Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
Littattafan Hausa (1987-2026)
Fita
Shiga Ciki
Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Maraba.
Wannan kayan bincike ne da ya kunshi wallafe-wallafen Shaidun Jehobah a harsuna dabam-dabam.
Idan kana so ka saukar da wallafe-wallafe, ka shiga jw.org/ha jw.org.
  • Yau

Asabar, 13 ga Satumba

Kai mai daraja ne sosai.—Dan. 9:23.

Annabi Daniyel matashi ne a lokacin da Babiloniyawa suka kama shi suka kai shi zaman bauta a Babila, inda yake da nisa da Urushalima. Babu shakka, Daniyel ya burge su domin sun ga abin da mutum yake gani “daga waje,” wato, Daniyel yana da kyan gani, marar taɓo kuma ya fito daga iyalin da ake darajawa sosai. (1 Sam. 16:7) Waɗannan dalilan ne suka sa Babiloniyawan suka koyar da Daniyel don ya yi hidima a fadar sarki. (Dan. 1:​3, 4, 6) Jehobah ya ƙaunaci Daniyel saboda halayensa masu kyau. Mai yiwuwa shekarun Daniyel wajen 20 ne a lokacin da Jehobah ya kwatanta shi da Nuhu da Ayuba. Ko da yake Daniyel matashi ne, a gun Jehobah, shi mai adalci ne kamar Nuhu da Ayuba, waɗanda suka daɗe suna bauta masa da aminci. (Far. 5:32; 6:​9, 10; Ayu. 42:​16, 17; Ezek. 14:14) Kuma Jehobah ya ci gaba da ƙaunar Daniyel har iyakar rayuwarsa.—Dan. 10:​11, 19. w23.08 2 sakin layi na 1-2

Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana—2025

Lahadi, 14 ga Satumba

Ku fahimci . . . faɗinta, da tsawonta, da girmanta, da zurfinta.—Afis. 3:18.

Idan kana so ka sayi wani gida, za ka so ka je ka bincika kome da kome game da gidan kafin ka saye shi. Za mu iya bin wannan misalin yayin da muke nazarin Littafi Mai Tsarki. Idan ka karanta Littafi Mai Tsarki cikin hanzari, “koyarwa mai sauƙi ta kalmar Allah” ce kawai za ka fahimta. (Ibran. 5:12) Amma kamar yadda kake bukatar ka shiga cikin gidan da muka ambata, kana bukatar ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kyau don ka ƙara fahimtar abubuwa da ke ciki. Wani abin da zai taimaka mana sosai shi ne, neman alaƙar da ke tsakanin abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa a wani wuri, da abin da ya faɗa a wani wuri dabam. Ka yi ƙoƙari ka san abubuwan da ka yi imani da su da kuma dalilin da ya sa ka yi imani da su. Don mu ƙara fahimtar abubuwan da ke Littafi Mai Tsarki, muna bukatar mu fahimci koyarwarta masu wuyar fahimta. Manzo Bulus ya shawarci ꞌyanꞌuwansa Kiristoci su yi nazarin Kalmar Allah da kyau domin su ‘fahimci . . . faɗinta, da tsawonta, da girmanta, da zurfinta.’ Yin hakan zai sa su “kafu sosai cikin” bangaskiya. (Afis. 3:​14-19) Ya kamata mu ma mu yi hakan. w23.10 18 sakin layi na 1-3

Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana—2025

Litinin, 15 ga Satumba

ꞌYanꞌuwa, ku lura da annabawan da suka yi magana da sunan Ubangiji. Ku bi gurbi na jimrewarsu cikin wahala.—Yak. 5:10.

Akwai labaran mutane da yawa da suka nuna haƙuri a cikin Littafi Mai Tsarki. Me zai hana ka ka yi nazari game da su? Alal misali, an naɗa Dauda ya zama sarkin Israꞌila tun yana yaro, amma sai da ya jira har na shekaru da yawa kafin ya zama sarki. Simeyon da Hannatu sun bauta wa Jehobah da aminci yayin da suke jiran Almasihu da aka yi alkawarin sa. (Luk. 2:​25, 36-38) Yayin da kake yin nazari game da labaran nan, ka bincika amsoshin tambayoyin nan: Mene ne ya taimaka ma wannan mutumin ya iya yin haƙuri? Ta yaya ya amfana don ya yi haƙuri? Ta yaya zan yi koyi da shi? Za ka kuma iya koyan darasi daga marasa haƙuri. (1 Sam. 13:​8-14) Za ka iya yin tambayar nan: ‘Mene ne ya sa suka ƙasa yin haƙuri? Wane sakamako ne hakan ya jawo musu?’ w23.08 25 sakin layi na 15

Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana—2025
Maraba.
Wannan kayan bincike ne da ya kunshi wallafe-wallafen Shaidun Jehobah a harsuna dabam-dabam.
Idan kana so ka saukar da wallafe-wallafe, ka shiga jw.org/ha jw.org.
  • Hausa
  • Raba
  • Wadda ka fi so
  • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
  • Ka'idojin Amfani
  • Tsarin Tsare Sirri
  • Saitin Tsare Sirri
  • JW.ORG
  • Shiga Ciki
Raba