“Ku Yi Wannan Abin Tunawa Da ni”
“Sa’anda ya yi godiya, ya kakkarya, ya ce, Wannan jikina ne, wanda shi ke dominku: ku yi wannan abin tunawa da ni.”—1 KOR. 11:24.
1, 2. Wane tunani ne wataƙila almajiran Yesu suka yi kafin su tafi Urushalima?
‘YANZU babu gajimare kuma muna iya ganin hilalin wata. Babu shakka, masu tsaro a Urushalima sun ga wannan hilalin watan jiya daddare. Da zarar majalisar Yahudawa suka san da hakan, sai suka sanar cewa an shiga sabon wata, wato watan Nisan. Bayan haka, sai labarin ya yaɗu a ko’ina babu ɓata lokaci, har a garin da manzannin Yesu suke. Babu shakka, Yesu zai so ya tafi Urushalima kafin a yi Idin Ƙetarewan.’
2 Wataƙila tunanin da wasu cikin almajiran Yesu suka yi ke nan kafin su tafi Urushalima a rana ta ƙarshe tare da shi. A lokacin suna Perea, wato garin da ke hayin Kogin Urdun. (Mat. 19:1; 20:17, 29; Mar. 10:1, 32, 46) Da zarar Yahudawan sun gane cewa sun shiga ranar 1 ga Nisan, sai su ƙirga kwanaki 13 bayan wannan ranar kuma su yi Idin Ƙetarewa a faɗuwar rana ta 14 ga Nisan.
3. Me ya sa Kiristoci suke ɗaukan kwanan watan Idin Ƙetarewa da muhimmanci?
3 Kwanan watan Jibin Maraice na Ubangiji da ya yi daidai da na Idin Ƙetarewa, zai faɗa a ranar 14 ga Afrilu, 2014 bayan faɗuwar rana. Wannan rana ce ta musamman ga Kiristoci na gaske da kuma wasu da suke son saƙonmu. Me ya sa? Domin abin da ke littafin 1 Korintiyawa 11:23-25. Ayoyin sun ce: “Yesu a cikin daren da aka bashe shi ya ɗauki gurasa; sa’anda ya yi godiya, ya kakkarya, ya ce, Wannan jikina ne, wanda shi ke dominku: ku yi wannan abin tunawa da ni. Hakanan kuma ya ɗauki ƙoƙon.”
4. (a) Waɗanne tambayoyi ne za mu iya yi wa kanmu game da Tuna da Mutuwar Yesu? (b) Ta yaya muke sanin kwanan watan da za a Tuna da Mutuwar Yesu kowace shekara? (Ka duba akwatin nan “Taron Tuna da Mutuwar Yesu na 2014.”)
4 Yesu ya umurci mabiyansa su riƙa tunawa da mutuwarsa a kowace shekara, kuma wannan ne kaɗai idin da ya ce su riƙa yi. Babu shakka, za ka so ka halarci wannan taron. Kafin lokacin, za ka iya tambayar kanka: ‘Ta yaya zan yi shiri don wannan Idin? Waɗanne abubuwa ne za a yi amfani da su a lokacin? Wane tsari za a bi sa’ad da ake Idin? Me ya sa Idin da kuma abubuwan da za a yi amfani da su a lokacin suke da muhimmanci a gare ni?’
GURASAR DA RUWAN INABIN
5. Wane shiri ne Yesu ya ce almajiransa su yi don Idin Ƙetarewa?
5 A lokacin da Yesu ya gaya wa almajiransa su nemi ɗakin da za su yi Idin Ƙetarewan, bai ce su saka wasu kayan ado masu yawa a ciki ba. Maimakon haka, ya so almajiransa su nemi daki mai tsabta da zai ɗauki dukansu. (Karanta Markus 14:12-16.) Manzannin za su shirya wasu abubuwa kamar su gurasa marar yisti da kuma ruwan inabi don Idin. Bayan Yesu ya gama Idin Ƙetarewan, ya mai da hankali ga abubuwa biyu da za a riƙa amfani da su sa’ad da ake Tuna da Mutuwarsa.
6. (a) Bayan Idin Ƙetarewan, mene ne Yesu ya ce game da gurasar? (b) Wane irin gurasa ake amfani da shi a taron Tuna da Mutuwar Yesu?
6 Manzo Matta ya shaida hakan kuma daga baya ya rubuta cewa: “Yesu ya ɗauki gurasa, ya yi godiya, ya karya; ya ba almajiran, ya ce, Ku karɓa, ku ci.” (Mat. 26:26) ‘Gurasar’ da aka yi amfani da ita tana kama da na Idin Ƙetarewan domin ba ta da yisti. (Fit. 12:8; K. Sha 16:3) Ana yin gurasar da garin alkama da kuma ruwa kuma ba a sa yisti ko gishiri a ciki, saboda haka, gurasar ba ta tashi. Gurasar za ta kasance a bushe don a iya kakkarya ta. A yau kafin ranar Tuna da Mutuwar Yesu, dattawa sukan gaya wa wani ya yi irin wannan gurasar. Za a iya yin ta da garin alkama da ruwa kuma a gasa ta ko a toya ta a kwano mai ɗan māi. Idan babu garin alkama, za a iya yin amfani da garin shinkafa ko dawa ko gero ko masara ko kuma makamantansu.
7. Wane irin ruwan inabi ne Yesu ya yi amfani da shi, kuma wane iri ne muke amfani da shi a yau sa’ad da muke Tunawa da Mutuwar Yesu?
7 Matta ya ci gaba da cewa: “[Yesu] ya ɗauki ƙoƙo, ya yi godiya, ya ba su kuma, ya ce, Dukanku ku sha daga cikinsa.” (Mat. 26:27, 28) Ruwan inabi ne ke cikin moɗar da Yesu ya yi amfani da ita. Ta yaya muka san cewa ba sabon ruwan inabi ba ne aka yi amfani da shi? Domin lokacin da ake girbin inabi ya riga ya wuce da daɗewa. Ba a yi amfani da ruwan inabi ba sa’ad da aka yi Idin Ƙetarewa na farko a ƙasar Masar. Amma Yesu bai ce laifi ba ne a sha shi a lokacin Idin ba. Ya ma yi amfani da ruwan inabi a Jibin Maraice na Ubangiji. Don haka, Kiristoci ma a yau suna yin amfani da ruwan inabi sa’ad da suke taron Tunawa da Mutuwar Yesu. Wane irin ruwan inabi ne ya kamata a yi amfani da shi? Bai kamata a sa wani abu kamar kayan yaji a cikin ruwan inabin da za a yi amfani da shi a taron Tunawa da Mutuwar Yesu ba. Ruwan inabi zalla da aka yi a gida ko kuma na kasuwa ne za a yi amfani da shi, kamar su Beaujolais, Burgundy, ko Chianti.
GURASA DA RUWAN INABI MASU MA’ANA
8. Me ya sa Kiristoci suke ɗaukan abin da gurasar da kuma ruwan inabin suke wakilta da muhimmanci?
8 Akwai wani abin da manzo Bulus ya faɗa da ya nuna cewa wasu Kiristoci ma da ba manzanni ba za su riƙa yin Jibin Maraice na Ubangiji. Bulus ya rubuta wa ’yan’uwan da ke Koranti cewa: “Daga wurin Ubangiji na karɓo wannan da na bayar a gareku, cewa, Ubangiji Yesu . . . ya ɗauki gurasa; sa’anda ya yi godiya, ya kakkarya, ya ce, Wannan jikina ne, wanda shi ke dominku: ku yi wannan abin tunawa da ni.” (1 Kor. 11: 23, 24) Kiristoci suna ɗaukan abin da gurasar da kuma ruwan inabin suke wakilta da muhimmanci, domin an umurce su su riƙa Tunawa da Mutuwar Yesu a kowace shekara.
9. Wane irin ra’ayin ƙarya ne wasu suke da shi game da gurasar da Yesu ya yi amfani da ita?
9 Wasu ’yan coci sun ce “jikina” da Yesu ya ambata ba ya wakiltar wani abu, amma ainihin jikinsa ne. Don haka, sun gaskata cewa wani abin al’ajabi ya faru kuma gurasar ta zama ainihin jikin Yesu. Amma hakan ba gaskiya ba ne.a Me ya sa? Domin Yesu da kansa, wato jikinsa da kuma gurasa marar yisti suna gaban manzanninsa masu aminci sa’ad da suke taron. Hakika, wannan ya nuna cewa furucin Yesu yana wakiltar wani abu, kamar yadda ya yi a wasu lokatai.—Yoh. 2:19-21; 4:13, 14; 10:7; 15:1.
10. Mene ne gurasar da Yesu ya yi amfani da ita a Jibin Maraice na Ubangiji take wakilta?
10 Gurasar da ke gaban manzannin da za su ci ba da jimawa ba tana wakiltar jikin Yesu. Wane jiki ke nan? A dā, bayin Allah sun gaskata cewa gurasar tana wakiltar Kiristoci shafaffu, waɗanda Littafi Mai Tsarki ya ƙira “jikin Kristi.” Sun gaskata da hakan domin Yesu ya kakkarya gurasar kuma sa’ad da aka kashe shi, ba a karya ƙasusuwansa ba. (Afis. 4:12; Rom. 12:4, 5; 1 Kor. 10:16, 17; 12:27) Bayan sun yi bincike sosai, sai suka gano cewa gurasar tana wakiltar jikin Yesu na mutum. Sau da yawa, Nassosi sukan yi magana a kan yadda Yesu ya “sha wuya a jiki,” kuma aka kashe shi. Saboda haka, sa’ad da ake Jibin Maraice na Ubangiji, gurasar tana wakiltar jikin Yesu da “ya ɗauki zunubanmu.”—1 Bit. 2:21-24; 4:1; Yoh. 19:33-36; Ibran. 10:5-7.
11, 12. (a) Mene ne Yesu ya ce game da ruwan inabin? (b) Mene ne ruwan inabin da ake yin amfani da shi a Jibin Maraice na Ubangiji yake wakilta?
11 Sanin abin da gurasar take wakilta ta taimaka mana mu san abin da Yesu ya ce game da ruwan inabin. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Hakanan kuma ya ɗauki ƙoƙon bayan jibi, ya ce, Wannan ƙoƙo sabon alkawari ne cikin jinina.” (1 Kor. 11:25) Shin ƙoƙon da Yesu ya riƙe ne sabon alkawarin? A’a. Kalmar nan “ƙoƙo” tana nufin abin da ke ciki, wato ruwan inabin. Mene ne Yesu ya ce ruwan inabin yake nufi ko wakilta? Yana wakiltar jininsa da zai zubar dominmu.
12 A cikin Linjilar Markus, Yesu ya ce: “Wannan jinina ne na alkawari, wanda an zubar domin mutane dayawa.” (Mar. 14:24) Hakika, Yesu zai zubar da jininsa “domin mutane dayawa zuwa gafarar zunubai.” (Mat. 26:28) Saboda haka, ruwan inabin yana wakiltar ainihin jinin Yesu. Wannan jinin ne zai sa ya yiwu a gafarta “laifofinmu.”—Karanta Afisawa 1:7.
YIN IDIN TUNA DA MUTUWAR KRISTI
13. Yaya ake gudanar da taron Tunawa da Mutuwar Yesu?
13 Idan yanzu ne lokaci na farko da kake so ka halarci taron Tunawa da Mutuwar Yesu tare da Shaidun Jehobah, mene ne za ka yi zaton gani? Za a yi wannan taron a wuri mai kyau da kuma tsabta, domin kowane mutum da ya halarci taron ya zauna babu wata matsala kuma ya ji daɗin taron. Ko da yake za a iya saka ’yan furanni a wurin, amma ba za a saka su da yawa ba har su janye hankalinka ko kuma wurin ya yi kamar inda ake fati. Dattijon da ya ƙware ne zai yi jawabi mai kyau a kan abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Tunawa da Mutuwar Yesu. Zai bayyana mana abin da Kristi ya yi don mu sami ceto. (Karanta Romawa 5:8-10.) Mai jawabin zai tattauna game da bege guda biyu da aka bayyana a Littafi Mai Tsarki.
14. Sa’ad da ake jawabin Tunawa da Mutuwar Yesu, waɗanne bege biyu ne ake tattaunawa?
14 Bege na farko shi ne yin rayuwa tare da Kristi a sama kuma waɗanda suke da wannan begen ƙalilan Kiristoci ne, kamar su manzannin Yesu masu aminci. (Luk 12:32; 22:19, 20; R. Yoh. 14:1) Bege na biyu shi ne wanda yawancin Kiristoci masu aminci a yau za su mora. Za su sami gatan yin rayuwa a aljanna a duniya har abada. Sa’an nan za a amsa addu’ar da Kiristoci suka daɗe suna yi cewa a yi nufin Allah a duniya kamar yadda ake yi a sama. (Mat. 6:10) Littafi Mai Tsarki ya kwatanta irin rayuwa mai daɗi da za su more har abada.—Isha. 11:6-9; 35:5, 6; 65:21-23.
15, 16. Mene ne ake yi da gurasar sa’ad da ake Jibin Maraice na Ubangiji?
15 Bayan mai jawabin ya tattauna bege biyun, sai ya gaya wa masu sauraro cewa lokaci ya yi da za a yi daidai abin da Yesu ya yi a Jibin Maraice na Ubangiji. Kamar yadda aka ambata a baya, za a yi amfani da isharori guda biyu, wato gurasa marar yisti da kuma ruwan inabi. Za a iya ajiye waɗannan abubuwa biyu a kan teburi kusa da mai jawabin. Mai jawabin zai karanta Littafi Mai Tsarki don ya bayyana abin da Yesu ya yi da gurasar. Zai iya karanta littafin Matta, inda ya ce: “Yesu ya ɗauki gurasa, ya yi godiya, ya karya; ya ba almajiran, ya ce, Ku karɓa, ku ci; wannan jikina ne.” (Mat. 26:26) Yesu ya kakkarya gurasar don ya iya rarraba wa manzanninsa da suke hannun dama da kuma hagunsa. Sa’ad da ka halarci taron Tunawa da Mutuwar Yesu a ranar 14 ga Afrilu, za ka ga gurasa marar yisti a cikin ƙananan farantai.
16 Wani ɗan’uwa zai yi gajeriyar addu’a, kafin a soma zagayawa da farantan. Za a yi amfani da farantai da yawa don ’yan’uwan da za su zagaya da shi su iya yin hakan da wuri kuma bisa ƙa’ida. Ba a bin wata al’ada sa’ad da ake yin hakan kuma ana yinsa daidai da yanayin yankin. ’Yan’uwa ƙalilan (ko wataƙila babu waɗanda) za su ci gurasar kamar yadda ya faru a ikilisiyoyi da yawa a shekara ta 2013 sa’ad da aka zagaya da ita.
17. Ta yaya ake bin ja-gorar Yesu sa’ad da ake Tunawa da Mutuwar Yesu?
17 Bayan haka, mai jawabin zai karanta abin da Yesu ya yi da ruwan inabin: “[Yesu] ya ɗauki ƙoƙo, ya yi godiya, ya ba su kuma, ya ce, Dukanku ku sha daga cikinsa; gama wannan jinina ne na alkawari, wanda an zubar domin mutane dayawa zuwa gafarar zunubai.” (Mat. 26:27, 28) Za a sake yin addu’a, sa’an nan za a zagaya da ruwan inabin ga dukan waɗanda suka halarci taron, daidai yadda Yesu ya ce a yi.
18. Me ya sa yake da muhimmanci mu halarci taron, ko da babu ko kuma mutane ƙalilan ne suke cin gurasar da kuma shan ruwan inabin?
18 Waɗanda za su yi sarauta tare da Yesu a sama ne kaɗai za su iya cin gurasar kuma su sha ruwan inabin. Yawancin mutanen da za su halarci taron ba za su ci gurasar kuma su sha ruwan inabin ba, amma za su miƙa su ga na gaba da su ne kawai. (Karanta Luka 22:28-30; 2 Tim. 4:18) Yana da muhimmanci Kiristoci su halarci wannan taron ko da yake ba za su ci gurasar ko kuma sha ruwan inabin ba. Me ya sa? Domin halartan wannan taron yana nuna cewa suna ɗaukan hadayar da Yesu ya yi da muhimmanci. A lokacin Tunawa da Mutuwar Yesu, Kiristoci suna yin tunani a kan albarkar da za su samu don fansar Yesu. Alal misali, suna da begen kasancewa cikin “taro mai-girma” da za su tsira wa “babban tsananin.” Waɗanda suka ba da gaskiya su ne waɗanda suka “wanke rigunansu, suka faranta su cikin jinin Ɗan ragon.”—R. Yoh. 7:9, 14-17.
19. Mene ne za ka yi don ka shirya da kuma amfana daga Jibin Maraice na Ubangiji?
19 Shaidun Jehobah a dukan duniya suna yin shiri don wannan taro na musamman. Makonni da yawa kafin a yi taron, muna gayyatar mutane da yawa su halarta. Ƙari ga haka, ’yan kwanaki kafin taron, yawancinmu muna karanta wasu surorin Littafi Mai Tsarki da suka yi magana game da abubuwan da Yesu ya yi da kuma abubuwan da suka auku kafin su yi Jibin Maraice na Ubangiji a shekara ta 33 a zamaninmu. Muna tsara ayyukanmu da kyau kafin wannan taron, don mu iya halarta. Zai dace mu zo inda za a yi taron kafin a yi waƙa da addu’a don mu iya yi marabtar baƙin da za su zo kuma don mu ji dukan abin da za a faɗa a wurin. Dukan ’yan’uwa da baƙin da suka halarta za su amfana idan suka bi jawabin da nasu Littafi Mai Tsarki yayin da ake karanta da kuma bayyana shi. Abu mafi muhimmanci shi ne, halartan wannan taron zai nuna cewa muna godiya ga hadayar da Yesu ya yi kuma muna bin wannan umurnin da ya bayar cewa: “Ku yi wannan abin tunawa da ni.”—1 Kor. 11:24.
a Wani masani ɗan Jamus mai suna Heinrich Meyer ya ce, ba yadda zai yiwu manzannin Yesu su yi tunanin cewa suna cin ainihin jikin Yesu kuma suna shan jininsa, “domin bai mutu ba tukun (yana da rai).” Ya daɗa cewa Yesu ya yi amfani da “kalamai masu sauƙi” don ya bayyana wa manzanninsa abin da gurasar da kuma ruwan inabin suke nufi kuma zai so su fahimce shi sosai.