Gabatarwa
Ka taɓa ji kamar Allah ba ya amsa addu’arka? Ba kai kaɗai kake jin haka ba. Mutane da yawa suna roƙon Allah ya taimaka musu, amma sun ci gaba da fama da matsaloli. Talifofin da za mu tattauna a gaba za su taimaka mana mu kasance da tabbaci cewa Allah yana jin addu’o’inmu. Ƙari ga haka, za su nuna mana abin da ya sa Allah ba ya amsa wasu addu’o’in, da kuma yadda za ka yi addu’a don Allah ya amsa.