Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 7/15 pp. 3-8
  • ‘Ka Faɗa Mana, Yaushe Waɗannan Abubuwa Za Su Zama?’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Ka Faɗa Mana, Yaushe Waɗannan Abubuwa Za Su Zama?’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • A WANE LOKACI NE ZA A SOMA ƘUNCI MAI GIRMA?
  • A WANE LOKACI NE YESU ZAI HUKUNTA TUMAKI DA AWAKI?
  • A WANE LOKACI NE YESU ZAI ZO?
  • Mulkin Allah Ya Halaka Maƙiyansa
    Mulkin Allah Yana Sarauta!
  • “Fansarku Ta Kusa”!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Ku Kasance da Aminci a Lokacin Kunci Mai Girma
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Taimaka wa ’Yan’uwan Kristi da Aminci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 7/15 pp. 3-8

‘Ka Faɗa Mana, Yaushe Waɗannan Abubuwa Za Su Zama?’

“Me ne kuma alamar zuwanka da cikar zamani?”—MAT. 24:3.

MECE CE AMSARKA?

  • Wace nasaba ce ke tsakanin cikar annabcin Yesu game da ƙunci mai girma a ƙarni na farko da kuma a nan gaba?

  • Ta yaya almarar tumaki da awaki ta shafi ra’ayinmu game da wa’azi?

  • Wane lokaci ne Yesu yake nufi sa’ad da ya ambata zuwansa a Matta surori na 24 da 25?

1. Kamar manzannin Yesu, mene ne muke ɗokin sani?

YESU ya kusan kammala hidimarsa a duniya, kuma almajiransa suna ɗokin sanin abin da zai faru da su a nan gaba. ’Yan kwanaki kafin ya mutu, almajiransa guda huɗu sun tambaye shi cewa: “Yaushe waɗannan abubuwa za su zama? Me ne kuma alamar zuwanka da cikar zamani?” (Mat. 24:3; Mar. 13:3) Yesu ya yi wani annabci da ke cikin littafin Matta sura 24 da 25 da ya amsa wannan tambayar. A wannan annabcin, Yesu ya ambata abubuwa da yawa da za su faru. Kalamansa suna da muhimmanci a gare mu, da yake mu ma muna so mu san abubuwa da za su faru.

2. (a) Waɗanne abubuwa ne muka daɗa fahimta? (b) Waɗanne tambayoyi uku ne za mu tattauna?

2 Bayin Jehobah sun yi shekaru suna bincike da kuma addu’a don su san ma’anar annabcin Yesu game da kwanaki na ƙarshe. Sun ƙoƙarta don su daɗa fahimtar lokacin da annabcin Yesu zai cika. Amma, a wane lokaci ne za a soma “ƙunci mai-girma”? A wane lokaci ne Yesu zai hukunta “tumaki da awaki”? A wane lokaci ne Yesu zai “zo”? Waɗannan tambayoyin za su taimaka mana mu fahimci annabcin sosai.—Mat. 24:21; 25:31-33.

A WANE LOKACI NE ZA A SOMA ƘUNCI MAI GIRMA?

3. Mene ne muka fahimta a dā game da ƙunci mai girma?

3 A shekarun da suka shige, mun ɗauka cewa an soma ƙunci mai girma a lokacin Yaƙin Duniya na Ɗaya a shekara ta 1914. Mun kuma ɗauka cewa Jehobah ya “gajertar” da yaƙin a shekara ta 1918, don shafaffu da suke da rai a lokacin su samu zarafin yin wa’azi ga dukan al’ummai. (Mat. 24:21, 22) Sa’ad da aka yi wa’azin a ko’ina, sai a halaka Shaiɗan da mulkinsa. Saboda haka, mun ɗauka cewa ƙunci mai girma yana da sassa uku. Za a soma a shekara ta 1914 zuwa 1918, kuma za a dakatar da shi a shekara ta 1918, sa’an nan za a kammala ƙuncin a yaƙin Armageddon.

4. Wane bayani ne ya sa muka daɗa fahimtar annabcin Yesu game da kwanaki na ƙarshe?

4 Amma bayan da muka daɗa yin bincike, sai muka fahimci cewa wani sashe na annabcin Yesu game da kwanaki na ƙarshe zai cika a hanyoyi biyu. (Mat. 24:4-22) Wannan sashen ya cika a ƙarni na farko a yankin Yahudiya, kuma zai cika a nan gaba a duk faɗin duniya. Wannan ƙarin bayanin ya sa mun daɗa fahimtar wasu abubuwa.a

5. (a) Mene ne ya soma faruwa a shekara ta 1914? (b) Wannan mafarin wahala ya yi daidai da wane lokaci ne a ƙarni na farko?

5 Mun kuma fahimci cewa sashe na farko na ƙunci mai girma bai soma a shekara ta 1914 ba. Ta yaya muka sani? Domin Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa za a soma ƙunci mai girma sa’ad da aka kai wa addinin ƙarya hari, ba sa’ad da al’ummai suka soma yaƙi da juna ba. Saboda haka, abubuwan da suka soma faruwa a shekara ta 1914 ba ƙunci mai girma ba ne, amma “mafarin wahala ne.” (Mat. 24:8) Wannan “wahala” ta yi daidai da abin da ya faru a birnin Urushalima da kuma Yahudiya a shekara ta 33 zuwa 66 a zamanin Yesu.

6. Mene ne zai nuna cewa an soma ƙunci mai girma?

6 Mene ne zai nuna cewa an soma ƙunci mai girma? Yesu ya annabta cewa: “Sa’anda fa kun ga ƙyamar lalata, wadda aka ambace ta ta bakin annabi Daniyelu, tana tsaye a cikin tsatsarkan wuri (bari mai-karantawa shi fahimta), sa’annan waɗanda ke cikin Yahudiya su gudu zuwa duwatsu.” (Mat. 24:15, 16) Wannan annabci game da “ƙyamar lalata” da ke “tsaye a cikin tsarkakan wuri” ya cika ne da farko a shekara ta 66, sa’ad da sojojin Roma da ke wakiltar “ƙyamar lalata” suka kai wa birnin Urushalima da haikalinta hari. Yahudawa suna ɗaukan wurin nan da tsarki sosai. Annabcin zai samu cikarsa na biyu sa’ad da “ƙyamar lalata” na zamaninmu, wato Majalisar Ɗinkin Duniya ta kai hari ga Kiristendom, wanda mabiyansa suke ɗauka da tsarki. Za ta kuma kai hari ga sauran addinai. An kwatanta wannan harin a littafin Ru’ya ta Yohanna 17:16-18. Wannan harin ne zai zama somawar ƙunci mai girma.

7. (a) Ta yaya wasu suka “tsira” a ƙarni na farko? (b) Mene ne zai faru a nan gaba?

7 Yesu ya kuma annabta cewa za a “gajertar da waɗannan kwanaki.” Annabcin nan ya cika da farko a shekara ta 66, sa’ad da sojojin Roma suka janye harin. Hakan ya ba shafaffun Kiristoci da ke birnin Urushalima da Yahudiya damar gudu don su “tsira.” (Karanta Matta 24:22; Mal. 3:17) Mene ne zai faru a lokacin ƙunci mai girma? Jehobah zai “gajertar” da harin da Majalisar Ɗinkin Duniya za ta kai wa addinin ƙarya don kada ta halaka bayinsa.

8. (a) Waɗanne abubuwa ne za su faru bayan sashe na farko na ƙunci mai girma? (b) A wane lokaci ne mutum na ƙarshe cikin shafaffu 144,000 zai karɓi ladarsa? (Ka duba ƙarin bayani.)

8 Mene ne zai biyo bayan sashe na farko na ƙunci mai girma? Kalaman Yesu sun nuna cewa akwai wani abu da zai faru kafin yaƙin Armageddon. Me ke nan? An bayyana shi a cikin littafin Ezekiyel 38:14-16 da kuma Matta 24:29-31. (Karanta.)b Bayan haka, sai a soma sashe na ƙarshe na ƙunci mai girma, wato yaƙin Armageddon. Wannan yaƙin ya yi daidai da halakar birnin Urushalima da aka yi a shekara ta 70 a zamaninmu. (Mal. 4:1) Yaƙin Armageddon ne zai kawo ƙarshen wannan ƙunci mai girma da “ba a taɓa yi ba tun farkon duniya.” (Mat. 24:21) Bayan haka, Yesu zai soma sarautarsa ta shekara dubu.

9. Ta yaya annabcin da aka yi game da ƙunci mai girma ya ƙarfafa mu?

9 Ta yaya wannan annabci game da ƙunci mai girma ya ƙarfafa mu? Ya ba mu tabbaci cewa bayin Jehobah a matsayin rukuni za su tsira daga ƙunci mai girma, ko da wace irin wahala ce suka fuskanta. (R. Yoh. 7:9, 14) Mafi muhimmanci ma, muna farin ciki domin Jehobah zai nuna cewa shi ne Maɗaukakin Sarki kuma zai tsarkake sunansa a yaƙin Armageddon.—Zab. 83:18; Ezek. 38:23.

A WANE LOKACI NE YESU ZAI HUKUNTA TUMAKI DA AWAKI?

10. Mene ne muka yi zato a dā game da lokacin da za a hukunta tumaki da awaki?

10 Ka yi la’akari da wani sashe na annabcin Yesu, wato lokacin da za a hukunta tumaki da awaki. (Mat. 25:31-46) A dā, mun yi zato cewa an soma hukunta tumaki da awaki daga shekara ta 1914. Mun kuma kammala cewa awaki su ne waɗanda ba su saurari bishara ba kuma suka mutu kafin ƙunci mai girma, kuma ba su da begen tashin matattu.

11. Me ya sa za a ce ba a soma hukunta mutane a matsayin tumaki da awaki a shekara ta 1914 ba?

11 A Hasumiyar Tsaro ta 1995, an sake yin bayani a kan littafin Matta 25:31 wanda ya ce: “Sa’anda Ɗan mutum za ya zo cikin darajarsa, da dukan mala’iku tare da shi, sa’an nan za ya zauna bisa kursiyin darajarsa.” Babu shakka, Yesu ya zama Sarkin Mulkin Allah a shekara ta 1914, amma bai “zauna bisa kursiyin darajarsa” a matsayin Alƙalin “dukan al’ummai” ba. (Mat. 25:32; gwada Daniyel 7:13.) Duk da haka, almarar da ya bayar game da tumaki da kuma awaki ya kwatanta shi a matsayin Alƙali. (Karanta Matta 25:31-34, 41, 46.) Yesu bai soma hukunta mutane a matsayin tumaki da awaki a shekara ta 1914 ba, domin bai zama Alƙalin dukan al’ummai ba a wannan shekarar.c To, a yaushe ne Yesu zai soma wannan hukuncin?

12. (a) A wane lokaci ne Yesu zai hukunta dukan al’ummai? (b) Waɗanne abubuwa ne aka kwatanta a littafin Matta 24:30, 31 da kuma Matta 25:31-33, 46?

12 A annabcin da Yesu ya yi game da kwanaki na ƙarshe, ya bayyana cewa zai soma hukunci a matsayin Alƙali na dukan al’ummai ne bayan halakar addinan ƙarya. A littafin Matta 24:30, 31 da aka nuna a sakin layi na 8, Yesu ya ambata wasu abubuwa da za su faru a wannan lokacin. Idan ka bincika waɗannan ayoyin, za ka ga cewa abubuwan da Yesu ya ambata sun yi daidai da waɗanda ya yi zancensu a almararsa game da tumaki da kuma awaki. Alal misali, ɗan mutum zai zo cikin darajarsa tare da mala’iku, za a tattara dukan kabilu da al’ummai, kuma waɗanda aka hukunta a matsayin tumaki za su ‘ta da kansu’ domin sun kusan samun “rai na har abada.”d Waɗanda aka hukunta a matsayin awaki “za su yi baƙinciki” domin sun san cewa za a halaka su.—Matt. 25:31-33, 46.

13. (a) A wane lokaci ne Yesu zai ware tumaki daga awaki? (b) Ta yaya sanin hakan zai shafi yadda muke ɗaukan hidimarmu?

13 A taƙaice, mun koyi cewa Yesu zai hukunta mutanen dukan al’ummai a lokacin ƙunci mai girma. A yaƙin Armageddon da zai kawo ƙarshen ƙunci mai girma, za a halaka masu kama da awaki. Ta yaya sanin hakan ya kamata ya shafi hidimarmu? Ya taimaka mana mu san cewa wa’azin da muke yi yana da muhimmanci. Kafin a soma ƙunci mai girma, mutane suna da zarafin canja ra’ayinsu kuma su soma bin matsatsiyar hanya wadda “ta nufa wajen rai.” (Mat. 7:13, 14) A yanzu, mutane suna iya kasancewa da irin halin tumaki ko kuma na awaki. Amma, ya kamata mu tuna cewa a lokacin ƙunci mai girma ne za a hukunta su a matsayin tumaki ko kuma awaki. Saboda haka, ya dace mu ci gaba da ba dukan mutane zarafin saurarar saƙon Mulki.

A WANE LOKACI NE YESU ZAI ZO?

14, 15. A waɗanne ayoyi huɗu ne aka ambata zuwan Kristi a matsayin Alƙali a nan gaba?

14 Shin ƙarin bincike game da annabcin Yesu ya nuna cewa muna bukatar mu gyara fahiminmu a kan lokacin da wasu abubuwa za su faru? Annabcin ya ba da amsar. Bari mu ga yadda ya yi hakan.

15 A cikin annabcin da ke littafin Matta 24:29–25:46, Yesu ya mai da hankali ga abin da zai faru a waɗannan kwanaki na ƙarshe da kuma lokacin ƙunci mai girma. A cikin nassin, Yesu ya ambata ‘zuwansa’ ko bayyanuwarsa sau takwas. Ya ce game da ƙunci mai girma: ‘Za su kuwa ga Ɗan mutum yana zuwa a bisa gizagizai.’ ‘Ba ku sani ba cikin kowace rana Ubangijinku ke zuwa.’ ‘Cikin sa’ar da ba ku sa tsammani ba Ɗan mutum yana zuwa.’ A almarar tumaki da awaki da Yesu ya ba da, ya ce: ‘Ɗan mutum za ya zo cikin darajarsa.’ (Mat. 24:30, 42, 44; 25:31) Kowanne cikin waɗannan ayoyi huɗu suna nuni ne ga zuwan Kristi a nan gaba a matsayin Alƙali. A waɗanne ayoyi huɗu ne kuma Yesu ya ambata zuwansa?

16. A waɗanne nassosi ne kuma aka ambata zuwan Yesu?

16 Yesu ya ce game da bawan nan mai aminci, mai hikima: ‘Wannan bawa mai-albarka ne, wanda ubangijinsa sa’anda ya zo za ya iske shi yana yin haka.’ A cikin almararsa na budurwai goma, Yesu ya ce: ‘Sa’anda suna cikin tafiya garin saye, ango ya zo.’ Sa’ad da yake ba da almarar talanti, Yesu ya ce: ‘Ananan bayan da aka jima, ubangijin waɗannan bayi ya zo.’ A cikin wannan almarar, ubangijin ya ce: ‘Lokacin zuwana fa da zan karɓi abina.’ (Mat. 24:46; 25:10, 19, 27) Waɗannan ayoyin suna magana game da wane lokaci ne na zuwan Yesu?

17. Mene ne muka faɗa a dā game da zuwan Yesu da aka ambata a Matta 24:46?

17 A dā, mun faɗi a cikin littattafanmu cewa waɗannan nassosi huɗu na ƙarshe suna nuni ga zuwan Yesu a shekara ta 1918. Alal misali, ka yi la’akari da kalaman Yesu game da “bawan nan mai aminci, mai hikima.” (Karanta Matta 24:45-47.) Mun fahimci cewa zuwan da aka ambata a aya ta 46 yana nuni ga lokacin da Yesu ya “zo” a shekara ta 1918 don ya bincika yanayin ibadar shafaffu. Mun kuma fahimci cewa a shekara ta 1919 ne aka naɗa bawan nan ya kula da dukan abin da Ubangiji yake da shi. (Mal. 3:1) Amma, ƙarin bincike da aka yi game da annabcin Yesu ya nuna cewa ana bukatar a gyara fahiminmu a kan wasu fannoni na annabcin. Me ya sa?

18. Mene ne muka kammala game da zuwan Yesu bayan mun tattauna annabcinsa baƙi ɗaya?

18 A cikin littafin Matta 24:30, 42, 44, 46, kalmar nan “zuwa” tana nufin sa’ad da Yesu zai zo ya hukunta mutane a lokacin ƙunci mai girma. Kuma kamar yadda muka tattauna a sakin layi na 12, ‘zuwan’ Yesu da aka ambata a Matta 25:31 yana nufin lokacin hukunci a nan gaba. Saboda haka, ya dace a kammala cewa a lokacin ƙunci mai girma da ke zuwa ne Yesu zai zo ya naɗa bawan nan don ya kula da dukan abin da yake da shi, kamar yadda aka ambata a Matta 24:46, 47. Hakika, bincika annabcin Yesu baki ɗaya ya nuna cewa kowanne cikin nassosi takwas da suka ambata zuwansa, yana nufin lokacin da za a hukunta mutane a nan gaba a ƙunci mai girma.

19. Waɗanne gyare-gyare ne muka tattauna, kuma waɗanne tambayoyi ne za a amsa a talifofi na gaba?

19 Mene ne muka koya? A somawar wannan talifin, mun yi tambayoyi uku. Da farko, mun tattauna cewa ba a soma ƙunci mai girma a shekara ta 1914 ba, amma za a soma sa’ad da Majalisar Ɗinkin Duniya ta kai wa Babila Babba hari. Mun kuma tattauna abin da ya sa ba a soma hukunta tumaki ko awaki a shekara ta 1914 ba, amma za a yi hakan a lokacin ƙunci mai girma. A ƙarshe, mun bincika abin da ya sa za a ce Yesu bai zo don ya naɗa bawan nan mai aminci a shekara ta 1919 don ya kula da dukan abin da yake da shi ba, amma zai naɗa shi a lokacin ƙunci mai girma. Saboda haka, dukan waɗannan abubuwa za su faru a nan gaba, wato a lokacin ƙunci mai girma. Ta yaya wannan gyaran ya shafi yadda muka fahimci kwatancin bawan nan mai aminci? Kuma ta yaya ya shafi yadda muka fahimci wasu almara ko kuma kwatanci da Yesu ya yi da suke cikawa a waɗannan kwanaki na ƙarshe? Za mu tattauna waɗannan muhimman tambayoyi a talifofi na gaba.

a Sakin layi na 4: Don ƙarin bayani, ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Satumba, 1994, shafuffuka na 11-22 da kuma ta 1 ga Mayu, 1999, shafuffuka na 14-26.

b Sakin layi na 8: A cikin waɗannan ayoyi, an ambata cewa ana ‘tattara zaɓaɓu.’ (Mat. 24:31) Saboda haka, kamar dai dukan shafaffu da suke duniya bayan sashe na farko na ƙunci mai girma sun tafi sama kafin yaƙin Armageddon. Wannan ya sauya abin da ke cikin talifin nan “Tambayoyi Daga Masu Karatu” a cikin Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Agusta, 1990, shafi na 30 na Turanci.

c Sakin layi na 11: Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Nuwamba, 1995, shafuffuka na 8-24.

d Sakin layi na 12: Ka karanta labarin a Luka 21:28.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba