Sun Samu Almasihu!
“Mun sami Almasihu.”—YOH. 1:41.
1. Mene ne ya sa Andarawas ya ce: “Mun sami Almasihu”?
YOHANNA MAI BAFTISMA yana tsaye da almajiransa biyu. Yayin da Yesu yake zuwa kusa da su, Yohanna ya ce: “Duba, ga Ɗan rago na Allah!” Nan da nan, Andarawas da Yohanna, almajiran Yohanna mai Baftisma suka bi Yesu kuma suka kasance tare da shi a ranar. Daga baya, Andarawas ya tafi ya nemi ɗan’uwansa, Siman Bitrus, kuma ya yi wannan sanarwa: “Mun sami Almasihu.” Andarawas ya nuna wa Bitrus Yesu.—Yoh. 1:35-41.
2. Ta yaya yin nazarin annabce-annabce game da Almasihu zai taimaka mana?
2 Da shigewar lokaci, Andarawas da Bitrus da wasu za su yi nazarin Nassosi sosai kuma za su faɗa ba tare da yin shakka ba cewa Yesu ne Almasihu da aka yi alkawarinsa. Tattaunawa na annabce-annabce game da Almasihu da za mu yi yanzu zai taimaka mana mu kasance da bangaskiya mai ƙarfi ga Littafi Mai Tsarki da kuma Almasihu.
“Ga Sarkinki Yana Zuwa”
3. Waɗanne annabce-annabce ne suka cika sa’ad da Yesu ya shiga Urushalima a matsayin sarki?
3 Almasihu zai shiga Urushalima a matsayin sarki. Annabcin Zakariya ya ce: “Ki yi murna sarai, ya ɗiyar Sihiyona; ki yi sowa, ya ɗiyar Urushalima; ga sarkinki, yana zuwa wurinki; mai-adalci ne shi, mai-nasara ne kuwa; mai-tawali’u, haye a kan jaki, a kan aholakin jaki.” (Zak. 9:9) Wani marubucin zabura ya ce: “Mai-albarka ne shi mai-zuwa cikin sunan Ubangiji.” (Zab. 118:26) Taro mai girma sun yi ihu da farin ciki matuƙa yayin da Yesu ya shiga Urushalima. Yesu bai gaya musu abin da za su yi ba. Amma sun yi ainihin yadda annabcin ya faɗa. Sa’ad da kake karanta labarin, ka yi tunani kana wajen kuma cewa kana jin muryoyin taron.—Karanta Matta 21:4-9.
4. Ta yaya Zabura 118:22, 23 suka cika?
4 Yesu yana da tamani ga Allah, ko da yake mutane da yawa ba su amince da shi a matsayin Almasihu ba. Kamar yadda aka annabta, mutane da yawa marasa imani sun tsane Yesu kuma sun yi tunani cewa shi marar amfani ne. (Isha. 53:3; Mar. 9:12) Amma Littafi Mai Tsarki ya ce: “Dutse wanda magina suka waƙala shi ne ya zama kan ƙusurwa. Wannan aikin Ubangiji ne.” (Zab. 118:22, 23) Yesu ya yi magana game da wannan annabcin sa’ad da yake magana ga ’yan addini da suka tsane shi, kuma Bitrus ya ce wannan annabcin game da Yesu ne da ikilisiya. (Mar. 12:10, 11; A. M. 4:8-11) Yesu ne ya zama “dutse magabaci na ƙusurwa” na ikilisiyar Kirista. Ko da miyagun mutane sun ƙi shi, amma “zaɓaɓe ne mai-daraja wurin Allah.”—1 Bit. 2:4-6.
An Ci Amanarsa kuma An Yasar da Shi
5, 6. Mene ne aka annabta kuma ya cika game da cin amanar Almasihu?
5 Wani da ake gani abokin Almasihu ne zai ci amanarsa. Dauda ya annabta: “Aminina, wanda na yarda da shi, wanda mu kan ci tare da shi, ya tayar mani da duddugensa.” (Zab. 41:9) A zamanin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, cin abinci tare yana nuna abokantaka. (Far. 31:54) Saboda haka, cin amanar Yesu da Yahuda Iskariyoti ya yi ne ya fi tsanani. Yesu ya yi magana a kan yadda annabcin Dauda ya cika sa’ad da ya gaya wa manzanninsa game da wanda ya ci amanarsa: “Ba zancen ku duka na ke yi ba: na san waɗanda na zaɓa; amma domin nassin ya cika, wanda ya ci gurasata ya tayar mini da duddugensa.”—Yoh. 13:18.
6 Wanda ya ci amanar Almasihu zai karɓi azurfa talatin, farashin da ake biya a kan bawa! Matta ya faɗa cewa Yahuda Iskariyoti ya ci amanar Yesu don azurfa talatin kuma wannan cikawar annabcin Zakariya 11:12, 13 ne. Amma Matta ya ce abin da aka faɗa ta ‘bakin annabi Irmiya’ ya cika. A zamanin Matta, wataƙila an fara saka littafin Irmiya cikin jerin littattafan Littafi Mai Tsarki da ya haɗa da littafin Zakariya. (Gwada Luka 24:44.) Yahuda bai kashe wannan azurfa talatin ba, domin ya jefar da kuɗin a cikin haikali “ya tafi kuma ya shaƙe kansa.”—Mat. 26:14-16; 27:3-10.
7. Ta yaya Zakariya 13:7 ya cika?
7 Almajiran Almasihu za su yashe shi. Zakariya ya rubuta: “Ka bugi makiyayi, tumaki kuwa za su watse.” (Zak. 13:7) A ranar 14 ga Nisan na shekara ta 33 A.Z., Yesu ya gaya wa almajiransa: “A cikin daren nan dukanku za ku yi tuntuɓe saboda ni: gama an rubuta, Zan buga makiyayi, tumakin garke kuma za su watse.” Kuma hakan ne ya faru. Matta ya ce “dukan almajiran suka bar [Yesu] suka gudu.”—Mat. 26:31, 56.
Wasu Za Su Zarge kuma Su Doke Shi
8. Ta yaya Ishaya 53:8 ya cika?
8 Mutane za su kai Almasihu kotu kuma su kashe shi. (Karanta Ishaya 53:8.) A safiyar ranar 14 ga Nisan, dukan waɗanda suke Kotun Majalisa sun yi taro. Sun ɗaure Yesu da igiya kuma suka kai shi wurin Bilatus Ba-Bunti, Gwamnan Roma. Bilatus ya tuhumi Yesu kuma ya ce Yesu bai yi laifi ba. Amma sa’ad da Bilatus ya tambayi jama’ar ko suna son ya ’yantar da Yesu, jama’ar suka yi ihu: [“A rataye shi!” NW]. Suka ce suna son Bilatus ya ’yantar da Barabbas, wani mai-aikata laifi maimakon Yesu. Domin Bilatus yana son ya faranta wa taron rai, sai ya ’yantar da Barabbas. Sai ya ba mutanensa umurni su yi wa Yesu bulala kuma su rataye shi a kan gungume.—Mar. 15:1-15.
9. Mene ne ya faru a zamanin Yesu kamar yadda aka annabta a Zabura 35:11?
9 Masu shaidan zur sun ba da shaida game da Almasihu. Dauda ya rubuta: “Masu-shaidan ƙarya sun tashi, suna yi mani tambaya a kan abin da ban sani ba.” (Zab. 35:11) Kuma daidai yadda annabcin ya faɗa, “Manyan malamai kuwa da dukan fadanci suna ta neman shaidun zur a kan Yesu, domin su kashe shi.” (Mat. 26:59) Littafi Mai Tsarki, ya faɗa cewa mutane suna ba da shaidar zur game da shi, amma shaidarsu ba ta jitu ba. (Mar. 14:56) Maƙiyan Yesu ba su yi tunani ba cewa shaidun suna ƙaryace-ƙaryace game da shi. Suna son Yesu dai ya mutu.
10. Ta yaya Ishaya 53:7 ya cika?
10 Almasihu ba zai amsa wa waɗanda suke zarginsa ba. Ishaya ya annabta: “Aka wulakance shi, duk da haka ya yi tawali’u, ba ya buɗe bakinsa ba; kamar ɗan rago da a ke kai wurin yanka, kamar yadda tunkiya wurin masu-sosayanta tana shuru; hakanan ba ya buɗe bakinsa ba.” (Isha. 53:7) Sa’ad da “manyan malamai kuma da datiɓai suka yi ta sarassa [Yesu], ba ya amsa da kome ba.” Bilatus ya yi tambaya: “Ba ka ji suna shaida abubuwa dayawa a kanka ba?” Amma, Yesu “ko da magana ɗaya ba ya amsa masa ba: har mai-mulkin ya yi mamaki ƙwarai.” (Mat. 27:12-14) Yesu bai zagi maƙiyansa ba.—Rom. 12:17-21; 1 Bit. 2:23.
11. Ta yaya Ishaya 50:6 da Mikah 5:1 suka cika?
11 Ishaya ya annabta cewa za a doke Almasihu. Ishaya ya rubuta: “Na bada bayana ga masu-bugu, kumatuna kuma na bayas ga masu-tuge gashi: ban ɓoye fuskata daga kunya da zubda miyau ba.” (Isha. 50:6) Mikah ya annabta: “Za a bubbuga alƙalin Isra’ila da sanda a kumatu.” (Mi. 5:1) Don ya tabbatar da wannan annabce-annabcen, Markus ya ce: “Waɗansu fa suka fara tofa masa [Yesu] miyau, suka rufe fuskatasa, suka mammare shi, suna ce masa, ka yi annabci: dogarai kuma suka karɓe shi da dūka.” Markus ya ce sojoji za su bugi kansa da gora kuma su tofa masa miyau, su kuma durƙusa suna masa sujada. (Mar. 14:65; 15:19) Hakika, mutanen ba su da dalilin su bi da Yesu hakan ba.
Ya Kasance da Aminci ga Allah Har Mutuwa
12. Ta yaya Zabura 22:16 da Ishaya 53:12 suka cika?
12 Almasihu zai mutu a kan gungume. Dauda ya ce: “Jama’ar masu-mugunta sun sa ni tsaka; suka sossoke hannuwana da ƙafafuna.” (Zab. 22:16) Kamar yadda masu karatun Littafi Mai Tsarki suka sani da kuma yadda Markus ya gaya mana a cikin Linjilarsa, wannan annabcin ya cika. Markus ya rubuta cewa a misalin ƙarfe tara na safe suka rataye Yesu. Suka kafa ƙusa a hannayensa da ƙafafunsa a kan gungume. (Mar. 15:25) Wani annabci ya ce Almasihu zai mutu da masu zunubi. Ishaya ya rubuta: “Ya tsiyaye ransa har ga mutuwa, aka lissafta shi wurin masu-laifi.” (Isha. 53:12) Hakan ya cika sa’ad da “tare da shi an [rataye] mafasa guda biyu, ɗaya ga hannun dama, ɗaya ga na hagu.”—Mat. 27:38.
13. Ta yaya Zabura 22:7, 8 ta cika?
13 Dauda ya annabta cewa mutane za su zagi Almasihu. (Karanta Zabura 22:7, 8.) Mutane sun zagi Yesu sa’ad da yake shan wahala a kan gungumen. Matta ya gaya mana: “Waɗanda su ke wucewa suka yi masa baƙar magana kuma, suna kaɗa kansu, suna cewa, Kai mai-rushe wuri mai-tsarki mai-gina shi kuma cikin kwana uku, ceci kanka: idan kai Ɗan Allah ne ka sauko daga [gungume].” Manyan firistoci da marubuta da dattawa suka yi masa ba’a suka ce: “Ya ceci waɗansu, ya kasa ceton kansa. Sarkin Isra’ila ne shi; shi sauko yanzu daga [gungumen], mu kuwa mu a ba da gaskiya gareshi. Yana dogara ga Allah; bari ya cece shi yanzu, idan yana sonsa: gama ya ce, Ni Ɗan Allah ne.” (Mat. 27:39-43) Yesu ya sha wahala amma ya natsu kuma bai faɗa kome da ba daidai ba. Shi misali ne mai kyau a gare mu!
14, 15. Ta yaya annabce-annabce game da tufafin Almasihu da kuma ba shi ruwan tsami suka cika?
14 Za su jefa ƙuri’a don su rarraba tufafin Almasihu. Dauda ya rubuta: “Suna rarraba tufafina a tsakaninsu, a bisa rigata kuma suna jefa ƙuri’a.” (Zab. 22:18) Hakan ya faru domin Littafi Mai Tsarki ya faɗa cewa bayan sojojin Roma suka rataye Yesu a kan gungume, suka rarraba tufafinsa ta wajen jefa ƙuri’a.—Mat. 27:35; karanta Yohanna 19:23, 24.
15 Za su ba Almasihu ruwa matsarmama da mai tsami ya sha. Annabcin ya ce: “Suka ba ni matsarmama domin abincina; cikin ƙishina kuma suka ba ni ruwa mai-tsami in sha.” (Zab. 69:21) Matta ya gaya mana: “Suka ba shi [Yesu] ruwan anab garwaye da ruwan matsarmama, domin shi sha: amma sa’anda ya ɗanɗana, ya ƙi sha. Daga baya, wani daga cikinsu ya gudu, ya ɗauki soso, ya cika shi da ruwan tsami, ya sa shi a kan gora, ya ba shi domin ya sha.”—Mat. 27:34, 48.
16. Ta yaya Zabura 22:1 ta cika?
16 Zai kasance kamar Allah ya yatsar da Almasihu. (Karanta Zabura 22:1.) Markus ya gaya mana cewa a sa’a ta tara, wato, wajen ƙarfe uku na rana, Yesu ya kira da babbar murya: “Eloi, Eloi, lama sabachtani? watau, Ya Allahna, Ya Allahna, don me ka yashe ni?” (Mar. 15:34) Yesu bai rasa imani ga Ubansa na samaniya ba. Allah ya yashe Yesu kuma ya ƙyale maƙiyansa su gwada amincinsa. Kuma Yesu ya cika Zabura 22:1 sa’ad da ya yi kuka da babbar murya.
17. Ta yaya Zakariya 12:10 da Zabura 34:20 suka cika?
17 Maƙiya za su soke Almasihu, amma ba za su karye ƙashinsa ba. Mazaunan Urushalima za su “duba wanda suka soka.” (Zak. 12:10) Kuma Zabura 34:20 ta ce: “[Allah] yana kiyaye dukan ƙasusuwansa, ko ɗaya cikin ba ya karye ba.” Don ya tabbatar da wannan kalaman, manzo Yohanna ya rubuta: “Wani a cikin ’yan yaƙi ya soke shi [Yesu] da mashi wurin haƙarƙari; nan da nan jini da ruwa suka fito. Shi [Yohanna] wanda ya gani kuma ya bada shaida, shaidatasa gaskiya ce kuwa . . . Gama waɗannan abu suka faru domin nassin ya cika, Ba za a karye ƙashinsa ba.” Kuma wani nassi ya ce, “Za su duba shi wanda suka sūka.”—Yoh. 19:33-37.
18. Ta yaya aka binne Yesu tare da mawadata?
18 Za a binne Almasihu tsakanin kaburburan mawadata. (Karanta Ishaya 53:5, 8, 9.) Da maraice a ranar 14 ga Nisan, “wani mai-arziki ya zo daga Arimathiya sunansa Yusufu,” ya tambayi Bilatus ko zai iya ɗaukan jikin Yesu, kuma ya amince da hakan. Littafin Matta ya daɗa: “Yusufu kuwa ya ɗauki jikin, ya naɗe shi a cikin likafani mai-tsabta, ya ajiye shi cikin nasa sabon kabari, wanda ya rigaya ya sassaƙa daga cikin dutse: ya gangaro da wani babban dutse har ƙofar kabari, sai ya tafi.”—Mat. 27:57-60.
Ka Yabi Almasihu, Sarkinmu!
19. Ta yaya annabci da ke Zabura 16:10 ya cika?
19 Jehobah zai ta da Almasihu daga matattu. Dauda ya rubuta: “Ba za ka [Jehobah] bar raina ga Lahira ba,” wato, kabari. (Zab. 16:10) Ka yi tunanin irin mamakin da matan da suka zo kabarin suka yi sa’ad da suka ga wani mala’ika yana zaune cikin kabarin da aka binne Yesu. Mala’ikan ya gaya wa matan: “Kada ku yi mamaki; kuna neman Yesu, Ba-nazarat, wanda aka [rataye] shi; ya tashi: ba shi nan; ku duba, ga wurin da aka sa shi!” (Mar. 16:6) Bayan hakan, a ranar Fentakos na shekara ta 33 A.Z., manzo Bitrus ya yi magana ga rukunin mutane a Urushalima game da annabcin Dauda a Zabura 16. Ya ce game da Dauda: “[Dauda] ya rigaya ya ga wannan, zancen tashin Kristi ya yi da ya ce ba a bar shi cikin Lahira ba, Jikinsa kuma ba ya ga ruɓa ba.” (A. M. 2:29-31) Allah bai bar jikin Ɗansa ƙaunatacce ya ruɓe ba. Jehobah ya ƙara yin wani abin ban mamaki. Ya ta da Yesu daga matattu kuma ya komar da shi sama!—1 Bit. 3:18.
20. Mene ne annabce-annabce suka faɗa game da sarautar Almasihu?
20 Allah zai sanar cewa Yesu Ɗansa ne. (Karanta Zabura 2:7; Matta 3:17.) Sa’ad da Yesu ya shiga Urushalima, taron jama’a sun yabe shi da kuma Mulkinsa. A yau ma, muna yabon Yesu. Muna farin cikin gaya wa mutane game da shi da kuma Mulkinsa. (Mar. 11:7-10) Ba da daɗewa ba, Kristi zai halaka maƙiyansa sa’ad da ya ‘hau ya yi tafiya da albarka, domin gudunmuwar gaskiya da tawali’u da adalci.’ (Zab. 2:8, 9; 45:1-6) Sarautarsa za ta sa salama da ni’ma ta kasance a duniya baki ɗaya. (Zab. 72:1, 3, 12, 16; Isha. 9:6, 7) Yesu Kristi, ƙaunataccen Ɗan Jehobah, ya riga ya soma sarauta a matsayin Sarki a sama. Ɗaukaka ce mai girma mu zama Shaidun Jehobah kuma mu gaya wa mutane game da wannan gaskiyar!
Yaya Za Ka Amsa?
• Ta yaya aka ci amanar Yesu kuma aka yashe shi?
• Ta yaya annabce-annabce game da mutuwar Yesu suka cika?
• Me ya sa ka kasance da tabbaci cewa Yesu ne Almasihu?
[Hoto a shafi na 13]
Yadda Yesu ya shiga Urushalima a matsayin sarki ya cika waɗanne annabce-annabce?
[Hotona a shafi na 15]
Yesu ya rasu domin zunubanmu, amma yanzu shi Sarki Almasihu ne