Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp21 Na 1 pp. 8-9
  • Me Ya Sa Allah Ba Ya Amsa Dukan Addu’o’i?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me Ya Sa Allah Ba Ya Amsa Dukan Addu’o’i?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2021
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Kusaci Allah Cikin Addu’a
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Gatan da Muke da Shi Na Yin Addu’a
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Ka Rika Yin Addu’a don Ka Kusaci Allah
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Sashe na 11
    Ka Saurari Allah
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2021
wp21 Na 1 pp. 8-9

Me Ya Sa Allah Ba Ya Amsa Dukan Addu’o’i?

Ubanmu na sama, wato Jehobah, yana jin daɗin sauraron addu’o’in da muke yi daga zuciyarmu. Amma akwai abubuwan da idan muka yi, za su sa Allah ba zai ji addu’armu ba. Waɗanne abubuwa ke nan? Me ya kamata mu riƙa tunawa a duk lokacin da muke addu’a? Ga abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa.

Mutane sun taru a coci suna maimaita addu’a daga wani littafin addu’a.

“In kuwa kuna addu’a, kada ku yi ta maimaitawar banza.”​—Matiyu 6:​7, Littafi Mai Tsarki.

Jehobah ba ya so mu riƙa maimaita addu’o’in da muka haddace ko mu karanta su daga wani littafi. A maimakon haka, yana so mu gaya masa abin da ke zuciyarmu. Ya za ka ji idan abokinka ya zo ya yi ta maimaita maka abu ɗaya kowace rana? Abokan kirki suna gaya wa juna abin da ke zuciyarsu. Idan muna gaya wa Ubanmu na sama abin da ke zuciyarmu, hakan zai nuna cewa muna ɗaukansa a matsayin abokinmu.

Wani mutum yana fatan Allah zai ba shi sa’a a cacar da yake so ya yi.

“Sa’ad da kukan roƙa ba ku samu ba, gama kukan roƙa da mugun nufi.”​—Yaƙub 4:3.

Bai kamata mu ɗauka cewa Allah zai amsa addu’ar da muke yi game da wani abin da ba zai so mu yi ko mu samu ba. Alal misali, idan mutum ya je yin caca kuma ya roƙi Allah ya ba shi sa’a, kana ganin Allah zai amsa addu’ar? Allah da kansa ya ce kada mu zama masu haɗama kuma kada mu yi imani da sa’a da ƙaddara. (Ishaya 65:11; Luka 12:15) Don haka, Jehobah ba zai taɓa amsa irin wannan addu’ar ba. Kafin Allah ya amsa addu’armu, Kalmar Allah ta gaya mana cewa dole ne addu’ar ta jitu da nufinsa.

Wani limami yana wa sojoji addu’a.

“Idan mutum ya ƙi kasa kunne ga doka, addu’arsa ma abin ƙyama ce.”​—Karin Magana 28:9.

A zamanin Isra’ilawa, Allah ya ƙi ya amsa addu’o’in waɗanda suka yi masa rashin biyayya. (Ishaya 1:​15, 16) Allah bai canja ba har wa yau. (Malakai 3:6) Idan muna so Allah ya amsa addu’o’inmu, dole ne mu yi iya ƙoƙarinmu mu bi dokokinsa. Amma, idan mun yi abubuwan da ba su dace ba a dā fa? Hakan yana nufin Allah ba zai saurare mu ba? Ko kaɗan. Allah yana ƙaunarmu, don haka, zai gafarta mana idan muka tuba kuma muka yi iya ƙoƙarinmu mu faranta masa rai.​—Ayyukan Manzanni 3:19.

“Duk mai matsowa kusa da Allah dole ne ya ba da gaskiya cewa akwai Allah kuma yana ba da lada ga duk waɗanda suke nemansa.”​—Ibraniyawa 11:6.

Wata mata tana karanta Littafi Mai Tsarki.

Addu’a ba wani abin da zai kwantar mana da hankali sa’ad da muke cikin damuwa ba ne kawai. Amma hanya ce da za mu nuna wa Allah cewa mun yi imani da shi, muna ƙaunarsa kuma muna daraja shi. Manzo Yaƙub ya ce, idan ba mu ci gaba da “roƙa da bangaskiya” ba, kada mu ‘yi tsammani za mu sami wani abu daga wurin Ubangiji.’ (Yaƙub 1:​6, 7) Kafin mu iya kasancewa da bangaskiya, wajibi ne mu yi iya ƙoƙari mu san Allah ta wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki. Yin hakan zai taimaka mana mu kasance da tabbaci cewa Allah zai saurari addu’o’inmu.

KADA KU GAJI!

Ko da yake ba dukan addu’o’i ne Allah yake amsawa ba, akwai miliyoyin mutanen da yake amsa addu’arsu. Littafi Mai Tsarki ya faɗi abubuwan da za ka iya yi don Allah ya ji addu’arka. Za ka sami ƙarin bayani a talifi na gaba.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba