Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 8/15 pp. 23-27
  • Jehobah Ne “Allah Mai Ba Da Salama”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Ne “Allah Mai Ba Da Salama”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Misali Mafi Kyau da Za a Bi
  • Ka Koya Daga Misalin Ibrahim da Ishaƙu
  • Ka Koya Darasi Daga Misalin Yusufu
  • Misalai “Domin Koyarwarmu”
  • Tagwaye Da Suka Bambanta
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Yakubu da Isuwa Sun Shirya
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Allah Ya Albarkaci Ibrahim da Iyalinsa
    Littafi Mai Tsarki​—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa?
  • Yakubu Ya Sami Gādo
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 8/15 pp. 23-27

Jehobah Ne “Allah Mai Ba Da Salama”

“Allah mai ba da salama ya kasance tare da ku duka.”​—ROM. 15:33, Littafi Mai Tsarki.

1, 2. Wane yanayi ne aka bayyana a littafin Farawa surori 32 da 33, kuma da wane sakamako?

KA YI tunani a kan wannan labarin: ’Yan’uwa biyu maza sun kusan haɗuwa. Za su haɗu kusa da Penuel, kusa da kwarin Jabbok a gabashin Kogin Urdun. ’Yan’uwan nan Isuwa da Yakubu ne, kuma ba su ga juna da daɗewa ba. Shekaru ashirin da suka shige, Isuwa ya sayar da hakkinsa na ɗan fari ga ɗan’uwansa, Yakubu. Sa’ad da Isuwa ya ji cewa Yakubu yana dawowa gida, sai ya tafi da mazaje 400 don ya haɗu da shi. Sa’ad da Yakubu ya ji wannan, sai tsoro ya kama shi. Yana ganin cewa har ila ɗan’uwansa yana fushi da shi kuma zai so ya kashe shi. Saboda haka, Yakubu ya aika bayinsa su kai wa Isuwa kyautar dabbobi. A kowane lokaci da bayin suka kai masa ƙarin dabbobi, suna gaya wa Isuwa cewa kyauta ce daga ɗan’uwansa. Yakubu ya aika masa fiye dabbobi 550.

2 Mene ne ya faru sa’ad da suka haɗu? Yakubu ya nuna ƙarfin zuciya da tawali’u. Ya taka zuwa wurin Isuwa kuma ya rusuna a gaban ɗan’uwansa sau bakwai! Amma kafin wannan, Yakubu ya riga ya yi abu mafi muhimmanci. Ya yi addu’a ga Jehobah kuma ya gaya masa ya kāre shi daga hannun Isuwa. Jehobah ya amsa addu’arsa. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Isuwa ya sheƙo a guje kuma ya rungume shi, ya faɗa a wuyansa ya yi masa sumba.—Far. 32:11-20; 33:1-4.

3. Mene ne muka koya daga abin da ya faru tsakanin Yakubu da Isuwa?

3 Wannan yanayin ya nuna cewa ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu don sasanta matsaloli da ’yan’uwanmu a cikin ikilisiya. Idan ba mu yi hakan ba, salama da kuma haɗin kai na ikilisiyar za ta lalace. Yakubu bai yi wani laifi ba. Ba ya bukatar ya gaya wa Isuwa ya yi haƙuri. Isuwa ne bai ga muhimmancin hakkinsa na ɗan fari ba kuma ya sayar wa Yakubu don jar miya. Amma Yakubu ya yi iya ƙoƙarinsa don su sasanta. (Far. 25:31-34; Ibran. 12:16) Misalin Yakubu ya nuna cewa ya kamata mu yi ƙoƙari sosai don mu kasance da salama da ’yan’uwanmu. Ya kuma nuna cewa sa’ad da muka roƙi Jehobah ya taimake mu mu yi hakan, yana amsa addu’o’inmu. Akwai misalai da yawa a cikin Littafi Mai Tsarki da suka nuna yadda za mu kasance da salama da ’yan’uwanmu. Za mu tattauna game da wasu cikinsu.

Misali Mafi Kyau da Za a Bi

4. Mene ne Allah ya yi don ya ceci ’yan Adam daga zunubi da kuma mutuwa?

4 Jehobah ne misali mafi kyau na wanda ya kasance da salama. Shi “Allah na salama” ne. (Rom. 15:33) Ka yi tunanin duk abubuwan da Jehobah ya yi don ya yiwu mu zama abokansa. Muna yin zunubi don mu ’ya’yan Adamu da Hawa’u ne. Kuma waɗanda suka yi zunubi za su mutu. (Rom. 6:23) Don Allah yana ƙaunarmu sosai, yana son ya cece mu daga zunubi da mutuwa. Ya aika Ɗansa Yesu ƙaunatacce daga sama don a haife shi kamiltacce kuma ya mutu domin zunubanmu. Yesu ya yi farin cikin yin abin da Ubansa yake so kuma ya ba da ransa hadaya dominmu. (Yoh. 10:17, 18) Allah na gaskiya ya ta da ƙaunataccen Ɗansa, wanda daga baya ya miƙa wa Ubansa amfanin jinin da ya zubar, kuma hadaya ne domin kada masu zunubi da suka tuba su halaka har abada.—Karanta Ibraniyawa 9:14, 24.

5, 6. Ta yaya hadayar Yesu ta taimaka wa mutane su zama abokan Allah?

5 Zunubi ya sa ’yan Adam sun zama maƙiyan Allah. Ta yaya hadayar Yesu ya taimaki ’yan Adam? Ishaya 53:5 ya ce: “Horo kuma mai-kawo lafiyarmu a kansa ya ke; ta wurin dūkansa da ya sha mun warke.” Hadayar Yesu ta sa ya yiwu ’yan Adam masu biyayya su zama abokan Allah. Littafi Mai Tsarki ya kuma ce: “Wanda muna da fansarmu a cikinsa ta wurin jininsa, gafarar laifofinmu.”—Afis. 1:7.

6 Littafi Mai Tsarki ya ce game da Yesu: “Dukan cikar Allah ta nufa ta zauna cikinsa [Kristi].” Wannan yana nufin cewa Allah yana amfani da Yesu don ya sa nufinsa ya cika. Amma mene ne nufin Allah? Shi ne ya “sulhunta abu duka gareshi, bayanda ya yi salama ta wurin jinin” da Yesu Kristi ya zubar. Abu duka da Allah ya sulhunta a gare shi, kuma ya sa suka zama abokansa su ne “abubuwan da ke cikin sama” da kuma “abubuwan da ke bisa duniya.” Mene ne waɗannan abubuwan?—Karanta Kolosiyawa 1:19, 20.

7. Mene ne “abubuwan da ke cikin sama” da “abubuwan da ke bisa duniya”?

7 Domin hadayar Yesu, Kiristoci shafaffu sun “barata” a matsayin ’ya’yan Allah kuma sun “kasance da salama wurin Allah.” (Karanta Romawa 5:1.) Littafi Mai Tsarki ya kira su “abubuwan da ke cikin sama” don Allah ya ta da su zuwa sama don su yi rayuwa tare da Yesu Kristi. Za su yi “mulki bisa duniya” kuma su yi hidima a matsayin firistoci. (R. Yoh. 5:10) ’Yan Adam da suka tuba daga zunubansu ne “abubuwan da ke bisa duniya” da za su yi rayuwa har abada a duniya.—Zab. 37:29.

8. Ta yaya misalin Jehobah yake taimaka maka sa’ad da akwai matsaloli a cikin ikilisiya?

8 Kalaman Bulus ga Kiristoci shafaffu na Afisa sun nuna yadda ya nuna godiya don fansar. Ya ce Allah “mawadaci ne cikin jinƙai” kuma ya sa “lokacin da mu ke matattu ta wurin laifofinmu, ya rayar da mu tare da Kristi.” Ya ce Allah ya cece mu “ta wurin alheri.” (Afis. 2:4, 5) Dukanmu, waɗanda za su yi rayuwa a sama da waɗanda za su yi rayuwa a duniya, suna godiya don jin ƙai na Allah da kuma alherinsa. Muna godiya don kome da Jehobah ya yi don ’yan Adam su kasance da salama da shi. A wasu lokatai, muna da matsaloli da za su hana ikilisiya kasancewa da haɗin kai. A wannan yanayin, ya kamata mu yi tunani game da misalin Allah kuma mu kasance da salama da ’yan’uwanmu.

Ka Koya Daga Misalin Ibrahim da Ishaƙu

9, 10. Ta yaya Ibrahim ya nuna cewa yana son ya kasance da salama da mutane?

9 Littafi Mai Tsarki ya ce game da Ibrahim: “Ibrahim ya gaskanta Allah, aka lissafta wannan kuwa adalci a gare shi; aka ce da shi kuma abokin Allah.” (Yaƙ. 2:23) Hanya ɗaya da Ibrahim ya kasance da bangaskiya ga Jehobah ita ce ta wajen kasancewa da salama da wasu. Alal misali, waɗanda suke kula da dabbobin Ibrahim sun yi gardama da waɗanda suke kula da dabbobin Lutu, ɗan wansa. (Far. 12:5; 13:7) Ibrahim da Lutu sun yanki shawara cewa abin da ya fi dacewa shi ne su kasance a wurare dabam-dabam a cikin ƙasar. Ka lura da abin da Ibrahim ya yi a wannan yanayi mai wuya. Bai yi tunani ba cewa shi ne ya kamata ya tsai da shawara na ƙarshe game da batun tun da shi ne babba kuma yana da dangantaka na musamman da Jehobah. Maimakon haka, ya nuna cewa yana son ya kasance da salama da ɗan wansa.

10 Ibrahim ya gaya wa ɗan wansa: “Ina roƙonka, kada rikici ta kasance tsakanina da kai, tsakanin makiyayana da makiyayanka kuma; gama mu ’yan’uwa ne.” Kuma ya ci gaba: “Dukan ƙasan nan ba shimfiɗe ta ke a gare ka ba? ka ware dabam da ni, ina roƙonka: in ta hannun hagu ka ke ɗauka, ni in tafi zuwa na dama: in kuwa za ka wajen na dama, ni in nufa wajen na hagu.” Lutu ya zaɓa wuri mafi kyau na ƙasar, wurin da ya fi dausayi. Ibrahim ya yarda da zaɓin Lutu kuma bai yi fushi da shi ba. (Far. 13:8-11) Mun san da hakan domin sa’ad da maƙiya suka tsare Lutu a fursuna, Ibrahim ya yi hanzari don ya cece shi.—Far. 14:14-16.

11. Ta yaya Ibrahim ya kasance da salama da maƙwabtansa Filibiyawa?

11 Ka yi tunani kuma da yadda Ibrahim ya yi iya ƙoƙarinsa don ya kasance da salama da Filistiyawa, maƙwabtansa a ƙasar Kan’anan. Filistiyawa sun “ƙwace” rijiyar da bayin Ibrahim suka haƙa a Beer-sheba. A wannan yanayin, Ibrahim bai yi kome ba kuma bai ce ko uffan ba. Bayan hakan, sarkin Filistiya ya ziyarci Ibrahim don su yi alkawarin kasancewa da salama. Ibrahim ya yarda ya yi wa zuriyar sarkin kirki. Sai bayan hakan ne, Ibrahim ya gaya wa sarkin game da rijiya da aka sace. Sarkin ya yi mamaki da ya ji game da wannan, kuma ya mayar wa Ibrahim rijiyar. Kuma Ibrahim ya ci gaba da zaman lafiya a matsayin baƙo a wannan ƙasar.—Far. 21:22-31, 34.

12, 13. (a) Ta yaya Ishaƙu ya bi misalin mahaifinsa? (b) Ta yaya Jehobah ya albarkaci ƙoƙarce-ƙoƙarcen Ishaƙu don ya kasance da salama?

12 Ishaƙu ɗan Ibrahim yana son zaman lafiya kamar babansa. Ya yi iya ƙoƙarinsa don ya kasance da salama da Filistiyawa. Domin babu abinci a ƙasar, Ishaƙu da iyalinsa suka ƙaura daga busashiyar yankin Beer-lahai-roi a Negeb zuwa Gerar yanki mai dausayi. Wannan yankin Filistiyawa ne. Jehobah ya albarkaci Ishaƙu da amfanin gona masu kyau da dabbobi masu yawa. Filistiyawa suka soma kishinsa. Ba sa son wadatar Ishaƙu ta ci gaba da ƙaruwa, saboda haka suka cika rijiyoyinsa da datti. Daga baya, sarkin Filistiya ya gaya wa Ishaƙu: “Tashi daga wurinmu.” Don ya kasance da salama da Filistiyawa, Ishaƙu ya yi abin da sarkin ya gaya masa.—Far. 24:62; 26:1, 12-17.

13 Bayan da Ishaƙu da iyalinsa suka ƙaura, makiyayarsa suka haƙa wata rijiya. Makiyaya na Filistiyawa suka yi musu da makiyayar Ishaƙu domin rijiyar kuma suka ce ruwan nasu ne. Kamar mahaifinsa, Ishaƙu ba ya son ya yi faɗa. Maimakon hakan, ya gaya wa bayinsa su haƙa wata rijiya. Filistiyawa suka yi gardama game da wannan ma. Domin ya kasance da salama da Filistiyawa, Ishaƙu ya ƙaura da iyalinsa da kome da yake da shi zuwa wani wuri. Bayinsa suka haƙa rijiya a wannan wurin kuma Ishaƙu ya kira ta Rehoboth. Daga baya, ya ƙaura zuwa wurin da ya fi dausayi a Beer-sheba. Jehobah ya albarkace shi a wurin kuma ya gaya masa: “Kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai, kuma zan albarkace ka, in riɓanɓanya zuriyanka sabili da bawana Ibrahim.”—Far. 26:17-25.

14. Sa’ad da sarkin Filistiya ya zo ya yi alkawari da Ishaƙu, ta yaya Ishaƙu ya nuna cewa yana son ya yi zaman lafiya da shi?

14 Hakika, Ishaƙu yana iya yin faɗa don ya samu damansa na yin amfani da dukan rijiyoyi da bayinsa suka haƙa. Sarkin Filistiya ya san cewa Jehobah ya albarkaci Ishaƙu a kome da ya yi. Sa’ad da sarkin da rundunarsa sun ziyarci Ishaƙu a Beer-sheba kuma ya yi alkawari na kasancewa da salama da shi, ya ce: “Sosai muka gane Ubangiji yana tare da kai.” Amma don a yi zaman lafiya, Ishaƙu ya zaɓi ya ƙaura fiye da sau ɗaya. Ba ya son ya yi faɗa. A wannan lokacin ma, sa’ad da sarkin da rundunarsa suka ziyarce shi, Ishaƙu ya nuna cewa yana son ya yi zaman lafiya da sarkin. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana: “Ya yi masu buki, suka ci suka sha. Suka yi sammako da safe, suka rantse ma junansu: Ishaƙu kuwa ya sallame su, suka tashi wurinsa lafiya.”—Far. 26:26-31.

Ka Koya Darasi Daga Misalin Yusufu

15. Me ya sa ’yan’uwan Yusufu ba su iya kasancewa da salama da shi ba?

15 Littafi Mai Tsarki ya ce Yakubu ɗan Ishaƙu “kintsattse ne.” (Far. 25:27, LMT) Kamar yadda muka koya ɗazun, Yakubu ya yi iya ƙoƙarinsa don ya kasance da salama da ɗan’uwansa Isuwa. Yakubu ya koya daga misali mai kyau na mahaifinsa Ishaƙu. Shin ’ya’yan Yakubu sun koya daga misalinsa? Yakubu ya fi ƙaunar Yusufu a cikin yaransa maza goma sha biyu. Yusufu ya yi ladabi da biyayya ga mahaifinsa kuma shi ɗa ne da Yakubu zai iya tabbata da shi. (Far. 37:2, 14) Amma Littafi Mai Tsarki ya ce ’yan’uwan Yusufu suka soma kishinsa sosai har ba su iya yin magana cikin salama da shi ba. Sun tsane Yusufu sosai har suka sayar da shi a matsayin bawa kuma suka sa mahaifinsu ya gaskata cewa dabbar jeji ce ta kashe shi.—Far. 37:4, 28, 31-33.

16, 17. Ta yaya yadda Yusufu ya bi da ’yan’uwan ya nuna cewa yana son ya kasance da salama da su?

16 Jehobah ya albarkaci Yusufu. Da shigewar lokaci, Yusufu ya zama firayim minista, wato, mutum na biyu wanda ya fi iko a ƙasar Masar. Sa’ad da aka yi muguwar yunwa a ƙasar Kan’anan, ’yan’uwan Yusufu suka zo sayan abinci a ƙasar Masar. Sa’ad da suka haɗu da Yusufu, ba su waye shi ba wataƙila domin tufafin Masarawa da ya saka. (Far. 42:5-7) Da Yusufu ya bi da ’yan’uwansa yadda suka bi da shi da mahaifinsu. Maimakon haka, Yusufu ya yi abin da zai iya don ya kasance da salama da su. Kuma sa’ad da ya ga alama cewa ’yan’uwansa sun tuba, sai Yusufu ya bayyana kansa. Ya ce: “Amma yanzu kada ranku ya ɓāci, kada kuwa ku yi fushi da kanku, da kuka sayar da ni zuwa nan: gama Allah ne ya aiko ni a gabanku, domin in ceci rai.” Sai ya yi wa dukan ‘yan’uwansa sumba kuma, yana ta kuka a bisansu.—Far. 45:1, 5, 15.

17 Bayan rasuwar mahaifinsu, Yakubu, ’yan’uwan Yusufu suka yi tunanin cewa Yusufu yana iya yin ramako a kansu. Sa’ad da suka yi wa Yusufu magana game da wannan, sai “ya yi kuka” kuma ya ce “kada ku ji tsoro: ni in agaje ku, da ’ya’yanku ƙanana.” A wannan yanayin ma, Yusufu ya nuna cewa yana son zaman lafiya. “Ya yi masu ta’aziya ya yi masu magana mai-alheri.”—Far. 50:15-21.

Misalai “Domin Koyarwarmu”

18, 19. (a) Mene ne muka koya daga misalan da muka tattauna a wannan talifin? (b) Mene ne za mu koya a talifi na gaba?

18 Bulus ya rubuta: “Iyakar abin da aka rubuta a dā aka rubuta su domin koyarwarmu, domin ta wurin haƙuri da ta’aziyar littattafai mu zama da bege.” (Rom. 15:4) Mene ne muka koya daga Jehobah wanda ya fi nuna wa kowa misali, da kuma misalan Ibrahim da Ishaƙu da Yakubu da kuma Yusufu?

19 Idan muka yi tunani game da dukan abin da Jehobah ya yi don ya yiwu mu zama abokansa, za mu so mu yi kome da za mu iya don mu kasance da salama da mutane. Abin da muka koya game da Ibrahim da Ishaƙu da Yakubu da kuma Yusufu ya nuna cewa iyaye za su iya nuna wa yaransu misali mai kyau kuma su koya musu su kasance da salama da mutane. Mun koya kuma cewa Jehobah yana yin albarka ga ƙoƙarce-ƙoƙarcen waɗanda suke ƙoƙari suka kasance da salama. Hakan ya taimaka mana mu fahimci dalilin da ya sa Bulus ya rubuta cewa Jehobah “Allah na salama” ne. (Karanta Romawa 15:33; 16:20.) Talifi na gaba zai tattauna dalilin da ya sa Bulus ya faɗa cewa muna bukatar mu kasance da salama da kuma yadda za mu iya yin hakan.

Mene ne Ka Koya?

• Kafin ya haɗu da Isuwa, mene ne Yakubu ya yi don ya kasance da salama da shi?

• Yaya abin da Jehobah ya yi don ’yan Adam su kasance da salama da shi ya shafe ka?

• Mene ne ka koya daga misalan masu yin salama, wato, Ibrahim da Ishaƙu da Yakubu da kuma Yusufu?

[Hotona a shafi na 23]

Wane mataki mafi muhimmanci ne Yakubu ya ɗauka don ya kasance da salama da Isuwa?

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba