-
Ka Koyi Darasi Daga Kwatancin TalantiHasumiyar Tsaro—2015 | 15 Maris
-
-
MUGUN BAWA MAI ƘIWUYA
14, 15. Shin Yesu yana nufin cewa ’yan’uwansa shafaffu da yawa za su zama mugaye da kuma masu ƙiwuya? Ka yi bayani.
14 A kwatancin, bawa na ƙarshe ya binne talantinsa maimakon ya yi kasuwanci da shi ko kuma ya ba masu juya kuɗi. Wannan mugun bawa ne don bai so maigidan ya sami riba ba. Shi ya sa maigidan ya kira shi “mugun bawa mai-ƙiwuya.” Maigidan ya karɓi talantin daga hannunsa kuma ya ba wa bawa mai goma. Sai aka jefar da mugun bawan “cikin baƙin duhu.” A wurin ne zai “yi kuka da cizon haƙora.”—Mat. 25:24-30; Luk. 19:22, 23.
15 Ɗaya daga cikin bayin maigidan guda uku ya ɓoye talantinsa, shin Yesu yana nuna cewa kashi ɗaya cikin uku na mabiyansa shafaffu za su zama mugaye da kuma masu ƙiwuya? A’a. Ka yi la’akari da mahallin. A kwatancin bawan nan mai aminci mai hikima, Yesu ya yi maganar mugun bawa da yake dūkan ’yan’uwansa bayi. Ba wai yana nufin cewa za a yi wani rukunin mugun bawa ba. A maimakon haka, yana jan kunnen bawan nan mai aminci ne cewa kada ya zama kamar mugun bawa. Hakazalika, a almarar budurwai goma, Yesu ba ya nufin cewa rabin mabiyansa shafaffu za su zama kamar budurwai biyar marasa azanci. A maimakon haka, yana yi wa ’yan’uwansa shafaffu kashedi ne game da abin da zai faru idan suka daina kasancewa a faɗake da kuma a shirye.f Saboda haka, za mu iya cewa a kwatancin talantin, Yesu ba ya nufin cewa ’yan’uwansa shafaffu da yawa za su zama mugaye da kuma marasa ƙwazo. Akasin haka, Yesu yana yi wa mabiyansa shafaffu gargaɗi cewa su guji ayyuka da halayen mugun bawa kuma su yi ‘ciniki’ da talantin da aka ba su, wato su kasance da ƙwazo.—Mat. 25:16.
-