ABIN DA KE SHAFIN FARKO
Zai Dace Ka Yi Addu’a Kuwa?
‘Tun da yake Allah ya san kome har da tunanina da kuma bukatuna, ina amfanin yin addu’a?’ Wataƙila ka taɓa yin wannan tambayar, kuma hakan ba laifi ba ne. Yesu Kristi ma ya ce Allah “ya san abin da ku ke bukata, tun ba ku roƙe shi ba.” (Matta 6:8) Dauda sarkin Isra’ila ta dā ya fahimci hakan, shi ya sa ya ce: “Gama babu wata magana da ke bakina, sai dai, ka san ta duk, ya Ubangiji.” (Zabura 139:4) To idan haka ne, me ya sa muke bukatar yin addu’a? Domin mu amsa wannan tambayar, zai dace mu tattauna abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da addu’a.a
“Ku kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gare ku.” —Yaƙub 4:8
ADDU’A TANA SA MU KUSACI ALLAH
Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobahb ya san kome, amma shi ba kamar kwamfuta da ke adana bayanai game da mutane kawai ba tare da sanin mutanen ba. (Zabura 139:6; Romawa 11:33) Akasin haka, Jehobah ya san bayinsa ciki da waje kuma yana damuwa da abubuwan da ke damunsu domin yana so su kusace shi. (Zabura 139:23, 24; Yaƙub 4:8) Saboda haka, Yesu ya ƙarfafa mabiyansa su yi addu’a duk da cewa Ubansa ya san bukatunsu. (Matta 6:6-8) Yayin da muke ci gaba da gaya wa Mahaliccinmu abubuwan da ke zuciyarmu, za mu daɗa kusantarsa.
A wasu lokatai, zai yi wuya mu san ainihin abin da ya kamata mu yi addu’a a kai. Idan hakan ya faru, mu tuna cewa Allah ya san yanayinmu kuma zai iya biyan bukatunmu duk da cewa ba mu iya mun furta su ba. (Romawa 8:26, 27; Afisawa 3:20) A duk lokacin da muka fahimci cewa Jehobah ya taimaka mana, ko da a ƙananan hanyoyi ne, hakan zai sa mu kusace shi.
KOWACE IRIN ADDU’A CE ALLAH YAKE JI?
Littafi Mai Tsarki ya ba mu tabbaci cewa Allah Mai Iko Duka yana jin addu’o’in bayinsa masu aminci, amma ya kuma bayyana mana dalilan da suka sa ba ya jin wasu addu’o’i. Alal misali, a lokacin da mugunta ta zama gama-gari a ƙasar Isra’ila ta dā, Allah ya umurci annabinsa Ishaya ya gaya wa mutanen cewa: “Sa’anda ku ke yi mini yawan addu’o’i, ba ni ji ba: hannuwanku cike su ke da jini.” (Ishaya 1:15) Hakika, Allah ba zai amsa addu’o’in waɗanda ba sa bin dokokinsa ko kuma waɗanda suke addu’a da mugun nufi ba.—Misalai 28:9; Yaƙub 4:3, Littafi Mai Tsarki.
Akasin haka, Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Idan mun roƙi kome daidai da nufinsa, yana jinmu.’ (1 Yohanna 5:14) Shin hakan yana nufin Allah zai ba bayinsa kome da suka roƙa ne? A’a. Ka yi la’akari da misalin manzo Bulus wanda ya roƙi Allah har sau uku ya kawar masa da wani ‘masuki cikin jikinsa.’ (2 Korintiyawa 12:7, 8) Mai yiwuwa Bulus yana fama da wata mummunar ciwon ido ne, kuma babu shakka hakan ya sa shi baƙin ciki sosai. Allah ya ba Bulus baiwar yin mu’ujiza har ma ya taɓa ta da wani daga mutuwa, amma ga shi yana fama da ciwo. (Ayyukan Manzanni 19:11, 12; 20:9, 10) Bulus ya yi farin ciki don yadda Allah ya amsa addu’arsa, duk da cewa Allah bai yi hakan a hanyar da yake so ba.—2 Korintiyawa 12:9, 10.
‘Gaba gaɗi ke nan da mu ke yi a gabansa, idan mun roƙi komi daidai da nufinsa, yana jinmu.’ —1 Yohanna 5:14
Babu shakka cewa akwai wasu a cikin Littafi Mai Tsarki da aka amsa addu’arsu ta hanyar mu’ujiza. (2 Sarakuna 20:1-7) Amma, ko a wannan lokacin ma, hakan bai cika faruwa ba. Wasu bayin Allah sun damu domin suna ganin Allah ba ya jin addu’o’insu. Sarki Dauda ya yi tambaya: “Har yaushe za ka manta da ni, ya Ubangiji? Har abada ne?” (Zabura 13:1; LMT) Amma sa’ad da Dauda ya yi tunani a kan yadda Jehobah ya cece shi sau da sau, wannan mutum mai aminci ya daɗa dogara ga Allah. Dauda ya ci gaba da cewa: “Amma na dogara ga jinƙanka.” (Zabura 13:5) Kamar Dauda, bayin Allah a yau suna bukatar su nace da addu’a har sai sun ga tabbaci cewa Allah ya ji su.—Romawa 12:12.
YADDA ALLAH YAKE AMSA ADDU’A
Allah yana ba mu ainihin abubuwan da muke bukata.
Iyayen da suke ƙaunar yaransu sosai ba za su ba yaran dukan abubuwan da suka roƙa a duk lokacin da suka yi hakan ba. Hakazalika, a wasu lokatai Allah ba zai amsa addu’o’inmu a hanya ko kuma lokacin da muke zaton zai yi hakan ba. Amma za mu iya kasancewa da tabbaci cewa a matsayin Uba mai ƙauna, Mahaliccinmu zai biya mana bukatunmu a lokaci da kuma hanyar da ta dace.—Luka 11:11-13.
Allah yana iya amsawa a hanyoyin da ba za mu fahimta nan da nan ba.
Idan muna cikin wata matsala kuma muka roƙi Allah ya warware mana ita nan da nan, amma hakan bai faru ba fa? Shin za mu ce Allah bai ji addu’armu ba ne gaba ɗaya don ba mu gan wata mu’ujiza ba? Akasin haka, ya kamata mu bincika mu ga ko Allah ya taimaka mana a wasu hanyoyi da ba mu fahimta nan da nan ba. Alal misali, mai yiwuwa wani abokinmu ya kawo mana taimako a kan kari. (Misalai 17:17) Wa ya sani ko Jehobah ne ya tura wannan abokin namu ya taimaka mana? Ƙari ga haka, Allah yana iya yin amfani da Littafi Mai Tsarki wajen amsa addu’o’inmu. Idan muka karanta shi, za mu sami basira da za ta taimaka mana mu jimre da matsaloli.—2 Timotawus 3:16, 17.
A yawancin lokuta, Allah yana ba mutanensa ƙarfin jimre da matsaloli maimakon ya kawar da matsalolin. (2 Korintiyawa 4:7) Alal misali, Yesu ya roƙi Ubansa ya kawar masa da wata masifa domin a ganinsa fuskantar wannan masifar za ta iya ɓata sunan Allah. Maimakon Jehobah ya kawar da masifar, ya aiki mala’ika ya ƙarfafa Ɗansa. (Luka 22:42, 43) Hakazalika, Allah yana iya ƙarfafa mu ta yin amfani da wani amininmu a lokacin da muke bukatar hakan. (Misalai 12:25) Idan ta wannan hanyar ce Allah ya amsa addu’armu, sai mun mai da hankali sosai kafin mu fahimci hakan.
Allah yana amsa wasu addu’o’i a loton da ya dace.
Littafi Mai Tsarki ya ce Allah yana yi wa masu sauƙin kai alheri a “loton da ya zama daidai.” (1 Bitrus 5:6) Saboda haka, idan Jehobah bai amsa roƙonmu a lokacin da muke tsammani ba, bai kamata mu ɗauka cewa bai damu da mu ba. Maimakon haka, Mahaliccinmu yana bincika roƙe-roƙenmu don ya ga ko sun dace da mu, da yake ya san kome.
“Ku ƙasƙantar da kanku fa ƙarƙashin hannu mai-iko na Allah, domin shi ɗaukaka ku loton da ya zama daidai.”—1 Bitrus 5:6
Alal misali, a ce ɗanka yana so ka saya masa keke. Shin za ka tashi kurum ka sayo masa keken ne? Idan kana ganin bai isa tuƙa keke ba, za ka iya dakatawa har sai ya ɗan girma. Amma daga baya, za ka iya saya masa keken idan ka ga cewa yin hakan zai amfane shi, ko ba haka ba? Hakanan ma, Allah zai biya mana ‘muradin zuciyarmu’ a lokacin da ya dace idan muka ci gaba da roƙonsa.—Zabura 37:4.
KA KASANCE DA GABA GAƊI CEWA JEHOBAH YANA SAURARAWA
Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa Kiristoci su riƙa ɗaukan addu’a da muhimmanci sosai. Amma wasu suna iya cewa, ‘Ai yin hakan bai da sauƙi.’ A gaskiya, idan mun daɗe muna fuskantar wata matsala ko kuma rashin adalci, yana iya kasancewa da wuya mu dogara ga Allah. Amma, zai dace mu tuna da koyarwar Yesu game da naciya a batun addu’a.
Yesu ya ba da kwatancin wata gwauruwa matalauciya da ta riƙa zuwa wurin wani alƙali marar imani don tana so ya bi mata hakkinta. (Luka 18:1-3) Da farko, alƙalin ya ƙi ya taimaka mata, amma daga baya ya gaya wa kansa: “Sai in rama mata, kada ta ja raina da zuwanta yau da gobe.” (Luka 18:4, 5) Kalmomin Ibrananci da aka yi amfani da su a nassin nan sun nuna cewa alƙalin ya saurari gwauruwar don kada ta “buge shi a ido,” ma’ana, don kada ta “ɓata masa suna.”c Idan har alƙali marar adalci ya taimaka wa gwauruwa matalauciya don ba ya so a ɓata masa suna, to babu shakka Allahnmu mai ƙauna zai tabbata cewa an yi adalci ga waɗanda “suke yi masa kuka dare da rana”! Hakika Allah zai rama musu “da sauri,” kamar yadda Yesu ya faɗa.—Luka 18:6-8.
“Ku roƙa, za a ba ku.” —Luka 11:9
A wasu lokuta muna iya gajiya da neman taimako, amma bai kamata mu fid da rai ba. Ta wajen nacewa a yin addu’a, za mu nuna cewa lallai muna so Allah ya ja-gorance mu a duk rayuwarmu. Za mu fahimci yadda Allah yake amsa addu’o’inmu, kuma hakan zai sa mu daɗa kusantar sa. Hakika, za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah zai ji addu’o’inmu da suka dace idan muka ci gaba da yin su da bangaskiya.—Luka 11:9.
a Idan muna so Allah ya ji addu’o’inmu, wajibi ne mu ƙoƙarta mu yi abubuwan da yake bukata a gare mu. Idan muka yi hakan, za mu ga tabbaci cewa Allah yana jin addu’a, kamar yadda za a tattauna a wannan talifin. Don ƙarin bayani, ka duba babi na 17 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da Shaidun Jehobah suka wallafa ko kuma ka shiga dandalin www.jw.org/ha.
b Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah shi ne sunan Allah.
c A Isra’ila ta dā, Allah ya bukaci alƙalai su kula da mata gwauraye da kuma marayu.—Kubawar Shari’a 1:16, 17; 24:17; Zabura 68:5.