Jehobah Ne Babban Amininmu
“Aka ce da [Ibrahim] kuma abokin Allah.”—YAƘ. 2:23.
1. Mene ne muke iya yi da yake an halicce mu cikin surar Allah?
BAREWA ba ta gudu, ɗanta ya yi rarrafe. Hakika, wasu yara da yawa sun yi kama da iyayensu. Babu shakka, kowane yaro yana da wasu abubuwa da ya gāda daga babansa da mamarsa. Jehobah, Ubanmu na sama shi ne ya halicci dukan abubuwa masu rai. (Zab. 36:9) Mun yi kama da shi a wasu hanyoyi da yake mu ’ya’yansa ne. Tun da Allah ya halicce mu cikin ‘surarsa’ muna iya yin tunani da yanke shawara da kuma ƙulla abota da mutane.—Far. 1:26.
2. Me ya sa za mu iya ƙulla abota da Jehobah?
2 Jehobah zai iya zama babban Amininmu. Za mu iya ƙulla abota da shi don yana ƙaunarmu kuma mu muna ba da gaskiya gare shi da kuma Ɗansa. Yesu ya ce: “Allah ya yi ƙaunar duniya har ya ba da Ɗansa, haifaffe shi kaɗai, domin dukan wanda yana ba da gaskiya gare shi kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada.” (Yoh. 3:16) Mutane da yawa sun ƙulla abota da Jehobah. Bari mu bincika wasu cikinsu.
“IBRAHIM AMININA”
3, 4. Me ya sa abotar Ibrahim da Allah ya bambanta da wadda Isra’ilawa suka ƙulla da Allah?
3 Jehobah ya kira Uban Isra’ilawa, wato Ibrahim “aminina.” (Isha. 41:8) Har ila, littafin 2 Labarbaru 20:7 ya kira Ibrahim abokin Allah. Me ya sa Ibrahim ya iya ƙulla abota da Mahalicci? Domin yana da bangaskiya sosai ga Allah.—Far. 15:6; karanta Yaƙub 2:21-23.
4 Jehobah ya taɓa ƙulla abokantaka da ’ya’yan Ibrahim da suka zama al’ummar Isra’ila har ma ya zama Uba a gare su. Abin baƙin ciki shi ne, ba su ci gaba da kasancewa abokan Jehobah ba. Me ya sa? Domin sun daina ba da gaskiya ga alkawuran da Jehobah ya yi musu.
5, 6. (a) Ta yaya Jehobah ya zama abokinka? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu yi wa kanmu?
5 Idan ka ci gaba da koyo game da Jehobah, za ka kasance da bangaskiya sosai a gare shi kuma za ka ƙaunace shi. Ka yi tunanin lokacin da ka soma koya cewa Jehobah Allah ne da za ka iya ƙulla abota da shi. Ka kuma koyi cewa an haifi dukanmu cikin zunubi domin rashin biyayyar Adamu. Har ila, ka ƙara koya cewa ’yan Adam ba su da dangantaka mai kyau da Allah. (Kol. 1:21) Daɗin daɗawa, ka koya cewa Ubanmu na sama ba ya nisanta kansa daga mutane. Sa’ad da muka koya cewa Jehobah ya ba da Ɗansa hadaya, sai muka soma ba da gaskiya gare shi kuma muka ƙulla abota da shi.
6 Idan muka tuna da yadda muka koyi gaskiya game da Jehobah, za mu iya tambayar kanmu: ‘Ina ci gaba da wannan abota da na ƙulla da Allah kuwa? Shin ina dogara ga Jehobah sosai kuma ina ci gaba da ƙaunar babban Aminina kowace rana kuwa?’ Wani kuma da ya taɓa ƙulla abota da Jehobah shi ne Gideon. Bari mu bincika labarinsa don mu ga yadda za mu bi misalinsa.
JEHOBAH ALLAH MAI SALAMA NE
7-9. (a) Wane abu mai ban al’ajabi ne ya faru da Gideon, kuma da wane sakamako? (Ka duba hoton da ke shafi na 21.) (b) Ta yaya za mu zama aminan Jehobah?
7 Alƙali Gideon ya bauta wa Jehobah a mawuyacin zamani bayan da Isra’ilawa suka shiga Ƙasar Alkawari. Littafin Alƙalawa sura 6 ya ce mala’ikan Jehobah ya ziyarci Gideon a wani wuri da ake kira Ophrah. A lokacin, Midiyanawa sun yi ta yi wa Isra’ilawa barazana sosai. Saboda haka, Gideon yana sussukan alkama a wurin da ake matsa ruwan anab a maimakon ya yi a fili don kada mutane su gan shi. Gideon ya yi mamaki sosai sa’ad da mala’ika ya bayyana a gare shi kuma ya kira shi “jarumi.” Ko da yake Jehobah ya ceci Isra’ilawa a ƙasar Masar, amma Gideon ya yi shakka ko Jehobah zai sake cetonsu a wannan lokacin. Mala’ikan ya yi magana a madadin Jehobah kuma ya tabbatar wa Gideon cewa Allah zai taimake shi.
8 Gideon ya ga kamar ba zai yiwu ya “ceci Isra’ila daga hannun Midian” ba. Jehobah ya ba shi amsa kai tsaye cewa: “Hakika ina tare da kai, za ka kuwa buga Midianawa, sai ka ce mutum ɗaya ne.” (Alƙa. 6:11-16) Babu shakka, wataƙila Gideon ya so Allah ya ba shi alamar da za ta tabbatar masa cewa zai yi nasara. Kuma a wannan tattaunawar, Gideon bai yi shakkar wanzuwar Allah ba.
9 Mene ne ya faru da ya ƙarfafa bangaskiyar Gideon kuma ya sa ya kusaci Allah? Gideon ya dafa wa mala’ikan abinci. Sa’ad da Gideon ya lura cewa mala’ikan ya sa wuta ta fito daga sandar da ke hannunsa kuma ta ƙona abincin, sai ya gane cewa lallai Jehobah ne ya aiko mala’ikan. Gideon ya ce: “Kaitona, Ya Ubangiji Yahweh! gama na ga mala’ikan Ubangiji fuska da fuska.” (Alƙa. 6:17-22) Shin wannan abin da ya faru ya ɓata dangantakar da ke tsakanin Gideon da Allah ne? Ko kaɗan! Amma dangantakar da ke tsakaninsu ta daɗa danƙo. Ta yaya muka san hakan? Gideon ya kira bagadin da ya gina “Jehovah-shalom,” wato “Jehobah salama ne.” (Karanta Alƙalawa 6:23, 24.) Idan muka yi bimbini a kan abubuwan da Jehobah yake mana kowace rana, za mu fahimci cewa Shi babban Amininmu ne. Yin addu’a ga Allah yana sa mu daɗa kasance da salama da shi kuma dangantakarmu da shi ta daɗa danƙo.
‘WA ZA YA SAUKA CIKIN TENTIN JEHOBAH’
10. Mene ne littafin Zabura 15:3, 5 ya ce Jehobah yake so mu yi idan muna so mu zama aminansa?
10 Akwai wasu abubuwan da Jehobah yake so mu yi idan muna son mu zama aminansa. A littafin Zabura ta 15, Dauda ya faɗi abin da ya kamata mu yi idan muna son mu ‘sauka cikin tentin’ Allah, wato mu zama aminansa. (Zab. 15:1) Bari mu tattauna abubuwa biyu cikinsu: yin gaskiya a ko yaushe da kuma ƙin yin gulma. Dauda ya yi furuci game da waɗanda Jehobah yake so su zama aminansa cewa: “Shi wanda ba ya yin tsegumi da harshensa, . . . Ba shi karɓan toshi domin shi kāda marar-laifi ba.”—Zab. 15:3, 5.
11. Me ya sa ya kamata mu ƙi yin tsegumi?
11 A wata zabura, Dauda ya yi wannan gargaɗin: “Ka kiyayar da harshenka ga barin mugunta.” (Zab. 34:13) Idan muka ƙi bin wannan gargaɗin, za mu iya ɓata dangantakarmu da Ubanmu na sama. Babu shakka, tsegumi ɗaya ne cikin halayen babban magabcin Allah, wato Shaiɗan. An ɗauko kalmar nan Iblis daga Helenanci kuma tana nufin “mai tsegumi.” Mai da hankali da yadda muke yi wa mutane magana da irin abubuwan da muke faɗa game da su, zai taimaka mana mu kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah. Ƙari ga haka, ya kamata mu mai da hankali sosai da yadda muke ɗaukan waɗanda Jehobah ya naɗa su ja-goranci ikilisiya.—Karanta Ibraniyawa 13:17; Yahuda 8.
12, 13. (a) Me ya sa ya kamata mu riƙa yin gaskiya a ko yaushe? (b) Mene ne sakamako yin gaskiya?
12 An san bayin Allah da yin gaskiya. Manzo Bulus ya ce: “Ku yi addu’a dominmu: gama mun kawar da shakka muna da kyakkyawan lamiri, muna so mu yi tasarrufin kirki cikin dukan abu.” (Ibran. 13:18) Da yake mun ƙudura cewa muna so mu yi gaskiya “cikin dukan abu,” zai dace mu daina cutar ’yan’uwanmu Kiristoci. Alal misali, idan suna mana aiki, ya kamata mu nuna musu halin kirki kuma mu ba su kuɗin da muka yi alkawarin biyansu. Da yake mu Kiristoci ne, zai dace mu bi da kowa cikin gaskiya. Idan muna aiki a ƙarƙashin wani ɗan’uwa, zai dace mu nuna masa hali mai kyau kuma kada mu ɗauka cewa ya kamata ya ɗauke mu da muhimmanci fiye da sauran ma’aikatan.
13 Mutanen duniya suna yawan yabon Shaidun Jehobah don yin gaskiya. Alal misali, darektan wani babban kamfanin gini ya lura da yadda Shaidun Jehobah suke yin gaskiya kuma ya ce: “A kullum kuna cika alkawari.” (Zab. 15:4) Irin wannan halin yana sa mu ci gaba da kasancewa aminan Jehobah. Ƙari ga haka, yana kawo yabo ga Ubanmu mai ƙauna da ke sama.
KA TAIMAKI MUTANE SU ZAMA AMINAN JEHOBAH
14, 15. Ta yaya za mu iya taimaka wa mutane su zama aminan Allah sa’ad da muke wa’azi?
14 Ko da yake mutanen da muke musu wa’azi za su iya cewa sun gaskata akwai Allah, amma da yawa cikinsu ba sa ɗaukansa a matsayin babban Amininsu. Ta yaya za mu iya taimaka musu? Ka yi la’akari da umurnan da Yesu ya ba almajiransa 70 sa’ad da ya tura su biyu-biyu yin wa’azi. Ya ce musu: “Kowane gidan da kuka shiga ciki kuma, sai ku fara cewa, Salama ga wannan gida. Idan ɗan salama yana nan, salamarku za ta zama a kansa: in ba shi, sai ta komo muku kuma.” (Luk 10:5, 6) Mutane za su iya soma bauta wa Jehobah idan muka yi musu wa’azi da fara’a. Idan muka yi haƙuri sa’ad da magabta suka ba’ance mu, hakan zai sa su daina ba’ar kuma idan muka dawo wata rana za su saurari saƙon.
15 Sa’ad da muka haɗu da mutanen da suka shaƙu da addinin ƙarya ko kuma al’adun ƙarya, zai dace mu ci gaba da yi musu fara’a. Muna gayyatar kowa zuwa taronmu, musamman ma mutanen da suka gaji da yanayin wannan muguwar duniya kuma suke so su ƙara koyo game da Allah. Jerin talifofin nan “Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane” suna ɗauke da misalai masu kyau na irin waɗannan mutanen.
YIN AIKI TARE DA BABBAN AMININMU
16. Ta yaya za mu zama aminan Jehobah da kuma ‘abokan aikinsa’?
16 Mutanen da suke aiki tare suna yawan zama abokai. Duka waɗanda suka yi baftisma suna da gatan zama “abokan aiki” da kuma aminan Allah. (Karanta 1 Korintiyawa 3:9.) Hakika, yayin da muke yin aikin wa’azi da kuma almajirtarwa, mukan koyi abubuwa da yawa game da halayen Ubanmu na sama. Muna ganin yadda ruhu mai tsarkinsa yake taimakonmu mu yi wa’azin bishara.
17. Ta yaya taron gunduma da sauran manyan taron suke nuna mana cewa Jehobah babban Amininmu ne?
17 Yin wa’azi da ƙwazo zai sa mu kusaci Jehobah sosai. Alal misali, muna ganin yadda ƙoƙarce-ƙoƙarcen da magabta suke yi don su hana yin wa’azi yake cin tura domin Jehobah yana taimakonmu. Ka yi tunanin ’yan shekarun baya zuwa yanzu. Shin ba ka ganin yadda Allah yake kāre mu? Muna ganin yadda yake tanadar mana da koyarwarsa da ke kama da abinci, kuma hakan yana sa mu farin ciki. Sa’ad da muka halarci taron gunduma da sauran manyan taro, muna ganin yadda Jehobah yake sa a tattauna abubuwan da suke ci mana tuwo a ƙwarya da kuma yadda za mu magance su. Bayan wata iyali ta halarci taron gunduma, sai ta rubuta cewa: “Mun ji daɗin wannan taron sosai. Mun ga yadda Jehobah yake ƙaunar kowanenmu da kuma yadda yake so mu yi nasara.” Bayan da wasu ma’aurata suka halarci wani taron gunduma na musamman a ƙasar Ireland, sun faɗa cewa an karɓe su da hannu bibbiyu kuma an kula da su, sun daɗa da cewa: “Amma matuƙar godiyarmu ga Jehobah da kuma Sarkinsa Yesu Kristi ne. Su suka gayyace mu zuwa wannan ƙungiya mai haɗin kai. Ba kawai muna faɗin haɗin kai a baƙa ba ne, amma muna moransa kowace rana. Abubuwan da muka shaida a wannan taro na musamman a birnin Dublin yana tuna mana da gata mai kyau da muke da shi na yin bauta tare da dukanku.”
AMINAI SUKAN TATTAUNA DA JUNA
18. Me ya kamata mu tambayi kanmu game da yadda muke tattaunawa da Jehobah?
18 Dangantakar abokai takan daɗa danƙo idan suna sadawa da juna sosai. Sadarwa ta Intane da kuma aika saƙon tes sun zama ruwan dare a zamaninmu. Amma, ta yaya za mu kwatanta hakan da tattaunawa da babban Amininmu, Jehobah? Hakika, Jehobah “mai-jin addu’a” ne. (Zab. 65:2) Amma sau nawa ne muke neman lokaci don mu tattauna da shi?
19. Idan yana mana wuya mu bayyana wa Jehobah ainihin abin da ke damunmu a addu’a, mene ne zai taimaka mana?
19 Wasu bayin Jehobah suna jinkirin faɗa wa Jehobah ainihin abin da yake damunsu. Amma Jehobah yana son mu bayyana masa ra’ayinmu sa’ad da muke addu’a. (Zab. 119:145; Mak. 3:41) Idan yana mana wuya mu bayyana ainihin abin da yake damunmu, akwai abin da zai taimaka mana. Mene ne ke nan? Manzo Bulus ya ce: “Gama ba mu san yadda za mu yi addu’a kamar da ya kamata ba; amma Ruhu da kansa yana roƙo dominmu da nishenishe waɗanda ba su furtuwa; shi kuma wanda yake binciken zukata ya san ko menene nufin Ruhu, domin yana yin roƙo sabili da tsarkaka bisa ga nufin Allah.” (Rom. 8:26, 27) Idan muka karanta littattafai kamar su Ayuba da Zabura da kuma Misalai, za mu iya samun wasu abubuwan da za su taimaka mana mu iya bayyana wa Allah ainihin abin da ke damunmu.
20, 21. Wane ƙarfafa ne muke samu daga kalaman Bulus da ke Filibiyawa 4:6, 7?
20 Sa’ad da muke fuskantar wasu yanayoyi masu wuya, zai dace mu tuna da abin da Bulus ya rubuta wa Filibiyawa cewa: “Kada ku yi alhini cikin kowane abu; amma cikin kowane abu, ta wurin addu’a da roƙo tare da godiya, ku bar roƙe roƙenku su sanu ga Allah.” Idan muka yi addu’a ga Jehobah a wannan hanyar, za mu sami ƙarfafa. Bulus ya daɗa cewa: “Salama kuwa ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka, za ta tsare zukatanku da tunaninku cikin Kristi Yesu.” (Filib. 4:6, 7) Zai dace mu riƙa godiya don ‘Salama ta Allah’ da take tsare zukatanmu da kuma tunaninmu.
21 Yin addu’a zai taimaka mana mu ƙulla abota da Jehobah. Saboda haka, bari mu riƙa yin “addua ba fasawa.” (1 Tas. 5:17) Bari wannan talifin da muka nazarta ya sa mu riƙa ƙarfafa dangantakarmu da Allah kuma mu riƙa bin dokokinsa. Kuma bari mu riƙa yin tunani a kan albarka da yawa da muke morewa don Jehobah ainihi Ubanmu ne da Allahnmu da kuma Amininmu.