Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 10/15 pp. 23-27
  • Ka Dogara Ga Jehobah, “Allah Na Dukan Ta’aziyya”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Dogara Ga Jehobah, “Allah Na Dukan Ta’aziyya”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Jimrewa da Abubuwa da ke Kawo Wahala
  • Misalan Ta’aziyya daga Wurin Allah
  • Ƙarƙashinsa ne Madawwamin Hannuwan Allah Suke
  • Ka “Yi Wa Dukan Masu-makoki Ta’aziyya”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Yadda Allah Yake Karfafa Mu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
  • A Ina Za A Sami Ta’aziyya Ta Gaske?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ka Yi Wa Masu Makoki Ta’aziyya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 10/15 pp. 23-27

Ka Dogara Ga Jehobah, “Allah Na Dukan Ta’aziyya”

“Albarka ga Allah da Uba na Ubangijinmu Yesu Kristi, Uban jiyejiyenƙai, Allah na dukan ta’aziyya.”—2 KOR. 1:3.

1. Mene ne kowa yake bukata?

TUN daga lokacin da aka haife mu, muna bukatar ta’aziyya. Jariri yana kuka don ya sanar mana cewa yana bukatar ta’aziyya. Wataƙila yana son wani ya ɗauke shi ko kuma yana jin yunwa. Ko sa’ad da muka yi girma, sau da yawa muna bukatar a yi mana ta’aziyya. Musamman ma lokacin da muke cikin yanayi mai wuya.

2. Wane alkawari ne Jehobah ya yi wa waɗanda suka dogara a gareshi?

2 Waɗanda suke cikin iyalinmu ko kuma abokai suna iya ƙarfafa mu. Amma a wasu lokatai, ’yan Adam ba za su iya yin maganin baƙin cikin da muke yi ba. Allah ne kawai zai iya yi mana ta’aziyya ko yaya yanayinmu. Kalmar Allah ta tabbatar mana: “Ubangiji yana kusa da dukan waɗanda su ke kira bisa gareshi, . . . za ya kuma ji kukassu.” (Zab. 145:18, 19) Hakika, “idanun Ubangiji suna fuskanta wajen masu-adalci; kunnuwansa kuma a buɗe su ke ga jin ƙarassu.” (Zab. 34:15) Amma idan za mu sami taimakon Allah da ta’aziyyarsa, dole ne mu dogara a gareshi. Marubucin wannan zaburar ya nuna hakan dalla-dalla sa’ad da ya rera: “Ubangiji kuma za ya zama kagara mai-tsawo domin waɗanda a ke zalumtassu, kagara mai-tsawo cikin wokatan wahala; waɗanda sun san sunanka za su dogara gareka; gama ba ka yarfar da masu-nemanka ba, ya Ubangiji.”—Zab. 9:9, 10.

3. Ta yaya Yesu ya kwatanta ƙaunar Allah ga mutanensa?

3 Waɗanda suke bauta wa Jehobah suna da tamani a gareshi. Yesu ya faɗi hakan dalla-dalla sa’ad da ya ce: “Ba a kan sayar da gwara biyar a bakin anini huɗu ba? ko ɗaya kuwa a cikinsu ba a manta da shi wurin Allah ba. Amma har da gasussuwan kanku duka an ƙididdige su. Kada ku ji tsoro: kun fi gwarare masu-yawa daraja.” (Luk 12:6, 7) Ta wurin annabi Irmiya, Jehobah ya gaya wa mutanensa na dā: “Na yi ƙaunarka da madawamiyar ƙauna; domin wannan na jawo ka da rahama.”—Irm. 31:3.

4. Me ya sa za mu dogara ga alkawuran Jehobah?

4 Yin dogara ga Jehobah da kuma cikar alkawuransa za su iya ta’azantar da mu a lokatan wahala. Ya kamata mu dogara ga Allah kamar Joshua, wanda ya furta: “Babu wani abu ɗaya ya sare daga cikin dukan alherai waɗanda Ubangiji Allahnku ya ambace su a kanku: dukansu sun tabbata a gareku, babu wani abu ɗaya ya sare daga ciki.” (Josh. 23:14) Ƙari ga haka, za mu iya kasancewa da tabbaci cewa ko da muna shan wahala a yau, “Allah mai-aminci ne” kuma ba zai taɓa yasar da bayinsa masu aminci ba.—Karanta 1 Korintiyawa 10:13.

5. Yaya zai yiwu mu ta’azantar da wasu?

5 Manzo Bulus ya kira Jehobah “Allah na dukan ta’aziyya.” Yin “ta’aziyya” yana nufin kwantar da hankalin wani da ke wahala ko baƙin ciki. Ana yin hakan ta sa wanda yake baƙin ciki ya wartsake. (Karanta 2 Korintiyawa 1:3, 4.) Ubanmu na sama ya fi kowa da kome iko. Saboda haka, zai yi duk wani abin da zai yi don ya ta’azantar da waɗanda suke ƙaunarsa. Tun da yake Allah ya yi mana ta’aziyya, muna iya yi wa ’yan’uwanmu ta’aziyya “cikin kowane irin ƙunci.” Za mu iya yin hakan “ta wurin ta’aziyya wadda mu da kanmu muka ta’azantu da ita daga wurin Allah.” Wannan ya nuna cewa Jehobah yana da inganci ya ta’azantar da waɗanda suka raunana!

Jimrewa da Abubuwa da ke Kawo Wahala

6. Ka ba da misalan abubuwan da za su iya sa mutum ya sha wahala.

6 Muna bukatar ƙarfafa a yanayi da yawa na rayuwa. Wani abu da ya fi sa mutum baƙin ciki shi ne rasuwar wanda muke ƙauna, musamman abokin aure ƙaunatacce ko kuma ɗa ko ’ya. Wasu suna iya bukatar ƙarfafa domin sun sha wahalar wariya. Rashin lafiya da tsufa da talauci da matsalolin aure da mugayen abubuwa da suke faruwa a duniya suna iya sa mutum ya bukaci ƙarfafa.

7. (a) Wace irin ta’aziyya ce ake bukata a yanayi mai wuya? (b) Mene ne Jehobah zai iya yi don ya warkar da “karyayyar zuciya?”

7 A lokatan wahala, muna iya bukatar ta’aziyya da ke sanyaya zuciyarmu da hankalinmu da motsin ranmu da kuma lafiyarmu ta zahiri da ta ruhaniya. Alal misali, ka yi la’akari da zuciya. Kalmar Allah ta amince cewa zuciyarmu za ta iya zama ‘karyayye.’ (Zab. 51:17) Babu shakka, Jehobah yana iya bi da wannan yanayin, gama “yana warkar da masu-karyayyar zuciya, yana ɗaure raunukan su.” (Zab. 147:3) Ko a yanayi mai wuya, Allah zai iya sauƙaƙa karyayyar zuciya idan muka yi addu’a da cikakkiyar bangaskiya kuma muka yi biyayya ga umurninsa.—Karanta 1 Yohanna 3:19-22; 5:14, 15.

8. Ta yaya Jehobah yake taimaka mana sa’ad da hankalinmu ya raunana?

8 Domin muna fuskantar gwaje-gwaje iri-iri, wasu lokatai hankalinmu yana bukatar ta’aziyya. Ba za mu iya jimre da waɗannan gwaje-gwajen bangaskiya da ƙarfinmu ba. Amma, marubucin wannan zabura ya rera waƙa: “A cikin yawan wusuwasi da ke cikina ta’aziyyanka suna ji ma raina daɗi.” (Zab. 94:19) Bugu da ƙari, Bulus ya rubuta: “Kada ku yi alhini cikin kowane abu; amma cikin kowane abu, ta wurin addu’a da roƙo tare da godiya, ku bar roƙe roƙenku su sanu ga Allah. Salama kuwa ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka, za ta tsare zukatanku da tunaninku cikin Kristi Yesu.” (Filib. 4:6, 7) Karanta da kuma yin bimbini a kan Nassosi za su taimaka mana sosai wajen jimre da matsalolin da suka shafi hankalinmu.—2 Tim. 3:15-17.

9. Ta yaya za mu iya jimre da matsalar motsin rai?

9 A wasu lokatai, muna iya yin sanyin gwiwa sosai da har hakan ya shafi motsin ranmu. Wataƙila muna jin cewa ba za mu iya kula da wani hakki na Nassi ba ko kuma gatar hidima. A wannan yanayin ma, Jehobah zai iya ƙarfafa mu kuma ya taimaka mana. Alal misali: Sa’ad da aka ba Joshua aiki ya ja-goranci Isra’ilawa zuwa yaƙi da al’ummai magabta masu ƙarfi sosai, Musa ya gaya wa mutanen: “Ka yi ƙarfi ka yi gaba gaɗi, kada ka ji tsoro, kada ka firgita dominsu: gama Ubangiji Allahnka, shi ne ya ke tafiya tare da kai; ba za ya bar ka ba, ba kuwa za ya yashe ka ba.” (K. Sha 31:6) Da taimakon Jehobah, Joshua ya ja-goranci mutanen Allah zuwa cikin Ƙasar Alkawari kuma suka ci dukan magabtansu. Musa ya samu irin wannan taimako daga Jehobah a Jar Teku.—Fit. 14:13, 14, 29-31.

10. Idan mugun yanayi ya shafi lafiyarmu ta zahiri, mene ne zai iya taimaka mana?

10 Mugun yanayi yana iya shafan lafiyarmu ta zahiri. Hakika, cin abinci yadda ya dace da samun isashen hutu da motsa jiki da kuma yin tsabta suna iya kasance da sakamako mai kyau a gare mu. Yin tunani game da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da nan gaba, zai iya kyautata lafiyarmu ta zahiri. Saboda haka, sa’ad da muke fuskantar matsala, yana da kyau mu tuna da wahalar da Bulus ya sha da kuma kalamansa masu ban ƙarfafa: “Mun matsu ga kowane sashi, amma ba mu ƙuntata ba; mun damu, amma ba ya kai fid da zuciya ba; ana binmu da tsanani, amma ba a bar mu yasassu ba: an fyaɗa mu a ƙasa, amma ba a halaka mu ba.”—2 Kor. 4:8, 9.

11. Ta yaya za mu sha kan rashin lafiya ta ruhaniya?

11 Wasu gwaje-gwaje ma suna iya shafan lafiyarmu ta ruhaniya. Jehobah zai iya taimaka mana a wannan yanayin. Kalmarsa ta tabbatar mana: “Ubangiji yana talafan dukan waɗanda su ke faɗuwa, yana tada dukan tanƙwararru.” (Zab. 145:14) Don mu sha kan rashin lafiya ta ruhaniya, ya kamata mu nemi taimakon dattawan Kirista. (Yaƙ. 5:14, 15) Kuma yin tunani game da begenmu na rai madawwami a kai a kai zai iya ba mu ƙarfi da muke bukata a lokacin gwajin bangaskiyarmu.—Yoh. 17:3.

Misalan Ta’aziyya daga Wurin Allah

12. Ka kwatanta yadda Jehobah ya yi wa Ibrahim ta’aziyya.

12 Wani marubucin zabura ya ce: “Ka tuna wa bawanka maganan nan, wadda ka [Jehobah] sa in ƙalafa raina gareta. Wannan shi ne ta’aziyata cikin ƙuncina: Gama maganarka ta rayar da ni.” (Zab. 119:49, 50) A yau, muna da rubutacciyar Kalmar Jehobah, wadda ke ɗauke da misalan ta’aziyya da yawa daga wurin Allah. Alal misali, babu shakka Ibrahim ya damu sosai sa’ad da ya ji cewa Jehobah yana son ya halaka Saduma da Gwamarata. Wannan uban iyali mai aminci ya tambayi Allah: “Za ka halaka mai-adalci tare da miyagu?” Jehobah ya ta’azantar da Ibrahim ta wajen tabbatar masa cewa idan akwai mutane 50 masu adalci, ba zai halaka Saduma ba. Amma, Ibrahim ya yi wa Jehobah tambaya sau biyar kuma yana cewa: Idan akwai mutane masu adalci guda 45 ko 40 ko 30 ko 20 ko 10 kuma fa? A duk tambayoyi da ya yi, Jehobah cikin haƙuri da alheri ya tabbatar wa Ibrahim cewa ba zai halaka Saduma ba. Ko da yake babu ma mutane goma masu adalci a yankin, Jehobah ya ceci Lutu da ’ya’yansa mata.—Far. 18:22-32; 19:15, 16, 26.

