bayin Jehobah ne da suka riga suka yi baftisma, ga wasu maƙasudai na dogon lokaci da za ku kafa wa kanku. A lokaci lokaci, za ku so ku taimaka wa ikilisiyoyi su yi wa’azi a yankin da ba a yawan wa’azi a ciki. Kuna iya zaɓa ku yi amfani da ƙarfinku da lafiyarku ku yi aikin majagaba na ɗan lokaci ko na kullum. Dubban majagaba masu farin ciki za su gaya maka cewa hidima ta cikakken lokaci hanya ce mai ban albarka na tuna da Mahaliccinku a lokacin ƙuruciyarku. Za ku cim ma waɗannan maƙasudai sa’ad da kuke gida. Ikilisiyarku za ta kuma amfana idan kuka cim ma su.

11 Wasu maƙasudai na dogon lokaci za su sa ikilisiyar da ke wani gari ma su amfana. Alal misali, kuna iya shirin yin hidima a wani wuri ko ƙasa inda ake da bukata mai girma. Kuna iya taimaka wajen gina Majami’un Mulki ko rassa a wasu ƙasashe. Kuna iya soma hidima a Bethel ko kuma zama masu wa’azi a ƙasashen waje. Hakika, maƙasudi na farko mai muhimmanci da aka ambata a nan da za ku bukaci ku cim ma kafin ku cim ma yawancin maƙasudai na dogon lokaci shi ne yin baftisma. Idan ba ku yi baftisma ba tukuna, ku yi la’akari da abin da cim ma wannan abu mai muhimmanci a rayuwarku ya ƙunsa.

Cim ma Maƙasudin Yin Baftisma

12. Don waɗanne dalilai ne wasu suke yin baftisma, kuma me ya sa waɗannan ba isassun dalilan yin baftisma ba ne?

12 Yaya za ka kwatanta manufar yin baftisma? Wasu za su iya ganin cewa don ya kāre su daga yin zunubi ne. Wasu za su so yin baftisma don tsaransu sun yi baftisma. Wasu matasa mai yiwuwa sukan yi hakan ne don su faranta wa iyayensu rai. Amma, baftisma ba yarjejeniya da ke hana ku yin abubuwa da za ku so ku yi a ɓoye ba ne; kuma bai dace ku yi baftisma don matsi daga mutane ba. Za ku yi baftisma ne sa’ad da kuka fahimci abin da ya ƙunsa mutum ya zama Mashaidin Jehobah da kuma lokacin da kun tabbata cewa kuna shirye ku ɗauki wannan hakkin.—M. Wa. 5:4, 5.

13. Me ya sa za ku yi baftisma?

13 Dalili ɗaya da zai sa mutum ya yi baftisma shi ne cewa Yesu ya umurci mabiyansa su yi ‘almajirai . . . , suna yi musu baftisma.’ Ya kuma kafa misali ta wurin yin baftisma. (Karanta Matta 28:19, 20; Markus 1:9.) Ƙari ga haka, yin baftisma mataki ne mai muhimmanci ga waɗanda suke so su tsira. Bayan ya ambata cewa Nuhu ya gina jirgi da shi da iyalinsa suka tsira a lokacin Rigyawa, manzo Bitrus ya ce: “Daidai kuwa, bisa ga wannan misali, baftisma ke cetonku yanzu,. . . ta wurin tashin Yesu Kristi.” (1 Bit. 3:20, 21) Wannan ba ya nufin cewa kuna yin baftisma ainihi don samun kāriya ba ne. Maimako, kuna yin baftisma ne don kuna ƙaunar Jehobah kuma kuna son ku bauta masa da dukan zuciyarku da dukan ranku da dukan azancinku da dukan ƙarfinku.”—Mar. 12:29, 30.

14. Me ya sa wasu za su yi jinkirin yin baftisma, wane tabbaci kuke da shi?

14 Wasu za su iya yin jinkirin yin baftisma don tsoron cewa mai yiwuwa za a yi musu yankan zumunci a nan gaba. Kuna jin irin wannan tsoron ne? Idan haka ne, jin irin wannan tsoron yakan kasance da amfani. Zai iya nuna kun fahimci hakki mai muhimmanci na zama Mashaidin Jehobah. Da akwai wani dalili kuma? Wataƙila har yanzu ba ku amince ba cewa mizanan Allah shi ne hanyar rayuwa da ta fi kyau. A wannan yanayin, yin tunani game da sakamakon da waɗanda suka ƙi mizanan Littafi Mai Tsarki suke fuskanta zai sa ku tsai da shawara. A wani ɓangare kuma, zai zama kuna ƙaunar mizanan Allah amma ba ku amince da kanku ba cewa za ku iya rayuwa da ta jitu da su. Hakika, wannan zai iya zama alama mai kyau, don ya nuna ku masu tawali’u ne. Ballantana ma, Littafi Mai Tsarki ya ce dukan zukatan ’yan Adam ajizai sun fi komi rikici. (Irm. 17:9) Amma za ku iya yin nasara idan kun ci gaba da ‘tsare kanku bisa ga maganar Allah.’ (Karanta Zabura 119:9.) Ko da waɗanne dalilai kuke da su na jinkirin yin baftisma, kuna bukatan ku magance irin waɗannan batutuwa da kuma matsaloli.b

15, 16. Yaya za ku san kuna shirye don yin baftisma?

15 Amma, yaya za ku san ko kuna shirye don baftisma? Hanya ɗaya ita ce ku yi wa kanku irin waɗannan tambayoyi: ‘Zan iya bayyana wasu muhimman koyarwar Littafi Mai Tsarki ga wasu? Ina saka hannu a hidima ko da iyayena ba su yi hakan ba? Ina ƙoƙari na halarci dukan taron Kirista? Zan iya tuna takamammu misalai da na ƙi matsi na tsara? Zan ci gaba da bauta wa Jehobah ko idan iyayena da abokaina sun daina yin hakan? Na yi addu’a game da dangantakata da Allah kuwa? Na keɓe kaina gabaki ɗaya ga Jehobah cikin addu’a?’

16 Baftisma mataki ne da ke canja rayuwa, kuma abu ne da bai kamata a yi wasa da shi ba. Kun manyanta da za ku yi tunanin ɗaukan wannan matakin? Mutum ya manyanta ba ya nufin ba da jawabai masu kyau daga kan dakalin yin magana ko kuma ba da kalamai masu burgewa a lokacin taro. Yana bukatan iya tsai da shawarwari bisa fahimtar ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. (Karanta Ibraniyawa 5:14.) Idan kun kai lokacin da za ku yi hakan a rayuwa, kuna da gata mafi muhimmanci a gabanku, wato, bauta wa Jehobah da dukan zuciyarku da kuma yin rayuwa da ta nuna cewa kun keɓe kanku da gaske a gare shi.

17. Mene ne zai taimaka muku ku jure da gwaje-gwaje da wataƙila za su taso bayan kun yi baftisma?

17 Nan da nan bayan baftisma, za ku kasance da ƙwazo sosai na bauta wa Allah. Amma, ba da daɗewa ba, za ku fuskanci gwaje-gwaje da za su gwada bangaskiyarku da ƙarfinku. (2 Tim. 3:12) Kada ku ji cewa ku kaɗai ne za ku bi da waɗannan gwaje-gwajen. Ku nemi shawarar iyayenku. Ku nemi taimako daga wurin waɗanda suka manyanta a cikin ikilisiya. Ku ci gaba da abuta da waɗanda za su tallafa muku. Kada ku mance cewa Jehobah yana kula da ku, kuma zai ba ku ƙarfin da kuke bukata don ku fuskanci kowane yanayi da zai iya tasowa.—1 Bit. 5:6, 7.

Yaya Za Ku Cim ma Maƙasudanku?

18, 19. Yaya za ku amfana daga bincika abubuwa da suka fi muhimmanci a rayuwarku?

18 Duk da ƙoƙarinku, yana nufi ne cewa ba ku da isashen lokaci ku yi abin da kuke so da abin da kuke bukatan ku yi? Idan haka ne, ya kamata ku bincika abin da suka fi muhimmanci a rayuwarku. Don a ƙwatanta: Ku ɗauki bokitin roba kuma ku saka manyan duwatsu da yawa a cikinsa. Sa’anan ku cika bokitin da yashi. Kuna da bokiti cike da duwatsu da yashi. Ku juye yashin da duwatsun a ƙasa amma ku ajiye wannan yashin da duwatsun. Yanzu kuma, ku fara cika bokitin da yashin, sa’annan ku yi ƙoƙarin saka duwatsun cikin bokitin. Babu wurin da duwatsun za su shiga! Dalilin kuwa shi ne kun zuba yashin a cikin bokitin da farko.

19 Kuna fuskantar irin wannan ƙalubale a lokacin da kuke sarrafa lokacinku. Idan kun saka abubuwa kamar su nishaɗi a wuri na farko, ba za ku taɓa samun lokaci a rayuwarku don manyan abubuwa ba, wato, ayyuka na ruhaniya. Amma idan kuka bi gargaɗin Littafi Mai Tsarki na “ku gwada mafifitan al’amura” za ku ga cewa kuna da lokacin bauta wa Allah da kuma na yin nishaɗi.—Filib. 1:10.

20. Idan kuna fuskantar ɗawainiya da shakka lokacin da kuke ƙoƙarin cim ma maƙasudanku, mene ne za ku iya yi?

20 Sa’ad da kuke ƙoƙarin cim ma maƙasudanku, da ya haɗa da yin baftisma, za ku iya jin ɗawainiya da kuma shakka a wasu lokatai. Yayin da kuka ji hakan, ‘ku zuba nawayarka bisa Ubangiji, shi kuma za ya taimake ku.’ (Zab. 55:22) A yanzu kuna da zarafin yin aiki da ta fi al’ajabi da kuma muhimmanci a tarihin ’yan Adam, wato, wa’azi da kuma koyarwa a dukan duniya. (A. M. 1:8) Za ku iya zaɓa ƙin saka hannu cikin yin wannan aikin. Ko kuma ku zaɓa ku saka hannu sosai a yin wannan aiki da ta fi al’ajabi. Kada ku ja baya daga yin amfani da baiwarku don faɗaɗa ayyukan Mulkin. Ba za ku taɓa yin da na sani ba don bauta wa ‘Mahaliccinku kuma a cikin kwanakin ƙuruciyarku.’—M. Wa. 12:1.

[Hasiya]

a Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Agusta, 2009, na Turanci, shafuffuka na 15-18.

b Don samun taimako a wannan batun, ka duba littafin nan Questions Young People Ask—Answers That Work, Littafi na biyu, babi na 34.

Yaya Za Ka Amsa?

• Me ya sa za ku kafa maƙasudai?

• Waɗanne maƙasudai ne cim ma su ƙwalliya ce da ke biyan kuɗin sabulu?

• Mene ne cim ma maƙasudin yin baftisma ta ƙunsa?

• Ta yaya bincika abubuwa da suka fi muhimmanci a rayuwarku za su taimaka muku wajen cim ma maƙasudanku?

[Hoton da ke shafi na 13]

Kuna da maƙasudin karanta Littafi Mai tsarki kowace rana kuwa?

[Hoton da ke shafi na 15]

Mene ne zai taimake ka ka cim ma maƙasudinka na yin baftisma?

[Hoton da ke shafi na 16]

Wane darassi kuka koya daga wannan kwatancin?

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba