Ku Ji Abin Da Ruhu Ke Faɗa
“Kunnuwanka kuma za su ji magana daga bayanka, tana cewa, Wannan ita ce hanya, ku bi ta; yayinda ku ke juyawa ga dama, da yayinda ku ke juyawa ga hagu.”—ISHAYA 30:21.
1, 2. Ta yaya Jehovah ya yi magana da mutane duk cikin tarihi?
TSIBIRIN Puerto Rico gari ne mai gidan rediyo da yake da madubi na kawo nesa kusa da ya fi girma a dukan duniya. Shekaru da yawa, masana kimiyya suna zaton za su sami saƙo daga sararin sama a bayan duniya, ta wurin wannan kayan aiki mai girma. Amma ba su taɓa samun wannan saƙo ba. Akasarin haka, da akwai saƙonni daga bayan duniyar da mutane ke zama, da kowannenmu zai iya samu a kowane lokaci—ba tare da yin amfani da kayan aiki mai girma ba. Wannan ya zo ne daga Tushe da ya fi kowane abu da ake tsammani yana sararin sama. Waye ne Tushen waɗannan sadarwa, kuma su waye suke samunta? Menene saƙonnin suke faɗa?
2 Littafi Mai-Tsarki yana ɗauke da labarai da yawa na lokutta da mutane suka ji saƙo da kunnensu wanda ya fito daga wurin Allah. A wasu lokutta halittu na ruhu ne suke sanar da saƙonnin, waɗanda manzanni ne ga Allah. (Farawa 22:11, 15; Zechariah 4:4, 5; Luka 1:26-28) An ji muryar Jehovah sau uku. (Matta 3:17; 17:5; Yohanna 12:28, 29) Allah ya yi magana ma ta wurin annabawa, da yawa cikinsu sun rubuta abin da ya hure su su faɗa. Yau, muna da Littafi Mai-Tsarki, da ke ɗauke da labarai na waɗannan sadarwa, haɗe da koyarwar Yesu da na almajiransa. (Ibraniyawa 1:1, 2) Hakika Jehovah yana aika sanarwa ga mutane.
3. Menene manufar saƙon Allah, kuma menene ake bukata mu yi?
3 Duk waɗannan saƙo da Allah ya hure sun bayyana abubuwa kaɗan ne game da sararin sama ta zahiri. Sun mai da hankali ne akan al’amura da suka fi muhimmanci, waɗanda suka shafi rayuwarmu yanzu da kuma a nan gaba. (Zabura 19:7-11; 1 Timothawus 4:8) Jehovah yana amfani da su ya faɗi nufinsa kuma ya yi mana ja-gora. Hanya ɗaya ce da kalmomin annabi Ishaya ke cika: “Kunnuwanka kuma za su ji magana daga bayanka, tana cewa, Wannan ita ce hanya, ku bi ta; yayinda ku ke juyawa ga dama, da yayinda ku ke juyawa ga hagu.” (Ishaya 30:21) Jehovah ba ya sa mu dole mu ji ‘maganarsa.’ Yana garemu ne mu bi ja-gorar Allah kuma mu yi tafiya a hanyarsa. Shi ne ya sa Nassosi suka yi mana gargaɗi mu ji maganar Jehovah. Ƙarfafa na a “ji abin da ruhu ke faɗa” ya bayyana sau bakwai a littafin Ru’ya ta Yohanna.—Ru’ya ta Yohanna 2:7, 11, 17, 29; 3:6, 13, 22.
4. Daidai ne a kwanakinmu mu yi tsammanin Allah zai yi mana magana baki da baki daga sama?
4 A yau, Jehovah ba ya yi mana magana baki da baki daga sama. Ko a lokuttan Littafi Mai-Tsarki ma, irin wannan magana daga sama yana da wuya, wasu lokutta sai bayan ƙarnuka. A duk cikin tarihi, Jehovah ya yi magana da mutanensa sau da yawa a kaikaice. Haka yake a yau. Bari mu bincika hanyoyi uku da Jehovah yake magana da mu a yau.
“Kowane Nassi Hurare Ne”
5. Wane abu ne na musamman Jehovah yake amfani da shi yau wajen magana, kuma ta yaya za mu amfana daga wannan?
5 Littafi Mai-Tsarki hanya ce ta musamman da Allah yake magana da mutane. Allah ne ya hure, kuma kome da yake ciki zai amfane mu. (2 Timothawus 3:16) Littafi Mai-Tsarki na cike da misalai na mutane waɗanda suka tsai da shawara ko su saurari muryar Jehovah ko a’a. Irin waɗannan misalai sun tunatar mana abin da ya sa yake da muhimmanci a ji abin da ruhun Allah ke faɗa. (1 Korinthiyawa 10:11) Littafi Mai-Tsarki yana ɗauke da hikima mai kyau, yana ba mu shawara lokacin da muke fuskantar tsai da shawara a rayuwarmu. Kamar Allah ne yake tsaye a bayanmu, yana yi mana magana a kunne: “Wannan ita ce hanya, ku bi ta.”
6. Me ya sa Littafi Mai-Tsarki yake da fifiko fiye da sauran rubuce-rubuce?
6 Don mu ji abin da ruhu ke faɗa a cikin shafofin Littafi Mai-Tsarki, dole ne mu karanta shi kullum. Littafi Mai-Tsarki ba kawai sanannen littafi da aka rubuta da kyau, ɗaya cikin waɗanda suke da yawa a yau ba. Littafi Mai-Tsarki ruhu ne ya hure shi kuma yana ɗauke da tunanin Allah. Ibraniyawa 4:12 ya ce: “Maganar Allah mai-rai ce, mai-aikatawa, ta fi kowane takobi mai-kaifi biyu ci, tana kuwa hudawa har zuwa rarraban rai da ruhu, da gaɓaɓuwa da ɓargo kuma, tana kuwa da hanzari ga ganewar tunanin zuciya da nufe-nufenta.” Sa’anda muke karatun Littafi Mai-Tsarki, abin da yake ciki yana shiga cikin tunaninmu da motsuwa kamar takobi, yana bayyana yadda rayukanmu ya jitu da nufin Allah.
7. Me ya sa karatun Littafi Mai-Tsarki yake da muhimmanci, kuma yaya yawan yadda aka ƙarfafa mu mu yi shi?
7 “Tunanin zuciya da nufe-nufenta” za su iya canjawa da wucewar lokaci da kuma yadda abin da muke fuskanta a rayuwa ya taɓa mu—mai daɗi da mai wuya. Idan ba ma nazarin Kalmar Allah kullum, tunaninmu, halayenmu, da kuma yadda abu ke taɓa mu ba za su ci gaba da jituwa da ƙa’idodin ibada na ruhaniya ba. Saboda haka, Littafi Mai-Tsarki ya ba mu gargaɗi: ‘Ku ci gaba da gwada kanku ko kuna cikin imani; ku ci gaba da yi wa kanku ƙwanƙwanto.’ (2 Korinthiyawa 13:5) Idan za mu ci gaba da jin abin da ruhu ke faɗa, ya kamata mu yi biyayya ga umurnin mu karanta Kalmar Allah kullum.—Zabura 1:2.
8. Waɗanne kalmomi na manzo Bulus ya taimake mu mu gwada kanmu game da karatun Littafi Mai-Tsarki?
8 Abin tunawa da ke da muhimmanci ga masu karatun Littafi Mai-Tsarki shi ne: Ku ɗauka isashen lokaci don ku gane abin da ku ka karanta! A ƙoƙarin bin umurni na mu karanta Littafi Mai-Tsarki kullum, kada mu iske kanmu muna hanzarin karanta surori da yawa ba tare da gane ma’anar abin da muke karantawa ba. Yayin da karatun Littafi Mai-Tsarki kullum yana da muhimmanci, bai kamata abin da yake motsa mu ya zama bin tsarin karatun daidai kawai ba; ya kamata mu kasance da tabbataciyar sha’awa na koya game da Jehovah da ƙudurinsa. Game da wannan, yana da kyau mu yi amfani da kalmomin manzo Bulus mu gwada kanmu. Da yake rubuta wa ’yan’uwa Kiristoci, ya ce: “Ina durƙusawa a gaban Uba, shi yarda maku . . . Kristi kuma shi zauna cikin zukatanku ta wurin bangaskiya; domin ku, dasassu ne kafaffu kuma cikin ƙauna, ku ƙarfafa da za ku ruska, tare da dukan tsarkaka, ko menene fāɗin da ratar da tsawon da zurfin ƙaunar Kristi, ku sani kuma ƙaunar Kristi wadda ta wuce gaban a san ta, domin ku cika har zuwa dukan cikar Allah.”—Afisawa 3:14, 16-19.
9. Ta yaya za mu iya gina kuma yi marmari mu koya daga Jehovah?
9 Gaskiya ce, wasu cikinmu ba sa jin daɗin karatu, yayin nan kuma wasu suna son karatu sosai. Ko yaya halinmu yake, za mu iya gina kuma mu yi sha’awa mu koya daga Jehovah sosai. Manzo Bitrus ya bayyana cewa ya kamata mu yi marmarin ilimi na Littafi Mai-Tsarki, kuma ya gane cewa za a iya gina irin wannan marmari. Ya rubuta: “Kamar jarirai sabbabin haihuwa, ku yi marmarin madara mai-ruhaniya wadda ke sahihiya, domin ta wurinta ku yi girma zuwa ceto.” (1 Bitrus 2:2) Mutum ya hore kansa yana da muhimmanci idan za mu “yi marmarin” nazarin Littafi Mai-Tsarki. Yadda za mu soma son sabon abinci bayan mun ɗanɗana sau da yawa, halinmu game da karatu da kuma nazari zai canja zuwa mai kyau idan mun hore kanmu mu bi tsarin karatu kullum.
“Abinci a Lotonsa”
10. Su wanene suke “bawan nan mai-aminci, mai-hikima,” kuma yaya Jehovah yake amfani da su a yau?
10 Yesu ya nuna wata hanya da Jehovah yake amfani da ita wajen yi mana magana a yau a Matta 24:45-47. A wurin ya yi maganar ikklisiyar Kirista shafaffu daga ruhu— “ajin bawan nan mai-aminci, mai-hikima” waɗanda aka naɗa su su ba da ‘abinci [na ruhaniya] a lotansa.’ Ɗaɗɗaya, waɗanda suke cikin wannan aji ‘tumakin’ Yesu ne. Waɗannan tare da “taro mai-girma” na “waɗansu tumaki,” suna karɓan ƙarfafawa da ja-gora. (Ru’ya ta Yohanna 7:9; Yohanna 10:16) Da yawa na wannan abinci a lotansa yana zuwa ta littattafai da aka buga, irinsu Hasumiyar Tsaro, da Awake!, da wasu littattafai. Ana ba da ƙarin abinci na ruhaniya ta wurin jawabai da misalai a manyan taro, ƙananan taro, da taron ikklisiya.
11. Ta yaya muke nuna cewa muna saurara ga abin da ruhu ke faɗa ta wurin “bawan nan mai-aminci, mai-hikima”?
11 Sanarwa da “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” suke tanadar, ana shirya su ne su ƙarfafa bangaskiyarmu kuma su koyar da hankalinmu. (Ibraniyawa 5:14) Ana iya ba galibin mutane irin wannan umurni don kowanne ya yi amfani da shi wa kansa. A loto-loto, muna samun umurni da ya shafi takamaiman fasaloli na halayenmu. Wane hali ya kamata mu kasance da shi idan muna saurara da gaske ga abin da ruhu ke faɗa ta wurin ajin bawa? Manzo Bulus ya amsa: “Ku yi biyayya da waɗanda ke shugabannanku, ku sarayadda kanku garesu.” (Ibraniyawa 13:17) Gaskiya, dukan waɗanda suke cikin wannan shiri mutane ne ajizai. Duk da haka, Jehovah yana farin ciki da yake yin amfani da bayinsa ’yan Adam ko da su ajizai ne, ya ja-gorance mu a wannan lokaci na ƙarshe.
Ja-gora Daga Lamirinmu
12, 13. (a)Wane ƙarin hanyar ja-gora ne Jehovah ya ba mu? (b)Wane tasiri mai kyau lamiri zai iya yi a kan mutane waɗanda ba su da cikakken sani na Kalmar Allah?
12 Jehovah ya ba mu wani tushe na ja-gora—lamirinmu. Ya halicce mutum da azanci na sanin nagarta da mugunta. Halinmu ne. A wasiƙarsa zuwa Romawa, manzo Bulus ya bayana: “Al’ummai, waɗanda ba su da shari’a, kadan bisa ga tabi’a su ke aika abin da ke na shari’a, waɗannan, domin ba su da shari’a, sun zama shari’a ga kansu; da shi ke suna bayana aikin shari’a a rubuce cikin zukatansu, lamirinsu kuwa yana shaida tare, tunaninsu kuma yasu yasu suna kai ƙara ko kuwa suna kawo hujja.”—Romawa 2:14, 15.
13 Mutane da yawa da ba su san Jehovah ba, za su iya daidaita tunaninsu da halayensu cikin jituwa da ƙa’idodin ibada na nagarta da mugunta. Kamar suna jin murya a ciki da ke ja-gorarsu a hanya da take daidai. Idan wannan gaskiya ce ga waɗanda ba su da cikakken sani na Kalmar Allah, ya kamata wannan murya na ciki ta yi wa Kiristoci na gaskiya magana! Babu shakka, lamirin Kirista da aka gyara da cikakken sani na Kalmar Allah kuma wanda ke aiki cikin jituwa da ruhu mai tsarki na Jehovah zai kawo ja-gora da za a amince da shi.—Romawa 9:1.
14. Ta yaya lamiri da aka koyar da Littafi Mai-Tsarki zai taimake mu mu bi ja-goran ruhun Jehovah?
14 Lamiri mai kyau, wanda aka koyar da shi da Littafi Mai-Tsarki, zai tunatar mana hanya da ruhu ke so mu bi. Akwai lokutta da Nasossi ko littattafanmu masu tushe cikin Littafi Mai-Tsarki ba su yi magana ba, musamman game da wani yanayi da muka iske kanmu ciki. Duk da haka, lamirinmu zai iya yi mana kashedi, yana ba mu gargaɗi a kan tafarki da zai yi mana lahani. A irin wannan yanayi, yin banza da ja-goran lamirinmu, zai zama yin banza da abin da ruhun Jehovah ke faɗa. A wata sassa, ta wurin koya mu dogara ga lamirinmu na Kirista da aka koyar, za mu iya yin zaɓe masu kyau ko lokacin da ba ainihin abin da aka rubuta game da wani al’amari. Amma, yana da muhimmanci mu tuna cewa lokacin da babu ƙa’ida, ja-gora, ko doka daga Allah, ba zai yi kyau ba mu ɗora abin da muka tsai da shi a lamirinmu wa Kiristoci ’yan’uwa a abin da yake sarai al’amura na kanmu ne.—Romawa 14:1-4; Galatiyawa 6:5.
15, 16. Me zai sa lamirinmu ya daina aiki, kuma ta yaya za mu hana wannan faruwa?
15 Lamiri mai tsarki, da aka koyar da Littafi Mai-Tsarki kyauta ne mai kyau daga Allah. (Yaƙub 1:17) Amma dole ne mu tsare wannan kyauta daga tasiri na ɓatanci idan zai yi aiki sosai kamar abin tsare ɗabi’a. Al’adu, da kuma halaye da sun saɓa da mizanan Allah, idan an bi su, za su iya sa lamirinmu ya daina aiki kuma ya kasa motsa mu zuwa hanya da ke daidai. Ba za mu iya bin al’amura daidai ba kuma za mu iya ruɗan kanmu da gaskata cewa munanan ayyuka suna da kyau.—Gwada da Yohanna 16:2.
16 Idan mun ci gaba da yin banza da kashedi na lamirinmu, muryarsa zai dinga raunana har mu taurara a ɗabi’a ko kuma daina saurara. Mai-Zabura ya yi maganar waɗannan mutane lokacin da ya ce: “Zuciyarsu ta yi wojiya kamar kitse.” (Zabura 119:70) Wasu da suke yin banza da motsuwa na lamirinsu ba sa iya yin tunani da kyau. Ƙa’idodi na ibada ba ya ja-gorarsu kuma ba sa iya yin shawara da ya dace. Don mu guje ma irin yanayin nan, ya kamata muna saurara ga ja-gorar lamirinmu na Kirista ko lokacin da al’amari da muke fuskanta ƙarami ne.—Luka 16:10.
Masu Farin Ciki ne Waɗanda Suke Saurara Kuma Suke Yin Biyayya
17. Yayin da muke saurara ga ‘magana daga bayanmu’ kuma muka yi biyayya ga lamirinmu da aka koyar da Littafi Mai-Tsarki, ta yaya za a albarkace mu?
17 Yayin da muka kafa tsarin saurara ga ‘magana daga bayanmu’—yadda aka tanadar ta wurin Nassosi da bawan nan mai-aminci, mai-hikima—da kuma yayin da muke yin biyayya ga tuni na lamirinmu da aka koyar da Littafi Mai-Tsarki, Jehovah zai albarkace mu da ruhunsa. Ruhu mai tsarki zai ƙara iyawarmu mu saurara kuma fahimci abin da Jehovah ya gaya mana.
18, 19. Ta yaya ja-goran Jehovah zai amfane mu a hidimarmu da kuma a rayuwarmu?
18 Ruhun Jehovah zai ba mu ƙarfin zuciya mu fuskanci yanayi masu wuya da hikima da gaba gaɗi. Kamar yadda yake wurin manzanni, ruhun Allah zai iya motsa tunaninmu kuma ya taimake mu mu aikata kuma mu yi magana koyaushe cikin jituwa da ƙa’idodin Littafi Mai-Tsarki. (Matta 10:18-20; Yohanna 14:26; Ayukan Manzanni 4:5-8, 13, 31; 15:28) Haɗa ruhun Jehovah da namu ƙoƙarce-ƙoƙarce zai sa mu sami nasara yayin da muke yin shawara da ke da muhimmanci a rayuwa, yana ba mu gaba gaɗi mu tsai da waɗannan shawara. Alal misali, ƙila kana tunanin gyara yayin rayuwanka kuma ka ƙara lokaci don abubuwa na ruhaniya. Ko kuma ƙila kana fuskantar zaɓen rayuwa da ke da muhimmanci, irinsu zaɓen wadda za ka aura, bincika aiki da ka samu, ko kuma sayan gida. Maimakon barin tunaninmu na mutum ya zama abu na musamman da ya sa muke tsai da shawara, ya kamata mu saurara ga abin da ruhun Allah ke faɗa kuma ka aikata cikin jituwa da ja-goransa.
19 Muna godiya domin tuni mai kyau da shawara da muke karɓa daga Kiristoci ’yan’uwa, haɗe da dattiɓai. Amma dai, bai kamata mu jira sai wasu sun tuna mana da al’amura ba. Idan mun san tafarki mai kyau da za mu bi da kuma gyara da ya kamata mu yi a halayenmu da yadda muke tunani don mu faranta wa Allah rai, bari mu yi. Yesu ya ce: “Idan kun san waɗannan abu, masu-albarka ne idan kun yi su.”—Yohanna 13:17.
20. Wace albarka ce waɗanda suke saurarawa ga ‘magana daga bayansu’ za su samu?
20 Lallai, don mu san yadda za a faranta wa Allah rai, Kiristoci ba sa bukatan su ji murya ta zahiri daga sama, ko kuwa mala’ika ya ziyarce su. An albarkace su da rubutaccen Kalmar Allah da ja-goran ajin shafaffu cikin ƙauna a duniya. Idan sun yi biyayya sosai ga wannan ‘magana daga bayansu’ kuma suka bi ja-gorar lamirinsu da aka koyar da Littafi Mai-Tsarki, za su yi nasara a yin nufin Allah. Babu shakka za su ga cikar alkawarin manzo Yohanna: “Wanda ya aika nufin Allah ya zauna har abada.”—1 Yohanna 2:17.
A Taƙaice
• Me ya sa Jehovah yake magana da ’yan Adam?
• Ta yaya za mu amfana daga tsari na karatun Littafi Mai-Tsarki na kullum?
• Yaya ya kamata mu saurara ga ja-goran ajin bawa?
• Me ya sa ya kamata kada mu yi banza da ja-gorar lamiri da aka koyar da Littafi Mai-Tsarki?
[Hoto a shafi na 25]
Mutane ba sa bukatar kayan aiki masu girma don su samu saƙo daga Allah
[Inda aka Dauko]
Arecibo Observatory/David parker/Science Photo Library
[Hotuna a shafi na 27]
Jehovah yana yi mana magana ta wurin Littafi Mai-Tsarki da kuma ta wurin “bawan nan mai-aminci, mai-hikima”