Dandalinmu na Intane—Ku Yi Amfani da Shi Wajen Yin Nazari da Iyalinku ko Kuma Ku Kaɗai
Ku Karanta Mujallunmu na Kwanan Nan a Intane: Ku karanta Hasumiyar Tsaro da Awake! a Intane makonni da dama kafin a aika su zuwa ikilisiyoyinmu. Ku saurari karatun mujallu.—Ku danna “Littattafai/Mujallu.”
Ku Karanta Littattafan da Za Su Riƙa Fitowa a Dandalin Kaɗai: Daga yanzu, za a riƙa samun talifofi kamar su “Don Matasa” da “Abin da Na Koya Daga Littafi Mai Tsarki” da “Batun Nazari ga Iyali” da kuma “Tambayoyin Matasa,” a Dandalin ne kaɗai. Ku shiga Dandalin don ku sami talifofin da za ku iya karantawa sa’ad da kuke nazari ku kaɗai ko kuma da iyalinku.—Ku danna “Abubuwan da Aka Koyar Daga Littafi Mai Tsarki/Yara” ko kuma ku danna “Abubuwan da Aka Koyar Daga Littafi Mai Tsarki/Matasa.”
Ku Sami Labarai da Ɗumi-Ɗuminsu: Za ku iya karanta rahotanni da labarai masu ƙarfafawa kuma ku kalli bidiyo game da yadda aikinmu yake ci gaba a faɗin duniya. Ƙari ga haka, rahotanni game da bala’i da kuma yadda ake tsananta wa ’yan’uwanmu za su sa mu riƙa yin addu’a a madadin ’yan’uwanmu da waɗannan abubuwan suka shafa. (Yaƙ. 5:16)—Ku danna “Talifofin Labarai.”
Ku Yi Amfani da Laburare a Intane da Ke Dandalin Wajen Yin Bincike: Za ku iya karanta nassosin yini ta Intane a kwamfuta ko kuma wayar salula ko wata na’urar tafi da gidanka idan akwai wannan fasalin a yarenku ko kuma ku yi bincike daga cikin wasu littattafanmu na kwanan nan.—Ku danna “Littattafai/Laburare a Intane,” ko kuma ku shiga shafin www.wol.jw.org da na’urar da kuke amfani da shi.
[Hotunan da ke shafi na 4]
(Don ganin cikakken rubutun, ka duba littafin)
Ku Gwada Shiga Dandalin
1 Ku danna hoton ko kuma inda aka rubuta “Ka sauko da” don ku sauko da hoton. Bayan haka, hoton zai bayyana a nau’in PDF. Ku buga don ku yi amfani da shi wajen koyar da yaranku.
2 Ku danna alamar da ke kan bidiyo don ku soma kallo.