Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 10/15 pp. 7-11
  • Yadda Za Mu Jimre Da Matsalolinmu Da Gaba Gaɗi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Za Mu Jimre Da Matsalolinmu Da Gaba Gaɗi
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KA YI KOYI DA WAƊANDA SUKA NUNA GABA GAƊI
  • KADA KA ƘYALE MATSALOLI SU SA KA SANYIN GWIWA
  • ME YA SA MUKE NUNA GABA GAƊI?
  • YADDA ZA MU AMFANA DAGA TAIMAKON ALLAH
  • “Ka Yi Karfin Hali . . . Ka Kama Aikin”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Ƙauna Tana Ƙarfafa Gaba Gaɗi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ka Ba Ni Karfin Hali
    “Ku Rera Waka da Farin Ciki” ga Jehobah
  • Ka Ci Gaba Da Farin Ciki A Lokacin Wahala
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 10/15 pp. 7-11

Yadda Za Mu Jimre Da Matsalolinmu Da Gaba Gaɗi

“Allah mafakanmu ne da ƙarfinmu, taimako ne na kurkusa cikin wahala.”—ZAB. 46:1.

MECE CE AMSARKA?

Mene ne ya kamata mu yi idan ba ma son matsaloli su sa mu sanyin gwiwa?

Me ya sa muke bukatar mu nuna gaba gaɗi?

Waɗanne tanadi ne Jehobah ya yi domin ya taimaka mana mu jimre da matsaloli?

1, 2. Waɗanne matsaloli ne mutane da yawa suke fuskanta, amma mene ne kowannenmu yake so?

RAYUWA a zamaninmu tana da wuya sosai. Matsaloli dabam-dabam kamar girgizar ƙasa da guguwa da wutar daji da tufana da dutsen da ke aman wuta suna ba ’yan Adam kashi sosai. Bugu da ƙari, matsalolin iyali da na kanmu suna jawo mana takaici da tsoro. Littafi Mai Tsarki ya ce, ‘sa’a da tsautsayi’ sukan shafi dukanmu. Tabbas, hakan gaskiya ne.—M. Wa. 9:11.

2 Bayin Allah sun ci gaba da bauta masa duk da waɗannan matsaloli. Amma, dukanmu muna son mu kasance a shirye don mu jimre da matsalolin da za mu fuskanta a nan gaba tun da ƙarshe ya kusa. Mene ne zai taimaka mana mu kasance da aminci sa’ad da muke fuskantar matsaloli? Mene ne zai taimaka mana mu nuna gaba gaɗi?

KA YI KOYI DA WAƊANDA SUKA NUNA GABA GAƊI

3. Kamar yadda littafin Romawa 15:4 ya nuna, mene ne zai iya ƙarfafa mu sa’ad da muke fuskantar matsaloli?

3 Ko da yake mutane sun fi fuskantar matsaloli yanzu, amma hakan ba sabon abu ba ne. Wasu bayin Jehobah a zamanin dā sun nuna gaba gaɗi sa’ad da suka fuskanci matsaloli. Bari mu tattauna yadda za mu koyi darassi daga wurin su.—Rom. 15:4.

4. Waɗanne matsaloli ne suka auko wa Dauda, kuma mene ne ya taimaka masa?

4 Za mu soma da misalin Dauda. Sarki Saul yana son ya kashe Dauda. Amalakawa sun kai masa hari kuma sun kwashe matansa. Wasu cikin mayaƙansa da danginsa da kuma abokansa sun ci amanarsa. A wasu lokatai, hakan ya sa shi sanyin gwiwa. (1 Sam. 18:8, 9; 30:1-5; 2 Sam. 17:1-3; 24:15, 17; Zab. 38:4-8) Littafi Mai Tsarki ya nuna yadda hakan ya jawo wa Dauda taƙaici sosai. Amma hakan bai raunana imaninsa ga Jehobah ba. Ya ce: “Ubangiji shi ne ƙarfin raina; zan ji tsoron wanene?”—Zab. 27:1, karanta Zabura 27:5, 10.

5. Mene ne ya taimaki Ibrahim da Saratu su jimre da wahala?

5 Ibrahim da Saratu sun zauna a cikin tanti a ƙasar da ba tasu ba shekaru da yawa. Rayuwa ba cin tuwo ba ne a gare su. Sun jimre da yunwa da kuma hari daga ƙasashen da ke kewaye da su. (Far. 12:10; 14:14-16) Mene ne ya taimaka musu su jimre? Littafi Mai Tsarki ya ce Ibrahim yana jiran “birnin da ke da tussa, wanda mai-sifansa da mai-aikinsa Allah ne.” (Ibran. 11:8-10) Ibrahim da Saratu ba su ƙyale abubuwan da ke kewaye da su su janye hankalinsu ba.

6. Ta yaya za mu yi koyi da Ayuba?

6 Ayuba ya sha wuya sosai. Yaya kake ganin ya ji sa’ad da yake fuskantar waɗannan matsalolin? (Ayu. 3:3, 11) Ayuba bai san dalilan da suka sa yake fuskantar waɗannan matsalolin ba. Amma, bai karaya ba. Ya kasance da aminci da kuma imani ga Allah. (Karanta Ayuba 27:5, 6) Wannan misali mai kyau ne a gare mu.

7. Waɗanne matsaloli ne Bulus ya fuskanta a hidimarsa ga Allah, amma mene ne ya taimaka masa ya ci gaba da bauta wa Allah?

7 Ka kuma yi la’akari da misalin Bulus. Ya ce ya fuskanci, “hatsari cikin birni, hatsari cikin jeji, hatsari cikin teku.” Kuma ya ji ‘yunwa da ƙishi, cikin ɗāri da huntanci.’ Ya kuma ce ya ‘kwana da yini yana cikin zurfin teku,’ wataƙila saboda hatsarin da ya yi a jirgi. (2 Kor. 11:23-27) Duk da waɗannan abubuwan da ya fuskanta, bai karaya ba. A wani lokacin da ya kusan mutuwa don yana bauta wa Allah, ya ce: “Domin kada mu dogara ga kanmu, amma ga Allah wanda ke tada matattu: wanda ya tsame mu daga cikin mutuwa mai-girma haka, har kuwa zai tsame mu.” (2 Kor. 1:8-10) Mutane da yawa ba su taɓa fuskantar irin matsalolin Bulus ba. Amma, yawancinmu mun taɓa baƙin ciki kamar shi. Hakazalika, gaba gaɗinsa zai iya ƙarfafa mu.

KADA KA ƘYALE MATSALOLI SU SA KA SANYIN GWIWA

8. Ta yaya matsalolin yau za su iya shafarmu? Ka ba da misali.

8 Mutane da yawa suna fuskantar bala’i da matsaloli a yau kuma hakan yana sa su sanyin gwiwa. Hakan yana ma shafan Kiristoci da yawa. Wata ’yar’uwa mai suna Lania tana hidimar majagaba tare da maigidanta a ƙasar Ostareliya. Sai ta samu labari cewa tana da ciwon daji na mama. Wannan labarin ya kusan sa ta haukace. Ta ce, “Maganin da nake sha yana sa ni ciwo sosai kuma yana wulakanta ni.” Duk da haka, tana kula da mijinta ma da aka masa fiɗa a ƙashin baya. Mene ne za mu iya yi idan muna fuskantar irin wannan matsalar?

9, 10. (a) Wane dama ne bai kamata mu ba Shaiɗan ba? (b) Ta yaya za mu jimre da wahalar da littafin Ayyukan Manzanni 14:22 ya ambata?

9 Idan muna fuskantar mugun yanayi, ya kamata mu tuna cewa Shaiɗan ne yake neman ya sa mu daina bauta wa Jehobah. Amma dai, bai kamata mu ƙyale shi ya hana mu farin ciki ba. Littafin Misalai 24:10 ya ce: “Idan ka yi suwu cikin ranar ƙunci, ƙarfinka kaɗanna ne.” Ya kamata mu yi bimbini a kan misalan bayin Allah na zamanin dā da muka tattauna ɗazun. Yin hakan zai taimaka mana mu jimre da matsaloli, kuma za mu yi hakan da gaba gaɗi.

10 Ya kuma kamata mu tuna cewa ba za mu iya kawar da dukan matsalolinmu ba. (2 Tim. 3:12) Littafin Ayyukan Manzanni 14:22 ya ce: “Sai ta wurin wahala dayawa za mu shiga mulkin Allah.” Kada ka taɓa ƙyale matsaloli su sa ka sanyin gwiwa. Maimakon haka, ya kamata ka ɗauke su a matsayin damar nuna cewa kana da imani cewa Allah zai taimaka maka.

11. Me ya kamata mu yi idan ba ma son matsalolin rayuwa su sa mu sanyin gwiwa?

11 Ya kamata mu riƙa yin tunani a kan abubuwa masu kyau da suka faru mana. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Zuciya mai-jin daɗi ta kan sa fuska ta yi fara’a: amma ta wurin ɓacin zuciya ruhu ya kan karai.” (Mis. 15:13) Idan muna yawan tunani a kan matsalolin da ba za mu iya canjawa ba, hakan zai sa mu sanyin gwiwa. Muna godiya ga Jehobah domin yana taimaka mana da gaske. A wasu lokatai, muna sanyin gwiwa kuma Jehobah yana ƙarfafa mu a waɗannan lokatan. Yana yin amfani da Littafi Mai Tsarki da ’yan’uwanmu da kuma ruhun mai tsarkinsa don ya ƙarfafa mu. Yin tunani a kan waɗannan abubuwan zai taimaka mana. Kada ku riƙa tunani a kan matsalolinku. Amma ku riƙa iya ƙoƙarinku don jimrewa da kowace matsala kuma ku yi tunani a kan albarkarku.—Mis. 17:22.

12, 13. (a) Mene ne ya taimaki bayin Jehobah su jimre da bala’i? Ka ba da misali. (b) Ta yaya bala’i zai taimaka mana mu san abin da ya fi muhimmanci a rayuwarmu?

12 A kwana kwanan nan, bala’i ya auko wa ƙasashe da yawa. Za mu iya koyan darassi daga jimirin ’yan’uwan da ke waɗannan ƙasashen, ko da hakan bai kasance da sauƙi ba. A watan Fabrairu na 2010, girgizar ƙasa da ambaliyar ruwa sun auko wa ƙasar Chile. Sun halaka gidaje da dukiya da kuma sana’o’in ’yan’uwa da yawa. Duk da haka, sun ci gaba da bauta wa Jehobah. Wani ɗan’uwa mai suna Samuel da bala’in ya ragargaje gidansa ya ce: “Ko da wannan yanayi mai wuya ne sosai, amma ni da matata mun ci gaba da halartar taro da kuma yin wa’azi. Kuma hakan ya sa ba mu yi sanyin gwiwa ba.” Su da sauran ’yan’uwa sun ci gaba da bauta wa Jehobah da ƙwazo.

13 A watan Satumba na 2009, ambaliyar ruwa ta shanye birnin Manila a ƙasar Filifin. Ambaliyar ta halaka dukiya da dama na wani mutum mai wadata sosai. Kuma mutumin ya ce: “Ambaliyar ta shafi kowa kuma ta jawo wa mawadata da talakawa wahala.” Hakan ya tuna mana da shawara mai kyau da Yesu ya ba da: “Kada ku tara wa kanku dukiya a duniya . . . amma ku tara wa kanku dukiya cikin sama, inda asu da tsatsa ba su cinyewa, ɓarayi kuma ba su fasawa su yi sata.” (Mat. 6:19, 20) Ba shi da kyau mu daraja kuɗi da dukiya domin idan mun rasa su za mu yi sanyin gwiwa. Ya kamata bauta wa Jehobah ya zama abu mafi muhimmanci a rayuwarmu domin za mu iya ci gaba da zaman aminin Allah ko da mene ne ya faru mana.—Karanta Ibraniyawa 13:5, 6.

ME YA SA MUKE NUNA GABA GAƊI?

14. Me ya sa ya kamata mu nuna gaba gaɗi?

14 Yesu ya gaya wa almajiransa cewa matsaloli za su yi yawa sa’ad da ya soma sarauta, amma ya ce: “Kada ku firgita.” (Luk 21:9) Muna da dalilan yin gaba gaɗi domin Yesu Kristi wanda shi ne Sarkinmu da kuma Mahaliccinmu Jehobah suna taimaka mana. Bulus ya ƙarfafa Timotawus, ya ce: “Allah ba ya ba mu ruhun tsorata ba; amma na iko da na ƙauna da na horo.”—2 Tim. 1:7.

15. Mene ne wasu bayin Jehobah suka ce da ya nuna cewa sun dogara gare shi, ka bayyana yadda za mu yi koyi da su?

15 Littafi Mai Tsarki ya faɗi abin da wasu bayin Jehobah suka ce game da yadda suka dogara ga Allah. Alal misali, Dauda ya ce: “Ubangiji ƙarfina ne da garkuwata; zuciyata ta dogara gareshi, na sami taimako: domin wannan zuciyata tana murna ƙwarai.” (Zab. 28:7) Manzo Bulus ya ce: “Cikin dukan waɗannan al’amura mun fi gaban masu-nasara ta wurin wanda ya ƙaunace mu.” (Rom. 8:37) Sa’ad da Yesu ya san cewa an kusan kashe shi, sai ya faɗi abin da ya nuna cewa yana dogara ga Allah sosai. Ya ce: “Ba ni kaɗai nake ba, domin Uba na tare da ni.” (Yoh. 16:32, Littafi Mai Tsarki) Mene ne kalmomin waɗannan bayin Allah suka nuna? Dukansu sun nuna cewa suna dogara ga Jehobah sosai. Idan mu ma muna dogara ga Jehobah kamar su, za mu kasance da gaba gaɗi sa’ad da muke fuskantar wahala.—Karanta Zabura 46:1-3.

YADDA ZA MU AMFANA DAGA TAIMAKON ALLAH

16. Me ya sa ya kamata mu riƙa nazarin Littafi Mai Tsarki?

16 Idan muna da gaba gaɗi a matsayin Kiristoci, ba za mu dogara ga kanmu ba, amma za mu dogara ga Jehobah. Za mu iya yin hakan ta wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki. Wata ’yar’uwa da take fama da wani ciwon da ke yawan sa ta baƙin ciki ta faɗi abin da ke taimaka mata: “Ina karanta ayoyin da suke ƙarfafa ni a cikin Littafi Mai Tsarki sau da sau.” Bawan nan mai aminci, mai hikima ya ce mu riƙa Bauta ta Iyali da yamma. Kuna yin hakan kowane mako kuwa? Idan muna nazarin Littafi Mai Tsarki, hakan zai taimaka mana mu kasance da irin ra’ayin wani marubucin zabura wanda ya ce: “Ina ƙaunar shari’arka ba misali! Abin tunawa ne a gareni dukan yini.”—Zab. 119:97.

17. (a) Wane tanadi ne zai taimaka mana mu kasance da gaba gaɗi? (b) Ta yaya wani labari a cikin littattafanmu ya taimaka maka.

17 Jehobah yana yin amfani da littattafai da suke bayyana Littafi Mai Tsarki don ya taimaka mana mu nuna gaba gaɗi. Waɗannan littattafan suna taimaka mana mu dogara ga Jehobah. Alal misali, labarun ’yan’uwa da ke cikin littattafanmu sun taimaka wa mutane da yawa. Akwai wata ’yar’uwa a Asiya da take fama da wani ciwo da ke yawan sa ta baƙin ciki kuma labarin da ta karanta ya ƙarfafa ta. Labarin game da wani ɗan’uwa ne da ke wa’azi a ƙasar waje kuma ya shawo kan irin matsalar da take da ita. Ta ce: “Wannan labarin ya taimaka mini na fahimci matsalata kuma ya sa na kasance da bege.”

18. Me ya sa ya kamata mu riƙa addu’a a kowane lokaci?

18 Addu’a tana iya taimaka mana a duk yanayin da muke ciki. Manzo Bulus ya nuna muhimmancin addu’a. Ya ce: “Kada ku yi alhini cikin kowane abu; amma cikin kowane abu, ta wurin addu’a da roƙo tare da godiya, ku bar roƙe roƙenku su sanu ga Allah. Salama kuwa ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka, za ta tsare zukatanku da tunaninku cikin Kristi Yesu.” (Filib. 4:6, 7) Muna addu’a kuwa kullum domin mu iya jimre wa matsaloli? Wani ɗan’uwa mai suna Alex yana zama a Biritaniya. Yana wani ciwo da ke yawan sa shi baƙin ciki. Ya ce: “Ina nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma addu’a ga Jehobah, kuma hakan yana taimaka mani sosai.”

19. Me ya sa yake da muhimmanci mu halarci taron Kirista?

19 Taro wata hanya ce da Jehobah yake taimaka mana. Wani marubucin zabura ya ce: “Raina yana marmari, har ya yi yaushi domin muradin gidajen Ubangiji.” (Zab. 84:2) Kai ma kana jin hakan? Lani wadda aka ambata ɗazun ta ce halartar taro da kuma tarayya da ’yan’uwa suna da muhimmanci sosai a gareta. Ta kuma ce ta san cewa idan tana son Jehobah ya taimake ta, wajibi ne ta halarci taro.

20. Ta yaya yin wa’azi zai taimaka mana?

20 Muna kuma nuna gaba gaɗi ta wajen yin wa’azi da ƙwazo. (1 Tim. 4:16) Akwai wata ’yar’uwa a ƙasar Ostareliya wadda ta fuskanci matsaloli da yawa a rayuwarta kuma ga abin da ta ce: “Ba na jin daɗin yin wa’azi ko kaɗan, amma wani dattijo ya ce mu je tare. Sai na bi shi. Kuma bayan hakan, na soma jin daɗin yin wa’azi sosai. Babu shakka, Jehobah ne ya taimaka mini.” (Mis. 16:20) Mutane da yawa sun fahimci cewa suna ƙarfafa bangaskiyarsu duk sa’ad da suka ƙarfafa wasu. Hakan yana sa su daina damuwa da matsalolinsu kuma su riƙa tunani game da “mafifitan al’amura.”—Filib. 1:10, 11.

21. Wane tabbaci ne muke da shi sa’ad da muke fuskantar matsaloli?

21 Jehobah ya yi tanadin abubuwa da yawa da za su taimaka mana mu jimre da matsalolinmu. Za mu yi farin ciki sa’ad da muke fuskantar matsaloli idan mun ƙyale Jehobah ya taimaka mana. Za mu kasance da gaba gaɗi sa’ad da muka yi bimbini a kan misalan bayin Allah. Ko da yake matsalolinmu za su ƙaru domin muna zamani na ƙarshe, za mu iya ji kamar Bulus wanda ya ce: “An fyaɗa mu a ƙasa, amma ba a halaka mu ba; domin wannan fa ba mu yi yaushi ba.” (2 Kor. 4:9, 16) Jehobah yana taimaka mana mu kasance da gaba gaɗi don mu jimre da matsalolinmu.—Karanta 2 Korintiyawa 4:17, 18.

[Hasiya]

a An canja wasu sunaye.

[Hotona a shafi na 10]

Ka yi amfani da taimakon da Jehobah yake tanadarwa sa’ad da kake fuskantar matsaloli

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba