Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 8/1 pp. 9-14
  • Kiristoci Suna Bauta Cikin Ruhu Da Gaskiya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kiristoci Suna Bauta Cikin Ruhu Da Gaskiya
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Za a Iya Samun Gaskiya
  • Ta Yaya Za Mu Koyi Gaskiya
  • Gaskiya da Kuma Ɗan Allah
  • Gaskiya da Imani
  • Gaskiya Game da Kurwa
  • Gaskiya da Kuma Allah Uku Cikin Ɗaya
  • Gaskiya da Kuma Baftisma
  • Yin Koyi Da Allah Na Gaskiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Har Yanzu Gaskiya Tana da Muhimmanci Kuwa?
    Karin Batutuwa
  • Zan “Yi Tafiya Cikin” Gaskiyarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Ku Ci Gaba da “Bin Gaskiya”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 8/1 pp. 9-14

Kiristoci Suna Bauta Cikin Ruhu Da Gaskiya

“Allah ruhu ne; waɗanda su ke yi masa sujjada kuma, sai su yi sujjada cikin ruhu da cikin gaskiya.”—YOHANNA 4:24.

1. Wane irin bauta ke faranta wa Allah rai?

MAKAƊAICI Ɗan Jehovah, Yesu Kristi, ya nuna sarai bauta da ke faranta wa Ubansa na samaniya rai. Da yake wa’azi mai daɗaɗa rai ga wata Basamariya a rijiya kusa da birnin Sukar, Yesu ya ce: “Ku kuna yin sujjada ga abin da ba ku sani ba; mu muna yin sujjada ga abin da mun sani; gama ceto daga wurin Yahudawa ne. Amma sa’a tana zuwa, har ma ta yi yanzu, inda masu-yin sujjada da gaskiya za su yi ma Uba sujjada a cikin Ruhu da cikin gaskiya kuma; gama irin waɗannan Uban ya ke nema, su zama masu-yi masa sujjada. Allah ruhu ne; waɗanda su ke yi masa sujjada kuma, sai su yi sujjada cikin ruhu da cikin gaskiya kuma.” (Yohanna 4:22-24) Yaya za mu fahimci waɗannan kalmomin?

2. A kan menene Samariyawa suka kafa bautarsu?

2 Samariyawa suna da ra’ayin ƙarya na addini. Sun amince da littattafan Nassosi biyar na farko ne kawai hurarru—kuma waɗannan cikin nasu fassara ne kaɗai, da aka kira Littattafai Biyar na Samariyawa. Ko da yake Samariyawan ba su san Allah ba sosai, Yahudawa an danka musu sani na Nassi. (Romawa 3:1, 2) Ya sa ya yiwu Yahudawa masu aminci da wasu su more tagomashin Jehovah. Amma me wannan zai kasance a gare su?

3. Me ake bukata don a yi wa Allah sujjada “cikin ruhu da cikin gaskiya”?

3 Don su faranta wa Jehovah rai, menene Yahudawa, Samariyawa, da wasu mutanen dā dole su yi? Dole ne su bauta masa cikin “ruhu da cikin gaskiya.” Hakan dole ne mu ma mu yi. Ko da yake bauta wa Allah dole ta zama cikin ruhu, ko da himma, mai fitowa daga zuciya da ke cike da ƙauna da bangaskiya, yi wa Allah sujjada cikin ruhu musamman na bukatar mu kasance da ruhunsa mai tsarki kuma muna bari ya yi mana ja-gora. Ta nazari da amfani da Kalmar Allah, hankalinmu zai jitu da nasa. (1 Korinthiyawa 2:8-12) Don Jehovah ya amince da sujjadarmu, dole a yi ta cikin gaskiya. Dole ta jitu da abin da Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki, ya bayyana game da Allah da nufe-nufensa.

Za a Iya Samun Gaskiya

4. Ta yaya wasu suke ɗaukan gaskiya?

4 Wasu ɗaliban falsafa sun gina ra’ayin cewa mutane ba za su iya samun cikakkiyar gaskiya ba. Hakika, wani mawallafi daga Sweden Alf Ahlberg ya rubuta: “Tambayoyi da yawa na falsafa irin wannan ne cewa ba zai yiwu ba a ba da amsa ga wannan tambayoyi na falsafa.” Amma wasu sun ce akwai ɗan gaskiya, haka ne? Yesu Kristi bai yi tunani haka ba.

5. Me ya sa Yesu ya zo duniya?

5 Bari mu yi tunani cewa muna cikin masu kallon abin da aka kwatanta a gaba: A farkon shekara ta 33 A.Z. ne, Yesu yana tsaye a gaban Gwamnar Roma Bilatus Babunti. Yesu ya gaya wa Bilatus: “Domin wannan kuma na zo cikin duniya, domin in bada shaida ga gaskiya.” Bilatus ya yi tambaya: “Menene gaskiya?” Amma bai jira amsar Yesu ba.—Yohanna 18:36-38.

6. (a) Ta yaya aka ba da ma’anar “gaskiya”? (b) Wane umurni Yesu ya ba mabiyansa?

6 An ba da ma’anar “gaskiya” cewa “tarin abubuwa takamammu ne, aukuwa, da kuma lazu.” (Webster’s Ninth New Collegiate Dictionary) Amma, Yesu ya ba da shaida game da gaskiya ne galibi? A’a. Yana da wata gaskiya a zuciya. Ya ba mabiyansa umurni su sanar da irin wannan gaskiya, ya gaya musu: “Ku almajirtadda dukan al’ummai, kuna yi musu baftisma zuwa cikin sunan Uba da na Ɗa da na Ruhu Mai-tsarki: kuna koya musu su kiyaye dukan iyakar abin da na umurce ku.” (Matta 28:19, 20) Kafin ƙarshen wannan zamanin mabiyan Yesu na gaskiya za su sanar da “gaskiyar bishara” a dukan duniya. (Matta 24:3; Galatiyawa 2:14) Za a yi wannan wajen cika kalmomin Yesu: “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’annan matuƙa za ta zo.” (Matta 24:14) Saboda haka, yana da muhimmanci mu gane waɗanda suke koya wa dukan al’ummai gaskiya ta wa’azin bishara na Mulki.

Ta Yaya Za Mu Koyi Gaskiya

7. Yaya za ka nuna cewa Jehovah ne Tushen gaskiya?

7 Jehovah ne Tushen gaskiya ta ruhaniya. Hakika, mai Zabura Dauda ya kira Jehovah “Allah na gaskiya.” (Zabura 31:5; 43:3) Yesu ya fahimci cewa maganar Ubansa gaskiya ce, ya kuma sanar: “A cikin Annabawa an rubuta, Dukansu kuwa Allah za ya koya musu. Dukan wanda ya ji daga wurin Uban, har ya koyo kuma, ya kan zo wurina.” (Yohanna 6:45; 17:17; Ishaya 54:13) A bayyane yake, waɗanda suke neman gaskiya dole ne Jehovah ya koya musu, Mai Koyarwa Mai Girma. (Ishaya 30:20, 21) Masu neman gaskiya suna bukatar su samu “sanin Allah.” (Misalai 2:5) Kuma Jehovah cikin ƙauna ya koyar ko kuma idar da gaskiyar a hanyoyi dabam dabam.

8. A waɗanne hanyoyi ne Allah ya koyar ko idar da gaskiyar?

8 Alal misali, ta wurin mala’iku ne Allah ya bayar da Dokar ga Isra’ilawa. (Galatiyawa 3:19) Cikin mafarki, ya yi wa ubanni Ibrahim da Yakubu alkawari. (Farawa 15:12-16; 28:10-19) Allah ya yi magana daga sama, lokacin da Yesu ya yi baftisma kuma an ji waɗannan kalmomi masu ban mamaki a duniya: “Wannan Ɗana ne, ƙaunatacena, wanda raina ya ji daɗinsa sarai.” (Matta 3:17) Za mu yi godiya kuma cewa Allah ya koyar da gaskiya ta wurin hure marubutan Littafi Mai Tsarki. (2 Timothawus 3:16, 17) Ta wajen koyo daga Kalmar Allah, za mu “bada gaskiya ga gaskiya.”—2 Tassalunikawa 2:13.

Gaskiya da Kuma Ɗan Allah

9. Ta yaya Allah ya yi amfani da Ɗansa ya bayyana gaskiya?

9 Musamman Allah ya yi amfani da Ɗansa, Yesu Kristi, ya bayyana gaskiya ga mutane. (Ibraniyawa 1:1-3) Hakika, Yesu ya faɗi gaskiyar yadda babu wani mutumin da ya taɓa faɗa. (Yohanna 7:46) Har bayan da ya haura zuwa sama, ya bayyana gaskiya daga wurin Ubansa. Alal misali, manzo Yohanna ya samu “ru’ya ta Yesu Kristi, wadda Allah ya ba shi domin shi bayyana ma bayinsa, al’amura ke nan da za su faru ba da jinkiri ba.”—Ru’ya ta Yohanna 1:1-3.

10, 11. (a) Gaskiya da Yesu ya yi wa’azinta na da nasaba da menene? (b) Ta yaya Yesu ya sa gaskiyar ta bayyana a zahiri?

10 Yesu ya gaya wa Bilatus Babunti cewa ya zo duniya don ya ba da shaida ga gaskiya. Lokacin hidimarsa, Yesu ya bayyana cewa wannan gaskiya tana da nasaba da kunita ikon mallaka na Jehovah ta wurin Mulkin Allah da Kristi ne Sarki. Amma cika hidimar Yesu a ba da shaida ga gaskiyar ya ƙunshi fiye da wa’azi da koyarwa. Yesu ya sa wannan gaskiya ta bayyana a zahiri ta wajen cika ta. Saboda haka, manzo Bulus ya rubuta: “Kada kowanne mutum fa ya zarge ku a kan zancen ci, ko sha, ko zancen idi ko tsayawar wata ko ran asabar: su dai inuwar al’amuran da ke zuwa ne; amma aini na Kristi ne.”—Kolossiyawa 2:16, 17.

11 Hanya ɗaya da gaskiyar ta bayyana a zahiri ita ce ta haihuwar Yesu a Bai’talahmi da aka annabta. (Mikah 5:2; Luka 2:4-11) Gaskiyar ta kuma bayyana a zahiri a cikar kalmomin annabci na Daniel game da bayyanuwar Almasihu a ƙarshen ‘makonni na shekaru’ 69. Wannan ya faru sa’ad da Yesu ya ba da kansa ga Allah a baftisma kuma aka shafa shi da ruhu mai tsarki, a daidai lokacin da aka annabta, a shekara ta 29 A.Z. (Daniel 9:25; Luka 3:1, 21, 22) Gaskiyar ta ƙara bayyana a zahiri cikin hidimar Yesu mai wayarwa da yake shi mai shelar Mulki ne. (Ishaya 9:1, 2, 6, 7; 61:1, 2; Matta 4:13-17; Luka 4:18-21) Ta kuma kasance zahiri ta mutuwarsa da tashinsa daga matattu.—Zabura 16:8-11; Ishaya 53:5, 8, 11, 12; Matta 20:28; Yohanna 1:29; Ayukan Manzanni 2:25-31.

12. Me ya sa Yesu ya iya cewa “ni ne gaskiya”?

12 Tun da gaskiya game da Yesu Kristi ne, ya ce: “Ni ne hanya, Ni ne gaskiya, Ni ne rai: ba mai-zuwa wurin Uban sai ta wurina.” (Yohanna 14:6) Mutane sun sami ’yanci na zahiri domin sun tsaya a gefen “gaskiya” ta amince da matsayin Yesu cikin ƙudurin Allah. (Yohanna 8:32-36; 18:37) Domin masu kama da tumaki suna karɓan gaskiya kuma sun bi Kristi cikin bangaskiya, za su samu rai madawwami.—Yohanna 10:24-28.

13. Za mu bincika gaskiya ta Nassi a waɗanne fannoni uku?

13 Gaskiya da Yesu da almajiransa da aka hure suka koyar ne tsarin imani na Kiristanci na gaskiya. Waɗanda “suka yi biyayya ga imanin” ta haka “suna tafiya cikin gaskiya.” (Ayukan Manzanni 6:7; 3 Yohanna 3, 4) To, su wa suke tafiya cikin gaskiya a yau? Su wa da gaske suke koya wa dukan al’ummai gaskiya? Wajen amsa waɗannan tambayoyi, za mu mai da hankali a kan Kiristoci na farko kuma za mu bincika gaskiya ta Nassi game da (1) imani, (2) hanyar da suke sujjada, da kuma (3) halayensu.

Gaskiya da Imani

14, 15. Menene za ka ce game da halin Kiristoci na farko da Shaidun Jehovah game da Nassosi?

14 Kiristoci na farko sun ɗaukaka rubutacciyar Kalmar Jehovah sosai. (Yohanna 17:17) Mizanansu ne game da imani da ayyuka. Clement na Alexandria na ƙarni na biyu da na uku ya ce: “Su da suke kokawa don hali na musamman ba za su daina neman gaskiya ba, har sai sun samu tabbaci na abin da suka gaskata daga Nassosi.”

15 Kamar Kiristoci na farko, Shaidun Jehovah suna daraja Littafi Mai Tsarki sosai. Sun gaskata cewa “Kowane nassi hurare daga wurin Allah mai-amfani ne ga koyarwa.” (2 Timothawus 3:16) Bari mu bincika wasu imani na Kiristoci na farko da yin la’akari da abin da bayin Jehovah na zamani suka koya domin sun yi amfani da Littafi Mai Tsarki ya zama littafinsu na musamman.

Gaskiya Game da Kurwa

16. Mecece gaskiya game da kurwa?

16 Domin sun gaskata abin da aka ce a Nassosi, Kiristoci na farko sun koyar da gaskiya game da kurwa. Sun san cewa “mutum kuma ya zama rayayyen [kurwa]” lokacin da Allah ya halicce shi. (Farawa 2:7) Ƙari ga haka, sun gaskata cewa kurwa ta ’yan Adam na mutuwa. (Ezekiel 18:4, NW; Yaƙub 5:20) Sun kuma san cewa “matattu ba su san komi ba.”—Mai-Wa’azi 9:5, 10.

17. Ta yaya za ka yi bayanin begen matattu?

17 Duk da haka, almajiran Yesu na farko suna da tabbataccen bege cewa matattu suna cikin tunanin Allah kuma zai tashe su, ko a maido su zuwa rai. Bulus ya bayyana wannan imani sarai, ya ce: “Ina da bege ga Allah . . . za a yi tashin matattu, na masu-adalci da na marasa-adalci.” (Ayukan Manzanni 24:15) Daga baya ma, wanda yake da’awar shi Kirista ne Minucius Felix ya rubuta: “Wanene wawa ko kuma mara tunani da zai ce mutum da Allah ne dama ya yi, ba zai iya sake yinsa ba?” Kamar Kiristoci na farko, Shaidun Jehovah sun manne wa gaskiya ta Nassi game da kurwa ta mutum, mutuwa, da tashin matattu. Bari yanzu mu bincika game da Allah da Kristi.

Gaskiya da Kuma Allah Uku Cikin Ɗaya

18, 19. Me ya sa za a ce koyarwar Allah-Uku-Cikin-Ɗaya ba ta Nassi ba ce?

18 Kiristoci na farko ba su ɗauki Allah, Kristi, da ruhu mai tsarki cewa Allah uku ne cikin ɗaya ba. The Encyclopædia Britannica ya ce: “Furcin nan Allah uku cikin ɗaya ko kuma koyarwar ba ta bayyana cikin Sabon Alkawari ba, kuma Yesu da mabiyansa ba su yi niyyar saɓa wa Shema [addu’ar Ibrananci] cikin Tsohon Alkawari ba: ‘Ku ji ya Isra’ila: Ubangiji Allahnmu Ubangiji ɗaya ne’ (Kubawar Shari’a 6:4).” Kiristoci ba sa bauta wa allah uku cikin ɗaya na Roma ko kuma wasu alloli. Sun amince da maganar Yesu cewa Jehovah ne kaɗai za a yi wa sujjada. (Matta 4:10) Amma, suna gaskata da kalmomin Kristi: “Uba ya fi ni girma.” (Yohanna 14:28) Shaidun Jehovah suna da irin wannan ra’ayin a yau.

19 Mabiyan Yesu na farko sun nuna bambanci tsakanin Allah, Kristi, da kuma ruhu mai tsarki. Hakika, sun yi wa almajirai baftisma (1) cikin sunan Uban, (2) cikin sunan Ɗan, da kuma (3) cikin sunan ruhu mai tsarki, ba cikin sunan Allah-Uku-Cikin-Ɗaya ba. Hakanan ma Shaidun Jehovah suna koyar da gaskiya ta Nassi suna nuna bambanci tsakanin Allah, Ɗansa, da kuma ruhu mai tsarki.—Matta 28:19.

Gaskiya da Kuma Baftisma

20. Menene waɗanda suke son su yi baftisma suke bukatar su sani?

20 Yesu ya ba mabiyansa umurni su yi almajirai ta koyar da mutane gaskiyar. Don su cancanta don baftisma, suna bukatar su sami sani na Nassosi. Alal misali, dole su amince da matsayi da ikon Uban da Ɗansa, Yesu Kristi. (Yohanna 3:16) Waɗanda suke so su yi baftisma suna bukatar su fahimci cewa ruhu mai tsarki ba mutum ba ne amma iko ne da Allah yake aiki da shi.—Ayukan Manzanni 2:1-4.

21, 22. Me ya sa za ka ce baftisma don masu bi ne?

21 Kiristoci na farko, suna yin baftisma kaɗai wa mutane waɗanda suka tuba suka keɓe kansu babu ragi ga Allah don su yi nufinsa ne. Yahudawa da kuma shigaggu da suka taru a Urushalima a Fentakos na shekara ta 33 A.Z., sun riga sun sami sani na Nassosi na Ibrananci. Da jin manzo Bitrus ya yi magana game da Yesu Almasihu, wajen mutane 3,000 “suka karɓi maganarsa” kuma “aka yi musu baftisma.”—Ayukan Manzanni 2:41; 3:19–4:4; 10:34-38.

22 Baftisma na Kirista don masu bi ne. Mutane a Samariya sun karɓi gaskiya, kuma “sa’anda suka gaskata Filibbus, yana bisharar zancen mulkin Allah da sunan Yesu Kristi kuma, aka yi musu baftisma, maza da mata.” (Ayukan Manzanni 8:12) Da yake shi shigagge mai ibada ne da ya sani game da Jehovah, Bābā Bahabashe da farko ya yarda da maganar Filibbus game da cikar annabcin Almasihu kuma ya yi baftisma. (Ayukan Manzanni 8:34-36) Daga baya, Bitrus ya gaya wa Karniliyus da wasu mutanen Al’umma cewa “wanda ya ke tsoron [Allah], yana aika adalci kuma, abin karɓa ne gareshi” kuma duk wanda ya ba da gaskiya ga Yesu Kristi zai samu gafara na zunubai. (Ayukan Manzanni 10:35, 43; 11:18) Duka wannan ya yi daidai da umurnin Yesu na ‘mu yi almajirai, muna koya musu su kiyaye dukan abin da ya umurta.’ (Matta 28:19, 20; Ayukan Manzanni 1:8) Shaidun Jehovah suna bin irin waɗannan mizanai, suna yin baftisma kaɗai wa waɗanda suke da ilimin Nassosi kuma da suka keɓe kansu ga Allah.

23, 24. Wace hanya ce ta dace a yi baftisma ta Kirista?

23 Nitsarwa gabaki ɗaya cikin ruwa ita ce hanyar baftisma da ta dace don masu bi. Bayan aka yi wa Yesu baftisma cikin Kogin Urdun, sai ya ‘fito daga cikin ruwa.’ (Markus 1:10) An yi wa Bābā Bahabashe baftisma cikin “ruwa.” Shi da Filibbus “suka shiga ruwa” sai suka “fito daga cikin ruwa.” (Ayukan Manzanni 8:36-40) Nassosi sun nuna cewa baftisma ta nasabci binnewa kuma sun nuna cewa nitsarwa ce gabaki ɗaya a cikin ruwa.—Romawa 6:4-6; Kolossiyawa 2:12.

24 The Oxford Companion to the Bible ya ce: “Kwatancin baftisma na ainihi na Sabon Alkawari ya nuna cewa mutum da ake wa baftisma ana tsoma shi cikin ruwa.” In ji majiya ta Faransa Larousse du XXe Siècle (Paris, 1928), “Kiristoci na farko suna yin baftisma ta nitsarwa a duk inda aka samu ruwa.” Littafin nan After Jesus—The Triumph of Christianity ya lura: “A yawancin, [baftisma] na bukatar wanda yake son ya yi baftisma ya ba da gaskiya, sai a nitsar da shi gabaki ɗaya cikin ruwa cikin sunan Yesu.”

25. Menene za a tattauna a talifi na gaba?

25 Abubuwa da aka ambata a baya game da imani da ayyuka na Kiristoci na farko da ke bisa Littafi Mai Tsarki misalai ne kawai. Zai yiwu a ambata wasu abubuwa da suka yi daidai cikin imaninsu da na Shaidun Jehovah. A talifi na gaba za mu tattauna ƙarin hanyoyi na gano waɗanda suke koya wa mutane gaskiya.

Yaya Za Ka Amsa?

• Wane irin sujjada Allah yake bukata?

• Ta yaya gaskiya ta bayyana a zahiri ta wurin Yesu Kristi?

• Mecece gaskiya game da kurwa da mutuwa?

• Ta yaya ake yin baftisma ta Kirista, kuma menene ake bukata daga waɗanda suke so su yi baftisma?

[Hoto a shafi na 10]

Yesu ya gaya wa Bilatus: ‘Na zo in ba da shaida ga gaskiya’

[Hoto a shafi na 11]

Za ka iya bayyana abin da ya sa Yesu ya ce: ‘Ni ne gaskiya’?

[Hoto a shafi na 12]

Mecece gaskiya game da baftisma ta Kirista?

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba