Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 9/1 pp. 20-25
  • ‘Ka Nemi Salama, Ka Bi Ta Kuma’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Ka Nemi Salama, Ka Bi Ta Kuma’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Ku Zama Lafiya da Dukan Mutane”
  • Sada Zumunta a Hidima
  • Masu Zaman Lafiya a Cikin Iyali
  • Masu Neman Zaman Lafiya a Ikilisiya
  • ‘Salama ta Zama Mulkinku’
  • Ta Yaya Za Mu Zama Masu Salama?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • ‘Ku Zauna Lafiya Da Dukan Mutane’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ku Biɗi Salama
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 9/1 pp. 20-25

‘Ka Nemi Salama, Ka Bi Ta Kuma’

“Idan ya yiwu, ku zama lafiya da dukan mutane, gwargwadon iyawarku.”—ROMAWA 12:18.

1, 2. Waɗanne dalilai ne suka sa salama ta mutane ba za ta daɗe ba?

KA YI tunanin wani gida da ba shi da ƙarfi, katakonsa sun ruɓe, rufinsa yana rawa. Za ka so ka ƙaura zuwa gidan ka mai da shi gidanka? A’a ba za ka so ba. Ko sabon fenti ba zai canja gaskiyar cewa gidan ba shi da ƙarfi ba. Ko ba jima ko ba daɗe, gidan zai rushe.

2 Kowacce salama da take da tushe daga wannan duniya kamar wannan gidan take. An gina bisa yashi, wato—alkawura da kuma basirar mutum, “wanda babu taimako gareshi.” (Zabura 146:3) Tarihi dogon jeri ne na tashin hankali tsakanin al’ummai, ƙabilai, da kuma yare. Hakika, akwai ɗan lokaci na salama, amma wace irin salama? Idan al’ummai biyu suna yaƙi kuma aka samu salama domin an ci al’umma ɗaya ko kuma dukan al’ummai biyun sun ga cewa yaƙi ba riba, wace irin salama ce wannan? Ƙiyayya, tuhuma, da kuma kishi da suka jawo yaƙin har yanzu suna nan. Salamar da ‘fenti’ ne kawai don rufe ƙiyayyar, ba salama ba ce mai ƙwari.—Ezekiel 13:10.

3. Me ya sa salamar mutanen Allah ta bambanta daga duk wata salama ta mutane?

3 Duk da haka, da akwai salama ta gaskiya a wannan duniya da yaƙi ya raba ta. A ina? A tsakanin masu bin sawun Yesu Kristi, Kiristoci na gaskiya waɗanda suka bi kalmomin Yesu kuma suke ƙoƙari su bi hanyar rayuwarsa. (1 Korinthiyawa 11:1; 1 Bitrus 2:21) Salamar da ta kasance tsakanin Kiristoci na gaskiya masu launin fata dabam dabam, matsayi, da kuma ƙasashe ta gaskiya ce domin ta taso ne daga dangantaka ta salama da suke da ita da Allah, wadda tana bisa bangaskiyarsu ne ga hadayar fansa ta Yesu Kristi. Salamarsu kyauta ce daga Allah, ba aba ba ce da mutane suka yi. (Romawa 15:33; Afisawa 6:23, 24) Sakamakon miƙa kansu ga “Sarkin Salama,” Yesu Kristi, da kuma bauta wa Jehovah, “Allah kuwa na ƙauna da na salama.”—Ishaya 9:6; 2 Korinthiyawa 13:11.

4. Ta yaya Kirista zai “nemi” salama?

4 Salama ba ta zuwa haka kawai ga mutane ajizai. Saboda haka, Bitrus ya ce kowanne Kirista ya kamata ya “nemi salama, ya bi ta kuma.” (1 Bitrus 3:11) Ta yaya za mu yi wannan? Wani annabci na dā ya ba da amsar. Da yake magana ta bakin Ishaya, Jehovah ya ce: “Dukan ’ya’yanki kuma za su zama masu-koyi na Ubangiji: lafiyar ’ya’yanki kuma mai-girma ce.” (Ishaya 54:13; Filibbiyawa 4:9) Hakika, salama ta gaskiya tana zuwa ga waɗanda suka bi koyarwa ta Jehovah. Bugu da ƙari, salama, tare da ‘ƙauna, da farinciki, . . . tsawon jimrewa, nasiha, nagarta, aminci, tawali’u, kamewa,’ su ne ’ya’yan ruhu mai tsarki na Allah. (Galatiyawa 5:22, 23) Mutumin da ba shi da ƙauna, farin ciki, haƙuri, kirki, aminci, mai zafin hali, kamewa, ko kuma mugu ba zai more ta ba.

“Ku Zama Lafiya da Dukan Mutane”

5, 6. (a) Menene bambanci tsakanin kasancewa da zaman lafiya da kuma sada zumunta? (b) Ga su waye Kiristoci za su yi ƙoƙari su sada zumunta?

5 An fassara salama cewa yanayi ne da babu tashin hankali. Irin wannan fassarar ta ƙunshi yanayi da yawa da babu jayayya. To, har macacce ma yana da salama! Don mutum ya more salama ta gaskiya, yana bukatar fiye da kasancewa kawai da zaman lafiya. A Huɗubarsa a kan Dutse, Yesu ya ce: “Masu-albarka ne masu-sada zumunta: gama za a ce da su ’ya’yan Allah.” (Matta 5:9) Yesu yana magana ne da mutane waɗanda daga baya za su samu gatar zama ’ya’yan Allah a ruhaniya da samun rai mara mutuwa a sama. (Yohanna 1:12; Romawa 8:14-17) A ƙarshe, dukan mutane masu aminci da ba su da begen zuwa sama za su more “ ’yanci na darajar ’ya’yan Allah.” (Romawa 8:21) Masu zumunta ne kaɗai za su iya samun wannan begen. Kalmar Helenanci na “masu-sada zumunta” a zahiri tana nufin “masu kawo zaman lafiya.” Sau da yawa da bambanci tsakanin kasancewa da zaman lafiya—babu tashin hankali—da kasancewa mai sada zumunci. Kasancewa mai sada zumunci a Nassi na nufin aiki tuƙuru don ɗaukaka zaman lafiya, a wasu lokatai kawo zaman lafiya a inda dā babu.

6 Da wannan a zuci, ka yi la’akari da gargaɗin manzo Bulus zuwa ga Romawa: “Idan ya yiwu, ku zama lafiya da dukan mutane, gwargwadon iyawarku.” (Romawa 12:18) Bulus ba gaya wa Romawa yake yi ba kawai su kasance da kame kai, ko da yake wannan zai taimaka. Yana ƙarfafa su ne su sada zumunta. Da waye? Da “dukan mutane”—cikin iyali, ’yan’uwa masu bi, har da waɗanda ba sa imaninmu. Ya ƙarfafa Romawa su sada zumunta da wasu ‘gwargwadon iyawarsu.’ A’a, ba ya son su yi shirka domin salama. Maimakon jawo hamayya babu gaira tsakaninsu da wasu, ya kamata su bi su da zaman lafiya. Kiristoci za su yi haka ne ko suna sha’ani da waɗanda suke ciki ko kuma waje da ikilisiya. (Galatiyawa 6:10) Cikin jituwa da wannan, Bulus ya rubuta: “Kullum a biɗi abin da ke nagari zuwa ga juna ga dukan mutane kuma.”—1 Tassalunikawa 5:15.

7, 8. Ta yaya kuma me ya sa Kiristoci suke sada zumunta da waɗanda ba su yarda da imaninsu ba?

7 Ta yaya za mu sada zumunta da waɗanda ba su yarda da imaninmu ba kuma wataƙila sun yi hamayya da mu? Hanya ɗaya ita ce guje wa halin nuna mun fi daraja. Alal misali, da kyar zai kasance sada zumunta idan muka yi baƙar magana ga wasu. Jehovah ya bayyana hukuncinsa bisa ƙungiyoyi da kuma azuzuwa, amma ba mu da damar yin maganar wani kamar an riga an hukunta shi. Hakika, ba ma hukunta wasu, har ma da masu hamayya da mu. Bayan ya gaya wa Titus ya gargaɗi Kiristoci na Karita game da sha’aninsu da mutane masu iko, Bulus ya tunasar da su “kada su ambaci kowa da mugunta, su kasance marasa-faɗa, masu-laushin hali, suna nuna iyakacin tawali’u ga dukan mutane.”—Titus 3:1, 2.

8 Sada zumunci da waɗanda ba su yarda da imaninmu ba zai gabatar musu da gaskiya. Ko da yake, ba ma abokantaka da zai “ɓata halaye na kirki.” (1 Korinthiyawa 15:33) Duk da haka, za mu iya mai da hankali, kuma ya kamata mu bi da mutane da daraja da kuma kirki na ’yan Adam. Bitrus ya rubuta: “Kuna al’amura na dacewa wurin Al’ummai; domin, yayinda su ke kushenku kamar ma’aikatan mugunta, ta wurin nagargarun ayyukanku da su ke dubawa su ɗaukaka Allah cikin ranar ziyara.”—1 Bitrus 2:12.

Sada Zumunta a Hidima

9, 10. Wane misali manzo Bulus ya ƙafa na bi da marasa bi cikin zaman lafiya?

9 An san Kiristoci na farko domin gaba gaɗinsu. Ba su rage ƙarfin saƙonsu ba, kuma lokacin da suka fuskanci hamayya, suna shirye su yi wa Allah biyayya fiye da mutum. (Ayukan Manzanni 4:29; 5:29) Ko da yake, ba su birkice gaba gaɗi da taurin kai ba. Ka yi la’akari da halin Bulus yayin da ya kāre bangaskiyarsa a gaban Sarki Hirudus Agaribas na II. Hirudus Agaribas yana zina da ƙanwarsa, Bernice. Amma, Bulus bai fito ya yi wa Agaribas lacca ba a kan ɗabi’a. Maimakon haka, ya nanata abubuwa da dukansu biyu suka yarda da shi, ya bai wa Agaribas girman masani ƙwarai wajen al’adun Yahudawa kuma wanda ya gaskata da annabawa.—Ayukan Manzanni 26:2, 3, 27.

10 Bulus yana ɗaukaka mutumin ne kawai wanda zai iya ba shi ’yanci? A’a. Bulus ya bi shawara da ya bayar ne ya faɗi gaskiya. Babu aba da ya gaya wa Agaribas da ba gaskiya ba ce. (Afisawa 4:15) Amma Bulus mai neman zaman lafiya ne kuma ya san yadda zai “zama dukan abu ga dukan mutane.” (1 Korinthiyawa 9:22) Burinsa shi ne ya kāre ’yancinsa na wa’azi game da Yesu. Tun da ƙwararren malami ne, ya fara faɗar abin da Agaribas zai yarda da shi. Saboda haka, Bulus ya taimaki malalacin sarki, Kiristanci ya burge shi.—Ayukan Manzanni 26:28-31.

11. Ta yaya za mu zama masu neman zaman lafiya a hidimarmu?

11 Ta yaya za mu zama masu neman zaman lafiya a hidimarmu? Kamar Bulus, mu guji musu. Hakika, a wasu lokatai muna bukatar “faɗin maganar Allah banda tsoro,” mu kāre bangaskiyarmu da gaba gaɗi. (Filibbiyawa 1:14) Amma a yawancin lokatai ainihin burinmu shi ne mu yi wa’azin bishara. (Matta 24:14) Idan mutum ya ga gaskiya game da nufin Allah, zai fara kawar da ra’ayoyi na ƙarya na addinai kuma ya tsabtace kansa daga ayyuka marasa tsabta. Ga yadda ya yiwu, yana da kyau mu nanata abubuwa da masu sauraro za su so, farawa da abubuwa da dukanmu muka yarda. Zai kasance babu riba idan muka yi hamayya da mutum da, idan ka bi shi da basira, zai saurari saƙonmu.—2 Korinthiyawa 6:3.

Masu Zaman Lafiya a Cikin Iyali

12. A waɗanne hanyoyi ne za mu zama masu neman zaman lafiya a cikin iyali?

12 Bulus ya ce waɗanda suka yi aure za su “sha wahala a cikin jiki.” (1 Korinthiyawa 7:28) Za su fuskanci wahala iri dabam dabam. Tsakanin wasu abubuwa, wasu da suka yi aure za su fuskanci rashin jituwa a wasu lokatai. Ta yaya za a bi da wannan? Cikin salama. Mai neman zaman lafiya zai yi ƙoƙarin ya hana jayayya daga ci gaba. Ta yaya? Na farko, ta wajen tsare harshensa. Idan aka yi amfani da shi aka yi baƙar magana kuma aka yi zagi, wannan ƙanƙanin gaɓa da gaske “mugunta ne shi mara-hutu, cike da guba mai-mataswa.” (Yaƙub 3:8) Mai neman zaman lafiya yana amfani ne da harshensa ya gina maimakon ya rushe.—Misalai 12:18.

13, 14. Ta yaya za mu riƙe salama lokacin da muka yi kuskure cikin magana ko kuma lokacin da ake tashin hankali?

13 Domin ajizai ne mu, dukanmu wani lokaci muna faɗar abin da daga baya za mu yi nadama. Idan haka ya faru, ka yi sauri ka yi gyara—ka kawo zaman lafiya. (Misalai 19:11; Kolossiyawa 3:13) Ka guji kamuwa cikin “muhawara ta kalmomi” da kuma ‘gardama game da ababa da ba su da muhimmanci.’ (1 Timothawus 6:4, 5) Maimakon haka, ka duba da idon basira, ka yi ƙoƙari ka fahimci yadda matarka take ji. Idan aka yi maka baƙar magana, kada ka rama. Ka tuna cewa “mayarda magana da taushi ya kan juyadda hasala.”—Misalai 15:1.

14 A wasu lokatai, za ka bukaci ka bincika gargaɗi na Misalai 17:14: “Ka daina muhawara, tun ba ta zama faɗa ba.” Ka ja baya daga yanayi da yake so ya zama na faɗa. Daga baya, lokacin da aka huce, wataƙila za ku iya sulhunta cikin salama. A wasu yanayi, zai fi kyau a kira Kirista mai kula da ya manyanta ya taimaka. Waɗannan mutane masu basira kuma masu juyayi suna iya wartsakarwa lokacin da salama cikin aure ta fuskanci razana.—Ishaya 32:1, 2.

Masu Neman Zaman Lafiya a Ikilisiya

15. In ji Yaƙub, wane mummunan hali ne ya taso a tsakanin wasu Kiristoci, kuma me ya sa wannan hali “ta duniya” ce, “ta jiki,” kuma “ta Shaiɗan”?

15 Abin baƙin ciki, wasu Kiristoci na ƙarni na farko sun ba da tabbaci na kishi da kuma tsaguwa—waɗanda suke saɓani da salama. Yaƙub ya ce: “Wannan hikima ba hikima mai-saukowa daga bisa ba, amma ta duniya ce, ta jiki, ta Shaiɗan. Gama wurinda kishi da tsaguwa su ke, nan akwai yamutsai da kowane irin mugun al’amari.” (Yaƙub 3:14-16) Wasu sun gaskata cewa kalmar Helenanci da aka fassara ta “tsaguwa” tana nufin buri ne na son kai, kokawa domin matsayi. Da dalili mai kyau kuwa Yaƙub ya ce da ita “ta duniya, ta jiki, ta Shaiɗan.” A dukan tarihi, masu mulki na duniya sun nuna tsaguwa, kamar dabbobin daji suna yaƙi da junansu. Tsaguwa da gaske “ta duniya” ce, kuma “ta jiki.” Har ila kuma “ta Shaiɗan” ce. Wannan mugun hali mala’ika mai neman iko ne ya nuna shi da farko, wanda ya yi hamayya da Jehovah Allah ya zama Shaiɗan, sarkin aljanu.

16. Ta yaya wasu Kiristoci na ƙarni na farko suka nuna irin halin Shaiɗan?

16 Bulus ya aririci Kiristoci su yi tsayayya da koyar halin tsaguwa, domin ba ya kawo salama. Ya rubuta: “Daga ina fa yaƙe-yaƙe, daga ina husumai a tsakaninku? ba daganan ne ba, cikin sha’awoyinku da su ke yaƙi a cikin gaɓaɓuwanku?” (Yaƙub 4:1) A nan “sha’awoyinku” na nufin sha’awar haɗama ta abin duniya ko kuma muradin zama sananne, mai iko, ko kuma mai rinjaya. Kamar Shaiɗan, babu shakka wasu cikin ikilisiya suna so su zama masu ɗaukaka maimakon ‘ƙanana,’ kamar yadda Yesu ya ce mabiyansa na gaskiya za su zama. (Luka 9:48) Irin wannan halin zai iya hana ikilisiya salama.

17. Ta yaya Kiristoci a yau za su zama masu neman zaman lafiya a ikilisiya?

17 A yau, dole ne mu yi tsayayya da halin son abin duniya, kishi, da kuma dogon buri. Idan muka kasance masu neman zaman lafiya da gaske, ba za mu razana ba idan wasu cikin ikilisiya sun fi mu a wasu ayyuka, ba za mu kuma kushe wa wasu ba a gaban mutane ta wajen tambayar dalilin abin da suka yi. Idan mun ƙware a wani abu, ba za mu yi amfani da shi ba mu nuna mun fi wasu, kamar ikilisiyar za ta ci gaba ne kawai domin iyawarmu da kuma ilimi. Irin wannan halin zai jawo rabuwa ne; ba zai kawo salama ba. Masu neman zaman lafiya ba sa nuna ƙwarewarsu amma suna yin amfani da shi su yi hidima wa ’yan’uwansu kuma su daraja Jehovah. Sun fahimci cewa a ƙarshe, ƙauna ce—ba iyawa ba—take bayyana Kirista na gaskiya.—Yohanna 13:35; 1 Korinthiyawa 13:1-3.

‘Salama ta Zama Mulkinku’

18. Ta yaya dattawa za su ɗaukaka salama tsakaninsu?

18 Dattawan ikilisiya ne suke ja-gora wajen zama masu neman zaman lafiya. Jehovah ya ce game da mutanensa: “Zan sa salama ta zama mulkinki, adalci kuma ya zama mahukuncinki.” (Ishaya 60:17) Cikin jituwa da wannan kalmomin annabci, waɗanda suke hidima ta makiyaya na Kirista suna aiki tuƙuru wajen ɗaukaka salama tsakaninsu da kuma tsakanin tumakin. Dattawa za su iya kasancewa da salama tsakaninsu wajen neman zaman lafiya da kuma la’akari na “hikima mai-fitowa daga bisa.” (Yaƙub 3:17) Da bambanci da suke da shi wajen reno da kuma abin da suka fuskanta a rayuwa, dattawa a ikilisiya wani lokaci za su kasance da bambancin ra’ayi. Wannan yana nufin cewa ba su da salama ne? A’a, idan aka bi da irin wannan yanayin yadda ya dace. Masu neman zaman lafiya, cikin tawali’u za su furta ra’ayinsu kuma cikin girmama wasu za su saurari na wasu. Maimako ya dage bisa nasa ra’ayi, mai neman zaman lafiya zai yi la’akari da ra’ayin ɗan’uwansa cikin addu’a. Idan babu wani mizani na Littafi Mai Tsarki da aka taka, da zarafin amfani da ra’ayoyi dabam dabam. Idan wasu ba su yarda da ra’ayinsa ba, mai neman zaman lafiya zai bi kuma zai tallafa wa shawarar da jama’a suka tsai da. Da haka zai nuna yana da la’akari. (1 Timothawus 3:2, 3) Ƙwararrun dattawa sun san cewa neman salama ya fi muhimmanci fiye da dagewa bisa namu ra’ayi.

19. Ta yaya dattawa suke neman salama cikin ikilisiya?

19 Dattawa suna ɗaukaka salama da waɗanda suke cikin ikilisiya ta wajen tallafa musu da kuma kasancewa marasa kushe ƙoƙarce-ƙoƙarcensu. Hakika, a wasu lokatai wasu za su bukaci a yi musu gyara. (Galatiyawa 6:1) Amma ainihin aikin Kirista mai kula ba yin horo ba ne. Yana yabawa sau da yawa. Dattawa masu ƙauna suna ƙoƙari su ga dacewar wasu. Dattawa suna sha’awar aiki tuƙuru da ’yan’uwansu Kiristoci suke yi, kuma suna da tabbacin cewa ’yan’uwansu masu bi suna yin iyakar ƙoƙarinsu.—2 Korinthiyawa 2:3, 4.

20. Ta wace hanya ce ikilisiya za ta amfana idan duka suka kasance masu neman zaman lafiya?

20 Saboda haka, a cikin iyali, a cikin ikilisiya, da kuma bi da waɗanda ba su gaskata imaninmu ba, muna ƙoƙari mu kasance masu neman zaman lafiya, masu aikin salama. Idan muka koyi salama, za mu ƙara ga farin cikin ikilisiya. Ta haka, za a kāre mu kuma a ƙarfafa mu ta hanyoyi da yawa, kamar yadda za mu gani a talifi na gaba.

Ka Tuna?

• Me yake nufi a kasance mai neman zaman lafiya?

• Ta yaya za mu zama masu neman zaman lafiya da waɗanda ba Shaidu ba?

• A waɗanne hanyoyi ne za a koyi salama cikin iyali?

• Ta yaya dattawa za su ɗaukaka salama cikin ikilisiya?

[Hoto a shafi na 21]

Masu neman zaman lafiya suna guje wa halin nuna sun fi daraja

[Hotuna a shafi na 22]

Kiristoci masu neman zumunta ne a hidima, a gida, da kuma a ikilisiya

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba