Alhamis, 11 ga Satumba
Ku tabbatar wa waɗannan mutane irin ƙaunarku.—2 Kor. 8:24.
Za mu iya nuna wa ꞌyanꞌuwanmu ƙauna ta wajen yin abokantaka da su. (2 Kor. 6:11-13) Yawancinmu muna a ikilisiyoyi da akwai ꞌyanꞌuwa daga wurare dabam-dabam kuma halinsu ya bambanta. Wani abin da zai taimaka mana mu ƙara ƙaunar su shi ne, mu dinga lura da halayensu masu kyau. Idan muna ɗaukan ꞌyanꞌuwanmu kamar yadda Jehobah yake ɗaukan su, hakan zai nuna cewa muna ƙaunar su. Za mu bukaci ƙaunar ꞌyanꞌuwa sosai a lokacin ƙunci mai girma. Ta yaya Jehobah zai kāre mu a lokacin? Ku yi laꞌakari da abin da Jehobah ya ce bayinsa su yi a lokacin da aka kai wa birnin Babila hari. Ya ce: “Ku tafi ku shiga ɗakunanku, ku rufe ƙofofinku ku ɓoye kanku, sai fushina ya wuce.” (Isha. 26:20) Mai yiwuwa mu ma haka za a ce mu yi a lokacin ƙunci mai girma. w23.07 6-7 sakin layi na 14-16
Jumma’a, 12 ga Satumba
Yadda duniyar nan take, tana wucewa ne.—1 Kor. 7:31.
Ku yi abubuwan da za su sa mutane su ga cewa ku masu sanin yakamata ne. Ka tambayi kanka: ‘Shin mutane suna gani na a matsayin mai sanin yakamata? Ba na nacewa a kan raꞌayina kuma ina haƙuri da mutane? Ko dai suna gani na a matsayin mai tsattsauran raꞌayi, marar tausayi kuma mai taurin kai? Ina sauraran mutane kuma in bin shawararsu idan hakan ya dace?’ Yadda muke nuna sanin yakamata zai nuna ko muna yin koyi da Jehobah da Yesu. Muna bukatar mu nuna sanin yakamata idan yanayinmu ya canja. Irin canjin nan zai iya jawo mana matsalolin da ba mu zata ba. Alal misali, za mu iya soma rashin lafiya kwatsam. Faɗuwar tattalin arziki ko kuma wasu canje-canje a gwamnati za su iya sa rayuwa ta yi mana wuya. (M. Wa. 9:11) Ƙari ga haka, zai iya yi mana wuya idan ƙungiyarmu ta canja mana hidima, ko kuma ta ce mu koma yin hidima a wani wuri. Za mu iya jimrewa idan muka bi abubuwa guda huɗun nan: (1) ka amince cewa yanayinka ya canja, (2) ka mai da hankali ga abin da za ka iya yi yanzu ba abin da ka yi a dā ba, (3) ka mai da hankali ga abubuwan da kake morewa yanzu, (4) ka taimaka wa mutane. w23.07 21-22 sakin layi na 7-8
Asabar, 13 ga Satumba
Kai mai daraja ne sosai.—Dan. 9:23.
Annabi Daniyel matashi ne a lokacin da Babiloniyawa suka kama shi suka kai shi zaman bauta a Babila, inda yake da nisa da Urushalima. Babu shakka, Daniyel ya burge su domin sun ga abin da mutum yake gani “daga waje,” wato, Daniyel yana da kyan gani, marar taɓo kuma ya fito daga iyalin da ake darajawa sosai. (1 Sam. 16:7) Waɗannan dalilan ne suka sa Babiloniyawan suka koyar da Daniyel don ya yi hidima a fadar sarki. (Dan. 1:3, 4, 6) Jehobah ya ƙaunaci Daniyel saboda halayensa masu kyau. Mai yiwuwa shekarun Daniyel wajen 20 ne a lokacin da Jehobah ya kwatanta shi da Nuhu da Ayuba. Ko da yake Daniyel matashi ne, a gun Jehobah, shi mai adalci ne kamar Nuhu da Ayuba, waɗanda suka daɗe suna bauta masa da aminci. (Far. 5:32; 6:9, 10; Ayu. 42:16, 17; Ezek. 14:14) Kuma Jehobah ya ci gaba da ƙaunar Daniyel har iyakar rayuwarsa.—Dan. 10:11, 19. w23.08 2 sakin layi na 1-2