Ƙarin Bayani a Tun kafin Yesu ya ba da fansar, Jehobah yana yafe wa bayinsa. Me ya sa? Domin Jehobah ya san cewa Yesu zai riƙe aminci kuma zai ba da ransa. Don haka a gun Jehobah, kamar an riga an ba da fansar ne.—Rom. 3:25.