Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w04 7/1 pp. 20-24
  • ‘Ku Koya Musu Su Kiyaye Duk Iyakar Abin Da Na Umarce Ku’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Ku Koya Musu Su Kiyaye Duk Iyakar Abin Da Na Umarce Ku’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ‘Kuna Koya Musu Su Kiyaye Dukan Abubuwa’
  • ‘Duk Iyakar Abubuwa’
  • “Har Matuƙar Zamani”
  • Ka Nuna Ka Damu
  • “Kullum Ina Tare da Ku”
  • Yadda Za Mu Taimaka wa Mutane Su Bi Umurnan Kristi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • “Ku Je Ku Almajirtar”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ku Je Ku Sa Mutane Su Zama Almajiraina
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Ka Koyi Halayen Da Za Su Taimake Ka Ka Yi Almajirai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
w04 7/1 pp. 20-24

‘Ku Koya Musu Su Kiyaye Duk Iyakar Abin Da Na Umarce Ku’

“Don haka sai ku je ku almajirtar . . . kuna koya musu su kiyaye duk iyakar abin da na umarce ku.”—MATIYU 28:19, 20.

1. Wane taɗi Filibus da mutumin Habasha suka yi?

MUTUMIN Habasha ya yi tafiya mai nisa zuwa Urushalima. Ya je wajen domin ya bauta wa Allah Jehovah, wanda yake ƙauna. Babu shakka, yana ƙaunar hurarriyar Kalmar Allah kuma. Sa’ad da yake dawowa gida cikin karusarsa, yana karatun rubutun annabi Ishaya, almajirin Kristi, Filibus ya sadu da shi. Filibus ya tambayi Bahabashan: “Kana kuwa fahimtar abin da kake karantawa?” Mutumin ya ce: “Ina fa? Sai ko wani ya fassara mini.” Da haka Filibus ya taimaki wannan ɗalibi na Nassi ya zama almajirin Kristi.—Ayyukan Manzanni 8:26–39.

2. (a) A wace hanya ce amsar Bahabashan take da muhimmanci? (b) Waɗanne tambayoyi za mu bincika da suke da nasaba da umurnin Kristi na a almajirtar?

2 Amsar Bahabashan tana da muhimmanci. Ya ce: “Ina fa, sai ko wani ya fassara mini.” Hakika yana bukatar ja-gora, wanda za ya nuna masa hanya. Wannan kalamin yana nuna muhimmancin koyarwa da Yesu ya haɗa cikin umurnin da ya bayar na almajirantarwa. Wane umurni ya bayar? Domin mu sami amsar za mu ci gaba da bincika kalmomin Yesu da suke Matiyu sura 28. Talifi na baya ya yi zance a kan dalilin, da kuma inda za a yi wa’azin. Yanzu za mu yi la’akari da tambayoyi biyu da suke da nasaba da umurnin Kristi a almajirtar—me za a faɗa? kuma har yaushe?

‘Kuna Koya Musu Su Kiyaye Dukan Abubuwa’

3. (a) Ta yaya mutum yake iya zama almajirin Yesu Kristi? (b) Aikin almajirantarwa ya haɗa da menene?

3 Menene za mu koya wa mutane don ya taimake su su zama almajiran Kristi? Yesu ya umarci mabiyansa: “Don haka sai ku je ku almajirtar da dukkan al’ummai, kuna yi musu baftisma da sunan Uba, da Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki, kuna koya musu su kiyaye duk iyakar abin da na umarce ku.” (Matiyu 28:19, 20) Saboda haka, dole ne mu koyar da abin da Kristi ya umurta.a To, me za mu yi don mu tabbata cewa wanda aka koya masa umurnin Yesu zai zama almajiri kuma ya ci gaba da hakan? Mun ga wani abu da za mu yi a kalmomin Yesu masu daɗi. Ka lura: ‘Bai ce kawai ku koya musu abin da na umarce ku’ ba. Maimako, ya ce: ‘Ku koya musu su kiyaye duk iyakar abin da na umurce ku.’ (Matiyu 19:17) Menene wannan ke nufi?

4. (a) Menene yake nufi a kiyaye umurni? (b) Ka bayyana yadda za mu koya wa wani ya kiyaye umurnin Kristi.

4 Kiyaye umurni yana nufin “halin mutum ya jitu” da wani umurni—a yi biyayya ko kuwa kiyaye shi. Ta yaya za mu koya wa wani ya kiyaye, ko ya yi biyayya, da abubuwan da Kristi ya umurta? To, ka yi tunanin wani direba malami da yake koya wa ɗalibai su kiyaye dokokin kan hanya. A cikin aji malamin zai koya wa ɗaliban dokokin kan hanya. Amma, idan ɗaliban za su yi biyayya da dokokin, zai yi musu ja-gora sa’ad da suke tuƙi a kan hanya suna ƙoƙarin yin amfani da abin da suka koya. Haka ma, sa’ad da muka yi nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane muna koya musu umurnin Kristi. Muna kuma bukatar mu yi wa ɗaliban ja-gora sa’ad da suke faman yin biyayya ga umurnin Kristi a rayuwarsu ta yau da kullum da kuma a hidimarsu. (Yahaya 14:15; 1 Yahaya 2:3) Saboda haka, cika umurnin Kristi sosai na mu almajirtar yana bukatar mu zama malamai da kuma masu ja-gora. A ta haka ne za mu yi koyi da misalin da Yesu da Jehovah suka bar mana.—Zabura 48:14; Wahayin Yahaya 7:17.

5. Me zai iya sa wanda muke nazarin Littafi Mai Tsarki da shi ya yi jinkirin bin umurnin Kristi na mu almajirtar?

5 Koya wa mutane su kiyaye umurnin Yesu ya haɗa da taimakonsu su bi umurnin nan su almajirtar. Wasu mutanen da muke nazarin Littafi Mai Tsarki da su, zai iya musu wuya. Idan dā suna zuwan wani coci na Kiristendam ne, ƙila babu wani cikin malamansu na addini da ya koya musu su je su almajirtar. Wasu shugabannin coci sun yarda Kiristendam sun kasa ƙwarai a batun koya wa garkensu su yi wa’azi. Da yake magana game da umurnin Yesu su je cikin duniya su taimaki dukan iri-irin mutane su zama almajirai, masanin Littafi Mai Tsarki John R. W. Stott ya lura: “Kumamanci ne ƙwarai cewa Kiristoci a yau sun kasa bin muhimmin umurnin nan na yin wa’azi.” Ya daɗa cewa: “Kamar muna yin wa’azin ne kawai daga nesa. A wasu lokaci kama muke da mutane da suke yi wa mutanen da ruwa ke cinsu ihu. Ba ma shiga ruwan mu cece su. Domin ba ma son ruwa ya jiƙe mu.”

6. (a) Sa’ad da muke taimakon ɗalibin Littafi Mai Tsarki, ta yaya za mu bi misalin Filibus? (b) Ta yaya za mu nuna wa ɗalibi cewa mun damu da shi sa’ad da ya soma sa hannu a aikin wa’azi?

6 Idan wanda muke nazarin Littafi Mai Tsarki da shi yana wani coci dā, da “ba sa son ruwa ya jiƙe su,” a alamance, zai iya masa wuya ya sha kan tsoron ruwan nan, ya kuma bi umurnin Kristi na a almajirtar. Zai bukaci taimako. Saboda haka, za mu yi haƙuri sa’ad da muke koya masa kuma yi masa ja-gora ya daɗa fahiminsa da zai motsa shi, yadda koyarwar da Filibus ya yi ya wayar da Bahabashan kuma ya motsa shi ya yi baftisma. (Yahaya 16:13; Ayyukan Manzanni 8:35–38) Ban da haka, sha’awarmu mu koya wa ɗaliban Littafi Mai Tsarki su kiyaye umurni na mu almajirtar zai motsa mu mu yi aiki tare da su a yi musu ja-gora a lokaci na farko da suka fito wa’azi.—Mai Hadishi 4:9, 10; Luka 6:40.

‘Duk Iyakar Abubuwa’

7. Koya wa mutane su ‘kiyaye dukan abubuwa’ ta haɗa da koya musu waɗanne dokoki ne?

7 Ba za mu tsaya a koya wa sababbin almajirai kawai su almajirtar ba. Yesu ya umurce mu mu koya wa mutane su ‘kiyaye duk iyakar abin da’ ya umurta. Hakika waɗannan sun haɗa da dokoki biyu mafi muhimmanci—ka ƙaunaci Allah kuma ka ƙaunaci maƙwabcinka. (Matiyu 22:37–39) Ta yaya za a iya koya wa sabon almajiri ya kiyaye waɗannan dokoki?

8. Ka ba da misalin yadda za a iya koya wa sabon ɗalibi ya bi umurnin nuna ƙauna.

8 Ka sake tunanin ɗalibi mai koyon tuƙi. Sa’ad da ɗalibin yake tuƙi a kan hanya tare da malamin, yana koyo ba daga wurin malamin kawai ba amma kuma daga wurin wasu direbobi. Wataƙila malamin zai nuna masa wani direba da ya yi wa wani alheri ya ƙyale mutumin ya shige; ko kuma wanda ya rage wutar mota kada ta kashe wa mai zuwa ido; ko kuma direba da ya taimaka wa wani idon sani da motarsa ta ɓace. Irin waɗannan misalai sa koya wa ɗalibin darussa masu kyau da zai yi amfani da su sa’ad da yake tuƙi. Haka nan ma, sabon almajiri da yake tafiya a kan hanyar rai ba daga wurin malaminsa kaɗai yake koyo ba amma kuma daga nagargarun misalan wasu da yake gani cikin ikilisiya.—Matiyu 7:13, 14.

9. Ta yaya sabon almajiri zai koyi abin da yake nufi a kiyaye umurnin a nuna ƙauna?

9 Ɗalibin Littafi Mai Tsarki zai iya lura da mahaifiya gwauruwa da take ƙoƙarin zuwan Majami’ar Mulki da yaranta suna bin bayanta. Zai iya lura ya ga wani amintacce da yake zuwan taro duk da baƙin ciki da yake damunsa, wata gwauruwa da take kawo wasu tsofaffi zuwa kowane taron ikilisiya, ko kuma wani ƙaramin yaro da yake sharan Majami’ar Mulki. Ɗalibin Littafi Mai Tsarki zai iya lura da wani dattijo na ikilisiya da yake ja-gora a hidimar fage duk da yawan hakkin da yake da su a ikilisiya. Ƙila ya sadu da wani Mashaidi da ya naƙasa da bai iya tafiya ba, yana a gida amma idan aka je gai da shi yakan ƙarfafa mutum sosai. Ƙila ɗalibin ya lura da wasu aurarru da suke gyara rayuwarsu sosai don su kula da iyayensu tsofaffi. Ta wurin lura da Kiristoci masu alheri, masu ba da taimako, kuma amintattu, sabon almajirin yana koyo ta wurin misalan abin da yake nufi a bi umurnin Kristi a ƙaunaci Allah da kuma maƙwabci, musamman ’yan’uwa masu bi. (Karin Magana 24:32; Yahaya 13:35; Galatiyawa 6:10; 1 Timoti 5:4, 8; 1 Bitrus 5:2, 3) A wannan hanyar ce kowanne cikin ikilisiyar Kirista zai iya—kuma ya kamata—ya zama malami da kuma mai ja-gora.—Matiyu 5:16.

“Har Matuƙar Zamani”

10. (a) Har sai yaushe za mu ci gaba da almajirantarwa? (b) Wane misali Yesu ya kafa game da cika aikin?

10 Har yaushe za mu ci gaba da almajirantarwa? A duk matuƙar zamani. (Matiyu 28:20) Za mu iya cika wannan sashen umurni na Yesu kuwa? Muna ƙudura niyyar yin haka mu ikilisiya ta dukan duniya. A shekarun baya, mun yi farin cikin ba da lokacinmu, kuzari, da mallakarmu don mu nemi waɗanda “aka ƙaddara su wa samun rai madawwami.” (Ayyukan Manzanni 13:48) A yanzu, a kowacce rana cikin shekara, Shaidun Jehovah suna ɓatar da sa’o’i fiye da miliyan uku a yin wa’azin Mulkin da kuma almajirantarwa a dukan duniya. Muna yin haka domin muna bin misalin Yesu. Ya ce: ‘Abincina shi ne in aikata nufin wanda ya aiko ni, in kuma cika aikinsa.’ (Yahaya 4:34) Wannan shi ne abin da muke son mu yi. (Yahaya 20:21) Muna son mu soma aikin da aka ba mu; kuma mu cika shi.—Matiyu 24:13; Yahaya 17:4.

11. Menene ya faru da wasu ’yan’uwanmu Kiristoci, kuma wace tambaya ta kamata mu yi?

11 Har ila muna baƙin cikin cewa wasu ’yan’uwanmu sun raunana a ruhaniya saboda haka kuma sun daina cika umurnin Kristi na a almajirtar. Akwai wata hanya ce da za mu taimaka musu su sabonta tarayyarsu da ikilisiya kuma su sake soma sa hannu a almajirantarwa? (Romawa 15:1; Ibraniyawa 12:12) Yadda Yesu ya taimaki manzanninsa lokacin da suka raunana ya nuna abin da ya kamata mu yi a yau.

Ka Nuna Ka Damu

12. (a) Menene manzannin Yesu suka yi ba da daɗewa ba da zai mutu? (b) Yaya Yesu ya bi da manzanninsa duk da raunanarsu?

12 A ƙarshen hidimar Yesu a duniya, lokacin da ya kusan mutuwa, manzanninsa suka “yashe shi, suka yi ta kansu.” Kamar yadda Yesu ya faɗi, suka “warwatsa . . . kowa yā koma gidansu.” (Markus 14:50; Yahaya 16:32) Yaya Yesu ya bi da abokansa da suka raunana? Bai daɗe ba da aka ta da shi daga matattu, Yesu ya gaya wa mabiyansa: “Kada ku ji tsoro, ku je ku gaya wa ’yan’uwana su tafi ƙasar Galili, a can ne za su gan ni.” (Matiyu 28:10) Ko da yake manzannin sun raunana sosai, duk da haka Yesu ya kira su “ ’yan’uwana.” (Matiyu 12:49) Bai fid da tsammani wajensu ba. A wannan hanyar, Yesu ya nuna yadda yake da jinƙai kuma mai gafartawa ne shi, yadda Jehovah yake da jinƙai da kuma gafara. (2 Sarakuna 13:23) Ta yaya za mu iya yin koyi da Yesu?

13. Yaya za mu ɗauki waɗanda suka raunana a ruhaniya?

13 Ya kamata mu damu ƙwarai game da waɗanda suka raunana ko kuma daina sa hannu a hidima. Har ila muna tuna da ayyukan ƙauna da waɗannan ’yan’uwa masu bi suka yi a dā—ƙila na shekaru ma. (Ibraniyawa 6:10) Mun yi rashin tarayyarsu. (Luka 15:4–7; 1 Tasalonikawa 2:17) Amma, ta yaya za mu nuna mun damu da su?

14. Ta yaya za mu taimaki wani raunanne yadda Yesu ya yi?

14 Yesu ya gaya wa manzannin da suka raunana cewa su je Galili a can za su gan shi. Yesu ya gayyace su su halarci wani taro na musamman. (Matiyu 28:10) A yau ma, za mu ƙarfafa waɗanda suka raunana a ruhaniya su halarci taron Kirista a ikilisiya, kuma muna iya ƙarfafa su su yi haka nan sau da sau. Gayyata da aka yi wa manzanni ta kasance da amfani, domin “almajirai goma sha ɗayan nan suka tafi ƙasar Galili, suka je dutsen da Yesu ya umarce su.” (Matiyu 28:16) Mu ma za mu yi farin ciki idan wani da ya raunana ya ji gayyata da muka yi masa kuma ya soma halartan taron Kirista!—Luka 15:6.

15. Ta yaya za mu iya bin misalin Yesu mu marabce waɗanda suka raunana da suke zuwan taronmu?

15 Me za mu yi idan Kirista raunanne ya zo Majami’ar Mulki? Menene Yesu ya yi sa’ad da ya gan manzanninsa, waɗanda suka raunana na ɗan lokaci a inda suke taron? “Sai Yesu ya matso.” (Matiyu 28:18) Bai harare su ba daga inda yake zaune, amma ya je wajensu. Lalle manzannin sun saki jiki sa’ad da Yesu ya ɗauki wannan matakin! Mu ma sai mu ɗauki mataki kuma mu marabci raunannu a ruhaniya da suke ƙoƙarin su komo ikilisiyar Kirista.

16. (a) Menene za mu iya koya daga yadda Yesu ya bi da mabiyansa? (b) Ta yaya za mu iya bin yadda Yesu yake ɗaukan waɗanda suka raunana? (Dubi hasiya.)

16 Menene Yesu ya yi kuma? Da farko ya sanar: “An mallaka mini dukkan iko.” Na biyu kuma ya ba da aiki: “Ku je ku almajirtar.” Na uku kuma ya yi alkawari: “Ina tare da ku har matuƙar zamani.” Ka lura da abin da Yesu bai yi ba? Bai hukunta almajiran domin sun kasa ko domin sun yi shakkarsa ba. (Matiyu 28:17) Abin da ya yi yana da kyau ne? Hakika. Bai daɗe ba, manzannin suka sake soma “koyarwa da yin bishara.” (Ayyukan Manzanni 5:42) Za mu iya samun irin sakamako mai kyau na daɗaɗa rai daga ikilisiyoyinmu ta wurin bin yadda Yesu yake ɗaukan waɗanda suka raunana da kuma yadda yake bi da su.b—Ayyukan Manzanni 20:35.

“Kullum Ina Tare da Ku”

17, 18. Wace ƙarfafa ce ke cikin kalmomin Yesu, “kullum ina tare da ku”?

17 Kalmomin ƙarshe na umurnin Yesu ɗin nan, ‘kullum ina tare da ku,’ abin ƙarfafa ne ga dukan waɗanda suke ƙoƙarin su cika umurnin Kristi na a almajirtar. Ko da wace hamayya magabta suka kawo a kan aikin wa’azin Mulki kuma kowane irin tsegumi suka yi a kanmu ba za mu tsorata ba. Me ya sa? Yesu, Shugabanmu, wanda yake da ‘dukan ikon mallakar sama da ƙasa,’ yana tare da mu ya toƙara mana!

18 Yesu ya yi alkawari ‘kullum ina tare da ku’ abin ƙarfafa ce ƙwarai da ta’aziyya. Yayin da muke ƙoƙarin mu cika umurnin mu almajirtar, muna samun farin ciki a wasu lokatai, wasu lokatai kuma muna baƙin ciki. (2 Tarihi 6:29) Wasunmu muna baƙin cikin wani da muke ƙauna da ya mutu. (Farawa 23:2; Yahaya 11:33–36) Wasu suna fama da tsufa, sa’ad da ƙarfinsu yake raguwa. (Mai Hadishi 12:1–6) Har ila, a wasu lokatai baƙin ciki ya kan sha kan wasu. (1 Tasalonikawa 5:14) Da yawa a tsakaninmu na fama domin tattalin arziki. Duk da waɗannan damuwa, muna nasara a hidimarmu domin Yesu yana tare da mu “kullum,” har lokacin da muke wahala ma.—Matiyu 11:28–30.

19. (a) Menene umurnin aikin da Yesu ya bayar na almajirantarwa ya ƙunsa? (b) Menene ke taimakonmu mu cika umurnin Kristi?

19 Kamar yadda muka gani a wannan talifi da na baya, umurnin Yesu na a almajirtar ya shafi dukan fasaloli. Yesu ya gaya mana dalilin da ya sa ko kuma inda ya kamata mu cika umurninsa. Ya kuma gaya mana abin da za mu koyar kuma har yaushe za mu yi hakan. Hakika, cika wannan aikin ƙalubale ne. Amma domin ikon Kristi da yake goya mana baya da shi kuma yana gefenmu, za mu iya cika aikin! Ka yarda da haka?

[Hasiya]

a Wata majiya ta ce Yesu ya ce, “kuna yi musu baftisma . . . kuna koya musu,” ba a ‘yi musu baftisma kuma a koya musu’ ba. Saboda haka, umurnin a yi baftisma kuma a koyar ba “dole . . . suna biye da juna ba.” Maimakon haka, “koyarwa aba ce da ake ci gaba da yi, ana koyo kafin baftisma . . . kuma a ci gaba da hakan bayan baftisma.”

b Za a iya samun ƙarin zance a yadda ya kamata a ɗauki kuma taimaka wa waɗanda suka raunana cikin Hasumiyar Tsaro fitar 1 ga Fabrairu, 2003, shafofi 23–26.

Yaya Za Ka Amsa?

• Ta yaya muke koya wa mutane su kiyaye umurnin Yesu?

• Waɗanne darussa sabon almajiri zai koya daga wasu mutane cikin ikilisiya?

• Me za mu yi don mu taimaki waɗanda suka raunana a ruhaniya?

• Wane ƙarfi da ta’aziyya muke samu daga alkawarin Yesu “kullum ina tare da ku”?

[Hotuna a shafi na 21]

Muna bukatar zama malamai da kuma masu ja-gora

[Hotuna a shafi na 23]

Sabon almajiri yana koyo da kyau daga misalan wasu

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba