DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ZABURA 52-59
“Ka Zuba Nawayarka Bisa Jehobah”
Dauda ya fuskanci matsaloli sosai a rayuwarsa. A lokacin da aka rubuta Zabura 55, ya yi fama da . . .
Raini
Tsanani
Baƙin Ciki don Zunubinsa
Masifa Daga Iyalinsa
Ciwo
Cin Amana
Dauda ya jimre matsalolin da ya fuskanta ko da yake hakan bai kasance masa da sauƙi ba. Shi ya sa aka hure shi ya gaya wa waɗanda suke fuskantar irin yanayin da ya fuskanta cewa: “Ku zuba nawayarku bisa Ubangiji [Jehobah].”
Wane darasi za mu koya daga wannan ayar?
55:22
Ka yi addu’a ga Jehobah sa’ad da kake fuskantar wata matsala ko kuma kana baƙin ciki
Ka nemi ja-gora daga Littafi Mai Tsarki da kuma ƙungiyar Jehobah
Ka yi iya ƙoƙarinka don ka bi da yanayin bisa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki