Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 2/1 pp. 25-29
  • Ka Karɓi “Ruhu Na Gaskiya”?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Karɓi “Ruhu Na Gaskiya”?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ruhun Yana Ba da Shaida
  • Ruhun da Kuma Waɗansu Tumaki
  • Yin Kirki ga ’Yan’uwan Kristi
  • ‘Kada Su Kammala Sai Tare da Mu’
  • Haɗa Kai a Ruhu a Ranar Abin Tuni
  • Ruhun Allah Yana Ba Mu Tabbaci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Tattara Abubuwan Da Ke Cikin Sama Da Waɗanda Ke Bisa Duniya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ruhu Mai Tsarki Yana Shaida Mana
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Menene Jibin Maraice Na Ubangiji Yake Nufi A Gare ka?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 2/1 pp. 25-29

Ka Karɓi “Ruhu Na Gaskiya”?

“Uban . . . za ya ba ku wani Mai-taimako, domin shi zauna tare da ku har abada, shi Ruhu na gaskiya.”—YOHANNA 14:16, 17.

1. Wane abu ne mai muhimmanci Yesu ya sanar da almajiransa a sa’o’i na ƙarshe da yake tare su a ɗakin bene?

“UBANGIJI, ina za ka?” Tambaya ɗaya ke nan da manzannin Yesu suka tambaye shi a sa’o’i na ƙarshe da yake tare da su a ɗakin bene a Urushalima. (Yohanna 13:36) Da taron ya ci gaba, Yesu ya sanar da su cewa yanzu lokaci ya yi domin ya koma ga Ubansa. (Yohanna 14:28; 16:28) Ba zai kasance tare da su ba cikin jiki domin ya koyar da su, kuma ya amsa tambayoyinsu. Amma, ya ba su tabbaci, yana cewa: “Ni ma in roƙi Uban, shi kuma za ya ba ku wani Mai-taimako [ko kuma, mai ta’aziyya], domin shi zauna tare da ku har abada.”—Yohanna 14:16, hasiya ta NW.

2. Menene Yesu ya yi alkawari zai aiko wa almajirai bayan ya tafi?

2 Yesu ya bayyana wannan mataimaki kuma ya bayyana yadda zai taimake almajiransa. Ya gaya musu: “Waɗannan al’amura kuwa ban faɗa muku tun dafari ba, domin ina tare da ku. Amma yanzu ina tafiya wurin wanda ya aiko ni; . . . Yana da amfani a gareku in tafi: gama idan ban tafi ba, Mai-taimakon ba za shi zo wurinku ba; amma idan na tafi, zan aiko shi a gareku. . . . Sa’anda shi, Ruhu na gaskiya, ya taho, za ya bishe ku cikin dukan gaskiya.”—Yohanna 16:4, 5, 7, 13.

3. (a) Yaushe aka aiko da “ruhu mai-gaskiya” ga Kiristoci na farko? (b) Wace hanya ce ɗaya ta musamman ruhun ya kasance “mai-taimako” a gare su?

3 Wannan alkawarin ya cika a Fentakos na shekara ta 33 A.Z., kamar yadda manzo Bitrus ya shaida: “Wannan Yesu, Allah ya tashe shi, mu kuma duka shaidu ne ga wannan. Da shi ke fa an ɗaukaka shi ga hannun dama na Allah, ya kuma karɓi alkawari na Ruhu Mai-tsarki daga wurin Uba, ya zubo da wannan, abin da ku ke gani kuna ji kuma.” (Ayukan Manzanni 2:32, 33) Kamar yadda za mu gani a nan gaba, ruhu mai tsarki da aka zubo a ranar Fentikos ya kammala abubuwa da yawa ga Kiristoci na farko. Amma Yesu ya yi alkawari cewa “ruhu mai-gaskiya” zai ‘tuna musu dukan abin da ya gaya musu.’ (Yohanna 14:26) Zai sa su tuna hidimar Yesu da kuma koyarwarsa, har ma da kalmominsa, kuma su rubuta su. Wannan babu shakka zai kasance da muhimmanci ga manzo Yohanna da ya riga ya tsufa a ƙarshen ƙarni na farko A.Z., sa’ad da ya fara rubuta labarin Linjila. Wannan labarin ya haɗa da gargaɗi mai kyau da Yesu ya yi sa’ad da ya kafa Bikin Tuna da mutuwarsa.—Yohanna, surori 13-17.

4. Ta yaya “ruhu mai-gaskiya” ya taimaka wa shafaffun Kiristoci na farko?

4 Yesu kuma ya yi alkawari wa almajirai na farko cewa ruhun zai ‘koyar da su dukan abu’ kuma ya ‘ja-gorance su cikin dukan gaskiya.’ Ruhun zai taimake su su fahimci abubuwa masu zurfi na Nassosi kuma ya kāre haɗin kansu wajen tunani, fahimta, da kuma nufi. (1 Korinthiyawa 2:10; Afisawa 4:3) Saboda haka, ruhu mai tsarki ya ba wa waɗannan Kiristoci na farko iko su aikata su rukunin “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” su ba wa shafaffun Kiristoci ɗaɗɗaya abinci na ruhaniya a “lotonsa.”—Matta 24:45.

Ruhun Yana Ba da Shaida

5. (a) Menene Yesu ya bayyana wa almajiransa a daren 14 ga Nisan, 33 A.Z.? (b) Wane aiki ruhu mai tsarki zai yi wajen cika alkawarin Yesu?

5 A daren 14 ga Nisan, 33 A.Z., Yesu ya sanar da almajiransa cewa a nan gaba zai marabce su kuma za su zauna tare da shi da kuma Ubansa a sama. Ya gaya musu: “A cikin gidan Ubana akwai wurin zama dayawa; da ba haka ba, da na faɗa muku; gama zan tafi garin in shirya muku wuri. Kadan na tafi na shirya muku wuri kuma, shi in sake dawowa, in karɓe ku wurin kaina; domin wurin da ni ke, ku zauna kuma.” (Yohanna 13:36; 14:2, 3) Za su yi sarauta tare da shi a Mulkinsa. (Luka 22:28-30) Domin su samu irin wannan bege na sama, to, dole ne a ‘haife su daga ruhu’ su zama ’ya’yan Allah na ruhaniya kuma a naɗa su su zama sarakuna da kuma firistoci tare da Kristi a sama.—Yohanna 3:5-8; 2 Korinthiyawa 1:21, 22; Titus 3:5-7; 1 Bitrus 1:3, 4; Ru’ya ta Yohanna 20:6.

6. (a) Yaushe kira zuwa sama ta fara, kuma guda nawa aka kira? (b) Waɗanda aka kira sun yi baftisma cikin menene?

6 Wannan ‘kira zuwa sama’ ta fara ne a Fentikos na shekara ta 33 A.Z., kuma ainihinta, ta bayyana kamar ta ƙare a tsakiyar shekarun 1930. (Ibraniyawa 3:1) Adadin waɗanda ruhu mai tsarki ya hatimce su su kasance cikin Isra’ila ta ruhaniya 144,000 ne, an ‘fanshe su cikin mutane.’ (Ru’ya ta Yohanna 7:4; 14:1-4) An yi wa waɗannan baftisma cikin jikin ruhaniya ta Kristi, cikin ikilisiyarsa, da kuma cikin mutuwarsa. (Romawa 6:3; 1 Korinthiyawa 12:12, 13, 27; Afisawa 1:22, 23) Bayan baftismarsu cikin ruwa da kuma shafe su da ruhu mai tsarki, sun shiga cikin tafarkin sadaukarwa, rayuwar aminci har mutuwarsu.—Romawa 6:4, 5.

7. Me ya sa shafaffun Kiristoci ne kawai suke cin alamun yadda ya dace a Abin Tunin?

7 Tun da Isra’ilawa ne na ruhaniya, waɗannan shafaffu Kiristoci suna cikin sabon alkawari da aka yi da Jehovah da kuma “Isra’ila ta Allah.” (Galatiyawa 6:16; Irmiya 31:31-34) Sabon alkawarin, jinin Kristi da aka zubar ne ya kafa shi. Yesu ya faɗi haka sa’ad da ya kafa Bikin Tuna mutuwarsa. Luka ya rubuta: “Ya ɗauki gurasa kuma, sa’anda ya yi godiya, ya kakkarya, ya ba su, ya ce, Wannan jikina ne wanda an bayar domin ku: ku yi wannan abin tunawa da ni. Hakanan kuma bayan jibi, ya ɗauki ƙoƙo, ya ce, Wannan ƙoƙo sabon alkawari ne cikin jinina, wanda an zubar dominku.” (Luka 22:19, 20) Raguwa, ko kuma raguwar waɗannan 144,000 har yanzu suna duniya, waɗannan su ne suke cin gurasa da shan giya yadda ya dace a Bikin Tuna mutuwar Kristi.

8. Ta yaya shafaffu suke sani cewa an kira su zuwa sama?

8 Ta yaya shafaffun suka sani cewa an kira su zuwa sama? Suna ganin shaidar ruhu mai tsarki babu kuskure. Manzo Bulus ya rubuta wa irin waɗannan: “Iyakar waɗanda Ruhun Allah ke bishe su, waɗannan ’ya’yan Allah ne. . . . Ruhu da kansa tare da namu ruhu yana shaida, mu ’ya’yan Allah ne; idan ’ya’ya ne fa, magada ne kuma; magadan Allah, masu-tarayyan gādo da Kristi; in fa muna raɗaɗi tare da shi, domin kuma mu ɗaukaka tare da shi.” (Romawa 8:14-17) Wannan shaidar ta ruhu tana da ƙarfi sosai da waɗanda suke da ɗan shakka game da kira zuwa sama za su iya kammalawa cewa ba a kira su ba, kuma saboda haka za su daina cin alamun a Abin Tuni.

Ruhun da Kuma Waɗansu Tumaki

9. Waɗanne rukunoni biyu ne aka ambata a cikin Linjila da kuma littafin Ru’ya ta Yohanna?

9 Tuna adadin Kiristoci da aka kira su zama Isra’ila ta ruhaniya, Yesu ya kira su “ƙaramin garke.” An karɓe su cikin “garke” na sabon alkawari, akasarin “waɗansu tumaki” da ba su da iyaka waɗanda Yesu ya ce dole ne ya tara su. (Luka 12:32; Yohanna 10:16) Waɗannan waɗansu tumaki da aka tara a lokaci na ƙarshe za su zama “taro mai-girma” da aka ƙaddara musu tsira daga “babban tsananin,” da begen rayuwa har abada a cikin aljanna a duniya. Abin farin ciki, wahayin da aka ba Yohanna a ƙarshen ƙarni na farko A.Z., ya bambanta tsakanin taro mai girma da kuma 144,000 na Isra’ila na ruhaniya. (Ru’ya ta Yohanna 7:4, 9, 14) Shin waɗansu tumakin ma sun samu ruhu mai tsarki ne, idan sun samu, ta yaya wannan ya taɓa rayuwarsu?

10. Ta yaya aka yi wa waɗansu tumakin baftisma “cikin sunan Uba da na Ɗa, da na Ruhu Mai-tsarki”?

10 Ruhu mai tsarki ya yi aiki mai muhimmanci a rayuwar waɗansu tumaki. Sun nuna keɓe kansu ga Jehovah ta wajen yin baftisma “cikin sunan Uba da na Ɗa, da na Ruhu Mai-tsarki.” (Matta 28:19) Sun fahimci, mulkin mallaka na Jehovah, sun miƙa kai ga Kristi Sarkinsu kuma Mai Ceto, suna bin ja-gorar ruhun Allah, ko kuma ikon aiki, a rayuwarsu. Kowacce rana, suna koyon “ɗiyar ruhu” a rayuwarsu, na “ƙauna, farinciki, salama, tsawon jimrewa, nasiha, nagarta, aminci, tawali’u, kamewa.”—Galatiyawa 5:22, 23.

11, 12. (a) Ta yaya aka tsarkake shafaffun a hanya ta musamman? (b) Waɗanne hanyoyi ne aka tsarkake waɗansu tumaki kuma aka mai da su masu tsarki?

11 Dole ne kuma waɗansu tumakin su ƙyale Kalmar Allah da kuma ruhunsa mai tsarki su tsabtace su, ko kuma su tsarkakke su. Shafaffun an riga an tsarkake su a hanya ta musamman, ta wajen sanar da su adalai ne kuma tsarkakku amaryar Kristi. (Yohanna 17:17; 1 Korinthiyawa 6:11; Afisawa 5:23-27) Annabi Daniel ya yi maganar su cewa “tsarkaka na Maɗaukaki,” waɗanda suka samu Mulki a ƙarƙashin “ɗan mutum,” Yesu Kristi. (Daniel 7:13, 14, 18, 27) Da farko, ta bakin Musa da Haruna, Jehovah ya sanar da al’ummar Isra’ila: “Ni ne Ubangiji Allahnku: ku tsarkake kanku fa, ku zama masu-tsarki; gama ni mai-tsarki ne.”—Leviticus 11:44.

12 Kalmar nan “tsarkakewa” ainihi tana nufin “aikin ko kuma hanyar tsarkake, warewa ko kuma keɓewa domin hidima ko kuma amfani na Jehovah Allah; kasancewa da tsarki, a tsarkake, ko kuma a tsabtace.” Tun kamar ko kuma wajen shekara ta 1938, Hasumiyar Tsaro ta Turanci ta ce su Jonadab, ko kuwa waɗansu tumaki, “dole ne su sani cewa ana bukatar keɓewa da tsarkaka ga dukan wanda zai kasance cikin taro mai girma kuma ya rayu a duniya.” A wahayi game da taro mai girma, da yake rubuce a littafin Ru’ya ta Yohanna, ya yi maganarsu cewa sun “wanke rigunansu, suka faranta su cikin jinin Ɗan ragon” kuma suna yi wa Jehovah “bauta kuma dare da rana cikin haikalinsa.” (Ru’ya ta Yohanna 7:9, 14, 15) Da taimakon ruhu mai tsarki, waɗansu tumakin suna iyakar ƙoƙarinsu su cika bukatar Jehovah na tsarkaka.—2 Korinthiyawa 7:1.

Yin Kirki ga ’Yan’uwan Kristi

13, 14. (a) Daidai da alamar Yesu ta tumaki da awaki, bisa ga menene ceton waɗansu tumaki ya dangana? (b) A wannan zamani na ƙarshe, ta yaya waɗansu tumakin suka yi abin kirki ga ’yan’uwan Kristi?

13 Yesu ya nuna nasaba ta kud da kud tsakanin waɗansu tumaki da ƙaramin garke cikin almararsa ta tumaki da awaki, wannan annabci ya haɗa da “cikar zamani.” A wannan almarar, Kristi ya nuna sarai cewa ceton waɗansu tumaki na da alaƙa ta kusa da halin da suka nuna ga shafaffu, waɗanda ya kira “ ’yan’uwana.” Ya ce: “Sa’annan shi Sarkin za ya ce ma waɗannan da ke hannun damansa, Ku zo, ku masu-albarka na Ubana, ku gaji mulkin da an shirya dominku tun kafawar duniya . . . Hakika ina ce muku, Da shi ke kuka yi wannan ga guda ɗaya a cikin waɗannan ’yan’uwana, ko waɗannan mafiya ƙanƙanta, ni kuka yi ma.”—Matta 24:3; 25:31-34, 40.

14 Furcin nan “da shi ke kuka yi wannan” yana nuna tallafawa ne cikin ƙauna da aka yi wa ’yan’uwan Kristi haifaffu na ruhu, waɗanda duniyar Shaiɗan ta yi musu riƙon baƙi, har ma ta zuba wasu a fursuna. Sun bukaci abinci, tufafi masu kyau, da kuma magani. (Matta 25:35, 36, hasiya.) A wannan ƙarshen zamani, tun daga shekara ta 1914, da yawa cikin shafaffu suna samun kansu cikin irin wannan yanayi. Tarihin Shaidun Jehovah na zamani ya tabbatar da cewa abokanan tarayyarsu, waɗansu tumaki, sun tallafa musu, kamar yadda ruhu ya motsa su.

15, 16. (a) A wane aiki ne musamman waɗansu tumaki suka tallafa wa ’yan’uwan Yesu shafaffu a duniya? (b) Ta yaya shafaffun suka nuna godiyarsu ga waɗansu tumaki?

15 ’Yan’uwan Kristi shafaffu da suke duniya a wannan lokaci na ƙarshe sun samu tallafawa daga waɗansu tumaki wajen cika umurnin Allah na ‘wa’azin bishara kuwa ta mulki cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai.’ (Matta 24:14; Yohanna 14:12) Yayin da adadin shafaffun a duniya yana raguwa a cikin shekaru da suka shige, adadin waɗansu tumakin yana ƙaruwa da ya kai a zahiri miliyoyi. Dubbai cikin waɗannan sun yi hidimar cikakken lokaci—majagaba ko masu wa’azi a ƙasashen waje—suna yaɗa bisharar Mulki zuwa “iyakan duniya.” (Ayukan Manzanni 1:8) Wasu suna yin aikin wa’azi iyakar gwargwadonsu, kuma da farin ciki suna tallafa wa wannan aiki mai muhimmanci da kuɗi.

16 ’Yan’uwan Kristi shafaffu suna godiya ga wannan tallafawar na aminci daga abokan tarayyarsu waɗansu tumaki! Yadda suke ji an furta shi da kyau a cikin littafi nan Worldwide Security Under the “Prince of Peace” wanda ajin bawa suka yi tanadinsa a shekara ta 1986. Ya ce: “Tun daga Yaƙin Duniya na II, cikar annabcin Yesu na ‘cikar zamani’ yawanci domin aikin da ‘taro mai girma’ na ‘waɗansu tumaki’ suka yi ne. . . . Saboda haka, godiya mai yawa ta tabbata ga ‘taro mai girma’ na dukan duniya daga harsuna da yawa domin aiki mai yawa da suka yi wajen cika annabcin [Yesu] a Matta 24:14!”

‘Kada Su Kammala Sai Tare da Mu’

17. A wace hanya ce mutane amintattu na dā waɗanda za a tashe su daga matattu a duniya ba za su “kammala sai tare da” shafaffu?

17 Da yake magana tun yana ɗaya cikin waɗanda aka shafe kuma da yake magana game da maza da mata amintattu da suka rayu kafin Kristi, manzo Bulus ya rubuta: “Waɗannan duka fa, da aka bada shaida a kansu ta wurin bangaskiyarsu, ba su amshi alkawarin ba; Allah ya rigaya ya tanada wani abu mafi kyau domin mu [shafaffu], kada su kammala sai tare da mu.” (Ibraniyawa 11:35, 39, 40) A lokacin Alif, Kristi da kuma ’yan’uwansu shafaffu 144,000 a sama za su zama sarakuna da kuma firistoci kuma su ba da amfanin hadayar fansa ta Kristi a duniya. Saboda haka, waɗansu tumaki za su kamilta ‘a jiki da kuma a azanci.’—Ru’ya ta Yohanna 22:1, 2.

18. (a) Menene ya kamata gaskiyar Littafi Mai Tsarki ta taimake waɗansu tumaki su fahimta? (b) Ga wane bege waɗansu tumaki suke jira “bayyanuwar ’ya’yan Allah”?

18 Dukan wannan ya kamata ya saka a zuciyar waɗansu tumaki dalilin da ya sa Nassosin Helenanci na Kiristoci ya mai da hankali sosai bisa Kristi da kuma ’yan’uwansa shafaffu da kuma ainihin aikinsu wajen cika nufe-nufen Jehovah. Saboda haka, waɗansu tumaki sun ga gata ce su tallafa a dukan wata hanya da za ta yiwu ga ajin bawa shafaffu yayin da suke jiran “bayyanuwar ’ya’yan Allah” a Armageddon da kuma lokacin Alif. Za su iya saurarar lokacin “tsira daga bautar ɓacewa zuwa cikin ’yanci na darajar ’ya’yan Allah.”—Romawa 8:19-21.

Haɗa Kai a Ruhu a Ranar Abin Tuni

19. Menene “ruhu na gaskiya” ya yi ga shafaffu da kuma abokan tarayyarsu, kuma ta yaya musamman za su kasance da haɗin kai a maraice ranar 28 ga Maris?

19 A cikin addu’arsa ta ƙarshe a daren 14 ga Nisan, 33 A.Z., Yesu ya ce: “Ni ke yin addu’a . . . domin su duka su zama ɗaya; kamar yadda kai, Uba, kana cikina, ni kuma a cikinka, domin su kuma su zama cikinmu: domin duniya ta gaskata kai ne ka aiko ni.” (Yohanna 17:20, 21) Cikin ƙauna, Allah ya aiko Ɗansa ya ba da ransa domin ceton shafaffu da kuma duniyar mutane masu biyayya. (1 Yohanna 2:2) “Ruhu na gaskiya” ya haɗa kan ’yan’uwan Kristi da abokan tarayyarsu. A maraicen ranar 28 ga Maris, bayan rana ta faɗi, dukan azuzuwa biyu za su taru su yi Bikin Tuna mutuwar Kristi kuma su tuna da dukan abin da Jehovah ya yi dominsu ta wajen hadayar Ɗansa da yake ƙauna, Yesu Kristi. Bari kasancewarsu a wannan biki mai muhimmanci ya ƙarfafa haɗin kansu kuma ya sabonta ƙudurinsu su ci gaba da yin nufin Allah, da haka su ba da tabbacin cewa suna farin cikin kasancewa tsakanin waɗanda Jehovah yake ƙauna.

A Maimaitawa

• Yaushe aka aiko da “ruhu na gaskiya” zuwa ga Kiristoci na farko, kuma ta yaya ya kasance “mai-taimako”?

• Ta yaya shafaffu suke sani cewa an kira su zuwa sama?

• A wace hanya ce ruhun Allah yake aiki bisa waɗansu tumaki?

• Ta yaya waɗansu tumaki suka yi kirki ga ’yan’uwan Kristi, kuma me ya sa ba za su kammala ba ba tare da shafaffu ba?

[Hoto a shafi na 27]

An zubo “ruhu na gaskiya” bisa almajiran a ranar Fentikos shekara ta 33 A.Z.

[Hotuna a shafi na 29]

Waɗansu tumaki sun yi wa ’yan’uwan Kristi kirki ta wajen tallafa musu a cika umurnin Allah na a yi wa’azi

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba