Ƙarin Bayani
a A Afisawa 1:10, manzo Bulus ya ce za a tattaro “abubuwan da suke a sama.” A Matiyu 24:31 da Markus 13:27 kuma, Yesu ya ce za a tattaro “waɗanda aka zaɓa.” Amma abin da suke nufi ba ɗaya ba ne. Bulus yana magana ne a kan lokacin da Jehobah yake zaɓan waɗanda za su yi mulki tare da Yesu. Yesu kuma yana magana ne a kan lokacin da za a tattara sauran shafaffu da suka rage a duniya a kai su sama, wato a lokacin ƙunci mai girma.