Ƙarin Bayani
a Yawancin Israꞌilawa da suka ga abin ban-mamaki da Jehobah ya yi a Jar Teku ba su shiga Ƙasar Alkawarin ba. (L. Ƙid. 14:22, 23) Jehobah ya ce waɗanda suka kai shekaru 20 kuma an yi musu rijista, za su mutu a jeji. (L. Ƙid. 14:29) Amma, yawancin waɗanda ba su kai shekaru 20 ba sun tsira. Kuma su da Joshua, da Kaleb, da ꞌyaꞌyan Lawi da yawa, sun haye Kogin Urdun tare, kuma sun shiga ƙasar Kanꞌana.—M. Sha. 1:24-40.