Baftisma Cikin Sunan Wanene Da Kuma Menene?
“Ku tafi fa, ku almajirtar . . . kuna yi masu baftisma zuwa cikin sunan Uba da na Ɗa da na ruhu mai-tsarki.”—MAT. 28:19.
1, 2. (a) Menene ya faru a Urushalima a ranar Fentakos na shekara ta 33 A.Z.? (b) Menene ya motsa mutane da yawa a cikin taron su yi baftisma?
URUSHALIMA tana cike da taron jama’a daga ƙasashe da yawa. A ranar Fentakos na shekara ta 33 A.Z., ana wani idi mai muhimmanci kuma baƙi masu yawa suna wajen idin. Amma wani abin mamaki ya faru, kuma bayan hakan manzo Bitrus ya ba da jawabi mai motsawa da ya shafi mutanen sosai. Kalamansa sun taɓa wasu Yahudawa da shigaggu 3,000, suka tuba kuma aka yi musu baftisma cikin ruwa. Ta hakan, aka daɗa su ga sabuwar ikilisiyar Kirista da aka kafa. (A. M. 2:41) Baftismar da aka yi wa mutane da yawa a cikin tafkunan da ke kewaye da Urushalima ya jawo hayaniya!
2 Menene ya sa mutane da yawa suka yi baftisma? A ranar, “sai wani motsi kamar na hucin iska mai-ƙarfi ya fito sama.” A saman wani bene, aka cika wasu almajiran Yesu guda 120 da ruhu mai tsarki. Bayan haka, maza da mata masu ibada suka taru kuma suka yi mamakin jin waɗannan almajiran suna “zance da waɗansu harsuna.” Da suka saurari abin da Bitrus ya faɗa, har da kalamansa na kai tsaye game da mutuwar Yesu, mutane da yawa “suka soku cikin zuciyarsu.” Menene ya kamata su yi? Bitrus ya amsa: “Ku tuba, a yi wa kowane ɗaya daga cikinku baftisma cikin sunan Yesu Kristi . . . za ku karɓi ruhu mai-tsarki kyauta kuma.”—A. M. 2:1-4, 36-38.
3. A ranar Fentakos, menene aka bukaci Yahudawa da shigaggu da suka tuba su yi?
3 Ka yi tunanin yanayin addini na waɗannan Yahudawa da kuma shigaggu da suka saurari Bitrus. Sun riga sun amince da Jehobah a matsayin Allahnsu. Kuma daga Nassosin Ibrananci, sun san cewa ruhu mai tsarki, ikon da Allah ya yi amfani da shi a lokacin halitta da kuma bayan hakan ne. (Far. 1:2; Alƙa. 14:5, 6; 1 Sam. 10:6; Zab. 33:6) Amma suna bukatan ƙarin wani abu. Yana da muhimmanci su fahimci kuma su amince da hanyar ceto na Allah, wato, Almasihu Yesu. Shi ya sa, Bitrus ya nanata bukatarsu na yin “baftisma cikin sunan Yesu Kristi.” Wasu kwanaki kafin wannan lokacin, Yesu da aka ta da daga matattu ya umurci Bitrus da wasu su yi wa mutane baftisma “zuwa cikin sunan Uba da na Ɗa da na ruhu mai-tsarki.” (Mat. 28:19, 20) Wannan yana da ma’ana sosai a ƙarni na farko, kuma yana da ma’ana har ila. Menene wannan?
Cikin Sunan Uba
4. Ga mutanen da suke dangantaka da Jehobah, wane canji ne aka yi?
4 Kamar yadda aka ambata, waɗanda suka saurari jawabin Bitrus sun bauta wa Jehobah kuma a dā sun ƙulla dangantaka da shi. Suna ƙoƙarin su bi Dokarsa, dalilin da ya sa waɗanda suka zo daga wasu ƙasashe suka zo Urushalima ke nan. (A. M. 2:5-11) Amma, Allah ya canja yadda zai riƙa yin sha’ani da ’yan Adam. Ya ƙi Yahudawa a matsayin al’ummarsa na musamman; yin biyayya ga Dokar ba za ta ƙara zama hanyar samun amincewarsa ba. (Mat. 21:43; Kol. 2:14) Idan waɗannan masu sauraro suna son su ci gaba da yin dangantaka da Jehobah, suna bukatar wani abu dabam.
5, 6. Menene Yahudawa da shigaggu da yawa na ƙarni na farko suka yi domin su yi dangantaka da Allah?
5 Ba za su juya wa Jehobah baya ba, wanda Ya ba su rai. (A. M. 4:24) Waɗanda suka saurari bayanin Bitrus za su fahimci yanzu fiye da dā cewa Jehobah Uba ne mai kula. Ya aiko da Almasihu ya cece su kuma yana shirye ya gafarta wa waɗanda Bitrus ya gaya wa cewa: ‘Bari dukan gidan Isra’ila fa su sakankance, wannan Yesu, wanda kuka tsire shi, Allah ya maishe shi Ubangiji da Kristi.’ Hakika, waɗanda suka yi amfani da kalaman Bitrus yanzu za su samu dalili mai girma na nuna godiya ga abin da Uban ya yi wa dukan waɗanda suke son su ƙulla dangantaka da Allah!—Karanta Ayyukan Manzanni. 2:30-36.
6 Hakika, waɗannan Yahudawa da shigaggu a yanzu sun fahimci cewa dangantaka da Jehobah ta ƙunshi ɗaukansa a matsayin Mai Tanadin ceto ta wajen Yesu. Shi ya sa suka tuba daga zunubansu, har da ƙin Yesu da suka yi da kuma alhakin da suke da shi a matsayin rukuni, wajen saka hannu dumu-dumu ko kuma a kaikaice don kashe Yesu. Kuma hakan ya sa a cikin kwanaki na gaba sun “lizima a cikin koyarwar manzanni.” (A. M. 2:42) Suna so su “guso fa gaba gaɗi zuwa kursiyi na alheri.”—Ibran. 4:16.
7. Yaya mutane da yawa a yau suka canja ra’ayinsu game da Allah kuma aka yi musu baftisma cikin sunan Uba?
7 A yau, mutane miliyoyi daga wurare dabam-dabam sun koyi gaskiya game da Jehobah daga Littafi Mai Tsarki. (Isha. 2:2, 3) Wasu a dā masu musun wanzuwar Allah ne ko kuma waɗanda suka gaskata cewa Allah yana wanzuwa amma ba ya damuwa da halittunsa, amma suka amince da wanzuwar Mahalicci wanda za su iya ƙulla dangantaka mai kyau da shi. Wasu sun bauta wa allah-uku-cikin ɗaya ko kuma gumaka dabam-dabam. Sun koyi cewa Jehobah ne kaɗai Allah maɗaukaki, kuma yanzu suna kiransa da sunansa. Hakan ya yi daidai domin Yesu ya ce almajiransa za su yi baftisma cikin sunan Uba.
8. Menene waɗanda ba su san zunubin Adamu ba suke bukatan su gane game da Uban?
8 Sun kuma koyi cewa sun gāji zunubi daga Adamu. (Rom. 5:12) Wannan sabon abu ne da suke bukatan amincewa da shi. Za a iya kamanta irin waɗannan mutanen da mutum mai cuta da bai san yana da cutar ba. Wataƙila ya ga wasu alamu kamar azaba na wasu lokaci. Duk da haka, idan ba a yi bincike don sanin cutar ba, zai yi tsammanin cewa yana da ƙoshin lafiya. Amma, ba hakan ba. (Gwada da 1 Korantiyawa 4:4.) Idan ya gano ainihin cutar da ke damunsa fa? Zai kasance mai hikima idan ya nemi magani mai kyau kuma mai aiki sosai, ko ba haka ba? Haka nan ma, sa’ad da suka koyi gaskiya game da zunubi da muka gāda, mutane da yawa sun amince da “bincike” na Littafi Mai Tsarki kuma sun fahimci cewa Allah yana “warkarwa.” Hakika, dukan waɗanda suke bare daga Uban suna bukatan su juya ga Wanda zai iya “warkar” da su.—Afis. 4:17-19.
9. Menene Jehobah ya yi don ya sa dangantaka da shi ta yiwu?
9 Idan ka riga ka keɓe kanka ga Jehobah Allah kuma ka zama Kirista da ya yi baftisma, za ka san cewa abin al’ajabi ne ka ƙulla dangantaka da shi. Za ka fahimci cewa Ubanka Jehobah mai ƙauna ne. (Karanta Romawa 5:8.) Ko da yake Adamu da Hauwa’u sun yi masa zunubi, Allah ya yi wani abu domin zuriyarsu, har da mu, muna iya mu kasance da dangantaka mai kyau da shi. Ta yin hakan, Allah ya fuskanci azabar ganin Ɗansa ƙaunatacce ya sha wahala kuma ya mutu. Sanin hakan ya taimaka mana mu yi na’am da ikon Allah kuma mu yi biyayya da umurninsa domin muna ƙaunarsa. Idan ba ka yi hakan ba tukun, kana da dalilai na keɓe kanka ga Allah kuma ka yi baftisma.
Cikin Sunan Ɗa
10, 11. (a) Yaya yawan godiya da kake bukatan ka nuna wa Yesu? (b) Yaya kake ji game da yadda Yesu ya mutu a matsayin fansa?
10 Amma, ka yi tunani kuma game da abin da Bitrus ya gaya wa taron jama’ar. Ya nanata amincewa da Yesu, wanda yake da nasaba kai tsaye da yin baftisma “cikin sunan . . . Ɗa.” Me ya sa hakan yake da muhimmanci a lokacin, kuma me ya sa yake da muhimmanci a yanzu? To, amincewa da Yesu da kuma yin baftisma cikin sunansa yana nufin amincewa da hakkinsa a dangantakarmu da Mahalicci. An rataye Yesu a kan gungumen azaba domin a cire la’ana ta Doka daga Yahudawa; amma, mutuwarsa tana da amfani mai girma. (Gal. 3:13) Ya yi tanadin hadayar fansa da dukan ’yan Adam suke bukata. (Afis. 2:15, 16; Kol. 1:20; 1 Yoh. 2:1, 2) Domin ya cim ma hakan, Yesu ya jimre rashin gaskiya, ƙiyayya, azaba, kuma a ƙarshe mutuwa. Kana godiya don hadayarsa kuwa? A ce, kai ne yaro ɗan shekara 12 da yake tafiya cikin jirjin ruwa na Titanic, jirgin da ya bugi ƙanƙara mai girma kuma ya nitse a shekara ta 1912. Ka yi ƙoƙari ka yi tsalle ka shiga cikin kwalekwalen da ke ceton mutane a lokacin da jirgin ruwa yake son ya nitse a cikin teku, amma ya riga ya cika. Sai wani mutumi a cikin kwalekwalen da ke ceton ya yi wa matarsa sumba, sai ya yi tsalle ya koma cikin jirgin da zai nitse, kuma ya sa ka cikin wannan kwalekwalen ceto. Yaya za ka ji? Babu shakka za ka yi masa godiya! Za ka iya fahimtar yadda wani yaron da ya shaida hakan ya ji.a Duk da haka, Yesu ya yi maka fiye da hakan. Ya mutu don ka samu rai madawwami.
11 Yaya ka ji sa’ad da ka koyi abin da Ɗan Allah ya yi maka? (Karanta 2 Korantiyawa 5:14, 15.) Babu shakka ka yi godiya sosai. Hakan ya motsa ka ka keɓe kanka ga Allah kuma ‘ka daina rayuwa domin kanka, amma ga wanda ya mutu sabili da kai.’ Yin baftisma cikin sunan Ɗa yana nufin amincewa da abin da Yesu ya yi maka da kuma amincewa da ikonsa a matsayin “Sarki da Mai-ceto.” (A. M. 5:31) A dā, ba ka da wata dangantaka da Mahalicci, kuma ba ka da wani bege tabbatacce. Amma ta wajen ba da gaskiya ga jinin da Yesu Kristi ya zubar da kuma yin baftisma, a yanzu ka ƙulla dangantaka da Uba. (Afis. 2:12, 13) Manzo Bulus ya rubuta: “Ku kuma, da kuke dā rababbu ne, magabta ne kuma cikin hankalinku ga wajen munanan ayyukanku, duk da wannan yanzu [Allah] ya sulhunta ku cikin jiki na namansa [Yesu] ta wurin mutuwa, domin shi miƙa ku tsarkaka, marasa-aibi.”—Kol. 1:21, 22.
12, 13. (a) Yaya ya kamata yin baftisma cikin sunan Ɗan ya shafi yadda kake aikatawa idan wani ya yi maka laifi? (b) A matsayin Kirista da aka yi wa baftisma cikin sunan Yesu, wane hakki kake da shi?
12 Ko da yake an yi maka baftisma cikin sunan Ɗa, kana sane sosai da muradinka na yin zunubi. Irin wannan sanin yana taimakawa a kowace rana. Alal misali, idan wani ya yi maka laifi, kana tunawa cewa ku duka masu zunubi ne? Ku biyun kuna bukatan gafarar Allah, kuma ya kamata ku riƙa gafartawa. (Mar. 11:25) Don ya nanata wannan bukatar, Yesu ya ba da wani misali: Ubangijin wani bawa ya yafe masa bashinsa na talanti dubu goma. Daga baya wannan bawan bai yafe wa abokin bautansa da yake bi sule ɗari ba. Yesu ya bayyana wannan darasin: Jehobah ba zai gafarta wa wanda bai gafarta wa ɗan’uwansa ba. (Mat. 18:23-35) Hakika, yin baftisma cikin sunan Ɗan yana nufin amincewa da ikon Yesu da kuma yin ƙoƙarin bin misalinsa da koyarwarsa, har da kasancewa a shirye a gafarta wa wasu.—1 Bit. 2:21; 1 Yoh. 2:6.
13 Tun da yake kai ajizi ne, ba za ka iya yin koyi da Yesu gabaki ɗaya ba. Duk da haka, cikin jituwa da keɓe kanka da zuciya ɗaya ga Allah, ka yi koyi da Yesu iyakar ƙoƙarinka. Hakan ya ƙunshi ci gaba da ƙoƙartawa wajen tuɓe tsohon hali kuma ka yafa sabo. (Karanta Afisawa 4:20-24.) Idan kana daraja wani abokinka, wataƙila za ka yi ƙoƙari ka koya daga misalinsa da kuma halayensa masu kyau. Haka nan ma, za ka koya daga wajen Kristi kuma ka bi misalinsa.
14. Ta yaya za ka nuna cewa ka amince da ikon Yesu a matsayin Sarki na samaniya?
14 Akwai wata hanya kuma da za ka nuna cewa ka fahimci abin da yin baftisma cikin sunan Ɗa ya ƙunsa. Allah “ya sarayar da dukan abu kuma ƙarƙashin sawayensa [Yesu], ya sanya shi kuma shi zama kai a bisa abu duka ga ikilisiya.” (Afis. 1:22) Saboda haka, kana bukatar ka daraja yadda Yesu yake yi wa waɗanda suka keɓe kansu ga Jehobah ja-gora. Kristi yana amfani da ’yan Adam ajizai a cikin ikilisiya, musamman dattawa masu ruhaniya. An naɗa irin waɗannan maza “domin su shiriya tsarkaka . . . domin ginin jikin Kristi.” (Afis. 4:11, 12) Ko da mutum ajizi ya yi kuskure, Yesu a matsayin Sarki na Mulkin samaniya yana iya magance batun a lokacinsa da kuma hanyarsa. Ka gaskata da hakan?
15. Idan ba ka yi baftisma ba tukuna, waɗanne albarkai za ka samu bayan ka yi baftisma?
15 Har ila, wasu ba su keɓe kansu ga Jehobah ba kuma su yi baftisma. Idan ba ka yi hakan ba, daga abin da aka faɗa a baya ka fahimci cewa amincewa da Ɗan yana da kyau kuma zai nuna cewa kana godiya? Yin baftisma cikin sunan Ɗa zai sa ka samu albarka mai yawa.—Karanta Yohanna 10:9-11.
Cikin Sunan Ruhu Mai Tsarki
16, 17. Menene yin baftisma cikin sunan ruhu mai tsarki yake nufi a gare ka?
16 Menene yin baftisma cikin sunan ruhu mai tsarki yake nufi? Kamar yadda aka faɗa ɗazu, waɗanda suka saurari Bitrus a ranar Fentakos sun san cewa akwai ruhu mai tsarki. Hakika, sun ga tabbacin nan da nan cewa Allah ya ci gaba da yin amfani da ruhu mai tsarki. Bitrus yana cikin waɗanda “aka cika . . . da ruhu mai-tsarki, [wanda ya] soma zance da waɗansu harsuna.” (A. M. 2:4, 8) Furcin nan “cikin sunan” ba ya nufin sunan wani mutum. A yau, ana yin abubuwa da yawa “cikin sunan gwamnati,” wadda ba mutum ba ce. Ana yin su ne da ikon gwamnati. Hakazalika, wanda aka yi wa baftisma cikin sunan ruhu mai tsarki ya fahimci cewa ruhu mai tsarki ba mutum ba ne, amma iko ne da Jehobah yake aiki da shi. Kuma irin wannan baftisma tana nufin cewa mutum ya amince da aikin da ruhu mai tsarki yake yi wajen cika nufin Allah.
17 Ka san ruhu mai tsarki ta wajen nazarin Littafi Mai Tsarki. Alal misali, ka fahimci cewa an hure rubuta Nassosi ne ta hanyar ruhu mai tsarki. (2 Tim. 3:16) Yayin da kake samun ci gaba na ruhaniya, ka ƙara samun fahimi cewa ‘Uba na sama za ya ba da ruhu mai-tsarki ga waɗanda su ke roƙonsa,’ har da kai. (Luk 11:13) Wataƙila ka ga cewa ruhu mai tsarki yana aiki a rayuwarka. A wata sassa, idan ba ka yi baftisma cikin sunan ruhu mai tsarki ba, tabbacin da Yesu ya ba da cewa Uba yana ba da ruhu mai tsarki yana nufin cewa za ka samu albarka nan gaba yayin da ka samu wannan ruhun.
18. Wace albarka ce waɗanda aka yi wa baftisma cikin sunan ruhu mai tsarki suke samu?
18 A bayyane yake cewa a yau ma, Jehobah yana yi wa ikilisiyar Kirista ja-gora ta hanyar ruhunsa. Wannan ruhun yana taimaka wa kowannenmu a rayuwarmu ta yau da kullum. Yin baftisma cikin sunan ruhu mai tsarki ya ƙunshi fahimtar hakkinsa a rayuwarmu da kuma ba da haɗin kai ga wannan ruhun. Amma, wasu suna iya yin mamaki, yaya za mu yi rayuwa da ta jitu da keɓe kai da muka yi ga Jehobah da kuma yadda hakan ya shafi ruhu mai tsarki. Za mu bincika wannan a gaba.
[Hasiya]
a Ka duba Awake! na 22 ga Oktoba, 1981, shafuffuka na 3-8.
Ka Tuna?
• Menene yin baftisma cikin sunan Uba ya ƙunshi a gare ka?
• Menene yake nufi a yi baftisma cikin sunan Ɗa?
• Yaya za ka nuna cewa ka fahimci ma’anar yin baftisma cikin sunan Uba da kuma Ɗa?
• Menene yin baftisma cikin sunan ruhu mai tsarki yake nufi?
[Hotuna da ke shafi na 10]
Wace dangantaka ce sababbin almajirai suka ƙulla da Uba bayan Fentakos na shekara ta 33 A.Z.?
[Inda Aka Ɗauko]
Da izinin ma’adanar kayayyakin tarihi na Isra’ila, Urushalima