Ka Kusaci Allah
Idan Allah Ya Gafarta wa Mutum, Yana Mantawa Kwata-kwata Kuwa?
AMSAR wannan tambayar a taƙaice e ce. Jehobah ya yi wa waɗanda ya amince da su alkawari cewa ‘zai gafarta muguntarsu, ba zai kuwa ƙara tuna da zunubinsu ba.’ (Irmiya 31:34) Da haka, Jehobah ya tabbatar da mu cewa sa’ad da ya gafarta wa mai zunubi da ya tuba, ba ya ƙara tuna da zunuban. Amma hakan yana nufin cewa Mahaliccin dukan sararin samaniya ba zai iya tuna da zunuban ba ne gaba ɗaya? Abin da Ezekiyel ya faɗa ya nuna yadda Jehobah yakan gafarta wa mutane kuma ya mance.—Ka karanta Ezekiyel 18:19-22.
Jehobah ya furta hukunci bisa Yahuda mai rashin aminci ta bakin kakakinsa, annabi Ezekiyel. Al’ummar gabaki ɗaya ta bijire daga bautar Jehobah kuma ta cika ƙasar da rashin imani. Jehobah ya yi annabci cewa Babiloniyawa za su halaka babban birnin Yahuda, wato, Urushalima. Duk da wannan hukuncin, Jehobah ya ba da saƙo mai ban ƙarfafa. Kowa ya na da zaɓi, ko ya tuba ko ya ci gaba da yin mugunta. Amma abin da mutum ya shuka, shi za ya girbe.—Ayoyi na 19, 20.
Idan mutum ya tuba daga yin zunubi kuma fa? Jehobah ya ce: “Amma idan mugu ya juya ga barin dukan zunubansa da ya aikata, ya kiyaye dukan farillaina, ya yi abin da ke halal da daidai kuma, hakika za ya yi rai, ba za ya mutu ba.” (Aya ta 21) Hakika, idan mai zunubi ya tuba daga miyagun ayyukansa da gaske, Jehobah “mai-hanzarin gafartawa” ne.—Zabura 86:5.
Zunuban da ya riga ya yi kuma fa? Jehobah ya bayyana cewa “ba za a riƙe laifinsa da ya yi ko ɗaya a kansa ba.” (Aya ta 22) Ka lura cewa ‘ba za a riƙe laifinsa a kansa ba.’ Mene ne wannan yake nufi?
Game da wannan kalmar Ibrananci da aka fassara a cikin Littafi Mai Tsarki, “riƙe laifinsa,” wata majiya ta ba da bayani cewa: “Hakika, sau da yawa, [tana] nufin ɗaukan mataki ko kuma tana aukuwa ne tare da wasu kalmomin aikatau.” Saboda haka, kalmar nan “riƙe laifinsa” yana nufin “ɗaukan mataki.” Sa’ad da Jehobah ya gaya wa mai laifi da ya tuba cewa “ba za a riƙe laifinsa da ya yi ko ɗaya a kansa ba,” Jehobah yana nufi ne cewa daga baya ba zai ɗauki mataki a kan mutumin ba saboda zunuban nan da ya yi ba, wato, ba zai tuhume shi ko kuma hukunta shi ba.a
Kalmomin da ke Ezekiyel 18:21, 22 suna kwatanta yadda Jehobah yake nuna jin ƙai kuma idan muka tuna da hakan, muna samun ƙarfafa ƙwarai. Sa’ad da Jehobah ya gafarta mana zunubanmu, ba zai hukunta mu saboda waɗannan zunuban a nan gaba ba. Maimakon haka, yana mantawa da zunuban waɗanda suka tuba. (Ishaya 38:17) Kamar dai ya share waɗannan zunuban ne gaba ɗaya.—Ayyukan Manzanni 3:19.
Muna bukatar gafartawar Allah domin mu ajizai ne. Balle ma, muna yin zunubi a kowane lokaci. (Romawa 3:23) Amma Jehobah yana so mu san cewa idan muka tuba da gaske, yana shirye ya gafarta mana. Kuma sa’ad da ya gafarta mana, yana mantawa, wato, ba zai sake tuhumar mu ko kuma hukunta mu saboda waɗannan zunuban da ya yafe mana ba. Hakan yana da ban ƙarfafa! Jin ƙan da Allah yake nunawa yana motsa ka ka kusace shi ne?
[Hasiya]
a Hakazalika, “tuna da laifofi” yana nufin “saka wa masu zunubi.”—Irmiya 14:10.