13. Ta yaya Hannatu ta nuna cewa ta dogara ga Jehobah?

13 Hannatu matar Elkanah tana son ta samu ɗa. Amma ita bakararriya ce, kuma hakan ya sa ta baƙin ciki sosai. Ta yi addu’a ga Jehobah game da batun, kuma Eli Babban Firist ya gaya mata: “Allah kuwa na Isra’ila shi ba ki roƙonki.” Hakan ya ƙarfafa Hannatu, kuma “fuskarta ba ta ƙara nuna baƙinciki ba.” (1 Sam. 1:8, 17, 18) Hannatu ta dogara cewa Jehobah zai biya bukatar ta. Ko da yake ba ta san abin da zai faru ba, Hannatu ta samu kwanciyar hankali. Da shigewar lokaci, Jehobah ya amsa addu’arta. Ta yi ciki kuma ta samu ɗa mai suna, Sama’ila.—1 Sam. 1:20.

14. Me ya sa Dauda yake bukatar ta’aziyya, kuma wurin wa ya nemi taimako?

14 Wani misali na wanda Allah ya yi wa ta’aziyya shi ne Sarki Dauda. Da yake Jehobah yana ganin “zuciya,” sa’ad da ya zaɓi Dauda ya zama sarkin Isra’ila, ya san cewa Dauda yana da zuciyar kirki kuma yana ƙaunar bauta ta gaskiya. (1 Sam. 16:7; 2 Sam. 5:10) Amma, daga baya, Dauda ya yi zina da Bath-sheba kuma ya yi ƙoƙari ya ɓoye zunubin ta wajen sa a kashe mijinta. Sa’ad da Dauda ya fahimci tsananin zunubin da ya yi, sai ya yi addu’a ga Jehobah: “Ka yi mani jinƙai, ya Allah, bisa ga rahamarka: bisa ga yawan jiyejiyenƙanka ka shafe laifofina. Ka wanke ni sarai daga kuskurena, ka tsarkake ni daga zunubina. Gama ina sane da laifofina: zunubina yana gabana kullum.” (Zab. 51:1-3) Dauda ya tuba da gaske, kuma Jehobah ya gafarta masa. Amma, Dauda ya fuskanci sakamakon zunubinsa. (2 Sam. 12:9-12) Duk da haka, jin ƙan Jehobah ya ƙarfafa shi.

15. Yaya Jehobah ya taimaki Yesu gab da mutuwarsa?

15 Sa’ad da Yesu yake duniya, ya fuskanci yanayi da yawa masu wuya. Allah ya ƙyale a gwada Yesu, amma ya kasance da aminci a matsayin kamiltacce wanda a koyaushe yana dogara ga Jehobah kuma yana ɗaukaka ikon mallakarsa. Kafin a ci amanarsa kuma aka kashe shi, Yesu ya yi addu’a ga Jehobah: “Ba nawa nufi ba, naka za a yi.” Wani mala’ika ya bayana ga Yesu kuma ya ƙarfafa shi. (Luk 22:42, 43) Allah ya ta’azantar da Yesu ya ƙarfafa shi kuma ya tallafa masa a wannan lokacin.

16. Mene ne Allah zai iya yi game da wahalar da muke sha idan aka kashe mu domin amincinmu?

16 Jehobah zai iya taimaka mana mu kasance da aminci a gare shi ko idan rayuwarmu tana cikin haɗari domin amincinmu. Bugu da ƙari, begen tashin matattu yana ta’azantar da mu. Kuma muna sauraron ranar da za a kawar da maƙiyi na ƙarshe. (1 Kor. 15:26) Allah yana tunawa da bayinsa masu aminci da suka mutu da kuma wasu, ba zai mance da su ba, zai ta da su daga matattu. (Yoh. 5:28, 29; A. M. 24:15) Kasancewa da tabbaci ga alkawarin Jehobah na tashin matattu yana ta’azantar da mu don mu kasance da bege mai ƙarfi a lokacin tsanantawa.

17. Ta yaya Jehobah zai iya ta’azantar da mu sa’ad da wani ƙaunatacce ya mutu?

17 Sanin cewa za a ta da ƙaunatattunmu da suka mutu a sabuwar duniya mai ban al’ajabi da babu duk abubuwan da ke kawo wahala na zamani yana ƙarfafa mu. Kuma zai kasance gata ga “taro mai-girma” na bayin Jehobah da suka tsira daga wannan mugun zamani su marabci da kuma koyar da waɗanda aka ta da daga matattu a duniya!—R. Yoh. 7:9, 10.

Ƙarƙashinsa ne Madawwamin Hannuwan Allah Suke

18, 19. Ta yaya aka ƙarfafa bayin Allah sa’ad da ake tsananta musu?

18 A cikin kalaman waƙa mai iko da kuma daɗaɗawa, Musa ya tabbatar wa Isra’ilawa: “Allah madawwami shi ne mazauninka, ƙarƙashinka kuma madawwaman hannuwa su ke.” (K. Sha 33:27) Daga baya annabi Sama’ila ya gaya wa Isra’ilawa: “Kada ku ratse ga barin bin Ubangiji, amma ku bauta ma Ubangiji da dukan zuciyarku . . . Ubangiji ba za ya yarda jama’atasa ba sabili da sunansa mai-girma.” (1 Sam. 12:20-22) Muddin mun bauta wa Jehobah cikin aminci, ba zai taɓa yashe mu ba. A ko da yaushe zai riƙa taimaka mana.

19 Allah yana taimaka wa mutanensa da kuma yi musu ta’aziyya a waɗannan miyagun kwanaki na ƙarshe. Fiye da ƙarni guda, ana tsananta wa ’yan’uwanmu masu bi a dukan duniya da kuma saka su a kurkuku domin suna bauta wa Jehobah. Labaransu sun nuna cewa Jehobah yana ƙarfafa bayinsa a lokacin gwaji. Alal misali, an saka wani ɗan’uwanmu da ke ƙasar Rasha ta dā a cikin kurkuku na tsawon shekara 23 domin imaninsa. Duk da haka, ya samu littafin da ke bayyana Littafi Mai Tsarki da ya ƙarfafa shi da kuma yi masa ta’aziyya. Ya ce: “A duk waɗannan shekaru, na koya na dogara ga Jehobah kuma ya ƙarfafa ni.”—Karanta 1 Bitrus 5:6, 7.

20. Me ya sa za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah ba zai yasar da mu ba?

20 Ko da mene ne za mu fuskanta a nan gaba, yana da kyau mu tuna da kalamai masu ban ta’aziyya na marubucin wannan zabura: “Ubangiji ba za ya yarda mutanensa ba.” (Zab. 94:14) Ko da yake muna bukatar a ƙarfafa mu, muna da gata mai girma na ƙarfafa mutane. Kamar yadda za mu gani a talifi na gaba, muna iya saka hannu wajen yin ta’aziyya ga masu makoki a wannan duniya mai cike da wahala.

Yaya Za Ka Amsa?

• Waɗanne abubuwa ne za su iya sa mu baƙin ciki?

• Ta yaya Jehobah yake ƙarfafa bayinsa?

• Idan rayuwarmu tana cikin haɗari, mene ne zai iya ta’azantar da mu?

[Akwati/​Hoto a shafi na 25]

YADDA ZA MU JIMRE DA ABUBUWAN DA ZA SU IYA SHAFAN . . .

▪ zuciyarmu Zab. 147:3; 1 Yoh. 3:19-22; 5:14, 15

▪ tunaninmu Zab. 94:19; Filib. 4:6, 7

▪ motsin ranmu Fit. 14:13, 14; K. Sha 31:6

▪ lafiyar jikinmu 2 Kor. 4:8, 9

▪ lafiyarmu ta ruhaniya Zab. 145:14; Yaƙ. 5:14, 15

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba