Ku Ƙarfafa Aurenku Ta Wajen Tattaunawa Sosai
“Magana a kan kari tana kama da tuntuwa na zinariya cikin kwanduna na azurfa.”—MIS. 25:11.
1. Ta yaya tattaunawa da kyau ya taimaki wasu ma’aurata?
“NA FI son kasancewa tare da matata da kowa,” in ji wani ɗan’uwa a ƙasar Kanada. Wannan ɗan’uwan ya daɗa cewa: “Idan ina farin ciki, ina da wadda za ta taya ni yi, kuma idan ina baƙin ciki ina da wadda za ta sa in jimre.” Wani miji a ƙasar Ostareliya ya ce: “A cikin shekara 11 da muke tare da matata, ba ranar da ke shigewa da ba ma tattaunawa da juna.” Ya ce tattaunawa da kyau ya taimaka musu su amince da juna sosai kuma hakan ya sa aurensu ya yi gam. Wata ’yar’uwa a ƙasar Costa Rica ta ce: “Tattaunawa sosai ya taimaka mana mu yi farin ciki a aurenmu. Hakan ya sa mun kusaci Jehobah, kuma ya kāre mu daga gwaji. Ƙari ga haka, ya sa mu kasance da haɗin kai kuma mu ƙaunaci juna sosai.”
2. Me ya sa zai kasance da wuya ma’aurata su riƙa tattaunawa sosai?
2 Kuna tattaunawa sosai da juna? Hakika, akwai lokacin da tattaunawa zai kasance da wuya, domin dukanku ajizai ne kuma halayenku sun bambanta. (Rom. 3:23) Wataƙila al’adunku da yadda aka rene ku sun bambanta, kuma hakan zai shafi yadda kuke tattaunawa. Waɗannan dalilan ne suka sa wasu manazartan aure masu suna John M. Gottman da Nan Silver suka ce: “Wajibi ne ma’aurata su yi ƙoƙari sosai idan suna son su riƙa tattaunawa sosai kuma su sa aurensu ya kasance na dindindin.”
3. Mene ne ya taimaka wa ma’aurata su ƙarfafa aurensu?
3 Ma’aurata suna bukatar su ƙoƙarta sosai idan suna son su yi farin ciki a aurensu. (M. Wa. 9:9) Alal misali, Ishaƙu da Rifkatu sun ci gaba da ƙaunar juna duk da cewa sun yi shekaru da yawa tare. (Far. 24:67) Ma’aurata da yawa ma a yau sun ci gaba da ƙaunar juna sosai. Mene ne ya taimaka musu? Suna faɗin ra’ayinsu da yadda suke ji cikin bangirma da kuma daraja. Suna nuna halaye kamar su basira da ƙauna da daraja da kuma tawali’u. Yanzu za mu ga yadda waɗannan halayen za su taimaka wa ma’aurata su riƙa tattaunawa sosai.
KU KASANCE DA BASIRA
4, 5. Ta yaya kasancewa da basira zai taimaka wa ma’aurata su fahimci juna sosai? Ka ba da misalai.
4 Misalai 16:20 ta ce: “Wanda ya [kasance da basira] ga magana za ya sami nagarta.” Kalmar Allah ta koya mana yadda za mu kasance da basira da kuma hikima don mu yi farin ciki a aurenmu. (Karanta Misalai 24:3.) Alal misali, littafin Farawa 2:18 ya gaya mana cewa Allah ya halicci tamace ta zama mataimakiyar namiji. Hakan yana nufin cewa namiji da tamace sun bambanta don su taimaka wa juna. Shi ya sa yadda mata suke tattaunawa ya bambanta da maza. Yawancin mata suna son faɗin yadda suke ji, su yi taɗi game da mutane da kuma ƙawayensu. Saboda haka, tattaunawa sosai irin na abokai yana sa mata su san cewa ana ƙaunarsu. Maza da yawa ba sa son faɗin yadda suke ji, amma sun fi son taɗi game da ayyuka da matsaloli da kuma yadda za a magance su. Maza kuma suna son a yi musu ladabi.
5 Wata ’yar’uwa a Biritaniya ta ce, “Mijina yana son ya magance matsaloli nan da nan maimakon ya saurari abin da zan faɗa.” Ta bayyana cewa hakan yakan ɓata mata rai domin tana son ya saurare ta, kuma ya yi ƙoƙari ya fahimci yadda take ji. Wani miji ya ce, “A lokacin da ba mu daɗe da yin aure ba, ina saurin magance duk matsalar matata. Amma, na koyi cewa abin da take bukata shi ne in saurare ta.” (Mis. 18:13; Yaƙ. 1:19) Miji mai basira yakan lura da yadda matarsa take ji kuma ya bi da ita yadda za ta san cewa yana ƙaunarta. Ya nuna mata sarai cewa ra’ayinta da yadda take ji suna da muhimmanci a gare shi. (1 Bit. 3:7) Mata mai basira tana ƙoƙari ta fahimci ra’ayin mijinta. Idan mata da miji suka yi abin da Allah yake bukata a gare su, za su yi farin ciki a aurensu kuma su yi aiki tare don su tsai da shawarwari masu kyau.
6, 7. (a) Ta yaya ƙa’idar da ke cikin littafin Mai-Wa’azi 3:7 za ta taimaka wa ma’aurata su kasance da basira? (b) Ta yaya mata za ta iya nuna fahimi, kuma mene ne miji zai yi?
6 Ya kamata ma’aurata su san cewa akwai “lokacin shuru da lokacin magana.” (M. Wa. 3:1, 7) Wata ’yar’uwa da ta yi aure shekara 10 ta ce: “Da akwai lokacin da ya dace in yi wa mijina magana a kan wasu batutuwa. Idan ya shagala da aiki, nakan ɗan jira. Hakan ya sa muna tattaunawa da juna da kyau.” Sa’ad da mata ta yi magana da kyau kuma “a kan kari,” mijinta zai saurare ta da farin ciki.—Karanta Misalai 25:11.
7 Ya kamata miji ya saurari matarsa kuma ya yi ƙoƙari ya gaya mata yadda yake ji. Wani dattijo mai aure shekara 27 ya ce: “Ina ƙoƙartawa don in gaya wa matata abin da ke cikin zuciyata.” Wani ɗan’uwa da ke da aure shekara 24 ya ce: “Ba na son yin magana game da matsalolina, domin a ganina zan manta da su idan ban yi maganarsu ba. Amma, na fahimci cewa faɗin yadda nake ji ba kasawa ba ce. Sa’ad da nake son in furta yadda nake ji, nakan yi addu’a don in yi amfani da kalmomi da suka dace kuma a hanyar da ya kamata. Sai in numfasa kuma in soma magana.” Yana da muhimmanci ma’aurata su zaɓi lokacin da ya dace don tattaunawa, wataƙila sa’ad da suke bincika nassin yini ko kuma karanta Littafi Mai Tsarki tare.
8. Mene ne zai iya taimaka wa ma’aurata su so kyautata yadda suke tattaunawa?
8 Zai iya yi wa ma’aurata wuya su kyautata yadda suke tattaunawa da juna. Amma, suna bukatar su riƙa yin addu’a kuma su ƙoƙarta wajen kyautata yadda suke tattaunawa. Za su so yin hakan idan suna ƙaunar Jehobah, suna son su faranta masa rai kuma suna daraja aurensu. Wata ’yar’uwa da ke da aure shekara 26 ta ce: “Ni da mijina mun ɗauki ra’ayin Jehobah game da aure da muhimmanci, saboda haka, ba ma tunanin rabuwa da juna. Hakan ne ya sa muke ƙoƙartawa don mu magance matsalolinmu ta wajen tattauna su tare.” Ma’aurata da suke da aminci ga Allah za su sa shi farin ciki kuma zai albarkace su.—Zab. 127:1.
KU CI GABA DA ƘAUNAR JUNA
9, 10. Mene ne ma’aurata za su yi don su daɗa ƙaunar juna?
9 Ƙauna “magamin kamalta” ce, kuma hali ne da ya fi muhimmanci a aure. (Kol. 3:14) Yayin da ma’aurata suke farin ciki da kuma baƙin ciki tare, hakan yana sa su daɗa ƙaunar juna. Suna daɗa kusantar juna kuma suna farin ciki kasancewa tare. Irin wannan ma’aurata ba sa bukatar su yi wa juna abin a-zo-a-gani, kamar yadda ake nunawa a talabijin ko kuma fim. Amma, sukan yi wa juna abubuwa da ba su taka kara ya karye ba, kamar su rungumar juna da yin murmushi da yaba wa juna da kuma taimaka wa juna. Ko kuma su tambayi juna, “yaya aiki yau?” Waɗannan abubuwa suna da muhimmanci a aure. Wasu ma’aurata da suke da aure shekara 19, sun ce suna kira ko kuma aika wa juna saƙo ta waya a kowace rana, “don su san abin da yake faruwa da juna.”
10 Idan mata da miji suna ƙaunar juna, za su ƙoƙarta su san halayen juna sosai. (Filib. 2:4) Hakan zai sa su daɗa ƙaunar juna, ko da yake su ajizai ne. Da shigewar lokaci, ma’aurata za su ci gaba da sanin halayen juna, kuma hakan zai sa su daɗa farin ciki a aurensu. Saboda haka, idan kana da aure, ka tambayi kanka: ‘Na san halayen matata ko mijina sosai kuwa? Na fahimci ra’ayinsa ko nata a kan wasu batutuwa? Shin ina tuna da halayen mijina ko matata da suka sa na ƙaunace shi ko ita da farko?’
KU DARAJA JUNA
11. Me ya sa yake da muhimmanci ga ma’aurata su daraja juna? Ka ba da misali.
11 A wasu lokatai, ko ma’aurata da suka fi farin ciki a aurensu ma suna fuskantar matsaloli. A wani lokaci ra’ayinsu yakan bambanta. Ibrahim da Saratu ba su yarda da ra’ayin juna ba a wasu lokatai. (Far. 21:9-11) Amma, hakan bai sa aurensu ya yi tsami ba. Me ya sa? Domin suna daraja juna. Alal misali, Ibrahim ya ce wa Saratu “ina roƙonki.” (Far. 12:11, 13) Saratu ta yi wa Ibrahim biyayya kuma ta ɗauke shi a matsayin ‘shugabanta.’ (Far. 18:12) Ma’aurata da suke wa juna baƙar magana, suna nuna cewa ba sa daraja juna. (Mis. 12:18) Kuma hakan yana sa aurensu a cikin haɗari.—Karanta Yaƙub 3:7-10, 17, 18.
12. Me ya sa ma’aurata za su ƙoƙarta su riƙa magana da juna cikin alheri nan da nan bayan aure?
12 Nan da nan bayan aure, ya kamata ma’aurata su ƙoƙarta wajen daraja da kuma yi wa juna magana cikin alheri. Yin hakan zai sa su riƙa tattaunawa sosai. Wani miji ya bayyana cewa, a shekara ta farko da suka yi aure, ba su fahimci ra’ayi da halaye da kuma bukatun juna ba. A wasu lokatai, hakan yana sa su baƙin ciki. Amma, sun ƙulla dangantaka ta kud da kud ta wajen kasancewa da basira da kuma fara’a. Ya ce yana da muhimmanci su kasance da tawali’u da haƙuri, kuma su dogara ga Jehobah. Wannan shawara ce mai kyau a gare mu!
KU KASANCE DA TAWALI’U
13. Me ya sa tawali’u yake da muhimmanci sosai don a yi farin ciki a aure?
13 Ma’aurata suna iya tattaunawa cikin alheri da salama idan su “masu-tawali” ne. (1 Bit. 3:8) Wani ɗan’uwa da ke da aure shekara 11 ya ce: “Tawali’u yana sa a magance matsaloli nan da nan, domin mai tawali’u ne yakan ce, ‘yi haƙuri.’” Wani dattijo da yake da aure shekara 20, kuma yana farin ciki a aurensa ya ce, “a wasu lokatai, kalmomin nan ‘Yi haƙuri,’ sun fi ‘Ina ƙaunarki’ muhimmanci.” Ya bayyana yadda addu’a ta taimaka masa da matarsa su kasance da tawali’u. Ya ce, “sa’ad da ni da matata muka yi addu’a tare ga Jehobah, muna tuna cewa mu ajizai ne, kuma muna tuna da alherin da Allah ya yi mana.” Hakan yana taimaka musu su kasance da ra’ayin da ya dace game da kansu da kuma matsalarsu.
14. Ta yaya fahariya take ɓata aure?
14 Fahariya tana sa ya yi wa mata da miji wuya su tattauna kuma su magance matsalolinsu. Mutum mai fahariya ba ya son ya ce ‘Ka yi haƙuri, don Allah ka gafarce ni.’ Maimakon haka, sai ya riƙa ba da hujja don abin da ya yi, ko kuma ya ga laifin wani. Idan aka ɓata wa mai fahariya rai, ba ya ƙoƙartawa ya sasanta da mutum. Yakan yi baƙar magana ko kuma ya ƙi yin magana gabaki ɗaya. (M. Wa. 7:9) Hakika, fahariya illa ce ga aure. Ya dace mu tuna cewa “Allah yana tsayayya da masu-girman kai, amma yana bada alheri ga masu-tawali’u.”—Yaƙ. 4:6.
15. Ta yaya Afisawa 4:26, 27 za ta taimaka wa ma’aurata su magance matsalolinsu?
15 Maimakon ma’aurata su riƙa fahariya, ya kamata su warware matsalolinsu nan da nan. Bulus ya gaya wa Kiristoci: “Kada rana ta faɗi kuna kan fushinku, kada kuwa ku ba Shaiɗan dama.” (Afis. 4:26, 27) Mene ne zai faru idan ma’aurata ba su bi wannan shawarar daga Kalmar Allah ba? Wata ’yar’uwa ta ce: “Sakamakon, shi ne rashin barci daddare!” Ya fi kyau a warware matsalar nan da nan cikin salama. Hakika, ma’aurata suna bukatar su huce kafin su tattauna batun. Ya kamata su yi addu’a ga Jehobah don ya taimaka musu su kasance da tawali’u. Hakan zai sa su mai da hankali don su magance matsalar, maimakon kowannensu ya riƙa kāre kansa.—Karanta Kolosiyawa 3:12, 13.
16. Ta yaya kasancewa da tawali’u zai taimaka wa ma’aurata su riƙa daraja halaye masu kyau da kuma iyawar juna?
16 Tawali’u zai taimaka wa ma’aurata su riƙa daraja halaye masu kyau da kuma iyawar da kowannensu yake da shi. Alal misali, wataƙila mata tana da iyawa ta musamman da ke amfanar iyalin. Miji mai tawali’u ba zai riƙa kishin matarsa ba, amma zai ƙarfafa ta ta ci gaba da yin amfani da iyawarta. Ta yin hakan, zai nuna cewa yana ƙaunarta da kuma daraja ta. (Mis. 31:10, 28; Afis. 5:28, 29) Mata mai tawali’u ba za ta riƙa fahariya ba ko kuma rena mijinta don iyawarta. Ballantana ma, su biyu “nama ɗaya” ne, kuma abin da ya ɓata wa ɗaya rai zai kasance hakan ga ɗayan.—Mat. 19:4, 5.
17. Mene ne zai sa ma’aurata su riƙa farin ciki a aurensu kuma su ɗaukaka Allah?
17 Babu shakka, kuna son aurenku ya kasance kamar na Ibrahim da Saratu ko Ishaƙu da Rifkatu. Kuna son aurenku ya kasance na dindindin kuma ku riƙa farin ciki. Har ila, kuna son aurenku ya daraja Jehobah. Idan haka ne, ku riƙa daraja aure yadda Allah yake yi. Za ku kasance da basira ta wajen karanta Kalmarsa. Ku riƙa daraja iyawar juna don ku ci gaba da ƙaunar juna. (W. Waƙ. 8:6) Ku ƙoƙarta ku kasance da tawali’u, kuma ku daraja juna. Idan kuka yi waɗannan abubuwan, za ku yi farin ciki a aurenku kuma hakan zai faranta wa Jehobah rai. (Mis. 27:11) Wani ɗan’uwa da ke da aure shekara 27 ya ce: “Ban san yadda rayuwata za ta kasance ba tare da matata ba. Muna daɗa ƙaunar juna, domin muna ƙaunar Jehobah kuma muna tattaunawa da juna a kai a kai.”